Showing 51001 words to 54000 words out of 98809 words

Chapter 18 - TAZARA COMPLETE by UMMU-ABDOUL & KHADIJA SIDI.txt

kenan ya hana ni, ya ki kai ni ya kuma ki ba ni kudin mota da na tafi....."


"Innalillahi wainnailaihi rajiun, wai shi Saifullahi ya hana ki zuwa makaranta? Bayan nan ya zo ya gaishe mu kafin ya shige cikin gida ya ce da mu ya dawo daga kai ki makaranta ne? Shin dama ba lafiya lau ku ke zaune ba Amatullah? Me ya sa ba ki kira kin sheda mana a waya ba?"
Tambayoyin da Baba Sasa ya jero mata kenan. Shi kuwa Baba Anas gyada kai kawai ya ke.


"Wallahi Baban Sasa karya ya ke, ya hana ni zuwa makarantar, hatta wayar ma shi ya kwace tun ranar da na kira... .."


"Daina rantsuwa Amatullah, wallahi idan dai Saifullahi ne zai aika, jairi ka na ganin shi sim sim yaran nan bai da girma sai na jikin sa!"
Baba Anas ne ya katse ta. Cike da bacin rai ya tashi ya shiga ciki a fusace kafar shi ko takalmi Babu. Baban Sasa kuwa shi har a lokacin bai yarda Saifullahi zai iya aikata hakan ba, duk da kuwa Amatullah ba ta taba masa karya ba.


A dakin Hajiya ya tadda shi, yayi rashe rashe ya na cin wainar gero da kunu. Kallo ɗaya ya yiwa mahaifin na sa ya tabbatar da bacin ran da ke tattare da shi


"Babu shakka, dole ka rashe a nan kana cin kumallo hankali kwance tun da ka hana 'yar mutane zuwa makaranta"


Cewar Baba Anas ya na kallan sa cike da takaici, in da Saifullahi ya kware ya na mai fuzar da wainar da ya kai bakin sa jin maganar da mahaifin na shi yayi, har ya na kwarewa. Baba Anas bai kula da kwarewar da Saifullahi yayi ba, ya kara da


"Matar ka tana zaure, ka taho maza ka yiwa Baban Sasa dalilin hana ta zuwa makarantar da ka yi har tsahon kwana uku, da kuma dalilin kwace wayar ta da ka yi, mugu azzalumi! "


Har ya juya zai tafi ya dawo, ya na mai nuna sa da dan yatsa ya ce


"Ka tabbatar ka na da kwakkwarar hujja na aikata wannan zalincin, ka da ka manta na ɗau alkawarin yanda ka yiwa Amatullah kwatankwacin yanda zan yiwa uwar ka...."


Furucin yayi daidai da fitowar Hajiya daga uwar daka, ta na mai sallallami ta ta ke tambayar Baba Anas ko lafiya.


Saifullahi ya nuna da danyatsa ya ce
"Ga ki ga shi ai! Ka da ka sake ka kara minti biyar cikin gidan nan! Ka fito maza ka same mu!"


Ya juya ya fita a fusace. Saifullahi ma aje abinci yayi ya biyo bayan sa, Hajiya na tambayar ba'asi ya ce da ita ta jira zai mata bayani.


Shigar sa zauren ya tadda Amatullah zaune kusa da Baban Sasa har lokacin ba ta dena kuka ba. Bakin ciki da takaicin ganin ta ne ya tokare ma sa ƙirji, Baba Sasa kuwa bin shi yayi da kallo mai wuyar fassara. In da Baba Anas ke bin shi da harara. Kusa da Amatulah ya tsungunna, cikin nuna kulawa ya ce


"Amatullah me ya faru? Me ya sa ki ka zo gida ki dagawa Baban Sasa hankali? Ba kya la'akari da rashin lafiyar shi ......"


"Ungo nan!"
Baban Sasa ne ya masa dakuwa, kana ya kara da
"Kai din ka yi la'akari da rashin lafiyar ta wa ne da za ka hana diyar mutane zuwa makaranta? Akan wani dalilin ma?"


"Ban fa hana ta zuwa makaranta ba Baban Sasa....."


"Wallahi ya hana ni, rabona da makaranta kwana uku kenan!"


Kallan sa su ke in da yayi kasa da na sa kan.
"Yau da na tambaye ka na ina yarinyar nan ta ke ina ka ce ka baro ta?"


Baban Sasa ya sake tambayar shi, shiru ka ke ji Saifullahi ya kasa amsa masa.


"Shirun da ka yi ta tabbatar mana da gaskiyar Amatullah, menene hujjar ka?"
Shiru ka ke ji, duk bakin Saifullahi yau Amatullah ta daure shi da jijiyoyin sa, bai taɓa tsammanin za ta masa haka ba.


"Tun da shi ya ka sa amsa mana, ke Amatullah sai ki fada mana, a wani dalili ya hana ki zuwa makaranta?"


Cikin faduwar gaba Saifullahi ya daga kai, ya kai kallan sa ga Amatullah, ita ma din kallan sa ta ke. Idanun sa cike da magiya ya ke duban ta, cikin dabara ya dan girgiza mata kai alamar ta rufa masa asiri. Amatullah ta kawar da kan ta da sauri.
"Ke mu ke sauraro Amatullah, kada ki ji komai ki faɗa mana gaskiya, idan ba ki faɗa mana damuwar ki ba wa za ki faɗa mana"
Cewar Baba Anas wanda ya lura da irin kallan da Saifullahi ya ke mata. Murya sanyaye ba tare da ta sake yarda sun hada idanu da Saifullahi ba ta ce


"Wai cewa yayi....dama cewa yayi sai an zubar....."


Nauyi ya sa ta kakare ta kasa karasa maganar, Saifullahi kuwa kallan ta ya ke cikin fargaba, cikin ran sa ya ke


'ashe yarinyar nan ba matar rufin asiri ba ce!!'


"Sai an zubar da me?


Baba Anas da ya fara dago jirgen ne ya tambaye ta, cikin adduar Allah ya sa zatan shi ba daidai ba ne


"Juna biyun da na ke dauke da shi......"


"Laa ilaha illa Allahu Muhammadu rasulillahi sallallahu alaihi wasallam!!!"


Baba Anas ne ya doka Salati, in da shi kuwa Baba Sasa hannun ya sa bisa kirjin sa tsabagen yanda maganar ta dake shi.

"Kai Saifullahi ba ka da daraja! Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun"


Faɗin Baban Anas cikin jimami, shi kuwa Saifullahi ji yayi kamar ya rufe Amatullah da duka tsabagen sabon tsanar ta da ya ji ya mamaye zuciyar shi. Kai a sunkuye ya furta


"Ba wai na ce a zubar da cikin ba ne dan wani mummunar manufa, gani na yi fama ta ke da makaranta yanzu aka ce ta yi nauyi ko ta haihu wahala za ta sha, ita a wahale abin da ta haifa a wahale karshen ta ma karatun na ta ya lalace........"


"Ungu nan!"
Baban Sasa da har yanzu hannun sa ke bisa kirjin sa ne ya katse shi ta hanyar masa dakuwa.


"Dan tselan uwa kai!!! Ka damu da makarantar ta shi ne ka hana ta zuwa makaranta har tsahon kwana uku? Yau na yi danasanin aura maka yarinya mai daraja irin Amatullah, da gaskiyar ka Anas wannan yaro be da daraja! Ashe dan aure zai guji dan sa na aure....? Har ka hana yar mutane zuwa makaranta saboda ta ki aikata mugun nufin ka!! Wannan rayuwa ina za ta kai mu....... "


Baban Sasa ya fashe da kuka. Hakan ba karamin tadawa Amatullah hankali yayi ba, shi kuwa Baba Anas daɗa hasala yayi in da ya rufe Saifullahi da zagi ta inda ya ke shiga ba ta nan ya ke fita ba. Sai da aka dau wasu mintina kafin a samu Baban Sasa ya yi shiru.
Ya na mai share hawaye da hannun rigar sa ya ce


"Wallahi Saifullahi ka ba ni kunya, ka ci mutuncin zumunci! Albasa ba ta yi halin ruwa ba"


"Allah ya ba ka hakuri Baban Sasa, na yi kuskure ina mai neman afuwan ku"


Cewar Saifullahi, cikin ran sa kuwa lissafin yanda za mayarwa da Amatullah kwatankwacin tozarcin da ta masa a yau, dan gani ya ke duniya ba shi da makiyi da ya wuce ita.


"Wallahi, wallahi, wallahi ba ka bi na bashin rantsuwa ciwon kai idan Amatullah ta yi a sanadiyar cikin nan, kuma ya zamanto kai ne sila Allah ya isa ba zan kuma yafe ma ka ba!"


Baba Anas ya furta ya na mai nuna shi da dan yatsa. Kana ya kara da
"Makaranta wajibi ne, ko da wasa kada ka kuskura na ji ka sake hana ta zuwa makaranta, wallahi sai na tsine maka Saifullahi!"


A firgice ya dago ya na duban Baba Anas, in da ya girgiza masa kai cikin jaddadawa ya ce
"Kwarai da gaske! Kalle ni da kyau! Ba ka isa ka shiga tsakanin mu ba, ba isa ka ɓata zumuntar mu ba, ka yi kaɗan! Ilimin ka da wayon ka su amfana ma ka da komai ba! Allah wadar da ilimi irin na ka! A sanadiyar ka mahaifina ya zubda hawaye wanda ni ina ɗan sa ban saka ya zubar ba, sai kai jika! Allah wadar na ka ya lalace. ... "


"Ah ah Anas kada ka masa baki, yanzun ma yaya bare kuma ka masa baki! Ace ɗan sunnah ya ki ɗan sunnah?" Cewar Baban Sasa, "kai Saifullahi ka ba ni kunya, albasa ba ta yi halin ruwa ba!"


Saifullahi da ya gama haɗa zufa faɗi ya ke
"A yi hakuri Baban Sasa, in sha Allah za a gyara"


"Ina wayar ta da ka karbe"


"Dama ba karbewa na yi ba, sabuwa na yi niyar siya mata, Amma in sha Allah zan mayar mata da kayan ta"


"Eh ka gaggauta mayar mata da shi! Yanzu karfe nawa ki ke da lecture?"
Baba Anas ya tambayi Amatullah, ta wutsiyar idanu ta dubi Saifullahi, ganin yanda ya ke kallonta ta kasan idanu cike da tsana ya sanya ya yin karya, ta ce


"Dama na safiya ne, kuma lokacin ya kure yanzu, sai dai gobe idan Allah ya kai mu"
"Allah ya kai mu, kai ka ji Saifullahi gobe ta na da makaranta, ka kai ta, ka kuma dauko ta, kuma juna biyu in ka ga ba ta haife shi ba toh Allah ya rubuta dama ba zai zo duniya ba, Amma ciki dai sai ta haife, ta shi ki shiga ciki Allah ya maki albarka"


Dama umarnin da ta ke jira kenan. Cikin sauri ta tashi ta shige ciki, nan ta bar Saifullahi gaban su Baban Sasa har lokacin ba su daina masa faɗa ba.
[3/23, 8:42 AM] Zuraiyah Zuzu 🌟: TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀
✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL


BABI NA ASHIRIN DA HUDU


Gwaggo ta yi mamakin ganin ta dan a tunaninta Amatullah na makaranta. Kamar yanda ta faɗawa su Baban Sasa haka ta labartawa Gwaggo. Sam Gwaggo ba ta ji daɗin yanda ta yiwa Saifullahi ba, a cewar ta me ya sa ba ta fara faɗa ma ta ba.


Hajiya kuwa idan ran ta yayi dubu ya baci musammam yanda Baba Anas ya haɗa ta da Saifullahi ya mu su wankin babban mayafi. Bayan fitar Baba Anas Hajiya ta dada jaddawa Saifullahi maganar auren Ayush, ta ba shi shawarar ya fito fili ya shaidawa su Baban Sasa muradin shi na kara aure.


Sai da yamma likis Amatullah ta yiwa Gwaggo sallama ta koma gida dan kuwa mijin na ta tun azahar ya bar gidan. Haka ta wayi gari ba tare da ta sanya shi a idanun ta ba, sai gani ta yi ya aje mata kudi bisa centre table tare da yar takarda wanda aka rubuta


"Jikar Baban Sasa ina da tabbacin wannan zai kai ki makaranta ya dawo da ke"


Ko da ta dirga da gaske zai kai ta din ya dawo da ita, sai dai iyakan abin da zai mata kenan, babu batun kudin cin abinci.


"Oh ni Amatullah ciki ya jawo min zama da yunwa, amfanin sana'a kanan! Allah na rokeka ka ganar da miji na"


Cewar Amatullah yayinda ta zura kudin cikin jakar ta. Dakin Saifullahi ta je, kofa a rufe, da kwankwasa ta ji shiru sai ta yanke hukuncin kila ba ya ma gidan. Bayan ta tabbatar ta aje masa komai na karin kumallo ta ɗauki hanya.


Saifullahi kuwa tun sassafe ya ɗauki hanyar Abuja domin karbar offer din aikin da ya samu a ministry of power and housing a matsayin injiniya. Ya doka sammako ne ba dan komai ba sai saboda ganin Amatullah da ba ya son yi, dan gani ya ke idan su ka hadu Allah kaɗai ya san yanda zai kasance tsakanin su tsabagen haushi da tsanar ta da ya yi.


Ranar da yunwa Amatullah ta wuni, in da ta yi danasanin rashin kullo wani abinci da ba ta yi daga gida ba. Ganin abincin Saifullahi yanda ta barshi ya tabbatar mata Saifullahi ba ya gida. Cikin sosawar rai da damuwa ta shiga kiran wayar shi, Amma babu amsa har ta hakura. Abincin na shi ta ci, da niyar girka ma sa wani. Hakan ko ta yi amma har bayan Isha'i babu Saifullahi, ta fara tsorata ta na kokarin kiran Baban Sasa sai gashi ya dawo.


"Sannu da zuwa ya Saifullahi"


Cewar Amatullah in da ta tashi ta na kokarin karbar jakar hannun shi. Hannu ya daga mata cike da hantara ya ce


"Ke tafi can!! Wa ya ce mi ki ina bukatar sannun ki bare ki karbi jakar hannu na? Salon ki ƙala min sharri gun Baban Sasa ki ce na haɗa ki da jaka mai nauyi ɗan gwal din na ki ya zube?"


"Ya Saif...."


"Yiwa mutane shiru dallah!"
Ya tsayar da ita ta hanyar daka mata tsawa. Shiru ta yi tana duban shi har ya shige dakin sa. Yanda ta jera masa abinci haka ta sake kwashe su da safe, kamar jiya yau ma ya aje mata kudin mota babu na abinci. Haka ta ɗauki kuɗin ta na mai rokan Allah ya sa ya gane, dan kuwa dai ba karamin kewan mijin ta take ba, yanda ya kaurace mata ba ta jin za ta iya jurewa. Karin kumallan da ta yi musu ta ɗan ɗiba cikin yar karamar kula ta saka a jaka, dan kuwa jiya ta ji a jikin ta.


Haka rayuwa ta kasancewa Amatullah har tsahon sati guda suna zaman doya da manja. Ranar da ya kaiwa Baban Sasa offer letter ɗin shi ranar ya masa batun karo auren da ya ke son yi. Baba Anas wanda ya zo ya tadda Saifullahi na shaidawa Baban Sasa lamarin ne ya so ya hana. A hasale ya ce da Saifullahi
" Shin har yaushe ka yi auren da za ka zo mana da maganar kai gaisuwa wajan wata kuma? Kai mai gudun haihuwa ina kai ina kara aure?"


Shiru Saifullahi yayi ya na mai dukar da kai. Duk da maganar ta sosawa Baban Sasa rai, sai ya kawar da san zuciya ya na mai murmushi ya ce
" Ai ina ga Anas zai fi kyau mu kalli wannan magana ta shi ta fuskar arziki, ka ji dai yace yarinyar nan tun kafin auren shi da Amatulah su ke tare, duk da kuwa ya san da maganar alkawarin da na ɗauka, kuma gashi yanzu ya sami aiki Alhamdulillah, kuma karin aure abu ne da Allah ya halatta mana, fatan mu Allah ya sanya alkhairi"


Farin cikin ran Saifullahi ba ya misaltuwa. A lokacin ya ji duk wani bakin cikin Amatullah da ya kunsa sanadiyar kawo shi kara da ta yi ya gushe. Ta je ta yi ta haihuwa ta lalace tunda zai auri Ayush din shi ya more rayuwa.


"Sai ka shaidawa Anas sunan mahaifin yarinyar da unguwar da su ke dan a yi bincike ko cikin satin nan ko? Idan Allah ya sa aka sami yanda ake so zuwa karshen wata sai a kai gaisuwa kamar yanda ka bukata"


Cewar Baban Sasa ya na mai duban Saifullahi da farin ciki ya bayyana karara a fuskar shi.


"Toh Baban Sasa na gode kwarai Allah ya kara lafiya, bari na je na rubutu yanzun nan ma"


Cike da annashuwa ya tashi ya shige ciki ba tare da ya tsaya jin amsar Baban Sasa ba. Baba Anas na mai girgiza kai ya ce
"Ka ga yanda yaran nan ya ke rawan kai! Allah ya sa ba lasisin wulakanta mana diya ya samu ba"


Baban Sasa na mai jinjina kai ya ce
"Ko shakka ba na yi Saifullahi ba zai wulakanta Amatullah ba, Amma tun ranar da Amatulah ta kawo karar sa wajan mu, na dan yi danasanin auren nan, Allah ya sa karshen danasanin kenan"


"Amen dan son Rasulillahi"


Cewar Baba Anas. Kamar yanda ya ce ba a jima ba ya kawo takarda mai ɗauke da sunan mahaifin Ayush da sunan unguwar da su ke a Kano ya bawa Baba Anas kafin ya mu su sallama ya tafi. Ranar ba Saifullahi ba hatta Hajiya wuni su ka yi cikin farin ciki.


Amatullah kuwa ko da ta dawo daga makaranta a gajiye, gashi zuciyar ta na tashi ta yi amai ranar ya kai su uku, gashi ko ta yi girki ma ba ci Saifullahi ya ke yi ba sai ta yi kwanciyar ta falo. Nan bacci ya fara ɗaukar ta sama sama. Kamar daga sama ta ji ana tashin ta.


Cikin wannan hali Saifullahi ya dawo ya tadda ita. Ganin babu kular abinci ya tabbatar mishi cewa yau ba ta kawo ma sa abinci ba yanda ya saba gani, kai tsaye kitchen ya nufa ba dan yana jin yunwa ba, sai dan ya tabbatar da abin da ya ke zato. Aikuwa dai zatan shi ya tabbatar ba ta yi girkin ba. Falo ya sake dawowa ya na duban ta. Yanda ta yi rashe rashe ta na bacci hankalin ta kwance ba karamin kular da shi ta yi ba. Wato ta samu hutu ta dena girki tunda ba ya cin abinci maimakon ta zo ta lallabe shi ta bashi hakuri ganin ya dena cin abincin ta yanda yayi zato. Ransa bai kara baci ba sai da ta gyara kwanciya ta na mai ajiyar zuciya yayinda rigar jikin ta ya dan daga, dan shafaffen cikin ta ada wanda ya dan tasa yanzu ya bayyana gare shi, kallan cikin ya ke cike da takaici ya san nan da wani dan watanni cikin zai zama kato kamar kwarya, duk wannan shape din na ta ɓaci zai yi ta koma kamar buntuntuna.


'gwara ma na aje girmen kai na more rayuwa ta kafin cikin ya girma ta zama mara fasali!'


Cewar Saifullahi cikin ran sa yayinda sha'awar ta ya taso masa har cikin ran sa. Dakin sa ya nufa yayi wanka sannan ya fito. Nan ya tadda ta tana ta baccin ta har lokacin ba ta tashi ba. Cikin takaici ya shiga kiran sunan ta


"Amatullah! Ke Amatullah!!"


Cikin magagin bacci ta ke duban Saifullahi da ya ke tsaye gaban ta


"Malama ina abinci na?"


Tambayar da ya jefe ta da shi kenan. A hankali ta murje idanu, kana ta tashi zaune duk da jirin da ke dibar ta. Kallan sa ta ke cikin nuna rashin fahimtar maganar da ya furta mata. Ganin haka ya sake faɗin


"Kin dena ji ne? Na ce ina abinci na?"


Sai da ta yi hamma, ta na mai rufe bakin ta da tafin hannun ta sannan ta ce


"Ganin ka dena cin abincin ne gashi kuma ba dadi na ke ji ba ya sa ban dafa ba Ya Saifullahi"


Amsar ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login