Showing 21001 words to 24000 words out of 98809 words

Chapter 8 - TAZARA COMPLETE by UMMU-ABDOUL & KHADIJA SIDI.txt

ji Dee Yusuf"


Karaf a kunnan Saifullahi, tuni ya ɗago ya na mai duban gefan da mai maganar ke tsaye, jingine jikin mota, irin motar nan ne masu numfashi, yaro kuwa gida ya shige a guje domin kiran Amatullah.
Kallon shi ya ke cike da mamakin abin da idanunsa ke gane masa, dan kuwa bai taba tsammanin wanda ya kai daidai da rabin Dee zai kusanci bagidajiya kamar Amatullah ba.
Sanye ya ke cikin farar shadda gidzna dinkin nan da ake kira tazarce. Ba wani aiki shaddar ta sha ba amma yanayin kwarjini da jiki irin na Dee Yusuf sai kayan ya karbe shi kwarai. Hular kanshi zannabukar ba karamin Kara ma sa kyau ta yi ba, haka kuma takalmi har da agogon hannun sa babu wanda be sanya gwiwar Saifullahi sanyi ba, dan kuwa in dai kwarjini, wayewa da kuma ado ne kowa ya ga Dee sai dai ya shafa Fatiha.


"Wai kuma Amatullah ya zo nema?"


Tambayar da ya ke yiwa kan sa kenan yayinda yaji wani abu mai kama da kishi ya tokare masa kahon ciyarsa.


Amatullah kuwa kamar daga sama sai ga yaro ya shigo, da karfin sa ya furta


"Wai Amatullah ta zo in ji Deee Yusuf"


Gaban ta yayi mummunar faduwa, tuni ta kai kallan ta ga Gwaggo wacce ta tsaya cak ba tare da ta dauke idanu daga kan tsintar da ta ke ba, sauran ahalin gidan kuwa idanu su ka zubawa Amatullah, musammam Hajiya wacce da ma kiris ta ke jira, aikuwa sai ta sa guda


"Ayyiriri ahayye!! Ashe dai sirikin na mu ne a tafe....."


"Ka je ka ce ba na nan"


Amatullah ce ta katse harguwar Hajiyar. In da shi kuma yaro ya sake juyawa da gudun shi. Hajiya na fadin
"Toh fa, toh menene na munafuncin kin fita? Na ce dama abin da ki ke jira kenan?"


Shiru Amatullah ta yi mata, in da ta ke rokan Allah ya rufa mata asiri Dee ya tafi, ko wa ya mata wannan aika aikan be kyauta mata ba.


Yaro na fitowa ya dubi Dee wanda idan ya lura da Saifullahi toh sam bai nuna wata alama ba. Ya ce
"Amatullah din ta ce ba nan...."


Saifullahi ya tsinci kan shi ya na mai sakin numfashi, wanda hakan yayi daidai da saukar Baba Anas, kuma ya ji furacin yaro. Bayan ya sallami mai achaba, ya na duban Saifullahi ya ce


"Saifullahi bako mu ka yi ne?"


Ganin Mahaifin na sa Saifullahi ya taso, shi kuwa Dee karasowa yayi gaban Baba Anas har kasa ya durkusa ya gaishe shi. Hannu Baba Anas ya bashi ya na mai tada shi tsaye, idanun sa kan Saifullahi, shi kuwa Saifullahi cikin shan kamshi ya furta
"Baba ni ma ganina da shi kenan, kamar Amatullah ya ce ya ke nema"


Jin haka Baba Anas ya dada faɗaɗa fara'a, cikin farin ciki ya furta


"Assha, bakon Amatullah shi ne za ku bar shi a waje haka? Sannu da zuwa, shiga maza ka yiwa Amatullah magana, sai kuma ka kimtsa mu su wannan falon na zaure"


Jigum Saifullahi yayi cikin jinjina maganar, shi ne ma zai je ya kira Amatullah?


"Ba ka ji ba ne Saifullahi ka tsaya sororo kamar soko?"


Cewar Baba Anas cikin nuna kulewa da yanda Saifullahi ya yi. Ran sa idan yayi dubu ya baci haka ya wuce ciki ya na jin Baba Anas na tambayar Dee ya manya da mutan gida.
Ganin Amatullah wani saban bakin ciki na ya turnuke zuciyar Saifullahi, tsayawa yayi ya na duban ta takaici ya sa ya kasa bude baki ya aiwatar da sakon da Baba Anas ya aiko shi. Hajiya ce ta ce
"Ah ah Saifu yaya ka shigo ka tsaya hakan nan? Na ce dai lafiya?"


Kafin ya kai ga ba ta amsa Baba Anas ya shigo, tun daga soro ya ke fad'in
"Kai Saifullahi ka fada mata? Ina Amatullahi din ne? Kai ka ji shasha nan ka zo ka yi tsaye?"


Ya karasa maganar ne ya na duban Saifullahi wanda ya haɗe fuska kamar wanda be taɓa fara'a ba a rayuwar shi ba. Baba Anas na duban Amatullah wacce ke raba idanu ya ce


"Ke Amatullah ba a shaida mi ki kina da bako a waje ba?"


Kai ta girgiza al'amar ah ah dan fargaba ta kasa magana.


"Ahaf kai kuwa Saifullahi ba ka yi kyawun hali ba, in dai wannan yaro na waje shi Amatullah ke bida wallahi ya min dadi, yaro ana ganin sa an ga dan manyan mutane, ga kamala ga kwarjini wallahi har kasa ya durkusa ya gaishe ni, maza ta shi ki je Amatullah, Allah ya sanya alkhairi, ya tabbatar mana da alkhairin sa"
Jin haka ya sanya Gwaggo jin sanyi cikin ranta, ashe dai dan mutunci Amatullah ta samu. Taikaici da bakin ciki ya sanya Saifullahi ji kamar kasa ta bude ya shige, nan ya kara tsanar Amatullah. Juyawa kawai yayi ya fice ya bar mu su gidan.
Amatullah kuwa da kyar kamar wacce kwai ya fashewa a ciki ta fita, kan ta a kasa ta wuce su Gwaggo, cikin ranta addua ta ke Allah ya sa kar Baban Sasa ya ji zuwan Dee, da niyar sallamar sa ba tare da bata lokaci ba ta isa ga falon da Baba Anas yayi masa iso.
Dan karamin falo ne mai dauke da setin kujerun kushin. Karamar kujera ya samu ya zauna ya na mai sakar zuci, damuwar shi Allah ya sa kar fushin da Amatullahi ke yi da shi ya karu, musammam jin yaro ya ce ta ce a sheda ma sa ba ta nan. Sallaman ta da shigar ta falon lokaci daya ne, ganin ta kamar wacce aka jefo ya sanya Dee tashi tsaye, ya na mai idanun ta da ya cika da kwalla ya ce
"Amatullah......"
Hannu ta daga masa tare da faɗin


" Dakata malam! Ka rufa min asiri ka fita ka bar gidan nan!"


"Amatullah........"


"Na ce ka fita!!!!!"


Amatullah ta katse shi cikin tsawa da fada. Wanda hakan ba karamin motsa zuciyar Dee yayi ba, amma maimakon ya fita, sai ya koma ya zauna abin sa. Cike da takaici yayinda hawaye ke fita daga idanun ta, daya na bin daya, ta zo gaban shi ta tsugunna, cikin murya mai karya zuciya ta fara magana


" Me zai sa ka zo gidan mu bayan ka san babu aure a tsakanin mu? Me zai sa ka dada tayar min da hankali bayan tashin hankalin da na ke ciki? Ka rufa min asiri ka tafi, wallahi sati daya ya rage Baban Sasa ya saka ranar aure na da Saifullahi....."


Zufa ne ya fara keto masa, hannu ya sa ya cire hular kan shi yayinda shi ma din ya sauko daga kujera, farar shaddar da ke jikin sa bai hana shi zaman dirshen a kan carpet ba. Fadi ya ke


"Me ka faruwa Amatullah?"


"Ka tashi ka tafi!"


Shiru ne ya biyo baya, kafin daga bisani ya furta
"zan tafi, na mi ki alkawarin zan tafi, Amma sai kin saurare ni, kin kuma faɗa min abin da ke faruwa, dan Allah, dan soyayyar da ki ke yiwa Allah"


Hawaye ta share, ka na ta ce
"Zan faɗa ma ka, zan kuma saurare ka, amma ka sani wannan shi ne magana ta karshe da zai shiga tsakanin mu"


Kai gyada mata alamar amincewa. Nan ta kwashe duka halin da ta ke ciki ta fada masa, ta kare da


"Duk yanda na so kujewa auren Saifullahi dole sai na aure shi, duk yanda na so na ji furucin soyayya daga gare ka a banza, domin kuwa bakin alkalami ya bushe, tun ran gini tunran zane......."


yanda ya ke zaune dirshen kasa haka ita ma ta zauna, idanun sa sun kaɗa sun yi jawur, ji ya ke ina ma Amatullah halaltacciya ce a gare, da ya janyo ta jikin sa, ya rungume ta har sa ya yaye mata gaba daya damuwar ta, wanda ya ke sila da wanda ba shi ne sila ba. A hankali ya fara magana kamar haka


"Ba mu da zabi akan addinin da aka haife mu da shi Amatullah, haka mu ka tashi mu ka tsinci kan mu ciki. Kamar yadda ki ka sani sunan mahaifina Yusuf, Musulmi ne kamar ke...."


1983


"Duk wanda ke Department of Mass communication ya shaidi soyayyar da ke tsakanin Yusuf Haɗeja da Binta Sule. Duk da yana gaba da ita da shekara biyu hakan bai hana soyayyarsu tafiya yadda ya dace ba, Mahaifina asalinsa Fulanin Haɗeja ne, dogo ne fari kyayyawa mai cike da haiba. Ya fito gidan malanta, don a ƙaidar gidansu yaro baya wuce shekara goma sha ɗaya bai haddace ƙur'ani ba. Hakan ya kasance da shi.
Ko da ya je ma iyayensa da zancen mahaifiyata ba su yi na'am ba kasancewar ta yar ƙasar gongola, sun ce garin su da nisa, da dadin baki ya sha kan iyayensa su ka amince amma bayan da bincikensu ya tabbatar masu da cewa mahaifiyata ma'abociyar littafi ce da soyayya ya sanya ta amsar musulunci, nan su ka tuɓure su ka ƙi.
"Yusufa ka rasa matar da zaka aura sai wacce ta tuba a dalilin soyayyar ka"
Baffansa Sheikhi ya faɗi cikin ɗacin rai.


"Baffa ka dubi girman Allah kar ka haramta min abin Ubangiji ya halalta min" yace cikin hawaye. Kallonsa Baffan yayi na yan mintoci kafin ya ce
"Sannu tatacce ɗan uwan koko, tun da ka matsa zan jagoranci komi" ya faɗi yana mai kauda kai, godiya mahaifi na ya shiga yi har sai da Baffan nasa ya ce ya tashi ya tafi.
A karshen shekarar aka ɗaura auren iyaye na. Auren bai hana su kammala karatunsu ba duk da kasancewarsu ƙarkashin gandun mahaifansa.
Rayuwa su ke cikin kwanciyar hankali matukar suna cikin garin Kano ne, amma da zarar sun isa Haɗeja duk wani kwanciyar hankali kan kare musu saboda kyara da mahaifiya ta ke samu daga yan uwan mahaifina, wasu kan kira ta da tubabba wasu ma kai tsaye arniya su ke kiran ta. Girkin da ake yi tare a cikin gidan aka ɗauke mata a bisa hujjar ba sa cin abincin arna.
Takan zauna a ɗaki ta yi kuka, ta ji takaicin kasancewa cikin mutanen da basu darajar ɗan adam ba. Duk da cewa ta taso cikin al'ummar da akan samu bambancin addini a ahali ɗaya, ta san akwai karramawa ta musamman ga duk musulmin da ya zaɓi barin musulunci zuwa addinin Yesu kiristi duk kuwa da a can ba ta ganin ana wulakanta wainda su ka musulunta.
A haka mahaifi na ya kammala jarrabawarsa ta karshe a fanin jarida tare da samun gurbin aiki a gidan rediyo Nijeriya Kaduna. Murna sosai su ka yi don a tunaninsu damar yin rayuwar farin ciki ne ya zo masu.
"Wai naga se kumbure-kumbure ka ke, ni da za ka bari da kewa ma farin cikin nasaranmu yafi na kewan" tace tana jan kumatunsa, in idanunta ba su faɗi mata ƙarya ba hawaye ta gani kwance a idanunsa.
"ina baƙin cikin halin da za ki shiga bayan na tafi, ki kula da kanki ki kula da ajiyar da ke tattare da ke" yace yana mai rungume ta, jikinta yayi sanyi, amma ta daure ta kara masa ƙarfin guiwa.
Cikin kewan juna ya ɗauki jiki zuwa Kaduna in da zai ƙarasa duk wani abin da ake bukata don fara aiki.


Ita ta raka shi har tasha in da ya shiga motar da za ta wuce da su sannan ta wuce makaranta in da za ta ɗauki darasi.
Kwana uku bayan tafiyar sa tana gida tana nazarin littafanta aka yi sallama.
Sai da ta yane jikinta da mayafi sannan ta fita, yayyin mijinta biyu ta iske tsaye kowanne fuskarsa turɓune.
Gaida su tayi cikin sanyin jiki tana mai kaucewa daga bakin kofa don su shigo.
"kulle gidan ki taho mu je" Nasiru ya faɗi a kausashe, faɗuwar gaba ta ji amma ba ta tuna komi na sharri ba.
Babu wanda ya ce da ita komi har su ka isa Haɗeja, taron da ta gani a kofar gida ya sanya ta tunanin mutuwa a ka yi.
"wa ye ya rasu?" ta ce a zuciyarta. Haka ta tsallake mazan waje ta shiga gida, duk da ta na ganin yadda ake bin ta da kallo.
Dakin mahaifiyar babana ta isa, nan ta iske mutane zazzaune, gaida su tayi amma babu wanda ya amsa mata hakan bai hana mata zama ba, tana zaune wasu mata su ka shigo,
"Yusufa kuma sa'i yayi, Ubangiji Allah ya rahama masa" su ka ce suna masu tashi bayan sun ƙarasa musu ta'aziyya.
'Yusufa kuma sa'i yayi' ta kara maimaitawa, tana mai fassara kowane kalma.
'sa'i na nufin lokaci wani lokaci ake ma ta'aziyya?' ta ce a ranta tana ƙaryata tunanin da ke yawo mata a kwakwalwa.
Tashi ta yi a firgice ta yi waje dakin sheikhi ta isa idanunta a rufe, bata damu da maluman da aka yi ma masauki a ciki ba ta isa gareshi tana kuka
"Baffa na ji ana Yusufa sa'i yayi? Me ya same shi? Don Allah ka faɗa min" tace cikin kuka da tashin hankali.
"Dama tun kwanaki ukun nan ba a ɗauko ki ba?" ya tambaya cikin ɓacin rai.
"Yau su Nasiru su ka zo bamu dade da isowa ba" tace tana share hawaye.
"Binta ki yi hakuri, duk mai rai jiran lokaci yake yi. Yusuf ko kura ba su kai ba motar su ta hantsala. Yau kwanan sa uku a kushewa, sai kiyi hakuri" ya faɗi yana mai jin sabon radadin mutuwar. Bude baki yayi da niyyar cigaba da mata nasiha ya ga ta sulale ta suma.
Kwana bakwai tayi tana jinya nan ma babu wanda ya kula da ita duk a dalilin tubabba ce musuluncinta bai cika ba.
Bayan an sallame ta babu wanda ya mata bayanin takaba, sai ma juya mata baya da kowa yayi. Babu mai bata abinci, balle a san halin da ta ke ciki.
Ranar da mahaifina ya cika kwanaki arba'in da rasuwa ta musu sallama ta koma makaranta, abin mamaki sai ta iske su Nasiru a ƙofar gida, ba su ce mata komi ba su ka kwashe komi na gidan da sunan gadon mahaifi na ne, ita kuma tun da tubabba ce ba ta da gadonsa.
Tayi kuka sosai kamar ranta zai fita don hatta katifar kwanciyar su sai da suka ɗauka, cikin wannan yanayi ta shiga makaranta ko za ta samu kawar da za ta laɓata a hostel.
"Binta Yusuf" ta ji an kira ta, share kwallan da ya zubo mata tayi ta juyo.
"pastor Abu kai ne da kanka" tace cikin murmushi. Ba za ta mance karamcinsa ba don duk da kasancewarsa pastor ya goyi bayan aurenta da Yusuf sai dai shi bai so ta bar addininta ba.
"Ina kika bar Yusuf" yace bayan sun gaisa, ba ta iya ɓoye hawayenta ba, ta ce masa
"yau kwanan sa arba'in karkashin kasa" sai ta saki kuka, ganin suna kan hanya ne ya ja ta gefe.
"kwana arba'in Binta kuma kike nan? Ba kin musulunta ba? Kin manta 4 month 10 days su ke yi? Gidan ku fa da musulmi. Tsaya su dangin sa ya su ka bari kika fito" yace cikin ɗacin rai.
"sun ce basu yarda da musulunci na ba, sun ce ni tubabba ce, sun kira ni arniya" ta fadi cikin kuka, nan ta shiga fadin halin da ta ke ciki, shi kuma bai yi ƙasa a guiwa ba ya kaita gidansa.
Daki ɗaya suka ware mata, nan take duk wani ibada nata, in ba wani kwakkwaran dalili ba, bara shiga makaranta. Mutane na ta shigowa mata ta'aziyya yayin da mabiya addinin kirista ke bata duk wani kulawa.
Bayan ta rubuta jarrabawa ta je garinsu Hong na jihar Adamawa. Sai a lokacin iyayen ta su ka ji zancen rasuwar Yusuf, sun yi alhini kuma sun ji haushin halin da yar su ta shiga.
Cikin ta na da wata tara ta haihu, lokacin ta hakura da musulunci ta koma addininta na gado, addinin da ke karrama duk wanda ya shige ta, addinin da ta ga basa nuna yatsa ga wasunsu.
Washegarin haihuwarta yayan ta, Baffa na Haruna ya tashi tun daga hong har Haɗeja ya sanar masu da haihuwa, nan su ka ce da shi sun bar musu don basu da bukatar jinin arna. Yana dawowa ya sanya min suna David. Bayan shekara guda ta sake aure, mijin ta shi yayi min komai, dangin mijin ta su suka zame min dagin uba, su na sani Amatullahi......."


Nisawa yayi yayinda ya ke kallan furkar Amatullah, be gushe ba ya cigaba
"Amatullah, na taso a matsayin Margi ba bahaɗeje ba, duk wani gata da yaro zai samu na samu daga mijin mahaifiya ta da Baffani na. Na taso cikin al'umma da zaki iya iske mata musulma miji kirista ko mata kirista miji musulmi...."


Kan gwiwowin sa biyu ya tsaya yayinda hawaye ke zuba daga idanun sa, ya ce
"Sanadiyyar abin da ya sami mahaifiya ta, Ni da ke Amatullah kowannan mu za mu iya yin addinin mu, Wallahi babu abin da zai hana ki musuluncinki, ki dubi girman Allah ki amince da aurena, in ma so kike na je Haɗeja dangin mahaifi na su zo neman aurena wallahi na amince. Kiyi min rai Amatullah, ki amince da son da nake maki....."
[1/29, 1:57 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: FIKRA WRITERS ASSOCIATION


TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀


✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL


BABI NA GOMA


Kamar saukar aradu haka maganar Dee ya sauka kunnen Hajiya, wacce ta yi ƙaryan zagawa bayi amma ta ɓige da zuwa soro domin ganin wannan saurayi da Baba Anas ke ta zuokarin ɓoye fuskarta cikin hijabi gudun kar a gane halin da ta ke ciki ta dada shiga cikin tashin hankali, dama fitowarta kenan ganin tunanin da ta ke yi a ɗaki zai iya tarwatsa zuciyarta fara maganar Hajiya ya sa ta ji ina ma bata fito ba.
"Amarsu ki je Baba na kira"
ta ce tana kallon Amatullah wacce ke tsure kamar wacce ta yi wa sarki ƙarya.
Haka ta tashi sumsum ta wuce hawaye na rigarigen saukowa kuncinta.
Tana juya baya Hajiya ta shiga bada labarin abin da ta jiyo, nan yan gidan aka shiga tsine ma boko da abin da ke ciki acewarsu bokon da ta zurfafa ne ya sa ta kula bamaguje a matsayin masoyi.
Goggo Mairo ta rasa in da za ta sa kanta yadda ta ga hajiya da ta kawo labarin ko wurin ba ta bari ba amma an fara canza labari

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login