Showing 57001 words to 60000 words out of 98809 words

Chapter 20 - TAZARA COMPLETE by UMMU-ABDOUL & KHADIJA SIDI.txt

ya ce masa bayan sun yi musabaha.


"Eh wallahi amma shigowata gidan kenan, na fita da safe" ya faɗi yana mai saurin tada motar.


"Can Layin sarkin zan je dama, amma tun da can kayi ga wannan ka kai musu na san za su buƙata" yace yana mai miƙa masa filas ɗin ruwan zafi da kulan abincin da ya riga ya sanya a motar.


"Ai inshaAllah yaci ta sauka yanzu, Allah ya buɗe idanunsu lafiya" Baban Huda ya sake faɗi ma Saifullah da gaba ɗayansa yayi mutuwar tsaye. Godiya ya shiga yi ma Baban Huda ganin da gaske ba Amaru ta nufa ba.


"Nagode fa, Allah ya saka maku da Aljanna" ya sake faɗi har da yar duƙawarsa.


"Haba Engineer wannan godiya haka, ai yi ma kai ne. Ka yi sauri ka isa na san yanzu kila suna bukatar sa, it's over 3 hrs fa da muka isa, don ma da kyar su ka amsheta ne" yace yana taɓo kafaɗun Saif.


Jiki na ɓari Saifullah ya isa tudun wadan, ko da ya isa Amatullah na barci, wani sabon ni'ima ya ji ya saukar masa ganin bai ga kowa daga Amaru ba.


Har ƙasa ya durƙusa ya gaida maman Huda duk da a shekaru ba zata girme shi ba, amma har cikin ransa yake jin rufin asirin da su ka masa a matsayin gagarumi.


"Ga Danlami fa, ka ji murya da ya saki kukan maraba da duniya" tace tana miƙa masa jariri naɗe cikin zani babu ko rigar sanyi sai wata yar shalaushalon riga.


Tunanin in da Amatullah ta samo rigar yayi don shi dai ya san bai saya ba.
Hannu ya sa ya karɓe shi yana kallo, tsantsan kamar da yaron yayi da su ya sanya shi jin wani iri, bai sani ba ko hakan ne soyayyar ɗa da mahaifi da ake faɗi ko kuma kiyayyar da yake ma cikin ne ya shafi yaron.


"Allah ya raya mana Muhammad Jamoh" yace yana mai miƙa ma maman Huda.


A wajen ya sanya waya ya kira Baban Sasa.
"Muhammad Jamoh ya iso fa Baban Sasa" yace cikin shaƙiyanci bayan sun gaisa.


"In yi guɗa ne Saifullah" yace cike da murna


"Ka taso kawai ka tare shi, amma kuma kar ka shafa masa tsufa. Wallahi bana tunanin za a samu wani tsatsonka da zai yi kama da kai kamar shi" yace yana ƙara leƙen yaron.


Baban Sasa ya kasa ɓoye murnar sa, a haka su ka yi sallama ya tashi yana mai dogara sanda zuwa cikin gida. Abin da yafi shekaru rabon da ya taka, nan ya faɗi masu haihuwa gida ya karaɗe da murna.


Saifullahi kuwa sallama yayi ma maman Huda ya shiga kasuwar tudunwada ya siyo kayan maza, da shawul da kayan sanyi. Ko da ya koma asibiti Amatullah ta farka har ana shirin sallamarsu.


***
Ko da su ka isa gida, maman Huda taimakawa tayi ta wanke Jamoh tas, ta sa masa kaya masu kyau cikin wanda Saifullah ya siyo, jariri ya shiga bacci cikin kwanciyar hankali.


A lokacin ne yan Amaru su ka shiga tururuwa, suna shiga da fice, ga lafiyayyen tuwo da Goggo mairo ta bayar a kawo mata, taci ta hantse.


"ku haɗa mata kayan amfaninta, mu samu mu wuce bayan la'asar" kawai yaji Inna Hafsatu ta faɗi.


Bai ɓata lokaci ba ya kalle su yace
"Babu fa inda za ta je, anan za ta zauna, na riga da na tanadi wacce za ta zo ta mata wanka, mun yi ciniki har na biya rabi" yace yana cijewa.


"An taɓa haka ne Saifullahi. Haihuwar fari fa, kuma kwatakwata Amatullah sha tara take fa bana. Don Allah ka duba dai" inna Hafsatu ta sake fadi cikin magiya.


"Gaskiya mun gama magana da iyayenmu maza, kuma sun amince da tsarin" ganin saurin da yake amfani da shi ya sa tayi shiru kafin ya kai ga zagin ta.


A haka suka yini cur suka tafi ba tare da Amatullah ba, ko da suka koma ma Goggo Mairo da yanda aka yi, har cikin ranta taji babu daɗi amma sanin mahimmancin bin umurnin miji ya sa ta ce a bar zancen dawowarta.
[3/30, 12:08 AM] Zuraiyah Zuzu 🌟: TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀
✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL


BABI NA ASHIRIN DA SHIDA


Gaba ɗaya Saifullah ba zai ce ga halin da ya shiga ba, ya kan ji wani irin zugi tun daga tafin ƙafarsa har saman kansa in ya tuna da wai shi aka haifa wa ɗa.


Ƙanwarsa Asiya ya nema ya bata kuɗi naira dubu talatin ta shiga kasuwar sabon gari ta haɗo duk wani abin buƙata na jariri.


Sannan ya ware wasu kudaden ya ba da aka siyo Rago aka yanka ma Amatullah na ƙauri.
Bai gushe ba sai da ya ɗauko Ƙanwar Hajiyarsa Inna Jamila don ta zauna da Amatullah. Ranar a gajiye ya kwanta cikin wani annashuwa dan ko ba komai ya san yayi bajin ta gurin Baban Sasa, ya samu ya dan wanke kan shi daga bakin cikin da Amatulah ta ku kuntsa masa.


Amatullah kuwa ko da aka watse aka barta da inna Jamila mamaki komai ya dinga ba ta, wai itace yau da ɗa, ɗan ma ita tayi nakudarsa ta haifa. In ta fakaici idon inna Jamila sai ta tsura ma yaron idon cikin so da ƙauna. Tayi godiya ga Allah ya fi sau a ƙirga, ta ga mugun wautarta na amincewa cire cikin da farko.


"Ashe dai haihuwa kyauta ce da bawa bai isa ya siyo ma kansa ba" tace a ranta tana mai istigfari na kusan butulce ma Allah a farko.


Cikin kwana biyu Saifullah ya shayar da ita mamaki, kula sosai yake ba ta da yaron ta, duk ya fita sai ya shigo mata da tsaraba, wani irin rawan jiki ya ke musamman idan Inna Jamila na kusa ba, ita dai na ta ido, na ciki na cikin, dan kuwa ta tabbatar komai ya yi na ganin ido ne, Saifullahi ba kaunar ta ya ke ba bare ɗan da ta haifa, ba za ta taɓa mance yanda ya tsallake ya barta ta na tsaka da nakuda ba.


Zirga-zirga da yake wajen tabbatar da komi ya zo cikin sauki ya sanya gaba ɗaya baya ba Ayush wani kulawa, da ita yake kwana ya tashi cikin begenta da kidayan kwanakin da yayi saura na bikin su. Kullum ya ƙirga ya ga saura fiye da kwana ɗari sai ya ji inama ana fast-forward a rayuwa.


***


Bayan kwana uku, Amatullah zaune bakin gado ta ci ado cikin atamfa. Sun gama rigima da Inna Jamila wacce ta ke yiwa jariri wanka ya na mai tsallar kuka, akan Amatullah ba ta san ɗaure cikin ta, ita kuwa azabar ciwon da ta ke ji saboda dinkin da aka mata ga wani ciwon ciki da take fama da shi ya sa sam ɗaure cikin baya gaban ta. Saifullahi ne ya shigo gaishe da Inna da Jamila kamar yanda ya saba, kallo ɗaya Amatullah ta ma sa ta kawar da kai. Ganin ana yiwa jaririn wanka ba karamin dadi ya ji ba, ya na mai godewa Allah yau ba sai Inna Jamila ta masa gwalegwalen ɗaukar jinjirin ba, ya durkusa har kasa ya gaishe ta. Ita ma Amatullah a dake ta gaishe shi duka gudun kar Inna Jamila ta dago jirgin ta.


Bayan sun gama gaisawa Saifullahi ya tashi ya na shirin fita Inna Jamila ta tsayar da shi ta hanyar faɗin


"Ni kuwa Saifullahi sai na ga zai fi idan ka mayar da Amatulah gida, ka ga dai haihuwar fari ne, gashi an mata dinki yanda ta ke da raki ba na ji za ta iya kula da kan ta"


Saifullahi na mai sosa kyeya ya ce
"Ai Inna Jamila kar ki damu, Zan kasance mai kula da ita da kai na, ba na so su yi nisa da ni ko kadan....."


Ya karasa maganar ya na mai ƙasa da kan sa, cike da takaici Amatullah ke kallon sa, a sanin ta ba dan komai ya ke gudun komawar ta gida ba sai dan gudun kar asirin shi ya tonu. Ita kuwa Inna Jamila kai ta jinjina ta na mai faɗin


"Yaran zamani, toh ai shikenan"


Sinsin ya fice gudun kar Inna Jamila ta sake furta wani abu.
"Yanzu Inna haka za ku bar ni da shi? Wallahi babu abin da zai yi min, Yaya Saifullahi macijin sari ka noke ne....."


"Kul!"
Inna Jamila ta katse ta cikin tsawatarwa, ta kara da


"Kar na sake ji, ku yaran zamani sam ba ku da godiyar Allah, ki duba yanda yaron nan ke mi ki hidama Amatullah, tsabagen rashin godiyar Allah ki kira shi macijin sari ka noke?"


"Duk wannan hidimar da ki ga yanayi na ganin ido ne. ..."


"Lahaila!"
Cewar Inna Jamila ta na mai jinjina kai, ba ta gushe ba ta kara da
"Ba ki da godiyar Allah ƴar nan! To kuwa duk wanda bai godewa Allah ba ya ƙi godewa azabar shi ba!"
Shiru Amatullah ta ma ta, cikin ran ta kuwa faɗi ta ke ai shikenan, duk randa ya kashe ni kwa gane. Haka Inna Jamila ta kare wankan jinjira ta na mita har sai da Amatulah ta yi danasanin lafazin ta tsabagen mitar Inna Jamila.


****
Zaune suke suna kallo, hankalinsu ya ɗauku ga series ɗin Korea da suke kallo, Zainab, Sa'adah da Farida sun natsu gaba ɗaya. Ayush rike da waya tana mai jan tsaki, hakan bai sanya sun waigo sun kalle ta ba, wani dogon tsaki ta sake ja wanda yayi daidai da shigowar Antyn ta mahaifiyar su zainab Anty Ruqayya wacce aka fi sani da Hajiya Haske.
Gidanta Ayush ta wuce a Abuja lokacin da ta ajiye ma Saifu leshi.


Tun rabuwar su ta lura gaba ɗaya hankalinsa ba shi a kanta, ita da kanta ta neme shi ta sanar masa da isarsu, tun ranar kuwa ba su sake wayar minti ɗaya ba, free call din sha biyu da rabin da su ke yi ma ko ta kira sai ta iske wayarsa a kashe.


"Baby Ish lafiya kuwa, don dai hankalinki baya kan talabijin balle na ce kallo kike" Hajiya Haske tace tana zama gefenta. Ita kanta Ayush ta san Anty Ruqayya na cikin wainda ke shagwaɓa ta, kanwar mahaifiyarta ce da ke sonta kamar ƴar da ta haifa. In dai ka ji su a rana toh akan rashi suturta jiki ne, don Hajiya haske irin matan nan da kuɗi bai sanya su canza shigarsu ba.


"Maami Saif ne fa, yau kwana biyar kenan sai share ni yake, yanzu ina shiga Facebook na iske an ɗaura hoton jariri har ana tagging dinsa, the baby looks so much like him" tace cikin shagwaɓa


"Common baby, ba yana da aure ba, menene in matarsa ce ta haihu" Hajiya Haske ta faɗi tana rungumar Ayush.


"Maami Alkawari ya min fa, cewa yayi ni zan fara haifar masa yara". Tace tana dakin kukan da ta makale shi a makoshi. Rarrashinta Hajiya Haske ta dinga yi tana bata baki yayin da su zainab su ka zo su ka tsaya cirko cirko cikin tausayin yar uwar su.


"Common Ayush, we are in 21st century fa, 2011 muke ba 90s ba, har namiji zai ce miki haka ki yarda, ni wallahi shi ya sa na so ki amince ma Baba Hashim ɗinmu, ga kyau ga ilimi ga naira, amma kin nace ma baƙauyen zaria" zainab da suke sa'anni da Ayush ta faɗi cikin jin zafi.


"Ba Baba Hashim kaɗai ba, shin wa ya kira ku nan ma" hajiya haske ta ce tana janye Ayush cikin ɗaki. Nasiha sosai ta ke mata akan haihuwan Saif ba komi ba ne in har da gaske yaron da ta gani ɗansa ne. Kuma tun da su duka sun shaida son da yake ma Ayush sun san tabbas tana shiga ragamar gidan zai koma hannunta.


"Ki yarda da kanki, sannan kada ki ce zaki dinga soloɓiyanci, ba a taɓa aurenmu mun zama bora ba, tabbas sai dai mu mulki gida" hajiya Haske ta ƙarasa da faɗin haka. Wanda hakan ya fi komi kwantar da hankalin Ayush, ta san iyayenta tsaye su ke akanta.


Komawa wajen yan uwanta tayi su ka cigaba da kallo, da ga baya kuma su ka fara hira inda Sa'adah ce ta buɗe musu ƙofa da faɗin
"Wai ni Ayush me kika shirya ma Saif dinnan ne, makaho fa bai san ana kallonsa ba sai ka zungure shi" ta ce tana mai sassauta muryarta.


"Kuma fa wallahi haka ne, shi wai ga munafuki ba, yana can suna soyewa da matarsa ke yana bin ki da daɗin baki, watau shi ya san daɗin haihuwa ko" Farida ta ce tana mai jan tsaki.


Hankalin Ayush yayi matukar tashi ta maida hankalinta gaba ɗaya gare su tana son jin me suke nufi. Su kuma ganin haka ya sanya su fadi kamar haɗin baki
"Comment on the pic" sai a lokacin taji wani daɗi, take ta ɗauko wayarta ta shiga Facebook tare da neman hoton don tayi sharhi akai.


"Me zan sa?" tace kamar za ta yi kuka.


"Welcome to the world darling. May Allah bless your parents with much love and harmony" zainab ta amshi wayar ta rubuta tare da karanta musu. Shewa su ka yi gaba ɗaya suna tafawa.


"Kin san yana gani dole ya shiga tsilla-tsilla" zainab ta fadi cikin dariya.
Da haka su ka cigaba da kallo suna sharhi zukatansu fal da murna.


***


Saifullah na zaune bayan isha'i, ya dawo gidan da balango in da ya miƙa ma Amatullah nata kamar yanda yake mata tun bayan haihuwarta. Sam ba ta mamakin kyautata mata da ya ke kokarin nunawa Inna Jamila ya na yi, ta san kaɗan daga aikin Saifullahi.


Tun da ya dawo ya ɗauki wayarsa ya shiga Facebook, nan ya iske sanarwan sharhin Ayush a kan hoton da bai san da zaman sa ba.


" Hasbunallah" yace yana mai miƙewa tsaye. Shi dai ya san bai faɗi mata komi dangane da cikin ba balle a je zuwa haihuwa.


'in ta fasa fa' sashin zuciyarsa ta faɗi masa hakan ya sa ya ƙara firgicewa. Wani takaicin Amatullah da abin da ta haifa ya tokare masa ƙirji, cikin rawan hannu ya lalubo lambar Ayush ya kira.


"He is calling" tace cikin murna ta na nuna ma yan uwanta. Dama ta faɗa musu zai kira daga gani don son da yake mata bata da haufi akai.


"Ki ɗauka, kar ki nuna ɓacin rai ki ce ya haɗa ki da matar za ki mata barka, make sure you leave him in suspense" zainab tace yayin da sa'adah da farida su ka amince da shawarar.


"how far babe" yace bayan ta ɗauki wayar. Danne zuciyarta ta yi kar ta ƙunduma masa Ashar.


"maimakon ka sanyo ni muyi jegon tare sai a yi min wariyar launin skin" tace cikin dariya. Shiru yayi kamar ruwa ya ci shi, sai da ta sake faɗin "Hello" sannan yayi gyarar murya ya ce


"Kiyi haƙuri, ni mai laifi ne, wallahi ba yanda kike zato bane, duk yadda na so a zubar da cikin nan ta ƙi amincewa. I did all I could wallahi" yace kamar zai yi kuka.


Dariya ta yi sosai, zuciyar ta fal da murna ta ce
"Subhanallah! Saboda so na zaka saɓa ma Allah, ai tun da dai aka yi kuskuren shiga inda ba muhalli ba ai hakuri ake da duk abin da ya biyo baya. Yanzu dai bani maman Babyn na mata barka" tace muryarta sarai ba alamun ɓacin rai.


"Bana gida ai, rabon da na sa su a ido tun washegarin haihuwan. I've been busy ne a kammala gidan ki, jiya na ga wani gu da ba'a yi da kyau ba, gaba ɗaya can na yini har yau. Ni gaba ɗaya auren mu ne gaba na" ya samu kansa da shirgo ƙarya.


"Amma ai ba zai hana ka kashe kudin suna ba ko, don duk son mu da yin classy biki, taron sunan nan ma is very important" tace tana mai addu'ar haƙanta ya cimma ruwa.


"Suna kuma, ai in kin ga nayi recognizing wani ɗa a gidan nan toh Queen Ayush ce ta haihu, kin san Allah ɗaya tun ranar da ta haihu na faɗi suna but yanzu ba sai gobe ba zan kira na ce ba suna kar ma su da rai" yace cikin rudewa. Bai kashe wayar ba ya kira Baban Sasa yana mai haɗa conference call.


"Baban Jamoh jikan Jamoh" baban Sasa ya faɗi cikin raha. Gaishe shi Saifullah yayi suka dan yi raha sannan yace.


"ni dai Baban Sasa ban son taron sunan nan, taron gulma ne kawai, ka ga a ɗan zuwa barka ana neman zuga yarinyar nan. Don Allah ka tsawatar, kowa yayi zamansa ya mana addu'a daga can" yace cikin muryar magiya. Shiru Baban Sasa yayi ya ce


"Ayi haka Saifullah, kar mu tauye ma yarinyar nan fa da yawa"


"Baban Sasa ni duba zaman lafiyar mu nake, nan jiya na shigo na ji ana mata kirarin jinin Jamoh ba su zaman kishi, Baban Sasa in ba dai fasa auren nan zan yi ba" ya ce sanin da yayi baban Sasa ba zai taɓa yarda da fasa auren ba.


"mu kuma ka maida mu mutanen banza ko, iyayenku ne matsorata amma ni cikakken bazazzage ne, cikin zage-zagin ma Bamalle, sai da na yi huɗu ras" yace cikin dariya, shima Saifullah dariya yayi.


"Zan faɗa masu, Allah ya raya mana Muhammad Jamoh" Baban Sasa yace nan su ka yi sallama Saifullah cike da farin ciki.


"Babe believe me, wallahi ba abin da ba zan iya yi don farin cikinki ba" yace bayan ya ajiye wayar baban Sasa.


Tsaki ta ja cikin nuna takaici ta ce
"Toh wai ka birge ne nan, ku yi sunanku lafiya ni bacci zan yi" bata jira amsarsa ba ta kashe wayar.


Kansa ya rike gaba ɗaya ya rasa me zai yi ya wanke kansa wajen Ayush, ya san ta sarai a haukarta ma sai ta iya fasa auren. Kwata kwata bai yarda da amincewarta ba yafi ganin sa a shigo shigo ba zurfi ta masa.


***
Kamar yadda ya tsara ilai kuwa hakan ya faru, Amatullah na ji tana gani baban Sasa ya sanya dokar rashin bikin suna tare da tsawatar ma yaya da jikokinsa akan zuwa gidan Amatullah akai akai.

Mamaki sosai ya cika ahlin gidan don shi bai furta cewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login