Showing 66001 words to 69000 words out of 98809 words
Chapter 23 - TAZARA COMPLETE by UMMU-ABDOUL & KHADIJA SIDI.txt
kafin yanke hukunci! Ga wannan yarinya ta zo mana da batun rashin lafiyar Amatullah, ya na da kyau a saurare ta"
"Shin yaushe mu ka fara sauraran magana daga bakin bare?"
Cewar Baban Sasa ya na mai kallan Mimi a wulakance. Haka ma Saifullahi wani mugun harara ya jefi Mimi da shi, cikin jandadin furucin Baban Sasa ya yi saurin fadin
"Yo to wannan ai bakin su daya ma, ai dai ku na gani tare da arnen ta zo, da ita su ke bugewa suna aikata masha'an su"
"Aw ku na nufin ya zo har gidan nan!"
Cewar Baban Sasa cike da nuna bacin rai.
Ita kuwa Mimi da ran ta ya fara baci ganin yanda su ke kyamar su kiri kiri, ba tare da jiran izini ba ta fara jawabi kamar haka
"Sunana Hanna Dauda, resiting 300lvl da Amatullah ke yi ya sa na zama kawarta don na dade da saninta a matsayin mai ƙoƙari.
Handout, abinci, duk Amatullah bata san su ba, duk rana duk sanyi a motar haya take zuwa duk da ɗanyen jego......."
"Dakata yarinya, wannan wani irin zancen banza ki ke faɗa mana! Ita Amatullah din ce ta fada mi ki haka? Kai Saifullahi ina gaskiyar maganar nan"
Baban Sasa ne ya katse Mimi, in da duka dakin kallon Saifullahi da ya fara zufa har ta kan hanci su ke. Ya na mai girgiza kai ya shiga karyata Mimi, faɗi ya ke
"Karya ta ke! Wallahi karya ta ke min babu abin da ban ɗaukewa Amatullah ba!"
Mahaifin Amatullah wanda idanun sa suka cika da kwalla ne ya furta, ke mu ke sauraro yarinya. Mimi ta nisa sannan ta cigaba kamar haka
"Tun last week na lura da tana wari kaɗan kaɗan duk da kasancewarta mai tsafta, Amma na kasa faɗa mata, sai ɗazu da kan ta tazo min da maganar, cewar dinkin da aka mata tun na haihuwa ya nan ya zame mata ciwo, shi ne ya ke fitar da ɗan wari......"
"Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun"
Cewar Mahaifin Amatullah. Baban Sasa ya kara da
"Amatullah mai tsafta ce ta ke da ciwo a jiki har ya na fitar da wari? Saifullahi ka na da masaniya akan haka?"
Saifullahi na mai share zufa da bayan hannun sa, shirun da yayi ya tabbatarwa ya san da wannan lalurar. Hakan ya bawa Mimi damar cigaba da faɗin
"ko da mu ka je asibiti, likita ta duba Amatullah ta mana bayanin cewa ta na cikin tsaka mai wuya, muddin ba a yi mata aikin gaggawa ba, Baba a duba wayar Saifullah Amatullah ta kira shi, kusan sau biyar ta kira shi tun kan a shiga da ita tiyata, bai daga ba, da aka fito da ita na sake kiran shi, be daga ba, shi ne na tura ma sa sakon text......"
"Wa ki ka kira? Wa ku ka kira? Wa ki ka turawa sakon text? Ga dai waya ta nan tun safe ta ke hannuna! Kuma in banda sharri da wata wayar Amatullah zata kira ni ita da wayar ta ta lalace kusan wata ɗaya ta wuce?"
Saifullahi ne ya katse ta cikin rashin sukuni, dan kuwa dai idanun sa sun fara raina fata.
Maimakon ta bashi amsa, sai ta budi na ta wayar ta ce
"Malam Saifullahi halan wanna number din ta ka ce 080********"
"Kwarai kuwa numbarsa ce kuwa"
Baba Anas ya amsa mata, shi kuwa Saifullahi wani gumi ne ya shiga keto masa dan jin ta karanto numbar shi na karamin waya, Dan kuwa dai wannan wayar ta shi a silent ta ke tun shigar sa masallaci da ya saka ya manta bai cire ba.
"Ba ni wayoyin ka Saifullahi!"
Baba Anas ya faɗa cikin umarni. Jiki sanyaye Ya mika ma sa wayoyin.
"Wanne daga ciki numbar da ta kira yanzun nan ta ke?"
Yayi nuni ga ɗan karamar wayan cikin ran sa ya na adduar Allah ya sa ba wuka ya dabawa kan sa ba. Baba Anas na dubawa sai ga missed calls ba adadi, ya umarci Mimi ta karanto numbar ta, ta karanto. Nan maganar Mimi ya tabbata, missed calls dai gasu nan reras, haka zalika sakon da ta turawa Saifullahi, wanda shi kan shi bai san da shi ba.
Baban Sasa kallon Saifullahi kawai ya ke. Mahaifin Amatullah ne ya ce da Mimi
"Yarinya dan Allah karasa jawabin ki ko ma san halin da yarinyar nan ta ke ciki"
Mimi na mai gyada kai ta cigaba da magana kamar haka
" Wallahi ban san cousin ɗina ya san Amatullah ba, kiran sa kawai nayi ya zo ya cece mu don Bill dinmu 15, 000 wanda an mata aikin ne don emergency mu ka je. Baba lokacin da Amatullah ta ga Dee wallahi ba ta da wani zaɓi da ya wuce ta biyo mu don ni na san da lafiyar ta lau ba za ta ko kalle shi ba, haka mu ka kai ta gida, Nan kofar gidan mu ka ga Saifullahi in da ya shiga aibantata tare da faɗi mata kalamin zargi tare da shegenta ɗan sa na cikin sa"
Mimi ta karasa maganar ba tare da furta sakin da Saifullahi yayiwa Amatullah ba, tsabagen nauyin da kalmar ta yi mata.
Zufa ne ya rufe Saifullahi, shi kuwa Baban Sasa hawaye ne ke fita daga idanun sa wiwi, Mahaifin Amatullah kuwa wani sanyi ne ya ratsa zuciyar sa an wanke diyar sa akan zargin da mijin ta ya ke mata.
"Allah ya isa, Saifullahi Allah ya isa tsakanina da kai, ka zalinci Amatullah, ka haince ni, da ka fada min ba ka san yarinyar nan da ba mu cuce ta mun aurar da ita ga kai ba!"
Cewar Baban Sasa hannu bisa kirjin sa da ke harbawa tsabagen ciwo da ya ke ma sa.
"Saifullahi za ka gama da duniya lafiya kuwa?"
Cewar Baba Anas. Baba Zubairu na mai girgiza kai ya
"Ah ah kar ku masa baki, kuskure ne da aikin shedan......"
"Akwai shedanin da ya wuce shi kan shi Saifullahi? Ya azabtar da ƴa, ya kuma saka mata da zargi, kazafi fa? Allah ya wadar na ka ya lalace, na dai faɗa ma ka yanda ka kuntata mata haka zan kuntatawa ita uwar ta ka mai zuga ka!"
Nan fa gaban Saifullahi ya fadi, dan kuwa dai ya saki Amatullah, gashi Baba Anas na maganar ramuwar gayya. Cike da nadamar abin da ya aikata, dan kuwa be taba tunanin abin zai juye ma sa haka ba
"A yi hakuri Baba, wallahilazim na rantse da Allah ban san ta je asibiti ba, ban ga kiran su da sakon wayar na su ba, wayar tawa a shiru ta ke "
Cewar Saifullahi ya na mai share zufa.
"Ba ka san tana asibiti ba? Ba ka san ta na da ciwo ba har ya kai da fitar da wari? Saifullahi ai ko babu dangantaka na aure ai Amatullah kanwar ce Saifullahi"
Cewar Mahaifin Amatullah cikin nuna rashin jin dadi, in da su Baba Zubairu su ka shiga tofa albarkacin bakin su. Cikin jin daɗin yanda ta wanke Amatullah, ya na duban Mimi ya ce
"Yarinya ba mu san da wani baki za mu gode mu ku ba, ba mu san yanda za mu gode mu ku ba"
Cikin jin dadi da gamsuwa Mimi ta bashi amsa da
"Ba sai kun gode min ba ai yiwa kai ne, ni dai fata na a duba lamarin Amatullah, Allah kaɗai ya san halin da ta ke ciki...."
"Bari na koma gidan yanzu!"
Saifullahi ya katse Mimi yayin da ya tashi zumbul ya na kokarin sanya takalmi.
"Ka koma wani gida? Mahmuda je ka dauko min yarinyar nan kafin ya je ya karasa mana ita, nan za ka zauna har sai an kawo ta babu in da za ka!"
Cewar Baba Anas. Saifullahi da ya so komawa gida domin ya san yanda zai yi ya shawo kan Amatullah, dole ya dawo ya zauna. Nan Mimi ta musu sallama zuciyar ta cike da annushawa. Ganin Mahaifin Amatullah ya rakota har kofar gida ya tabbatarwa Dee haƙan su ya cimma ruwa, ko shakka babu Mimi ta wanke Amatullah, wani farin ciki ne ya mamaye zuciyar sa, wanda har sai da Mimi ta gane yayin da su ka hau hanya.
Ta na mai jinjina kai ganin yanda Dee ke murmushi, baki har kunne ta ce
" By the way ka ke murmushi na san ka gane mun yi nasara, but ina bin ka bashin bayani ka sani ko?"
Cike da jin dadi ya figi motar yayinda su ka hau bisa kwalta ya na mai maimaita
"Na sani Mama na, na sani Mama na!"
Ita ma din murmushin ta ke cike da annushawa.
****
Amatullah kuwa kamar yanda Baba Anas ya ce, Baba Mahmuda ne ya je gidan, ya tadda ta zaune dai in da su Mimi su ka bar ta. Ganin shi ta san Saifullahi ya je ya faɗa mu su ita mazinaciya ce, dan haka ko da ya ce ya zo ne su tafi, ba ta tambaye shi dalili ba, tashi ta yi tana tafiya da kyar. Ba karamin tausaya mata yayi ba, ya na mai mamakin rashin imani irin na Saifullahi, yana dana sanin kiyayyar da ya ke mata ita da mahaifiyar ta, a sanyaye ya ɗaukar mata Emjay, da sannu a hankali, ya na mata sannu har su ka isa motar, ya bude mata gidan baya ta zauna. Sai da ya bata Emjay sannan ya karbi mukullin gidan ya rufe ba su zame ko ina ba sai gidan Baban Sasa.
Ganin Amatullah babu wanda bai tausaya mata ba, hatta Saifullahi sai shigowar ta ya lura da yanayin tafiyar ta, wani kunya da nauyin iyayen su ne ya rufe shi, ina ma zai iya mayar da hannun agogo baya, da bai aikiata abin da ya aikata ba.
"Sannu, sannu Amatullah"
Kalaman da ta ke ji daga bakin iyayen ta kenan wanda shi ya ba ta ɗan kwanciyar hankali, ko babu komai sun san ba ta da lafiya. Kan katifa kusa da shi Baban Sasa ya umarci Amatullah ta zauna. Burin ta kar ta hada idanu da Mahaifin ta, bayan kazafin da Saifullahi ya mata, kuma ta tabbatar ya faɗa mu su ba ta san da wani ido za ta iya kallan sa ba.
"Sannu Amatullah"
Cewar Saifullahi wanda ke kallan Amatullah idanun sa cike da magiyar neman rufin asiri. Amatullah kuwa ko kallan sa ba ta yi ba bare ta san ya na wajan. Maimakon ta ji tsinuwa da la'antar da ta ke tsammani, sai ji ta yi Baban Sasa ya ce
"Amatullah ashe haka mu ka cutar da ke ba mu sani ba? Mu ka aurar da ke ga mara kaunar ki? Amatullah za ki iya yafe mana kuwa?"
Cike da mamaki ta daga iduna ta dubi Baban Sasa, wanda kallo ɗaya za ka masa ka tabbatar da tashin hankalin da ya ke ciki, cikin awa biyu kacal ya kara tsufa, numfashi na neman harde ma sa. Sai a sannan ta iya kallon mahaifin na ta, wanda idanun sa ke cike da kwalla. Kan ta ta sunkuyar, dan kuwa dai ba ta da ta cewa, ta faru ta kare an yiwa mai dami daya sata.
Baban Sasa bai gushe ba ya cigaba da faɗin
"Nan gidan za ki zauna har ki gama jinya, ba dan saki babu kyau ba da na umarci ja'irin nan ya sake ki a yau Amatullah..."
Cike da mamaki Amatullah ta ɗago kai ta na mai duban Saifullahi wanda ya shiga girgiza mata kai, alamar ta yi shiru. Cikin taikaci ta ce
"Baban Sasa ana yin wani saki ne bayan saki ukun da Allah ya halatta ma da namiji? In dai kuwa ba a yi ina mai tabbatar muku Saifullahi ya sake ni, ya sake ni saki uku!"
"Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun"
Cewar dukkan wanda ke cikin ɗakin har da uwa uba Saifullahi, in da wani ni'ima da farin ciki ya saukarwa mahaifin Amatullah, ya na mai hamadala cikin ransa. Saifullahi kuwa na shi salatin ba na komai ba ne sai na tsoran masifar da kalaman Amatullah za ta haifa masa. Hannu bisa kirji sai ga Baban Sasa na zubda hawaye, fadi ya ke
"Saifullahi ka shayar da ni bakin ciki, bakin cikin da tun da na zo duniya babu wanda ya shayar da ni kwatankwacin shi, Saifullahi ka cuceni ka cuci zumunci!"
"Ah ah Amatullah kada ki min haka, kar da ki sanya tazara a tsakanin mu ba zan iya jurewa ba! na yi kuskuran furta saki gare ki, Amma ban fadi iya adadin sakin ba, har ga Allah saki daya na mi ki ba uku ba, Allah ya ga zuciya ta! Dan Allah Baba ku duba lamarin nan"
[4/5, 5:49 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼♂🤦🏿♀
✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL
BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS
Hawaye bai daina zuba daga idanun Baban Sasa ba yayin da ya ke duban Saifullahi, cikin dashassheyiyar murya ya furta
"Saifullahi har ka iya buɗar baki ka furta saki ga Amatullah? Ashe za ka iya sakin Amatullah?"
"Kukan nan na ka shi ke ɗaga mana hankali Baba, dan Allah ka sawa zuciyar ka salama ɗan yau ba a biye masa, sai ya kara ma ka ciwo"
Cewar Baba Zubairu cikin rarrashi.
"Ni kuwa na ke iya masa! Kai waye nan! Hafiz! Hafiz! ya ka nan!"
Baba Anas ne ya shiga kwallawa Hafiz Kira, in da ya shigo da saurin sa dama nan soro yayi laɓe ya na jin komai.
"Je ka kira min uwar yaron nan!"
Ya fada ya na mai nuna Saifullahi da ɗan yatsa. Gaban Saifullahi ne yayi mummunar faɗuwa ganin Hafiz ya fita da sauri, cikin sanyin murya ya ce
"Dan Allah Baba...."
"Dakata! Ba na so na sake jin ka tanka a nan idan har ba ni na ba ka izini ba!"
Jin haka Saifullahi ya sunkyar da kai. Amatullah kuwa burin ta a sallame ta shiga gida ta mike kafa ko ta sami saukin zugin da ciwon da ya ke mata.
Jim kaɗan sai ga Hajiya ta shigo da da sallamar ta. Gani yanda aka taru daki, fuskar Baban Sasa fal da hawaye, kuma ciki har da Saifullahi da Amatullah ta sha jinin jikin ta. Bai bari ta iya gaisar da Baban Anas na mai duban Saifullahi ya ce
"Zan ma ka tambaya ɗaya, kuma ka bani amsa cikakkiya, saki nawa ka yiwa yarinyar nan?"
Daf gaban Hajiya ya yanke ya fadi, ta na mai dafe kirji ta furta
"Saki?"
Saifullahi na mai sin da kai ya ce
"Saki daya na mata Ba.....!"
"Wallahi saki uku ya min......!"
Amatullah ta yi saurin katse shi. Kallan ta ya ke kallon da ta kasa gane manufar shi. Kai ta kawar gefe cikin halin ko in kula.
"Ina ga zai fi a bar shi a sakin ɗaya tun da shi yaro ɗaya ya ce yayi, kuma shi ne gaba da ita"
Baba Mahmuda ya ara ya yafa ba tare da ya san dalilin da ta sa Baba Anas ya ke tambaya ne. Baba Anas na mai gyaran murya ya ce
"Toh sai fa ku shaida, bisa ga alkawarin da na dauka, ni Anas na saki mata ta.......!"
"Inna lillaahi wa inna ilaihi ilaihi rajiun!"
Duka dakin su ka hau salati, wanda haka bai hana shi karasawa ba sai da ya dire da
"Saki daya kamar yanda Saifullahi ya ce ya saki Amatullah saki daya!"
"Inna lillaahi wa inna ilaihi rajiun"
Amatullah ce ke na ta salatin akan abu biyu, na farko sakin Hajiya, na biyu kuwa Jin Baba Anas ya yarda saki ɗaya Saifullahi ya mata ba uku ba.
Kukan Hajiya ne ya garwaye ɗaki, in da idanun Saifullahi su ka kada su ka yi jajur.
"Haba mana Anas! Ya za ka biyewa ɗan yau ka yi wannan danyen aika aika! Ya mu na so mu toshe wani ramin za ka bude wani?!!!!"
Cewar Baba Zubairu cikin faɗa faɗa.
Baba Salihu mahaifin Amatullah kuwa cewa yayi
"Assha! Assha! Assha! Malam Anas ba ka kyauta ba! Saki kuma? Ana zaune shekara da shekaru? Yanzu yaran nan za su sa ka furta saki hakan nan bakatatatan!"
"Ban yi dana sani ba! Wallahi da ya amsa ukun ya mata a yau sai na sau tashi uwar saki uku!"
Cewar Baba Anas in da maganar ta shi ta soki Hajiya da har lokacin kuka ta ke, da Saifullahi wanda zuciyar shi ke masa Kuna. Baba Sasa wanda kiris ya rage ya hadiyi zuciya dan takaici ya ce
"Anas ashe har yanzu akwai sauran ka a rayuwa! Ka dubi tsabar ido na! A gaba na ka furtawa mai dakin ka kalmar saki?"
Cike da ladabi Baba Anas ya sunkyar da kai ba tare da ya tankaba.
"Toh ina mai ba ka umarni ka mayar da ita ɗakin ta yanzun nan!"
Baba Anas na mai dukar da kai, har ran sa ba haka ya so ba ya ce
"Na mayar da ita Baba, na mayar da ita, Allah ya huci zuciyar ka"
Cikin dakiya da umarni Baban Sasa ya dubi Saifullahi ya ce
"Kai ma tun da saki daya ka mata, ina so ka mayar da ita a take kuma ......"
Kukan da Amatullah ta saki ne ya dakatar da Baban Sasa, cikin kunar zuciya jin za a mayar da ita gidan Saifullahi ta ce
"Ka duba girman Allah Baban Sasa na tuba, ka yafe min, tun da na ke ban taba ma ka musu ba, wallahi babu aure tsakani na da ya Saifullahi, wallahi saki uku ya min....."
Nan ta mayar da kallan ta zuwa ga Baban ta, ba ta gushe ba ta cigaba da fad'in
"Baba ko ba uku ya min ba, ai aure ya haramta tsakanin mu! Ai ba a zaman aure da zargi! Wallahi cewa yayi ba ɗan shi ba ne,! Ya kira ni mazinaciya! Na rantse da Allan da ya halicce ni ban taba kusantar zina ba bare na kai ga aikatawa! Tun ina budurwa ballanta sanda igiyar aure ke kaina! Da ku mayar da ni gidan Saifullahi gwara kun kai ni kushewata....!"
Cike da mamakin kiyayyar da ta ke masa Saifullahi ke kallon ta. Shi kuwa Baban Sasa mamakin yau Amatullah ce ke masa musu haka ya ke yi. In da nauyi da taikaicin Saifullahi ya kara mamaye Baba Anas. Mahaifin Amatullah ne ya runtse idanu ya ce
"Yi shiru Amatullah, babu wanda zai kai ki kushewar ki, auren Saifullahi ne daga yau kin gama shi da izinin Allah, na san Baba zai mi ki adalci"
Baban Sasa wanda kalaman Baba Salihu na karshe ne su ka ɗaure shi da jijiyoyin sa, duk da kuwa ya ga baƙin Baba Salihu, cikin danne bacin rai ya ce
"Tashi ki shiga ciki, zuwa gobe za mu yanke hukunci"
Da kyar ta ita tashi, in da