Showing 90001 words to 93000 words out of 98809 words

Chapter 31 - TAZARA COMPLETE by UMMU-ABDOUL & KHADIJA SIDI.txt

away from you kasancewar sai kin gama idda"


Cikin zuciyar ta fadi take
'na kusa gama Idda Dee, na yi period har sau biyu bayan mutuwar aure na, na ƙarshe nake jira'


Azahiri kuma shiru ta yi masa, sai murmushi kawai ta ke tamkar ya na ganin ta


"amma abin na neman rikita tunani na, ba na so na rasa ki a karo na biyu duk da dai ban sani ba ko kina da wanda ki ke so already......."


Ji ta yi kamar ta na jiyo bugun zuciyar ta tsabagen yanda gaban ta ke faduwa, idanun ta runtse yayinda murmushi ya bayyana a fuskar ta Jin Dee ya ce


" Idan ma akwai, I will still fight for sai in da karfina ya kare, please let me know idan kin gama idda sai na zo mu yi magana idan kin amince sai na tunkari tsoho mai ran karfe da sojoji na, I love you Amatullah, I still do. Allah ya tashe mu lafiya"


Ya kashe wayar. Wani irin daɗi ne ya ringa ziyarta zuciyar Amatullah yayin da maganar Dee ke mata shawagi cikin kwakwalwar ta


"I love you Amatullah, I still do"


Tun bayan rasuwar Emjay Amatullah ba ta sami baccin kirki ba sai a daren ranar. Ta yi bacci mai nishadi, cikin dare ta tashi ta yi nafilan dare ta yiwa Emjay addua tare da neman taimakon ubangiji akan maganar Dee.


****
Kamar yanda Amatullah ta tashi cikin walwala, haka Aysuh, dan kuwa ta samu Jamila ta turo mata maganin nan fargaban kar Saifullahi ya mata bazata irin daren rannan ya kau, dan tun ranar ba ta kara yarda sun hada shimfida ba.


Gogan na ta kuwa tun da garin Allah ya waye ya je kofar gida ya zauna, ya kasa ya tsare ya na jiran fitowar Amatullah ko ya ganta ya sami sanyi cikin ran sa.
Ile kuwa sai gata ta fito cikin shigar nan nata da ta saba. Ganin ta ya tashi da sauri ya na faɗin


"Amatullah an fito?"


Fuskarta babu yabo ba fallasa ta amsa da
"Eh, ina kwana ya Saifullahi?"


Ya na murmushi jin dadin yanda ta amsa masa ya karasa gaban ta, tare da faɗin


"Lafiya lau, kin tashi lafiya? Ya karin hakurin na mu?"


"Alhamdulillah"


Ta amsa a takaice. Saifullahi be gushe ba ya ce


"Amatullah ina so ki san na yi matukar bakin cikin rashin ɗan mu, Amma babu komai Allah da ya karbi Emjay zai ba mu wani in Sha Allah"


Daga idanu ta yi ta kalle shi jin kalaman shi na karshe, ganin yanda ta ke kallan sa ya gyara tsayuwa ya ce


"Wato Amatullah ina so ki yi hakuri ki mance rayuwar da mu ka yi a da, ki sani cewa na yi nadamar duk kurakurai na, haka kuma na yafe na ki kurakuren, ina fatan za ki yafe nawa, ya kamata mu sasanta mu gyara zumuncin mu, abin da ya wuce ya wuce....."


Fuskarta ɗauke da murmushi irin na ya ke ta ce


"Ya Saifullahi na makara, bari na tafi makaranta dan Allah"


"Oh maganar tawa ba ta da muhimmanci Amatullah?"


Kai ta girgiza tare da faɗin
" Ko kusa ba haka na ke nufi ba"


Amsar na ta ya bashi damar faɗin
"Na sani Amatullah, na san ki na so na, kamar yanda ni ma na ke son ki, duk abin da ya faru tsakanin mu sharrin shedan ne"


Nan zaton Amatullah ya tabbata, na Saifullahi ya ɗan fara samun matsala sanadiyar rikicin matar shi, dan shi ne kadai bayanin yanayin da ya ke ciki. Sai a sannan ta lura da lalacewar da yayi, yayi baki ya rame. Ta na mai kallan agogan hannun ta ta ce


"Ya Saifullahi na makara, bari na tafi"


"Toh ko na sauke ki ne......?"


"Toh tantabara uban Alkawari! Idan ka gama yamadidin ka zo ina jiran ka!"


Cewar Ayush, wacce ta leko ko mayafi babu bare hijab sanye cikin kananan kaya riga da siket. Hannun ta rike da kugu. Kallo ɗaya Amatullah ta yi mata cikin ran ta tace


'eh lallai wayayye sai wayayyiya'


A zahira kuma kallon Saifullahi ta yi, wanda kunya da takaicin Ayush ya lullube shi kamar kasa ta tsage ya shige, ta ce


"Ah ah ba dumuwa, zan tafi kawai, na gode"


Ta juya ta yi tafiyar ta, ta na jiyo Ayush na faɗin
"To ko za ka bi ta ne? Ina ga kai ka ce bagidajiya ce amma ji yanda ka ke makalkale ta kamar bunsuru!"


A fusace ya nufota ya na fad'in
"Ni ne bunsurun Aisha? Me ya sa ba ki da mutunci ne ke"


Ayush ta shige ciki da sauri Saifullahi ya bita ya na faɗa tamakar mahaukaci. Jama'ar gidan har sun saba da ya wuce sai a bishi da zunde da baki, su Baban Sasa kuwa suna sane su ka masa kunne uwar shegu, babu mai shiga lamarin sa tun ranar da yayiwa baban Sasa dibar albarka har ta kai shi ga kwanciyar abisibiti.


***


Hutun mid semester ta dawo bayan sun shafe sati tara suna karatu,ganin zarya daga amaru ba zai fishe ta ba ya sa ta koma wajen mimi suke zaune a ɗakin ta, sosai ta ke jin sassauci na damuwar rasuwar Emjay, da taimakon Mimi, da addu'a har ma iyayenta ta samu ta ɗan ribaci damuwar.


Zaune take tana taya Mama gyaran Alayyaho yaro ya shigo ya sanar mata da saƙon Baban Sasa. Ba ta kawo komi ba ta isa gareshi amma ganin Saifullah, Baba Anas, Baba Salihu da Baba Zubairu zaune ya sa ta ɗan sha jinin jikinta.
Gaida su tayi sannan ta samu waje ta zauna cikin zulumin kiran da ake mata.


"Amatullah!" Baban Sasa ya kira ta ya na mai kallon ta.


"Na'am" Tace cikin sanyin murya.


"Mijinki ya zo ya same mu nan ya ce ya maida aurenku, kamar yadda musulunci ta bashi damar maida aurenku. Ki yi hakuri, ki rungume ƙaddararki ki cigaba da biyayya. Ubangiji Allah ya miki albarka ya dubi gabanki da bayanki" Baban Sasa ya ce yana mai yin fuska irin na tausayi da rokon alfarma ta amshi bukatarsu.


Shiru ya biyo bayan wajen, murmushin da ke fuskar Amatullah ya sanya ma Baban Sasa saukin raɗaɗin da yake ji na ganin kamar bai kyauta mata ba, don shi burinsa ɗaya ya buɗe ido ya ga Amatullah da Ɗan Yusuf a matsayin ma'aurata, ɗazu kamar ya taya ma Dee da ya kawo masa ziyara amma baya son abin da zai sa a gaba ya kalli Amatullah da wannan duban, hakan ya sa ko da wasa bai taɓa yi ma Dee yusuf maganar ta ba shi ma bai masa ba.


Bayan fitar Dee ne Saifullah ya shigo masa a fujajan ya sanar masa ya maida auren Amatullah, tunda yana da yaƙini ba ta fara jini ba, yanzu kila ta fara tun da ba shayarwa take ba. Bai amsa masa ba sai da ya tara iyayensa sannan ya aika a kira Amatullah.


"Yanzu sai ku natsu ku fahimci juna tare da tsaida ranar tariya" Baban Sasa ya ƙara ganin tayi shiru tana murmushi.


"Baban Sasa ai na fita idda tun sati uku zuwa huɗu da suka wuce" tace tana sunkuyar da kai haɗe yin murmushi mai sauti.


Ajiyar zuciya Baba Salihu da Baba Anas su ka yi a tare.
"Ƙarya ta ke wallahi Baba, ai mace bata al'ada in tana shayarwa kuma bai isa a ce tayi tsarki uku bayan rasuwan Emjay ba" Saifullah ya ce a rikice.


"Na rantse da Allah" tace cikin ƙara gaskata kanta.


"Baba a kira Mama ita ce shaida, tun Emjay na da wata shida na fara, kuma ban taɓa tsallake wata ba" tace tana mai neman agajin Allah don gaba ɗaya bata yi tunanin zai ƙaryata.


"Kwantar da hankalinki Amatullah, rabu da shi da guntun jahilcin da ke ɗan tafiya da shi" Baba Anas yace yana mai jan tsaki a ƙarshe.


"Ke haka ake yi ba sanarwa, ai sai ki faɗi gudun faɗawa halaka" Baban Sasa ya ce yana mai jin wani iri a zuciyarsa, ba zai ce yana cikin farin ciki gaba ɗaya amma tabbas ya dawo daga rakiyar auren Saifullah da Amatullah.


"Yanzu ai shike nan, tun da kin gama idda ke ce ke da damar zaɓa ma kanki miji, muna masu baki shawara da ko ji tsoron Allah yayin zaɓenki. Allah ya tabbatar da Alkhairi" Baba Anas ya sake faɗi, nan saura duk suka mara masa baya.


Mutuwar zaune Saifullah yayi, ya rasa ina zai tsoma kansa, kallon su yake kamar mai neman ɗauki. Gaba ɗaya rayuwa ta tsaya masa chak. Ta ina zai fara, ya san ba yanda za a yi Amatullah ta saurare shi, kamar ba wata hanyar da zai sa a mata dole.
Hakan ya sanya bai ko san sanda Amatullah ta fice daga ɗakin ba, dawowa yayi daga duniyar tunani ya iske babu Amatullah ba mahaifinta a ɗakin.


Ba ƙaramin natsuwa ta samu ba ganin babu wanda ya tursasa ta akan amince ma Saifullah, da farin ciki ta baro ɗakin, ba ta yi tafiya mai nisa ba Mahaifinta ya tsaida ita, shi kanshi yayi farin ciki da ganin farin ciki kwance akan fuskar ƴar sa.


"kiji tsoron Allah Amatullah, in kin tabbatar da saki uku ya miki ki sani babu sauran halaccin zama tsakaninku har sai kin yi wani auren, amma in dai shi ke da gaskiya kiji tsoron Allah, kada ki haramta masa abin da Allah ya halalta masa, babu mai miki dole" yace mata suna masu jerawa zuwa sashin su.


"Wallahi Babanmu sau uku yana furta cewa ya sake ni" tace cikin shagwaɓa.


"toh shi kenan. Allah yayi albarka" yace yana murmusa mata.


"Aameen Yaa Rabbi"


***


Tun kusan sati biyu da ya wuce ya kamata Ayush ta ga period din ta, Amma shiru ta ke ji, abu tun ba ya damun ta har ya fara ba ta tsoro. Babu shiri ta kira Jamila ta shaida mata halin da ta ke ciki, ta kare da


"Wallahi idan har cikin Saifu na ɗauka sai na zubar!"


"Dole ki zubar Ayush, ko ni ba zan ba ki shawarar haihuwa wannan gidan en kauyen ba!"


Cewar Jamila cikin jaddadawa. Kana ta kara da
"Kin san Allah tun wuri ki nemi pregnancy test strip, da kin ga positive ki kira ni, kuma kar ki bari kowa ya sani, in da hali ma ki fita ki samo da kan ki"


Aysuh ta tashi cikin sauri kamar wacce aka tsikara, ta ce da Jamila


"Yanzu ma kuwa"


Ta kashe wayar. Cikin kankanin lokaci ta samu ta shirya, ta yi ficewar ta ba tare da ta faɗawa kowa ba. Sai da ta taka da kafar ta har zuwa titi sannan ta samu chemist ɗin da ta siya. Da kyar ta iya dawowa gida tsabagen gajiya. Sai kuma da ta dawo tsoro da fargaban result din ya sanya ta kasa yi nan ta ke, ta yanke hukuncin bari sai da safe ta na tashi daga bacci dama ya fi ba da sakamako mai kyau.


Daren ya mata tsawo sosai, a kan kunnuwarta aka yi kiran sallah farko, cikin sauri ta shiga bahaya ta yi fitsari tare da tsoma tsinken gwajin. Ganin yanda layuka biyu ke ƙara fitowa raɗa raɗa ya sanya ta firgita, Sam ta manta cewa sun yi da Jamila akan kada wanda ya sani.
"Wayyo! Saifullah ka cuce ni, Allah ya I'd shege tsinanne" ta ce iya ƙarfinta tana sakin robar fitsarin a ƙasa.
A firgice ya tashi ya nufota yana tambayar lafiya, ransa duk a jagule saboda tabbacin ahlin gidan sun gama jiyo ta.
Idanunsa suka fara sauka a tsinken gwajin sakamakon ya fito raɗoraɗo a kai, bai san lokacin da ya sa hannu ya ɗago ta tare da haɗa ta da jikinsa ba, dukansa take ta ko ina tana zagi don gaba ɗaya cikin da ta tsinci kanta da shi ya fi kibiya zafi a ƙahon zuciyarta.
[4/24, 12:28 AM] Zuraiyah Zuzu 🌟: [4/23, 6:30 PM] +234 809 229 4372: TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀
✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL


BABI NA TALATIN DA BIYAR


TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀
✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL


BABI NA TALATIN DA BIYAR


"Ban kyauta ba na sani Babe, kin dai san ke nake so, ki yi shiru ki faɗa min abin da kike so ayi, yanzu kina ihu cikin dare kowa zai san ciki gare ki kuma ba za mu iya ɗaukan ko wani mataki ba" yace mata cikin raɗa, sai a lokacin ta tuna zancen ta da Jamila, take ta haɗiye duk wani kuka da kururuwa da ya ke zuwa mata.


"Ba wai bana son haihuwa da kai bane honey pie, Kai ma ka san son da nake maka ya sa na bar kuɗi da jin daɗin rayuwa don na kasance tare da kai" tace ganin ya bata goyon baya, ita kanta ta san wasu abubuwan da take masa ne ya sanya ya ke mata abin da ya ke mata, itama ba yin kanta bane, shi ya kulle ta a akurki.


"Na sani babe, amma ai baki taɓa natsuwa kin min bayani ba, na taɓa hana ki abin da kike so ne?" ya sake fadi bayan ya janyeta daga bahaya zuwa cikin ɗakin ta su ka zauna a kan gadonta.


"Tell me what you want babe, your wish is always my command your highness" yace mata yana kallon cikin idon ta. Nan ya mata kwarjini sosai ta kasa cewa komi, shiru tayi ta sunkuyar da kai amma tunawa da tayi dama na zuwa ne sau ɗaya in ta wuce dole sai mutum ya jira wata.


"A cire cikin nan don Allah, mu jira har mu koma gidan mu, ka ga a gidan nan wace tarbiyya zamu ba yaya, ko mun yi a ɗaka da ya shiga cikin gida za a wargaza masa" ta faɗi a hankali. Kiris ya ƙunduma mata Ashar, amma ya danne saboda in ya biye mata da faɗa shi ke da asara in ta zubar.


"Haka ne kuma fa, kinga ban taɓa tunanin nan ba, yanzu dai ki bari sai mu kai ayi flushing din sa out, this week will be a very busy week Amma I promise you ba za a wuce next week ba zai bi ma kwararar" yace yana rungumarta, ji yake kamar ƙaya yake runguma a jikinsa, tunanin dole ya nemo yanda zai shawo kan Amatullah yake don tabbas itace macen rufin asiri macen arziki.


Lallashinta ya dinga yi yana mata alkawura na ƙarya da in da kan aurensu ne toh tabbas za su zama na gaskiya ne.
Kiran sallah na biyu ya tayar da shi daga gareta, alwala yayi ya gabatar da raka'atanil Fajr sannan ya wuce masallaci. Daga yanayin kallon da ya ga iyayensa na masa ya san tabbas sun ji muryar Ayush, addu'a yayi Allah ya sa Hakan ya sa su tausaya masa su maida masa da auren Amatullah.


***
Sati ɗayan da ya wuce babu abin da yake sai fafutukar son Magana da Amatullah, kasancewar ta koma makaranta ya sanya abin ya masa wahala. A tunaninsa hostel take, sai ya kwashi jiki ya je gaban Amina hall ko Ribadu hall ya zauna yana ƙirga masu shiga da fita hostel ɗin.


Ganin hakan bai cika masa burinsa ba ya koma zaman faculty of pharmaceutical sciences. Nan ma haka yake ƙarasa shawagin sa ba tare da ya ganta ba, sau biyu yana hango ta a aji suna ɗaukan darasi nan zai hakince ya jira amma kamar wacce ke rufe ido ba ya sanin lokacin da suke ficewa.


Asali duk zuwan shi Mimi ce ke ganinsa sai ta fitar da su ta wata ƙofar ba wanda ya ke jira ba.
"Ai nan gani nan bari malam" takance a ranta a duk lokacin da ta hango shi.


Ya kan kira Amatullah amma in zai kira sau ɗari ba ta ko ɗagawa, haka saƙonni daban daban na ban hakuri, soyayya da alkawari duk sai dai ta karanta ta share.


Yau ma kamar yanda ya saba ya shigo sashin na su, ya iske suna karatu, nan ya nemi izinin malamin akan yana son ganin matarsa. Amatullah bata an kare da shi ba sai ganin da tayi yana nuna ta da yatsa.


Nan malamin ya kalle ta ya ce " Oya Go and meet your husband" ji tayi duk wani bakin ciki ya taru ya tsaya mata a maƙoshi, niyyarta ta ƙaryata saninsa amma tunawa da tayi kallon matar aure ake mata har lokacin ya sanya ta mike jiki a sanyaye.


Tana fita ta tsaya a kansa ba tare da tace kanzil ba,
"Don Allah muje ki bani minti ɗaya kacal, don Allah ba don ni ba" yace kamar zai mata kuka. Da har za ta juya sai kuma wata zuciyar tace da ita ta bishi.


Sun Kai daidai matakalar benen da za ta saukar da su ƙasa su ka ci karo da Dee ya hawo kenan.
"Cutie ina zuwa ne haka, Prof ya fita ne" yace yana mai tsare ta da idanu yana mai isar da wani irin saƙo mai narka zuciya. Murmushi ta yi tare da raɓewa gefe, ita ba ta sauka ba ita ba ya juya ba.
Waigawa yayi ya ga Saifullah ya tsaya yana huci kamar kumurci.


Dawo da kallonsa yayi gareta ya na mai murmushin da ke rikitata ya ce
"okay Mamana" yace yana mai sunkuya mata kamar mai ladabi haɗe da nuna mata hanya ta wuce. Sai da ta zo daidai saitinsa sannan ya ce


"I love you"


cikin amon da hatta Saifullah da yaji sai da tsigar jikinsa ya tashi saboda sanyin da amon ya fitar.


Tsaki ya ja yayi gaba, Amatullah kuwa da yake jin kanta kamar wacce ke yawo a gajimare da kyar ta iya kai kanta ƙasan bene inda Saifullah ke tsaye.




"Kar dai ki ce iskancin da kike kenan a makaranta kina zubar da mutuncin hijabi" yace a hasale


"ka ga ai wainda ba sa son ganin iskancin ba su biyo ni ba, lafiya kake nema na"


Tace cikin tsiwar da ita kanta bata san tana da shi ba. Kallon ta yake cike da mamaki, don shi a iya zaman da su ka yi na shekara biyu a matsayin mata da miji zai rantse ko Yatsa aka sanya mata a baki furzarwa za ta yi ba za ta ciza ba.


"Ki dubi girman Allah ki amincewa son da nake miki, Amatullah wallahi duk lalacewana ba kamar tubabbe ba wanda ba tabbas a musuluncin sa, wallahi Amatullah warin Arnanci yake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login