Showing 12001 words to 15000 words out of 98809 words
Chapter 5 - TAZARA COMPLETE by UMMU-ABDOUL & KHADIJA SIDI.txt
Hamza, aminina" Yana mai murmushin yake, Hamza kuwa tuni ya gano rashin jin daɗin ganinsa da Dee ya yi.
Zama tsayuwa yayi a kujerar da ke gabansu, kallon Amatullah yake na ƙurilla wanda har hakan ya saukar mata da rashin natsuwa.
"Malam tashi mu wuce dama mun gama tutorial ɗin yau, sai mun yi waya mamanah" ya faɗi cikin ɓacin rai, yafi kowa sanin halin abokinsa Hamza, ko kara aka ɗaura ma zani in dai zai samu dama toh sai ya kwance, hakan na daga cikin dalilin da ya hana masa ganin Amatullah duk yadda ya so yi.
A ɓangaren Hamza kuwa ayyanawa ransa mallakar Amatullah a shimfiɗarsa yayi ko da hakan na nufin ɓata duk wani alaka tsakanin sa da Dee Yusuf.
Ba a san ransa ba, haka yana ji yana gani su ka yi sallama da ita, yau ko rakiya ba ta samu ba, nan ya bar ta, ya ja Hamza su ka fice.
***
"wa ya faɗa maka inda nake?" Dee Yusuf ya samu kansa da faɗi bayan sun yi tafiyar kurame na dan wasu mintoci
"Facebook" ya faɗi yana dariyar ƙeta, "Baba ashe babbar Haja ka samu shi yasa kake ɓoyeta, oboi fully loaded ina ma zan ganta without Hijab" ya ƙara faɗi yana mai kwatanta surarta da hannunsa. Baƙin ciki sosai ya cika Dee Yusuf har ya rasa abin da zai ce. Kafin daga bisani ya tsaya cak, gaban Hamza ya sha, ya na mai daura hannu bisa kafar Hamza ya ke kallan sa ido cikin ido ya furta
"Hamza Amatullah mace ce mai daraja a guna, ina rokan ka arziki ka tauna harshen ka kafin ka furta lafazi dangane da ita, na yafe ma ka yanzu, Amma na rantse maka da Allah ka kuskura ka sake sai na bata ma ka!!!!!"
Bai ƙara komi ba ya wuce ya barshi a nan, shi kan shi Hamza yayi mamakin Amininsa, kamar yadda Dee ya cika da mamakin kansa, wai shine da kishin mace har haka.
Addu'a ya shiga yi bayan ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun simintin da ke gaban hostel ɗinsu na Danfodio.
"Yaa Ubangiji kar ka sanya Amatullah juyan baya bayan na yaye mata lullubin da ke tattare da ni.
***
Tun bayan da ya amsa kiran Baban Sasa yake cikin ƙunci, gaba ɗaya tunaninsa ya ɗauke akan musababbin kiran.
" In ba so kake ƙasa su rufen ido ba ka dawo a ɗaura aurenku" kalaman baban Sasa su ka dawo masa kamar a lokacin ya ke faɗi masa.
"Watau wannan bagidajiyar ba ta ji magana ba kenan" ya fadi ya mai jan tsuki, da aka aka kira su jirgin su zai tashi. Jiki a sanyaye ya Mike ya isa inda ake bukatar su, ba don soyayyarsa da Baban Sasa ba babu abin da zai sa ya koma Nijeriya a wannan lokacin.
Duk kwanakin da ya ɗauka kafin isowa Nijeriya bai ga daɗewarsu ba illa ma sauri da ya masa, hakan ya sa da ya tsinci kansa a kofar gidan Jamoh kamar yadda ake kiran gidan ya ji gaba ɗaya ya tsani kasancewarsa ahlin gidan.
An yi murna da zuwan sa, tarbo na musamman mahaifiyar Amatullah ta yi masa wanda hakan al'adar ta ne tun yana ƙarami.
Sai da ya ci yayi Nak sannan ya fara ganin gari, da yake shi ba mai wasu abokai bane tun asalinsa balle yanzu da yake ganin zama cikin masu ƙaramin tunani na nufin koma baya, duk da ma'anar ƙaramin tunani a wajen Saifu daban yake da saura.
***
"A sanya biki nan da sati biyu, mu ne dangin amarya mu ne dangin ango" fadin baba Zubairu kasancewarsa babba gaba ɗaya a gidan ya sanya ba wand ya ja da zancen sa.
"Kai Saifullah sai ka samu lokaci ka je ka ɗauko kanwar taka don ta san halin da ake ciki" Baba Anas mahaifi ga Saifullah ya fadi. Shi dai Saifullah bakin cikin duniya ya taru ya cika masa ƙirji, bai ce komi na sannan bai iya gardama ba ya tashi ya mike. Bai jira wani ɓata lokaci ba samaru ya wuce.
Amatullah na zaune tana jiran kiran Dee Yusuf inda ya kan ce da ta fito zuwa koyon karatu. Karan wayarta ne ya dawo da ita daga duniyar tunani, ganin lambar a kulle ya sanya ta saurin ɗauka don a tsammaninta Dee ne bai network ya sanya haka nan.
"Ki fito wajen basket ball din ku" aka ce haɗe da kashe wayar, kamannin muryar da na mahaifansu ne ya sanya ta tunanin ko daga gidan su ne.
'kila Baban Sasa ya samu cikawa' tace tana mai share hawayen da ya gangaro mata na rashin madafa. Cikin sauri ta ja hijabin ta ba tare da ta damu ta dubi kan ta a madubi ba bare ta dan gyara maikon da ke fuskar ta, ta fice fuuu don ba za ta so abin da take tunani su tabbata ba.
Isar ta wajan basketball ta tsaya cak ganin wanda ke tsaye bakin mota, duk da dai baya ya bata hannun cikin aljihu bai sa ta kasa gane shi ba, ba ta san lokacin da ta fara tasbihi ta na mai neman tsari daga ubangijin ta, fad'i ta ke
"Allahumma ajirni fi musibati......."
[1/19, 6:44 AM] Safiyya Ummu-Abdoul Writer: FIKRA WRITERS ASSOCIATION
TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼♂🤦🏿♀
✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL
BABI NA BAKWAI
"Salamun alaikum"
Ta faɗa cikin faɗuwar gaban abin da zai biyo baya. Juyowa yayi fuska murtuke, bin ta yayi da kallo tun daga sama har kasa, irin wannan kallon na hadarin kaji.
A wulakance ya amsa da
"Waalaikumus salam, na baki minti goma cal ki haɗo kayanki ki fito"
Iya abinda ya ce kenan ya buɗe mota ya shige.
"Ki haɗo kayan ki mu tafi?"
Ta daɗa nanatawa cikin ranta, shikenan ta faru ta ƙare ramamme ya zagi maye. Karfin hali ta yi ta ƙarasa jikin motar, da ya ke ya ɗaga gilashin sai ta kwankwasa a hankali. Sai da yayi minti biyar kafin ya sauke tare da faɗin
"Menene kuma? Ba ki ji abin da na ce ba ne?"
"Dama cewa na yi ya jikin Baban Sasa?"
"Oh so ki ke na ce ya mutu ko? Toh ya nan daram da ran sa......"
"Alhamdulillah"
Amatullah ta furta ta na mai ajiyar zuciya ta juya ba tare da ta sake tambayar ba'asi ba. Tana zancen zuci ta isa hostel, har ta wuce shi ba ta sani ba sai ji ta yi ya kira sunan ta
"Amatullah?"
Juyowa ta yi ta na mai murmushin yake domin ɓoye ma sa damuwar da ta ke ciki. Sanye ya ke cikin shadda brown ɗikin yar shara, kan sa sanye da irin wannan hular ta yarbawa, ƙafafunsa cikin baƙin takalmi, hannun shi mai sanye da baƙin agogo ɗauke da leda baka. Kallo daya za ka masa ka amince da jimla daya, "Dee Yusuf namiji ne", namijin ma ɗan kwalisa, amma sam bai ɗaurawa kan sa girman kai kamar Saifullahi ba. Abin da Amatullah ke ayyanawa a ranta ke nan, a zahiri kuma cewa ta yi
"Yi hakuri, wallahi ban gan ka ba ne, ka kira ni ko? A ɗaki na bar wayar"
Kallo ɗaya ya mata ya gane damuwar da ke tattare da ita, haka kuma bai yi jinkirin tambayar dalili ba, ya na kokarin sanya idanun sa cikin na ta ya furta
"You're not ok, me ya faru? Ba ki da lafiya ne?"
Kai ta girgiza al'amar "ah ah" kafin daga bisani ta kara da
"Lafiya lau na ke, dama Yaya na ne ya zo ya ce da ni ana nema na a gida, amma ina tunanin jikin kaka na ne yayi tsanani"
Cike da tausayawa ya ce
"Ayya Mama nah, Allah ya ba shi lafiya, Wai da na zo ne mu yi maganar nan da na ce mi ki ina son na fada mi ki, Amma babu komai sai kin dawo ma yi"
Ba haka Amatullah ta so ba, duk da dai ta san maganar gizo ba ya wuce na koki, ta dade da dago jirgin sa, maganar ta sa dai ba zai wuce na soyayyar da ta ke gani a kwayar idanun sa ba kamar yanda ita ma ta ke jin sa cikin zuciyar ta, kuma ta ke mai fatan ji daga bakin sa, ba dan zuwan Saifullahi ba da ta ji.
"Ko ya ki ka ce Mama nah"
Dee Yusuf ne ya sake magana jin tayi shiru kamar mai tunani, cikin jin kunya ta ce
"Eh sai na dawo din"
Ledar hannun sa ya mika mata
"Ga shi Allah ya sa za su yi mi ki, yar ajin mu na ga ta na siyarwa na mi ki sha'awar su....."
Ta na mai girgiza kai ta ce
"Ah ah dan Allah kar dawainiyar ta yi yawa....."
Kallan da ya mata ya sa ta karbar ledar ba tare da sake masa mu su ba, ta na mai fadin
"Allah ya saka da alkhairi"
"Amen, toh maza je ki fito sai na raka ki ko? daga nan na gaisa da yayan ki....."
"Na shiga uku"
Cewar Amatullah domin kuwa ta manta da Saifullahi na jiran ta.
"Wallahi na manta ya na jira na, na san yayi fushi ma, ka bari za ku gaisa wata rana, today is not a good day, na gode sosai"
"Toh Mama nah, zan iya kiran ki ko?"
Ta gyada kai alamar "eh"
"Take care of yourself, a gaida mutan gida"
"Za su ji"
Tana gama fadin haka ta shige ciki da sauri dan kuwa ta san ta wuce minti goman da Saifullahi ya ba ta, yana nan ya cika yayi ɓam. Jakar ta kawai ta dauka, sai kuma ledar da Dee ya bata duk da dai har lokacin ba ta san me ledar ke dauke da shi ba. Zulaikha ba ta nan dan haka ba ta samu sun yi sallama ba, cike da fargaban wulakancin Saifullahi ta iske shi cikin mota kan sa kife bisa sitiyari.
Bude motar ta yi tare da sallama, yanda ya dago kai ya kalle ta ne ys sa ta yi saurin shiga ta ja murfin motar ta rufe. Yanda ya figi motar ne kamar wanda za su tashi sama ya sanya Amatullah runtse idanu ta na mai addua'ar Allah ya kai su gida lafiya.
Tafiyar kurame su ka yi babu um babu um um har su ka isa gida. Isar su kofar gida tun kafin ya kashe motar ta fara kokarin fita, ga mamakin ta sa ya sa lock ya daɗa rufe motar ya na mai faɗin
"Ji mana, ban gama da ke ba"
Cike da alamun tambaya ta kalli fuskar sa, shi ma ɗin kallon ta ya ke ido cikin ido, dan haka sai ta yi kasa da na ta idanun.
"Ba na son ki Amatullah, ba na kaunar ki, sanadiyyar ki Baban Sasa na so ya shiga rayuwa ta, shin ke ba ki da zuciya ne? Ko kare ya cinye ne......?"
Ya na maganar ne a hankali be kuma fasa kallon ta ba, haka kuma hawayen da ke fita daga idanun Amatullah bai sa ya fasa maganar da ya ke ba
"Hawaye? Ni ma haka na ke hawayen zuci Amatullah......ina da wacce na ke so, wayayyiya ba bagidajiya irin ki ba......."
"Dan Allah ka bude min kofa na shiga gida....."
Amatullah ta katse shi, domin kuwa zuciyar ta cika ta yi dam, kiris ta ke jira ta fashe. Ya bude baki zai bata amsa ganin fitowar Baba Zubairu ya sake shawara ya cire lock din. Hakan ya ba ta damar fitowa ta na mai share hawayen fuskar ta gudun kar Baba Zubairu ya gani, amma ina ya riga ya lura da ita. Idanun shi kan ta har ta karasa gaban shi ta durkusa har kasa ta gaishe shi. Yana mai duban ta ya ce
"Amatullah lafiya kuwa na gan ki cikin damuwa haka har ki na hawaye?"
"Laaaa ba hawaye ba ne abu ne ya fada idanuna, lafiya lau Baba komi Alhamdulillah, dama damuwar na Baban Sasa ne, da fatan jikin na sa da sauki"
Ta bashi amsar ne ta na fara'ar yake.
"Toh jikin Baban Sasa dai sai godiya kin san jikin tsufa. Ango an dawo? Ina fatan dai ba kai ne ka ɓatawa amaryar ta ka rai ba"
Ya karasa maganar ne ya na kallan Saifullahi da ya iso gare su. Gaban Amatullah ne yayi mummnar faduwa jin an kira Saifullahi ango. Ba ta kara tsorata ba sai da ta ji amsar da Saifullahi ya bawa Baba Zubairu.
"Ah ah Baba Zubairu, ina ga dai sati biyun da ku ke san sakawa ne bai mata ba"
Yayi maganar ne cikin nishadi kai ba ka ce shine ke gasa mata magana duk lokacin da ya samu dama ba. Tashi ta yi da sauri gudun jin amsar da Baba Zubairu zai bayar, ta ce
"Bari na shiga gida na ga su Baban Sasa"
Ba ta ji ba ta gani, ba ta san amsar da su ka bata ba, haka ma ko da ta shiga gidan ma su mata maraba na yi amma ina babu wanda ta ke gani tsabagen tashin hankali. Dakin Gwoggon ta ta shige nan ta tadda ita zaune kan gado tana ta lissafin kudin kayan kitchen din da za su siyowa Amarya.
Kamar daga sama ta ga Amatullah ta zube mata a gaba, hannyen ta biyu ta ruko kafar Gwoggo, kuka take ta na fad'in
"Gwoggo ku rufa min asiri, ku ceto rayuwa ta wallahi Saifullahi ba ya kauna ta, ba ya so na ni ma ba na san shi kar ku aurar da ni ga makiyi na Gwoggo......."
"Amatullah me zan gani? Yanzu ashe ba za ki ji magana ta ba Amatullah? Ki na tunanin za mu cutar da ke ne Amatullah?"
Gwoggon ce ta ke magana cikin fada fada ganin Amatullah na neman kwance mata zani a kasuwa, ba ta gushe ba ta cigaba da fadin
"Kin sani gidan nan idan aka dauke Baban Sasa da shi Mahaifan Saifu wa ke kaunar mu Amatullah? Yanzu ba za ki rufa mana asiri ba ashe? So ki ke zaman gidan nan ya gagare ni? Na ce da ke idan har Saifullahi ba ya kaunar ki, ke dai ki yi addua, amma kada ki bari matsalar ta fito daga gare mu, ashe ba za ki ji magana ta ba Amatullah? Ashe ban isa da ke ba? Yau ina ranar haihuwa?"
Kai Amatullah ke girgiza mata, cikin shasshekar kuka ta saki kafar Gwaggo tare da fadin
"Ki yafe min Gwaggo, zan kasance mai biyayya a gare ki, Allah ya huci zuciyar ki"
Jin maganar Amatullah hankalin Gwaggo ya dan kwanta, nan ta cigaba da mata nasiha ta na mai nuna mata muhimmancin auren ta ga Saifullahi ba dan komai ba sai dan kara dankon zumunci.
***
Ranar Amatullah ba ta sami kan ta ba sai bayan isha'i, shi kan shi Baban Sasa shiru yaji ta, ba ta je ta gaishe shi ba sai da ya aiko yaro yayi kiran ta. Gwaggo ce ta yi karyan ta yi bacci tun da ta dawo ta ke ciwon kai gudun kar Amatullah ta je wajan Baban Sasa da kumburarran idanu.
Bayan ta idar da sallah, zaune cikin dakin ta bisa darduma, ta hangi ledar da Dee Yusuf ya ba ta sai sannan ta tuna tun fa da ta dawo aje kayan ko wayar ta ba ta sake dubawa ba, kuma ta ji karar wayar ba sau daya ba sau biyu ba, babu mamaki ma Dee din ya kira ta. Tashi ta yi ta dauko ledar tare da wayar , tsakiyar gadon tahaye yayinda ta zazzage ledar, idanun ta cike da kwallar farin ciki ganin hijabai gudu hudu sun zubo, sai kuma dan karamin Qur'ani da ta yi saurin riko shi kafin ya kai ga faduwa bisa gadon ta na mai furta
"Astagafirullah"
Ba ta san sanda ta rungume Qur'anin tare da hijaban ba, kamshin Dee Yusuf ke tashi daga cikin su, wani irin soyayya da ba ta taba yiwa da namiji ba ta ji ya na ratsa zuciyar ta.
"Dee Yusuf"
Ta ambaci sunan sa a hankali, wayan ta ne ya fara kara. Idanun ta rufe ba tare da ta duba wanda ke kira ba, tsabagen jin dadin kyautar da ya mata ta furta
"Dee Yusuf, kai masoyi ne"
"Da ki na da masoyi shi ne ki ka liƙe min haka kamar mayya?"
Ya bata amsa a wulakance wanda hakan ya sa ta buɗe idanu tare da tashi zaune ta na kallon wayar, maimakon ta ga number Dee da ta yi zato sai ganin bakuwar number, ta sake karawa a kunnen ta domin tabbatar da Saifullahi ne ko kuwa kunnan ta ke zagi. Nan kuwa ya tabbatar mata shi din ne ta hanyar fadin
"Ko ba kya ji? If really you have a local champion that you love, wanda na ta tabbatar bagidaje ne irin ki me ya hana ki fadawa su Baban Sasa? Ai kwarya ta bi kwarya......"
"Dakata Malam!!!!"
Amatullah ce ta katse shi a fusace domin kuwa yau ya wuce gona da iri. Cikin tsiwa da dama ita gwana ce kawai ta na raga ma sa ne ta furta
"Kar ka sake danganta Dee Yusuf da bagidaje domin kuwa babu abin da za ka nuna ma sa, sai dai shi ya nuna ma ka daraja da sanin kiman dan Adam!!!"
Shiru Saifullahi yayi daga alama dai maganar ta yi masa bazata. Har ta na tunanin ya katse, sai kuma ta ji ya furta
"Dee Yusuf din, ki na nufin shi ki ke so Amatullah?"
"Eh shi na ke so, shi na ke kauna, daidai da second daya ban taba jin son ka a rai na ba Ya Saifullahi, ya fi ka komai, mutunci, kima, daraja da kuma sanin muhimmancin ƴa mace.....biyayya ne ya sa na ke iya jurewa har na ke iya sauraran wula......"
"Kar ki damu Amatullah"
Yayi saurin katseta cikin muryar lallashi ya ke magana da har ita kan ta Amatullah sai da ta duba wayar cike da mamakin furucin na sa, fadi ya ke
"Ni dan uwan ki ne ba zan so a cutar da ke ba, inshaAllah zan yiwa Baban Sasa bayanin ba kya sona, ba za su mi ki dole ba tun da ba kya so na"
Ya na gama magana ya kashe wayar ba tare da ya bata damar sake tanka masa ba. Mamaki da tsoro ne ya kama Amatullah ganin yanda Saifullahi ya canza lokaci guda, ta na mai addua'ar Allah ya sa sauki ne ya zo mata daga Allah. Nan ta kashe wayar dan kar ma ya sake kiran ta.
***
Ɓangaran Saifullahi kuwa ya na aje wayar ya saki