Showing 96001 words to 98809 words out of 98809 words

Chapter 33 - TAZARA COMPLETE by UMMU-ABDOUL & KHADIJA SIDI.txt

da aka saka ranar bikin Amatullah ta dawo gida, gun Mama ta sauka in da Mama ta shiga tsuma ta tana mata gyara na musamman kai ka ce wannan aure shi ne na fari.


Ana saura sati biyu aka kawo lefe, ita kan ta Aysuh hadiyar zuciya ne kawai ba ta yi ba tsabagen yawa da haɗuwan kayan lefan Amatullah, dan kuwa rabin sa Saifullahi bai yi mata ba. Ganin lefen ya sa ta ji ta na so ta ga Dee ta kuma san shin dan gidan wanene haka?


Saifullahi kuwa bai tabbatar da tazaran da ke tsakanin sa da Amatullah ba sai randa akan idanun sa Baba Anas ya karbi sadakin Amatullah daga hannun wakili Dee Yusuf. Kuka yake wiwi ba tare da ya damu da jama'ar da ke gurin ba, tsabagen takaici ranar sai da ya fara tunanin anya kuwa Baba Anas mahaifin sa ne?


Shi kuwa ango sanye cikin farar shadda ya sha dinkin babban riga da aka yi mata aiki da farar zare, da ka gan shi ka ga angon zamani. Nan gaban gidan ya tsaya tare da abokan sa ya kira Mimi ya ce ta fito masa da amaryar sa ba zai iya tafiya ba idan har bai gan ta ba.


Amatullah da ta sha ado cikin farin leshi, ta yi kyau matuka har sheki ta ke. Jin umarnin Dee ta fara girgizawa Mimi kai, ita kuwa ta ce


"Toh ango yanzu za mu fito"


Ta na aje wayar ta ɗauko farar lafaya ta ce da Amatullah


"Oya we no go do hijab today, maza tashi ki naɗa mu fita Dee na jiran mu"


"Ni gaskiya ba zani ko ina ba!"


"Wallahi sai kin je!"


Nan musu ya kaure har sai da su Mama suka sa baki, Mama ce da kanta ta nada mata lafaya, hannun ta cikin na Mimi su ka nufo kofar gida, ashe Dee ya shigo daga zaure, ya na ganin su ya karasa gaban Amatullah, ya janyo ta jikin sa ya rungume ta tare da faɗin


"you're mine Amatullah, you're my halal!"


Mimi ta saka guɗa yayin da Amatullah ta ke kokarin zillewa daga jikin Dee cike da kunya. Yana dariya ya sake ta tare da fadin


"Lalle akwai rigima Mama nah, dole fa ki saba zama jiki na"


Cike da kunya Amatullah ta ce


"Ayya mana!"


Duka dariya su ke mata, yayin da su ka fito waje hannun ta cikin na ango, duk yanda ta so ta kwace ya hana ta. Saifullahi da ya ke waje tuni ya shige mota ya bar wajen ganin yanda Dee ke nan nan da Amatullah, ana ta daukan hoto tare da yan uwa da abokan arziki.


A daren ranar aka kai Amatullah gidan Dee ke zangon shanu gidan ya tsaru ainun irin wannan ginin zamanin ne da ake kira aljannan duniya. Da Ƴan uwan Dee da aka kai amarya da su sun nuna karbuwar Amatullah gare su, musammam yanda su ke jin labarin ta gurin Dee da Mimi.


Sai bayan da kowa ya watse Dee ya shigo gidan shi kaɗai dauke da ledar sa na kaza da yourgot. Ganin har lokacin Amatullah ba ta daina kuka na shi ya sa ya zauna ya rarrashe kayan sa, dan ya tabbatar har da kuka rashin Emjay ta ke.


Sai da ta yi shiru sannan ya sa ta dauro alwala su ka yi sallah. Kan ta ya dafa yayi mata addua tare da tambayar hukunce hukunce na game da wanka, da kuma abin da ya danganci sallah, ba dan ya fita sani ba kamar yanda ya ce mata, sai dan su kara karuwa da juna. Ita kanta ta yi mamakin yanda Dee ke bin kaidojin musulunci tamkar dama ciki aka haife shi.


Yanda ya ga Amatullah ta na dan rabe rabe ya gane sam ba ta sake da shi ba, cikin dabara ya jawo ta falo, nan ya sata gaba sai ta ci abinci. Haka nan ta ɗan tsattsakura, cikin sauri ta tashi ta ce bari ta je ta kwanta. Maimakon ta shiga ɗakin sa, sai ta wuce na ta ɗakin . Bin ta yayi da kallo ya na mai murmushi a zahiri kuma cewa yayi


"Amatullah ni mai hakuri ne, balle yanzu da babu wani tazara a tsakanin mu?"


Ya gyara zama ya na mai ƙara yiwa Allah godiya da hasken da ya bashi, lallai musulunci haske ne a rayuwar sa, haka zalika Amatullah haske ce a rayuwar sa, wannan shi ne haske kan haske.


Amatullah kuwa ko da ta je ɗakin ta, wanka ta yi, ta sanya kayan baccin ta tabi lafiyar gado. Amma sai ta nemi bacci a idanun ta ta rasa duk da kuwa ta kashe wutar dakin. Kusan minti ashirin ta yi kwance ta juya nan ta juya nan. Jin alamar an buɗe kofar ta an shigo tuni gaban ta ya shiga faduwa. Ba ta gasgata shigowa Dee yayi ba sai da ta ji ya kwanta bayan ta ya na mai janyo ta jikin sa. Ta yi kokarin kwacewa ya ce


"Shhhhhhhhh tsaya mana Mama nah, babu abinda zan mi ki"


Yanda ya yayi maganar tare da kwantar da kan sa jikin ta ya sanya ta daina kokarin kwacewa. Cikin jin dadi Dee ya ce


"That's my Girl"


Amatullah ta saki sansayyar ajiyar zuciya duk da har lokacin ba ta saki jikin ta ba.


"Amatullah?"


Amatullah ta amsa da "um"
Dee ya ce


"You know I love you ko?"
Amatullah ta amsa da "um"


"Owk, ina so ki saki jikin ji, just relax and sleep owk?"


Jin haka ta ce "um"


Amma cikin ranta cewa ta yi
"Relax a ina bayan ka kamkame ni haka!"
A zahiri kuma sai ta ɗan saki jikin ta, Dee na mai faɗa mata kalaman soyayya har bacci ya sace ta.




🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹


Ayyiriri!!!


Ga biki zuwa maza nemo zanin ɗaurawa


Kun taɓa jin labarin Diamond package?
Idan ba ku da labari ku zo ku ji da ɗumiɗuminsa.


Ba komi bane face DANGARTAKARMU mai cike da SARƘAƘIYA wanda ke haddasa AUREN SHEHU.


Package ne da Ummu-Abdoul, Aisha Yau Kura da Khadija Sidi suka haɗa don Ilmantar da mai karatu gami da Nishaɗantarwa.


Tikitin Karanta littafan nan guda uku Naira dubu ɗaya ne kacal, za a fara siyar da Tikitin daga yau za a rufe siyarwa 24th ga watan shawwal..


Biki ne na wance da wance, ku hanzarta nemo kuɗin zanen ɗaurawa don kar a bar ku a baya.


Biya 1000
0069724232
Abubakar Safiyyah Jibril
Sterling Bank


Sai ki tura shaidan biya ta whatsapp ga
07010137848..


Ku zo mu haɗe mu gwangwaje.
[4/24, 12:29 AM] Zuraiyah Zuzu 🌟: TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀
✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL


BABI NA TALATIN DA BAKWAI


In da Dee da Amatullah su ka yi kwanan farin ciki, Saifullahi da Ayush a nasu ɓangaran kwanan tashin hankali su ka yi, Dan kuwa Saifullahi ranar kamar wanda aka yiwa mutuwa, wani bakin kishin yau Amatullah za ta kwana da wani ba shi ba ne ya addabi rayuwar sa.
Matar shi da ta gane yanayin da ya ke ciki ba ta saurara masa ba, ba ta yi la'akari da jama'ar biki da ke gidan ba haka ta ringa neman sa da tashin hankali ta na mai daga murya. Sai barin ɓangaren sa yayi, ya koma falon Baban Sasa, nan ya sha kukan sa ya koshi kamar yaro dan goye. Yanda ya ga dare haka ya ga rana.


****
Sai da Amatullah ta yi kwana uku a gidan ta, a daren na hudu su ka raya sunnar manzon Allah SAW, cikin aminci da yardan juna, so da kauna tare da tausayi. Farin cikin da Amatullah ta ji ko rabin sa ba ta ji ba sanda ta kasance da Saifullahi a daren su na farko. Dee ya mata alkhairi babu adadi, ya Kuma mata albishirin zuwan su umarah da za su yi wata mai zuwa.
Tun da aka yi auren Dee da Amatullah Ayush ta dena ganin Saifullahi da gashi, musammam yanda ta ji labarin gidan Amatullah bakin jama'ar gidan. Kullum cikin gorin takaici ta ke yiwa Saifullahi, da ta kira shi bagidaje, sai ta kira shi local. Babban tashin hankali gare shi shi ne yanda in za ta yi kwatancen Mijin da ya hadu sai ka ji ta ambato mijin Amatullah. Wanan shi ne babban dalilin da ya kara lalata zaman auren su.


Kafin su tafi Umarah Dee ya kai Amatullah Abuja wajan mahaifiyar su, so da tararraya babu wanda ba ta sha ba. Ita kan ta Amatullah ta san ta yi dace, ba ga mijin ba, ba ga surikar ba. Dee ne ke kai ta makaranta ya ɗauko ta, shi ya tsaya tsayin daka akan karatun ta, su na gama exam su ka keta hazo zuwa kasa mai tsarki.


***
A kwana a tashi haka rayuwa ta cigaba da tafiya, cikin Ayush ya tsufa sosai har ta wuce EDD ɗin ta sannan aka yi inducing din ta, har an fidda rai ana shirin shiga da ita Cs Allah ya sauke ta lafiya, ta haifi ɗan ta namiji. Sai dai Allah da ikon sa yaron ya zo da matsalar down syndrome, irin wannan yaran masu halitta daban, wanda sukan dalalar da yawu haka kuma hannun sa daya shanyayye ne.


Tun da aka nuna mata ɗan da ta haifa ta ke kuka, haka ma Saifullahi wanda ya hau ta da faɗa, a cewar shi ita ta jawo musu masifar haihuwar nakasasshan ɗa, sanadiyar cikin da ta yi kokarin zubarwa, ta cuce shi ta zalunce shi.


Sai da su ka yi kwana huɗu a kwance gadon asibiti saboda yaron bai da isasshen lafiya, wata tsohuwa aka turowa Aysuh daga Kano domin kula da ita dan Hajiya ta juya mata baya. A kwana na biyar ne da kyar Amatullah ta lallaba Dee ya yarda ya kai ta asibiti ta duba shi, kasancewar Baban Sasa na ta tambayar ta ko ta je ta duba Ayush, bai san ita ma fama ta ke da laulayi ba.


Najaatu da Baba Anas ya tilasta mata zama da Ayush ce su ka gani a harabar gaban ɗakin. Gaishe su tayi a mutunce tana mai cike da fara'a, nan Amatullah ta ce ta shiga ta musu iso. Tashi tayi ta shiga ɗakin fuska ba yabo ba fallasa.


"Yaya Amatullah ce da mijinta su ka zo gaida ki"


Wata irin zabura da Ayush ta yi sai da ya firgita tsohuwar da ke zaune mata


"Kutmesi, watau don munafunci zuwa su ka yi su ga abin da na haifa su min dariya ko, toh wallahi ubansu yayi kaɗan" tace cikin hayagaga.


"Haba Aisha, ina laifin wanda ya gaishe ka, ai sau dubu ya fi wanda ya zage ka, ce musu su shigo yarnan" ta ce tana ƙarewa da isar da sakon ga Najaatu.


Tun da su ka shigo Ayush ta ɗaga idanu ta kalli Amatullah gaban ta yayi mummunar faɗuwa, ta ga yanda ta yi kiba ta yi kyau, abin ka da mai yaron ciki nan har wani sheki ta ke na musamman.


Da ya ke dare ne Amatullah sanye ta ke cikin bakar abaya da aka yiwa ado da shuɗin duwatsu, Daya daga cikin abayar da Dee ya siya mata zuwan su umarah ne, ta naɗe kanta da shudin mayafin kamar diyar larabawa, haka kuma bakar safar da ke sanye kafar ta bai hana shudin takalmin ta mai tsayi haskawa ba. Hankalin ta bai tashi ba sai da ta ga wanda ke biye da Amatullah ya yiwa mijin ta tazara a komai nesa ba kusa ba.


Sanye ya ke cikin kananan kaya, shudin riga da bakar wando, kusan ma anko su ka yi.


'kar dai wannan shi ne mijin na ta?'


Tambayar da ta yiwa kan ta kenan. Yanayin kallon da ta ke masa ya sanya Dee riko hannun Amatullah. Amatullah na gaishe da tsohuwar tare da yiwa Ayush ya mai jiki, amma ina gaba ɗaya hankalin Ayush na kan Dee.


Namiji har namiji, kyau, kwarjini da wayewa wane Saifullahi, bare nakasassan ɗan shi da ta haifa. Amatullah da idan ta lura da halin da Ayush ta shiga sam ba ta nuna ba, ta karɓi dan ta na mai faɗin


"Allah ya raya mana"


Tsohuwa ta amsa da "Aameen"


Ana haka sai ga Saifullahi, wanda kamar Ayush, shi ma ɗin ganin Amatullah ba ƙaramin firgita shi ya yi ba, ashe haka Amatullah ta ke da kyau bai taɓa sani ba, lalle ya yi asara babba a rayuwar shi.


Shi kuwa Dee shigowar Saifullahi da kuma yanayin da ya ga yana kallon Amatullah ne ɓata masa rai. A murtuke su ka gaisa da Saifullahi, ya ce da Amatullah


"Madam mu tafi ko?"


"Amatullah ta amsa da toh Mijin so"


Ta sa hannu a jaka ta ɗauko kudi dubu ashirin ta ajiyewa Ayush bisa gado.


Ayush ta bi kudin da kallon takaici, wai ita Aysuh tsohuwar matar Saifullahi ke yiwa kyautar kudi tsabagen lalacewar mijin ta. Amatullah ta musu sallama, hannun ta cikin na Dee su ka fice in da Ayush da Saifullahi su ka bi su day kallo cike da sha'awar ina ma dai su ne.


Zuwan Amatullah ne ya haddasa masifa tsakanin Ayush da Saifullahi, don cewa ta yi tir da bagidajen miji irin shi, dan Allah ya kama kafa da mijin Amatullah ko ya dan waye, abin ya masa yawa ga talauci ga gidadanci shi ya sa Allah ya bashi nakasassan da daidai da shi


Wannan maganar da Aysuh ta yi ba ƙaramin daci ta masa a rai ba, dan ko sallama bai mata ba ya tafi, ashe karshen ganin shi da ita kenan.


Washagari da sassafe ta haɗa nata ya nata, da kudin da Amatullah ta bata, ta tsallake dan jinjirin da ta haifa ta gudu gida ita da tsohuwar da aka aiko mata, wacce da ƙyar ta hillace ta, ta amince su ka gudu.


Ƙarfe goma ta musu a gidan su Ayush, kallon mamaki iyayen ke mata, har cikin ransu baƙi da ramar da tayi ya taɓa su.


"Wai idanunki kenan? Kin gama shanye romon Saif din ne kika dawo?" mahaifiyarta ta ce cikin tsananin ɓacin rai.
"Ummah!!" Ayush ta ce cikin hawaye.


"Ai tuni muka yafe ma Saifullah ke, ace don kin yi aure ba zaki waiwayo iyayenki ba, ko sau ɗaya baki zo ba, ko talaucin ya kai kun rasa na mota ne" tace ranta a ɓace


"Ummah ku yi haƙuri" Ayush ta ce cikin tausayin kai, haka dai suka haɗu suka wanke ta tas, sannan aka tabbatar tayi wanka ta ci lafiyayyen abinci, daga nan sai bacci ba tare da tuna wani ɗa da ta haifa ba.


Naja'atu ce ta ka kira Saifullahi ta shaida masa Ayush dai ta cika rigar ta da iska, bayan ta zauna ta jira ta ga in da za su ɓullo har ta gaji. Saifullahi bai yarda ba sai da ya zo ya ga zahiri, da gaske ta tsallake ta bar masa jinjiri. Nan ya tabbatar kiyayyar da ta ke masa kiyayyar gaske ce, tashin hankalin da ya shiga baya musaltuwa.


Daukan jaririn yayi in da yake kuka wiwi jinjiri na kuka, dan kuwa lokacin da ya kamata a bashi nono yayi, duk dama dai bai iya sha da kan sa sai dai a tatsa masa.


Tun da har ta na uwa za ta iya tsallakewa ta bar ɗan da ta haifa ya san lalle Ayush ta kai matuka wajan rashin mutunci. Saboda haka ya lashi takobin kin waiwayar ta har illa mashaAllah, duk sanda ta yi shirya ta turo ta karbi takardar ta.


Gun Hajiya dai ya koma, ya nemi yafiyar ta da kuma rokon ta da Allah ta koma asibiti ta na kula masa da Muhamad Jamoh, da ya ke sunan Emjay jinjiri ya ci. Hajiya ta ki yafe masa, sai da Baban Sasa ya sa baki sannan ta amince ta ce ya ci darajar masu daraja. Baban Sasa na mai duban Saifullahi ya ce


"Saifullahi duk yanda na so na tausaya maka, yau na kasa, tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan duka, ka ga dai yanda ta kasance da kai, ka ga kuma yanda Allah ya sakawa Amatullah, duk sanda yaran nan Dan Yusuf ya zo gare ni sai na yi da na sani , ina ma tun farko na yi imani da hukuncin Allah na aura masa jika ta, da yanda ya ke faranta min yanzu tun daga lokacin zan fara mora, wannan yaron Dan Yusuf ya koyar da ni ilimi a shekarun da na riga na tsufa, ya wayar min da kai cewa babu wani tazara tsakanin ni'imar ubangiji da dan adam, muddin ya kasance mai tsoran Allah, Allah yayiwa Dan Yusuf albarka, amma ka sani, yanda ba ka ci riba ba itama matar taka babu riban da zata ci, dubu sunyi kafin ku wani riba suka sami?"


Kai Sunkuye Saifullahi ya gaza motsawa ya yin da hawaye ki fita daga idanun sa cike da nadama, Nadama a lokacin da shi kanshi ya san ya makara.


ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH


Godiya ta musamman gare ku, mun gode kwarai da kasancewarku cikin wannan tafiya namu. Ku sani muna ƙaunar ki Fisabilillah.


Akwai sabuwar tafiya inshaAllah da zata zo bayan Sallah, ka da ku bari ayi babu ku..


Me za ku ce game da TZDM?


Mun gode
Ummu-Abdoul da Khadija Sidi ke muku fatan yin Ibada Karɓaɓɓe🌹💖❤️

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login