Showing 3001 words to 6000 words out of 98809 words

Chapter 2 - TAZARA COMPLETE by UMMU-ABDOUL & KHADIJA SIDI.txt

ta kasa gano mutum ɗaya a dangin ta da zai tsaya mata in zancen zai kai ga hukuma.
Tunawa da artabun da aka sha kafin Baban Sasa ya amince da karatunta kaɗai ya sanya ta cikin tashin hankali. Daɗin ƙarawa rikicin nata ba da mace ƴar uwarta ba da namiji, tilawar da ta haddace shine "babu ke babu ɗa namiji, mijinki saifullahi na dawowa daga Rasha zan ɗaura aure ku" karatu ne da duk ta je gaida baban Sasa sai ya biya mata, yanzu kuma sai a ce gata an kore ta daga jamia saboda ta yi faɗa da namiji.
"Me ya kai ni fitan karatun dare" tace hawaye na zubo mata sannu a hankali, hakan ya sa yin kuka ma'ishi sannan ta fara tuna asalinta don gaba ɗaya ta sadakar koranta za ayi




***


28th September 1989


Gidan Jamoh babban gida ne a unguwar Amaru cikin birnin Zaria. Gida ne ginin ƙasa wanda ke da sassa daban daban. Sun kasance cikin kason zage-zagi da aka fi sani da mallawa, wainda tarihi ya nuna suna cikin jinsin Zazzagawa uku da ke da gadon sarautan ƙasar Zazzau watau Mallawa, Katsinawa da Barebari.
Babba da yaro da ga tsatson gidan Jamoh na da kwale bibbiyu a duka gefen fuskarsu kamar kowane Bamalle.
Sanyin iskar damuna ke kaɗawa ƙarfe tara na safiyar Alhamis na ashirin da takwas ga watan Satumba shekara alif ɗari tara da tamanin da tara, Hakan bai hana tsoho Jamoh zama akan kujerarsa ta azara da yake shan hantsi duk safiyar duniya yana mai sauraren radiyo a ƙasar bishiyar da ya yalwata Inuwa a tsakiyar gidan.
"Baban Sasa! Baban Sasa!!" yaro ɗan kimanin shekaru takwas ya sheƙo da gudu yana faɗi.
"Ja'iri! Sai kace ni ubanka ne, karar min da sunan za ka yi" tsohon ya faɗi cikin sigar wasa. Dariya Yaron yayi yana mai zama akan cinyarsa.
"Innarmu ce tace in zo in faɗi maka Goggo Mairo ta sauka an samu yarinya" yace cikin murna yana yi yana wasa da gemun tsohon nan.
"Madallah ka ce mun yi mata, dena ja min gemu salon ta ce kai take so ba ni ba" ya karasa yana mai ɗaga Yaron sama ba za ka ce yana da karfin ɗaukan Yaron nan ba in ka kalli furfuran da ya rufe masa fuska. Sashin ɗansa ƙarami a maza ya je don ganin abin da aka haifa, saboda ya san ƙaidar sa ce duk aka haihu da an kimtsa shine mutum na farko da yake fara gani, Hakan aka yi a haihuwa talatin da uku da yaransa maza su ka masa ciki kuwa har na yau.
Addu'a yayi mata haɗe da huɗuba tare da raɗa mata suna kamar yadda yake yi a saura, in yayi ba ya faɗi ma kowa sai babban Ɗansa Zubairu.
Alhaji Jamoh Bamalle ne Usul, sannan shine cikakken ma'anar maraya, don yana da shekara ɗaya da rabi mahaifiyarsa ta rasu, bai cika shekaru biyu ba Allah ya ma mahaifinsa rasuwa.
Ya taso cikin gararanba a tsakar gidan babban gidansu, cikin ikon Allah lokacin da aka zo aka bukaci masarauta su ba da sunayen wainda za su je karatun boko wani kawunsa da ke aiki a fada ya bada sunansa.
Hakan ya sanya yayi karatu har ya kammala makarantar Barewa College wanda a lokacin sunansa Kaduna college kafin daga baya ya zama Govt college Zaria kafin daga baya ya koma Barewa college.
Tun bayan da ya kammala da shahadar grade II ya samu koyarwa a firamare bai sake komawa aji ba, da albashin sa ya auri matansa uku, da albashin sa ya raini yayansa goma sha shida inda ciki biyar ne mata saura duk maza ne, da Albashin sa ya mallaki filin nan har ya gine in da ya zama musu babban gida a yanzu a nan yaran sa duka goma sha ɗaya ke zaune da iyalinsu.
Hajiya Sahura itace uwar gida, yaranta takwas, Zubairu shine babba, sai Idris, sai Hamza, sai Hadiza, Madina, Bilkisu, Yusuf sai autanta Salihu.
Hajiya Talatu ce mata ta biyu a gidan ita yaranta shida duka maza, Anas, Dahiru, Yunusa, shuaibu, Mahmuda sai ƙaraminsu Muhammadu.
Amarya da yaran ke kira da Goggo Kadarko tun da ta haifi yan biyu Hasana da Husaina Allah ya mata cikawa, haka hajiya Talatu ta haɗa da nata yaran ta rike.
Daga Salihu sai yan biyu a tsarin shekarun yaran gidan Hakan ya sanya su ka taso su uku kamar yan uku, yana da shekara goma sha biyar su yan biyu na da sha uku aka tashi auren yan biyu, yayi kuka kamar ransa zai fita saboda shaƙuwa da ke tsakanin su, tun bayan aurensu ya maida hankali a karatun bokonsa don yana ganin shi kaɗai ne zai ɗebe masa kewa.
Yayi karatu har matakin digiri a Fannin sadarwa sannan ya samu aiki da radiyo Nijeriya Kaduna kafin yayi aure.
Aurensa na cikin auren da aka yi shelarsa a jihar Kaduna saboda duk maabota sauraron radiyo sun san Salihu Jamoh da shirye shiryensa masu ƙayatarwa musamman shirin jakar magori.
***
Aurensa da mairo ya samar da karin arziki ta wajen sa don bayan auren ya samu ƙarin girma a wajen aiki, sannan gidan an samu yalwan arziki sannan ita kanta kullum cikin yi ma mutane ihsani take da kaɗan din da ta mallaka. Hakan ya sanya surukan son mairo fiye da sauran matan yayan.
Tun ana ƙirga watannin auren har aka fara ƙirga shekaru Mairo ko ɓatan wata ba ta yi ba, nan matan yan uwa Salihu su ka sa mata karan tsana, amma duk sanda su ka jefeta da sharri sai ta maida musu da Alkhairi. Yayin da Allah ya azurta ta da cikin sai su ka fara zunɗenta suna fadin ƙaba ke damunta. Hakan bai sa ta canza musu ba ko ta neme su da sharri kullum dai Alkhairi, babu inda ta ke jin sanyi sai wajen matar Anas mai suna Hama, ita ce ta tsaya mata har ta sauka lafiya sannan ta aika ɗanta Saifullahi ya je ya isar ma kakansa Jamoh albishir ɗin haihuwa.
***
Ranar suna aka sanar da sunan jaririya a Amatullah, an yanka rago an ci abinci a wadace an sha kowa yana cikin farin ciki.
Rayuwar Amatullah ta kasance cikin gata, haihuwarta ta buɗe ma iyayenta samu yaya don duk bayan shekara biyu sai Goggo mairo ta haihu.
Amatullah na da shekara uku ta fara bin yayyinta na gidan zuwa makarantar Allo, tun ba ta fahimta har ta fara ɗaukan karatu.
Ko da ta kai shekaru shida aka sanya ta a makarantar islamiyyah kamar sauran yayyinta, gaba ɗaya rayuwarta sai ta zama daga sallan asuba za ta je Allo, ana tashin su karfe bakwai da kwata, nan za su dawo su karya sannan su tafi makarantar boko, su taso karfe ɗaya su ci abincin rana su huta ƙarfe hudu su tafi islamiyyah sai kuma shida, bayan sallan isha'i kuma su yi karatu da dare in da yayyinsu ke musu bitar karatun islamiyyah da Allo.
Amatullah hazikace mai saurin fahimtar karatu sannan ba ta da mantuwa Hakan ya sanya da wuya a yi jarrabawa ba ta zo na ɗaya zuwa na uku ba. Da wannan kokarin ta kammala firamare ta shiga sakandire na boko da islamiyyah.
Tana da shekara goma sha hudu aka aurar da sa'oi'inta da ke gidan bayan sun kammala hadda izu arba'in, da kyar Baba Jamoh ya amince da cigaban karatun Amatullah Shima bisa Yarjejeniyar ba ta da miji sai Saifullahi a cewar sa tun kafin ta kama nonon uwarta ya ma Saifullahi alkawarin auren Amatullah.


***


Da taimakon fitar Saifullahi karatu ƙasar waje ya sanya Amatullah kammala karatun sakandire, samun kyakkyawar sakamako ya sanya mahaifinta rokon Baba Jamoh akan barinta zuwa jami'a, da kyar ya amince bisa sharaɗin ko bayan ba shi aka aura Amatullah ga wanin Saifullahi bai yafe ba.
Wannan alkawarin Salihu Jamoh yayi shi a gaban dukkan yayyinsa da ita kanta Amatullah da mahaifiyarta.
"Ni dai in karanta pharmacy shi ne damuwata, ko wa Baban Sasa ya so ya aura min" tace a ranta tana murnar amincewar kakanta tsoho mai ran ƙarfe mai ikon akan Ahlinsa.
Bisa wannan Alkawari ta fara karatun Pharmaceutical science a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, nisa da rashin son zarya ya sanya mahaifinta tura ta hostel cike da yaƙinin za ta kama kanta kuma za ta zo da sakamako mai nagarta.


Wannan kenan.[1/8, 11:26 PM] Safiyya Ummu-Abdoul Writer: *previous post da ɗan kuskure*


FIKRA WRITERS ASSOCIATION


TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀


✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL




BABI NA UKU

A bakin gate ta iske abokan tafiyarta, nan su ka mata caa kowa da abin da yake tambayarta.
"Cewa yayi yana sonki hala" shine tambayar da ya fi tsaya mata, Zulaikha dai bata ce komi ba don ta san ita ɗin mai laifi ce.
"Haka kawai sai ya ce yana so na? A wajen photocopy fa muka haɗu kwanaki banda canji ya bada Naira 20 din ni shaf na manta ma" ta samu kanta da zabga ƙarya don bata son wani abu ya fito na abin da ke tsakanin ta da Dee.
"Har na fara murna, don wallahi ko ni da nake matar aure ina kyasa Dee Yusuf, in fa ya ce yana sonki mu ɗin gaba ɗayanmu za mu shiga wani sawu na masu aji ne" Faɗin Zuwaira da su ke kira da maman Jaafar. Ajinsu ɗaya, a shekarun za ta girme su amma kuma ƙawarsu ce, yanzu ma kasuwar da za su shiga ita za su raka siyayya.
Ba ta ce komi ba amma ita da ta san alkawarin da ke kanta ta san hakan ba mai yiwuwa bane ko da a ce shi ɗin kimtsattse ne ba tambaɗaɗɗe kamar yanda ta ke kallonsa ba.
Da hirar Dee Yusuf su ka isa kasuwa, ita dai jin su take yi don ba su isa kasuwa ba har sai da kawayen ta su ka hasko kalan yaran da za su haifa in aurenta da Dee Yusuf ya tabbata.
Daga kasuwa gidajensu su ka wuce suna fatan Allah ya Raya su zuwa sati biyu da karatun zango na biyu zai kankama. Sai a lokacin Amatullah ta samu ta keɓe da Zulaikha saboda su biyun hanyarsu ɗaya.
"In kashe ni za a yi ma kawai a kashe ko? ke babu abin da yayi tsalle ya tsinka miki mari" Amatullah ta ce tana hararar Zulaikha.
"Afuwan bibty, kin san na yi tunanin in na tsaya saura ma za su tsaya kuma ba zamu iya daƙile zancen ba, me ya ce miki?" ta ƙarasa tana mai neman karin bayani akan abin da ya wakana tsakanin kawarta da dodonta.
"Me kuwa zai ce min, da na gaji da tsayuwa ba tare da ya ce komi ba na yi wucewata na bar shi tsaye" Amatullah ta samu kanta da yin ƙarya a karo na biyu.
'wai me ye kike ɓoyewa ne' ta samu zuciyar ta da faɗi.
'ai sirri da daɗi' ɗayan sashi na zuciyar ta ke bada wannan amsar.
"Toh Allah shiga tsakanin nagari da mugu" ta tsinkayi zulaikha da faɗin haka. "Aameen" tace tana canza labarin su zuwa ga batun jarrabawar da su ka yi a ranar.
***
Sai da la'asar ta shiga gidan su, nan ta iske yan uwa da iyayensu kowa yai mata murnar kammala jarrabawa da fatan samun nasara.
"Baba mun dawo, ya karfin jikinka" tace yayin da ta shiga ɗakin baban Sasa, Shima addu'a ya bi ta da shi sannan ya ce da ita
"Ina so na shaida aurenku Baiwar Allah! Na ce a kira min Saifu, don ba zan so ƙasa ya rufe ido na ban cika ba, tun da har Allah ya bani tsawon ran kaiwa lokacin da duk kuka isa aure" jin sa take yi yayin da idanunta ke kallon laɓɓansa yana faɗa mata su, sai a lokacin ta ga tsantsan kamanninta da shi, sai a lokacin ta ke yarda da zancen da ake na suna kama da Saifullah don tun tana yarinya ta haddace babu mai kama da Baban Sasa sama da Saifullah.
"kin yi shiru Amatu" yace yana taɓo ta.
"Baaba, ashe haka nake kama da kai" tace tana dariya ƙasa ƙasa, shi ma sai ya shiga dariya.
"kin ga kenan duk wanda ya shiga gidanku zai tuna da ni ya min addu'a" ya ce cikin dariya. Haka su ka dinga tsokanar juna cikin nishadi, kiran sallan magariba ne ya tayar da ita bayan ta sa masa ruwan alwala a buta.
***
Yana zaune a harabar sashin su a jami'ar kimiyya na gwamnatin ƙasar Rasha da ke birnin Moscow watau MATI Russian State Technological University Moscow, tattaunawa su ke yi da abokan karatunsa akan sabuwar injimin da su ke kerawa don wani baje koli da jami'ar ke shirin aiwatarwa nan da kwana biyar, a nan wayarsa ta ɗauki ƙara. Kamar ba zai ɗauka ba amma jin kiɗan da ya tanadar ma jininsa ne ya sa shi saurin ɗauka, tsoronsa kar a ce Baban Sasa ne ya rasu, don shi ya san son da yake ma tsohon nan ko iyayen sa albarka.
"excuse me" ya ce yana mai zuwa gefe tare da tattara duk wani natsuwa da ya mallaka ya doka sallama bayan ya ɗaga.
"Saifuna ba zaka dawo in ganka ba" yace cikin halin ciwo.
"Alkawari Baba ba zan ƙara sati biyu ba, kai dai kar ka yarda ka bi su ko sun zo ɗaukan ka" yace cikin shaƙiyanci hakan ya sanya baban Sasa tuntsirewa da dariya. Ya tambaye shi jikin sa, da sauran ahlin nan ya amsa yana mai ƙara jin jinjina masa zancen zuwansa. A haka su ka yi sallama, ya koma wajen abokan karatunsa yana mai ba su hakuri.
Kwana goma ya ƙara akan ranar da su ka yi waya jirgi ya sauke shi a filin jirgin sama na murtala Muhammad da ke birnin ikko ƙarfe goma sha biyu da rabi na dare.
Kallo ɗaya za ka masa ka san bakin fata ne duk da rinewar da fatarsa ta yi ya rikiɗe kamar wani bakin bature. Shi ɗin ba wani dogo bane sannan babu mai kiransa gajere, zanensa na mallawa na kwance a gefen fuskarsa hakan na ɗaya daga cikin abin da ke ƙara maida fuskarsa abin kauna ga mata kamar yadda wata budurwar sa ta faɗa masa.
Daga ikko jirgin da ke tashi zuwa Kaduna ƙarfe shida na safiyar washegari ya bi, daga nan ya ɗauki shatar mota har Amaru.
Babu zato su ka tsinkayi muryarsa yana sallama, nan gida ya kacame da murna, duk ihun da ake Amatullah na zaune a ɗaki bata ko motsa ba cike take da fargaba da tsoro, cigaba da karatun ta tayi a cikin littafin Nurturing Eeman in children na Dr Aisha Hamdan. Wannan shine ɗabi'ar da ta fi so in ba ta komi toh ta samu littafin ƙaruwa na addini ta dinga karantawa.
***
Tun da ya shigo gidan idon sa ke kan yan matan da yake gani yana kasa kunnen wacce za a kira da Amatullah, dukkansu babu na yarwa saboda wasun su na da gaɓa-gaɓan jiki wasu kuma yan firit amma duk kyawawa ne daidai misali.
Bai manta hotonta da ya gani ƙarshe shekarun goma da suka wuce ba, ko a lokacin ya san ita din mai kyauce da abokansa za su yaba da ita. Bare kuma yanzu da aka ce ta shiga Jami'a, ya san zai same ta da wayewa, dan shi a rayuwar sa ya na san wayayyiyar mace.
Sunaye mabambamta ya ke ji ana kira duk babu Amatullah har dai ya hakura tare da sa ran ko tana makaranta ne.
Washegari Zulaikha ta kawo mata ziyara tare da duba jikin Baban Sasa, sun fito za ta raka ta ne su ka ci karo da shi a ƙofar gida. Sun gaisa cikin mutunci su ka wuce yana mamakin yanda duk in da ya gilma cikin zaria mata sanye da zumbura zumburan hijabi, su wainnan ma abin takaici har da safa ko me su ke rufewa oho 'watakila kutare ne' ya samu zuciyar sa da fadin haka. Tsaki yayi ya cigaba da abin da yake a kan wayarsa, a haka ta dawo, ta sanya kafa ɗaya kenan a cikin gidan kenan ta jiyo muryar yar gidan goggonsu ta bayanta tana fadin
"A'ah su Amatullah yan boko ne a garin" Hakan ya sanya ta juyowa cikin fara'a tace
"A'ah su matan aure ne a garin" nan su ka sa dariya, Hakan ya zama sarar su duk suka haɗu sai su yi amfani da kasancewarsu abokan wasanta su gasa mata magana akan rashin aure da boko. Shi ke nan da sun kira ta yar boko sai ta kira su matan aure.


Gaida Saifullahi tayi ya amsa kamar ya haɗe su ya maƙure, bakin cikin da ya saukar masa ba ƙarami bane don kwata-kwata bai sa ma ransa ko a mafarki aure zai haɗa shi da bagidajiya ba.
"Kai impossible!!!" ya faɗi Yana mai mikewa zuwa cikin gida don dai ya tabbatar wannan mai lullube jiki kamar raguwar kuturta ce matar da yake hasko su tare.
Yaro ya gani a yana wasa a tsakar gida daidai inda yake wajen zaman baban Sasa, tuno murnar da yake ciki lokacin da ya faɗi albishir din haihuwan yarinyar da aka ƙaƙaba masa da ada murna yake amma a yau gani yake babu bakin fata sama da haka.
"kai shiga ka kira min Amatullah" yace ma Yaron cikin tsawa-tsawa, a firgice Yaron yayi cikin gida yana mai kiranta.
Sai da ta ɓata kusan minti talatin kafin ta fito wanda hakan yayi nasaran ƙara harzuka shi.
Sanye take cikin hijabi ruwan bunsuru ko ganin atamfar da ke karkashi ba ayi, baƙar safa ce a kafafunta hannayenta duk suna cikin hijabi Hakan ya sanya babu abin da ya bayyana a gareshi face fuskarta.
"Assalamu Alaikum" tace cikin sanyin murya, kallon ta yake, fuskar nan nata sai sheƙi yake yi saboda rashin hoda, amma hakan bai hana kyawunta fitowa ba.
"ina yini" ta ƙara duk da kunnuwanta ba su ji ya amsa sallamar da tayi ba. Nan ma bai amsa ba, sai ta basar ta tsaya abin ta. Kallonta yake tun daga kai har ƙafa yana jin wani kyankyaminta na cika shi.
"Kinga, this will be the first and the last time da magana zai haɗamu, you better find your self a husband, amma ba Saif ba!, ki sani cewa akwai Tazara a tsakanin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login