Showing 87001 words to 90000 words out of 98809 words

Chapter 30 - TAZARA COMPLETE by UMMU-ABDOUL & KHADIJA SIDI.txt

wallahi na yi kuskure na yi nadama, ka duba girman zumunci ka min wannan alfarmar Baban Sasa, ka bani damar gyaran kuskuren da na yi, na ma ka alkawari zan zamo abin alfahari a gare ka"


Ganin yanda Saifullahi ke fitar da kwalla, da kuma yanda ya rame yayi baki gaba daya ya fita daga hayyacin shi ya sanya zuciyar Baban Sasa karyewa.

"Saifullahi"
Ya kira sunan sa a sanyaye.


"Na'am Babab Sasa"


"Amatullah ta ce saki uku ka yi mata, ka yi hakuri"


"Wallahi Baban Sasa daya dal na mata, ina ga zafin sakin ya sa ta dage a ukun na mata, Baban Sasa Amatullah na jin maganar ku, yarinya ce mai hankali, ladabi da biyayya, na tabbatar muddun ka ba ta umarni za ta bi, ka taimaka min Sasa"
Ya kare cikin shasshekan kuka.


Shiru Baban Sasa yayi ya na mai ɗan tuntuntuni, kafin daga baya ya furta


"Kar ka damu Saifullahi, zan yi iyakan kokari na in Sha Allah, idan Allah yayi da rabo za ta koma, ka kwantar da hankalinka kar ciwo ya kama ka"


Cikin jin daɗi Saifullahi ya riko kafafun Baban Sasa, faɗi ya ke


"Na gode! madallah, na san za ka min rana, Allah ya saka da alkhairi, yanzu zuwa gobe za ta komo min ko?"


Kai Baban Sasa ya girgiza ya ce
"Nan fa daya, ka yi hakuri zafin mutuwar nan ya ɗan bar ta, nan da sati biyu haka sai a mata magana"


Murna sai ta koma ciki, ran sa ya ki ya motsa dan kuwa gani yake in har ya tsaya kallon ruwa kwado zai iya masa kafa.


"Amma Baban Sasa ba ka gani jinkiri na iya haifar da fitina?"


"Fitinar me kuma? Ah ah kar ka damu in Sha Allah"


Jiki sanyaye yayi masa sallama. Kai tsaye dakinsa ya nufa. Ya na zancen zuci ya manta bai yi sallama ba, kan gado ya tadda Ayush ta yi daidai cikin shigar nan nata da ta saba ta na bacci har da mun shari, shigar da take rikita Saifullahi da shi a da, Amma yanzu kuwa sam ba sa burge shi, bare ta ɗaɗa shi da kasa. Ya na mai girgiza kai har zai juya ya fita idanun sa suka sauka kan ɗan karamin kwalin magani gefe a ƙasa, haka nan ya ji ya na so ya ga maganin menene. Ko da ya ɗauka ya duba sai gashi an rubuta


"emergency contraceptive"


Ya faɗa , ya maimaita! Wai shi Saifullahi matar shi, matar ma ta so ce ke shan Emergency contraceptive? Wato tsabagen dan kar ta haihu da shi? Ɓacin rai ya sanya ya manta makoki ya ke, dan kuwa idanun sa sun kada sun jajur. Nan take ya karasa wajan Ayush.


Sam be damu da baccin da ta ke ba cikin nuna isa, ya shiga neman hakkin sa. Duk yanda ta so ta kaurace masa ta kasa har sai da ya biyawa kan sa bukatan sa. Ta na samun ta kan, ta tashi cikin sauri naɗe cikin bargo, cikin tashin hankali ta shiga binciken maganin ta kwali daya dal da ya rage, domin kuwa ta sa a samo mata cikin unguwar ba a samu ba sai Jamila ta yiwa waya, ta mata alkawarin turo mata da shi nan da kwana biyu.


Ya na daga kan gado ya ke kallon ta, ta ƙaraci dube duben ta, Amma babu magani babu alamar sa. Ganin babu sarki sai Allah ta dubi Saifullahi ta ce


"Malam menene haka za ka far mani ina bacci kamar dabba! Wannan wani irin gidadanci ne! Kai wani irin bagidaje ne! God Saifullahi you so local! Too local for my liking! Wallahi da na san haka kake bagidaje da ban aure ka ba!"


Yanda ta ke maganar ne, da kalaman ta da ke shigar sa kamar kibiya tsabagen ɗaci ya sanya shi tunawa da lafuzzan sa ga Amatullah,


'bagidaje? Shi Saifullahi ne matar shi ta aure ke kira bagidaje? local? Shi Saifullahi shi ne local?'


Abin da zuciyar sa ke faɗi kenan, azahiri kuma kallon ta ya ke cike da tsana.
[4/21, 10:26 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀
✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL


BABI NA TALATIN DA BIYU




WANNAN BABI SADAUKARWA NE GA DUK WATA UWA DA TA RASA ƊANTA, WALAU TA HANYAR ƁARI KO MUTUWA. UBANGIJI ALLAH YA BAKU LADAN HAKURI ƳA SA SU ZAMA MASU CETO A GARE KU.
Much love
UMDIJA❤️💖💕


"how? Menene ya same shi? Me ya faru?"


Saifullahi ya sake tambaya jiki na rawa. Amatullah ta wuce ciki rugume da gawar Emjay, ɗakin Baban Sasa ta shige nan ta tadda shi kwance. Ganin shigowar ta ko sallama babu ya sanya shi tashi zaune, ya na mai faɗin


"Amatullah lafiya?"


Gaban sa ta shimfide gawar Emjay, ta ce


"Ka ga Emjay Baban Sasa, lafiyan sa lau mu ka tashi, Wai dan kawai ya ɗan yi mika mu ka kai shi asibiti, likitan ya ce wai ya mutu!"


Kallo ɗaya Baban Sasa ya masa ya san ko shakka babu tabbas babu rai jikin Emjay.


"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!"


Ya faɗa da kakkausar murya.


"Baban Sasa karya su ke, dan Allah ka tada min shi, Emjay tashi, tashi ɗan albarka"


Ta shiga jijjiga kafadar gawar. Ganin haka Baban Sasa ne ya mike tsaye, hannun Amatullah ya kama, ya na mai janye ta daga jikin gawar, ta na cijewa, faɗi ta ke


"Baba Sasa tsaya mu tashe shi"


Fitowa yayi da ita, ya na rike da hannun ta su ka nufi cikin gida, Amatullah ba ta fasa waigawa ba tana cewa


"Baban Sasa kar mu bar shi shi kaɗai cikin ɗaki, idan ya tashi bai ganni ba kuka zai yi"


A haka su ka isa har ɓangaran Gwaggo, in da ganin Amatullah da Baban Sasa ya sa duka ahalin gida su ka biyo bayan su. A tsakar gida su ka su ka tarar da Gwaggo, cikin alhini Baban Sasa ya ce


"Yaro ɗan wajan Saifullahi dai Allah ya amshi abin sa, sai ki masa addua Allah ya masa rahama, yanzu za mu shirya shi a kai shi"


Salati Gwaggo ta saka, haka ma sauran jama'ar da ke gurin. Amatullah har lokacin ba ta fasa karyata maganar mutuwar ba. Gwaggo ce ta shiga da ita ciki, in da yanayin gidan gaba ɗaya I ya canza, daga masu kuka sai masu salati da sallallami.


Baban Sasa ya koma ɗakinsa bayan ya shaidawa su Baba Anas a yi shirin yiwa Emjay wanka, a shirya shi cikin gaggawa, su Baba Idiris kuwa su ne su ka tafi makabarta domin haka kabari.


Saifullahi zama yayi dirshen a ƙasa in da Amatullah ta bar shi tare da Mimi. Surutai ya ke mara kan gado tamkar wanda ya zare. A haka Baba Anas ya zo ya same shi, ya ce da shi maza ya zo a shirya ɗan sa tare da shi.


Sai da Mimi ta nemi wayar Dee har sau wajan uku ta na Kira ba ya dagawa, daga bisani ta masa text, dan kila ya sa wayar a chaji ne ya shiga aji ya na bawa dalibai karatu.


Gab da la'asar aka shirya Emjay tsaf. Kafin a fita da shi aka ce da Amatullah ta zo ta masa sallama. Mama ce da Mimi su ka kai ta dakin Baban Sasa.
Sai da ta ga an rufe Emjay cikin lin
kafani sannan ta yarda lalle da gaske mai raba ɗa da mahaifiya yau ta mata yankar ƙauna. Gaban gawar ta zauna, hannun ta bisa gawar ta furta


"Yaro na? Ka na jin Maman ka? Yaro na naso ka, Ina son ka, Amma Allah ya fini son ka, ya karbe ka, na yafe ma ka, Allah ya rahamshe ka Emjay.....Allah....Alllah....Allah......"


Kukan da ya ci karfin ta ya sanya ta kasa karasa maganar, kawai sai ta sunkumi gawar ta na kuka ta na faɗin


"Ya Allah....Allah.....ya Allah!"


Daga Mimi har Mama duka kuka su ke, shi kan shi Baba Anas hawaye ke gudana daga idanun sa, bare Baban Sasa, wanda ji ya ke dama shi mutuwar ta ɗauka ta bar masa ɗan jikar sa.


Saifullahi wanda tun shigowar Amatullah kan sa ya ke sunkuye, ya taso daga in da ya ke, cike da tausayawa ya shiga kokarin karɓe Emjay, shi ɗin ma hawaye ya ke. Da kyar ya iya karɓan shi, su Mama su ka janye ta ciki. Nan ɗin ma su duka su ka shiryo cikin alwala don halartar sallah gareshi.


Ba tare da ɓata lokaci ba aka sallaci Emjay, amma tun a kabbarar farko Saifullahi ya gaza, sai kuka haka har aka idar da sallah. Mata su ka koma cikin gida yayin da maza su ka doshi hanyar maƙabarta. Saifullah ya ɗauki gawar cikin tabarma lullube da zanin goyan sa, ya ki bawa kowa har su ka isa makabarta. Baban Sasa kadai aka bari waje bisa tabarma kasancewar jikin sa ba zai bari ya iya zuwa makabartar ba.


Ganin har la'asar ta gota sosai ba su dawo ba ya sanya Baban Sasa tayar da sallar la'asar, hakan yayi daidai da isowar Dee Yusuf wanda bai sami sakon Mimi ba sai bayan da ya fito daga aji, kai tsaye ya nufo gidan su Amatullah. Ganin babu kowa wajan ya tabbatar ya makara an tafi kai Emjay. Dan haka gudun kar shi ma ya makara ya ɗora alwala, Baban Sasa ya kai raka'a biyun farko ya zauna tahiya shi ma yayi yi harama, ya na mai kabbara ya zauna gefen shi in da ya shiga mika tashi sallah ta hanyar bin Baban Sasa.


Sai da su ka zauna tahiyar karshe sannan jama'ar da su kai Emjay su ka shigo layin. Sam babu wanda ya lura da wanda ke bin Baban Sasa sallah, sai da su ka zo dab da su, wato daga Baba Mahmuda, Baba Anas, Baba Idris, Baba Hamza, har zuwa Saifullahi tsayawa su ka yi cirko cirko suna duban su, hakan kuma yayi daidai da lokacin da Baban Sasa yayi Sallama, ganin yanda su ka yi tsaya kamar sokwaye ya sanya shi waigawa gefensa, me zai gani? Dee ya tashi tsaye ya na mai kabbara ya shiga rama raka'oi biyun da ya rasa.


"Lahailaha illallahu!"


Cewar Baban Sasa!
"Kai Dan Yusuf dama ka na sallah?"


Ya faɗa tsabagen mamaki ya ma manta ba a yiwa Wanda ya ke sallah magana. Shi kuwa Baba Idris hargiza yayi cikin nuna bacin rai ya ce


"Isgilanci ne irin na arna! Mu za ka yiwa shakiyanci! Karya ya ke yi ba ya sallah! Yaudarar ku ya ke so yayi, dan ni wallahi babu arnan da zai yaudare ni!"


Baba Anas na mai taɓa kafadar Baba Idris ya ce


"Bari mu idar da sallah kila ma iya sauraran yashesshen zancen nan na ka!"


Ya na mai duban sauran jama'ar ya ce
"Ni dai ina da alwala, Idan da mai alwala ku zo mu yi jam'i ko? Lokacin sallah ya riga ya kure"


Ya na gama faɗin haka ya cire takalmi ya bi bayan Dee, haka ma Baba Mahmuda da wasu makotan su biyu da su ma din su ka ce suna da alwala. Takaici ya sa Baba Idiris shigewa ciki. Shi kuwa Saifullahi sallah Dee zame masa ta yi tamkar an sake masa wani rashin, lalle lokacin komawar Amatullah yayi ko da kuwa da tsiya da tsiya tsiya ne sai ya sake mallakar ta, ba zai yiyu ya na ji ya na gani ya rasa Emjay ya rasa uwar Emjay ba.
[4/23, 12:50 AM] Zuraiyah Zuzu 🌟: TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀
✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL


BABI NA TALATIN DA HUƊU


Buɗe baki yayi don ya mayar mata da martani, Amma ya kasa cewa komai dan takaici, kallon ta ya ke in da har lokacin ta dage tsakanin ta da Allah neman maganin ta take. A fusace ta sake waigo shi ta ce


"Wai dan Allah Saif menene haka?"


Can ta sake wani tunani, cikin sigar kissa da tausasa murya ta ce


"Saif wani kwallin magani na ke nima, dan Allah ba ka gan shi ba?"


Hankali kwance ya na mai ɓoye ɓacin ransa ya amsa da


"Wani cikin ɗan karamin kwali haka? An rubuta post pill kamar?"


Ras gaban ta ya faɗi, ta na mai fatan Allah ya sa bai karanta kwalin maganin ba ya san maganin menene ta ce


"Exactly, shi ne, maganin ciwon mara na ne"


Sai da ya tashi ya zo gaban ta ya tsaya sannan ya ce


"Eyaaaa Ina ga wani daban na gani ba wanda ki ke magana ba"


Ta na mai hadiyar yawo dan jika makoshin ta tsabagen tashin hankali ta ce


"Ba ni wanda ka gani din....."


"Ni na ce mi ki na ga wani abu?"


Idanun ta na mai kawo ruwa ta ce
"Saifullahi don't play smart with me! Na san ka gani wallahi! Dan Allah ka bani!"


Kallon ta yayi tun daga sama har kasa, sannan ya ce


"Ni da na ke bagidaje how can I play smart? Kar ki matsa min dalla malama! Ina da abin yi! Shirin dawowar uwar gida na dakinta na ke yi!"


Ya faɗa ya na mai kokarin wuce ta ya na mita, wani kukan kura ta saka ta na mai cinkwalar rigar shi ta ce


"Burauban nan kayyasa! Kai ka isa! Na ce Saifullahi ka isa ka dawo min da wannan bakar yarinyar bagida....."


"Ke Aisha!"


Ya daka mata tsawa, cikin gurnani da daga murya ya ce


"Wallahi na rantse da Allah ki ka sake ki ka zagi Amatullah sai na tattaka ki nan! Ta fiki daraja! Ta fiki ɗa'a! Ta fiki tarbiya! Ta fi min ke komai a rayuwa! Shasha wacce ba ta san ciwon kan ta ba!"


Ya na gama faɗin haka bai damu da kukan da Ayush ta saka ba, ko zagin da ta rufe shi da shi, ya fizge hannun ta daga cikin rigar sa, nan ƙasa ya zubar da ita ya fito ya barta ta na kuka ta na surfa masa zagi.


Bakin hanyar fita yayi kacibus da Hajiya ta na shirin shiga wajen na sa, cike da damuwa Hajiya ta ke duban sa, ta furta


"Saifullahi gidan na ka lafiya kuwa? Duka gidan nan fa ihu da kukan matarka ake ji sai ka ce ana zaman bariki?"


Saifullahi na mai girgiza ka ya ce
"Hajiya menene bambamcin yarinyar nan da ƴan bariki? Ina ƴan bariki ne ke shan maganin hana daukar ciki gudun kar su yo cikin shege? Idan dai haka shi ne wayewa Allah wadar da wayewa irin na Aisha!"


Hajiya na mai dafe kirji ta ce
"Me ka ke faɗa ɗan nan!"


Nan ya bawa Hajiya labarin maganin da ya tsinta ɗakinsa, ya kare da


"Ko tausayi na ba ta ji ta na gani na rasa ɗana, ashe ita kuma ta na nan ta na min bita da kulle dukan kabarin kishiya! Hajiya tun rasuwar Emjay Allah ya jarrabe ni da kewar yaron nan! Ba ni da buri da ya wuce na sake ganin jini na Hajiya!"


Kai Hajiya ta ke jinjinawa kawai, Saifullahi bai gushe ba ya kara da


"Saboda haka na yanke hukuncin dawo da Amatullah, Hajiya Amatullah ita ce cikon farin cikina! Hajiya ba zan iya rayuwa idan babu Amatullah ba, Hajiya Amatullah kaɗai za ta iya sharen kuka na, Hajiya ku taimaka min!"


"Amatullah fa ka ce Saifullahi?"


Hajiya ta fada a sanyaye, Saifullahi na mai jinjina kai ya furta


"Amatullah Hajiya"


Cikin sauri kar Hajiya ta ga kwallan da ke idanun sa yayi sauri ya wuce ta ya fice.


Jim Hajiya ta tsaya ta na mai jinjina maganar dawo da Amatullah, tabbas ta san Saifullahi bai yi sa'ar mace ba, dan kuwa Ayush sam ba macen arziki ba ce, ga kuɗin ga wayewar amma babu hali bare a moru da ita, ita sai da so samu ne da Saifullahi ya duba ya nemi wata diyar masu hannu da shuni, ko da kuwa nan cikin Zaria ne ba sai ya kai Kano ba, tunda diyar Kanawan ba ta zo da halin kirki ba.


Da wannan tunanin ta ja jikin ta ta koma na ta bangaran kafin Aysuh ta fito ta Bata rabon ta. Daren ranan duka gidan kwana aka yi ana gulmar Saifullahi da matar shi, dan kuwa zagi da ihun ta babu wanda bai ji ba. Ita kuwa Amatullah fama ta ke da period da ya yi mata bazata tsabagen tashin hankalin da ta shiga na rashin Emjay.


Washagari duk yanda Ayush ta hargitsa gidan domin neman maganin nan, sama ko kasa ba ta gani ba. Hauka ne kawai ba ta yi ba. Gashi tun daren jiya ta ke neman wayar Jamila amma ta kasa samu, sai da yamma dabara ta zo mata, ta kira gidan su ta ce da Mahaifiyar ta dan Allah ta tura ko da driver ne gidan Jamila ta na so ta yi magana da ita amma ta kasa samin ta. Mahaifiyar ta ta tambaya lafiya? Ya ta ji muryar ta haka. Ta na mai tabbatar mata lafiya lau kawai dama da sakon da za ta tura mata ne amma ta ji ta shiru. Da wannan ta amince ta tura driver gidan Jamila amma ya tarar ba ta nan. Hakan ya sa Ayush kara tsanan Saifullahi, ta kuma sha alwashin ba za ta kara bari ya kusance ta ba matukar ba maganin nan ta samu ba.


***
Sati biyu da rasuwar Emjay Amatullah ta koma makaranta, duk abin da take babu wani walwala dan kuwa har lokacin ba ta daina kukan rasuwar ɗan na ta ba.


Cikin dare ta sha kukan ta kenan yanda ta saba kafin ta yi bacci ta ji wayan ta na kara. Da kamar ba za ta ɗaga ba daga bisani ta sake shawara ta daga. Gaban ta ne ya fadi jin muryar da ya bakunci kunnen ta ya na mai faɗin


"Assalamu Alaikum"


Ta na mai gyara kwanciya, murya dashe ta amsa da


"Waalaikumus salam"


"God kar dai har yanzu kuka ki ke yi? Um Mama nah?"


Yanayin muryar tashi da kuma yanda ya ke mata maganar ne cike da rarrashi ya sa ta kasa amsa masa ta na mai runtse idanu. Babban farin cikin ta tun bayan rasuwar Emjay shi ne labarin musuluntar shi da ta ji Baba Anas Yana yiwa Baba Salihu bayan dawowar shi satin da ya wuce.


"Amatullah....."


Ya sake kiran sunan ta. Amatullah ta masa da


"Um"


Ya furta
"Ki yi hakuri Mama na...."


Shiru ne ya ƙara biyo baya, dan kuwa wani nauyi da kunyar Dee ta ke ji na babu gyara babu dalili. Dee kuwa da ya san ba amsa masa za ta yi ba ya kara da


"Dee ne sorry I called you this late,I couldn't help it, you keep crossing my mind. Amatullah I've been trying to stay

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login