Showing 63001 words to 66000 words out of 98809 words
Chapter 22 - TAZARA COMPLETE by UMMU-ABDOUL & KHADIJA SIDI.txt
duk a tunanin ta tsabagen haushin involving kan ta da ta yi cikin lamarin Amatullah da ta yi ne. Dan haka duk surutun ta sai ta sami kan ta da kame bakin ta. Haka su ka yi tafiyar kurame har su ka isa unguwar su Amatullah. Mimi na tambayar ta kwanar da za a shiga ta na fada mata shi kuma Dee na karya kan motar shi har su ka isa kofar gidan Amatullah, nan su ka yi kacibus da Saifullahi, ya fito daga gidan kenan ya ga wata hadaddiyar mota ta faka kofar gidan sa. Tuni ya shagala da kallon motor ya ma manta ya fito ne domin ya je gida ya shedawa Baban Sasa Amatullah fa ba ta dawo daga makaranta ba, gashi yayi neman duniya cikin makaranta har department din su amma be gan ta ba.
Hasken farin wata da kuma hasken fitar layin ne ya haske fuskar Dee da ke hakince gaban mota shi sam bai lura da Saifullahi ba, wanda ko a mafarki aka nuna masa Dee zai gane shi.
Ran Saifullahi bai baci sai da ya ga Mimi ta fito dauke da Emjay bisa kafadar ta, ta zo gidan baya ta budewa Amatullah wacce ta fito da kyar ta na faɗin
"Na gode sosai, madallah"
Dee wanda ya tabbatar da shi ta ke kai ya jinjina mata ta na mai sakar mata murmushin nan na sa mai kayatarwa. Duk abunda ke faruwa a kan idanun Saifullahi wanda ya cika yayi fal tsabagen wani bakin kishin da tun da ya ke a rayuwar sa be taba zatan ya na da shi ba.
Ita kan ta Amatullah sai a sannan ta lura da shi, ganin yanda ya hade girar sama da na kasa ya na huci kamar macici ya sanya Amatullah kokarin karbar Emjay daga hannun Mimi, ita kuwa ta ce
"Ah ah mana Maman Emjay bari na shigar mi ki da shi ai"
Amatullah na mai tasbihi da neman tsarin Allah daga halin Saifullahi wanda Sam bai lura da yanayin tafiyar da Amatullah ta ke yi ba tsabagen masifa ya rufe ma sa idanu su ka iso daf da shi, cikin sanyin murya ta ce
"Ya Saifullahi yi hakuri daga asibiti......!"
"Ke dallah yiwa mutane shiru!"
Saifullahi ya daka mata tsawar da ita kan ta Mimi sai da ta ja baya da sauri har ta na tuntube, Emjay tuni ya razana ya fashe da kuka, hakan ne ya ja hankalin Dee Yusuf, har ya sauke gilashin motar shi cike da mamakin abun da ke faruwa. Saifullahi wanda bai yi la'akari da ba su kadai ba ne ba, kuma a kofar gida su ke ya cigaba da bambami, ya na mai zargin Amatullah ta hanyar furta munana kalamai gare ta, fadi ya ke
"Macuciya! Azzaluma! Ashe da auren ki ba ki rabi da wancan arnan ba? Da auran ki kina bin namijin da ba na ki ba! Kin yi asara Amatullah......!"
"Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun, Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun, Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun!"
Iya ka abin da Amatullah ke iya furtawa kenan. Ita kuwa Mimi hankalin ta ne ya tashi, Ganin Dee ya fito daga mota a fusace ya tabbatar mata Dee Yusuf din ne arne kuma tsohon saurayin Amatullah da Saifullahi ya ke nufi, da sauri ta sha gaban shi ta na mai girgiza ma sa kai, idanun ta cike da magiya ta ce
"Dee I beg of you..Kar ka yi haka, kar ku tara mata mutane, she is ill for goodness sake! please ka koma mota, bari na kai ta ciki"
Saifullahi kuwa ya na huci ya ke fadin
"Ki bar shi ya karaso mana, me zai iya min kwartan banza kwartan hofi, ko da yake ku kwartanci a addinin ku ba komai ba ne, ita dai da ta ke musulma ita ta yi abin kunya....."
A fusace Dee ya furta
"Mimi!"
Mimi da idanun ta su ka cika da kwalla ta ce
"You're better than this, you can do better, please Dee"
Ya na mai jinjina kai ya koma mota, Mimi ta ja hannun Amatullah da tashin hankali ya sa dishi dishi ta ke gani. Allah ya so Saifullahi bai kai ga datse gidan ba su ka karaso, dan haka Mimi ce ta tura kofar gidan, hannun ta cikin na Amatullah su ka shige ciki suka bar Saifullahi tsaye ya na huci ya ke duban Dee da ya shige motar shi ya na mai dage gilashin mota.
Har ga Allah ya so yiwa Saifullahi dukan kawo wuka, Amma halin da Amatullah ke ciki, da kuma Mimi ya sanya shi zama cikin mota zuciyar shi na tafasa.
Ganin Dee Yusuf yayi banza da shi, ya sa ya shige ciki a fusace. A falo ya tadda Amatullah zaune, rike da Emjay da ke ta kuka amma ta kasa ko kallan sa bare ta kai ga rarrashi ko ba shi nono. Mimi da ke Allah Allah ta koma wajan Dee kar ya biyewa Saifullahi ta yi mata sallama, tare da bata hakuri sannan ta juya, ba ta kai ga fita ba ta ji Saifullahi ya ce
"Wannan yaron da ki ke rike da shi, ina kyautata zaton ba dana ba ne shi ya sa ki ka dage ba za a zubar da cikin ba, dan wancan kwartan na ki na waje ne...!!!"
Ba Amatullah ba ita kan ta Mimi a razane ta juyo ta na duban Saifullahi, Amatullah kuwa neman hawaye ta yi ta rasa, salatin ma ya kafe a bakin ta, duban shi kawai ta ke da idanun ta da su ka su ka yi jajur. Bai gushe ba ya kara da
"Ki hade na ki ya na na ki ki bar min gida, Ni Saifullahi na sake ki Amatullah, na sake ki! Na sake ki!"[4/1, 9:57 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼♂🤦🏿♀
✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL
BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI
kafin su samu farfaɗowa daga suman zaunen da su ka yi su ka tsikayo shi yana faɗin
"Sannan wallahi kar ki bari na dawo na isko ki a gidan nan, banza fasiƙa"
Wani irin abu ya tokare ma Mimi a wuya, ta na jin ana faɗin maza ba su da kirki ba ta taɓa yarda ba sai yau da ta ga zahiri.
Yanda Saifullahi ya gifta ta a fusace ya sanya Mimi jan gefe gudun kar ya buge ta. Ta koma wajen Amatullah ta na kokarin karɓan Emjay daga hannun ta ta ce
"Yi hakuri Amatullah, I don't even know what to say, da na san zuwa asibiti da zuwan mu gidan nan abin da zamu jawo mi ki kenan wallahi da ba mu zo ba, kin ce cousin din ki ne ko? Tashi mu kai ki gida kafin ya riga mu"
Maimakon ta sakar mata Emjay, sai daɗa riƙe shi ta yi gam. Ta na mai duban Amatullah da idanun ta da suka riga su kafe ta ce
"No Mimi, ba zan bi ku ba, ki tafi kawai"
"Why? Saboda me?"
Mimi ta tambaya cike da mamaki. Amatullah ta ɗaura Emjay kafadar ta, ta na mai jijjaga shi, cikin wani irin yanayi mai wuyan fassarawa, yanayi na tsantsan kunar zuciya ta ce
"Ya kira ni fasiƙa, ya shegentar da ɗan sa, duk dan a dalilin na shiga motar Dee, kuskuren shiga motar ɗan uwan ki ya janyo wannan kazafin a gare ni Mimi, yanzu sai na ƙara shiga ku kai ni gida? iyayen mu su gan na fito daga motar ɗan uwan ki? Ta Yaya zan wanke kai na?"
"Iyayen ki sun san wacece ke Maman Emjay, they know what their daughter is capable of doing saboda sun san sun bawa diyar su tarbiya mai kyau..."
"Hakan ya sa ba zan bari daidai da second ɗaya zargi irin wannan ya gifta a zukatan su ba, na gode Mimi.....I will find my way"
"Maman Emjay a wannan lokacin har kina tuna wani bayan ke, ba ki tunanin halin da ki ke ciki? you have to wake up and start loving your self" mimi tace tana mai danne takaicin da ya taso mata.
Ba ta san me yasa mata da dama basu damuwa da ƙaunar kansu ba, a dai barsu da son zuciya (selfishness) amma sam ba su san wani abu wai shi self love ba balle self esteem.
Amatullah na mai runtse idanu, murya can kasa ta ce
"Go ...... just go Mimi"
"I'm so sorry Amatullah"
Cewar Mimi kafin ta juya ta fita jiki a sanyaye. Sai bayan fitar ta Amatullah ta sami damar bawa Emjay nono, gaba ɗaya kwakwalwar ta ce ta daskare yayin da idanun ta ke kan Emjay wanda yana shan shanono ya na mai sakin ajiyar zuciya.
***
Yanda ya ga Mimi ta shiga motar ta zauna jiki sanyaye ya sanya shi faɗin
"How is she?"
"Very hurt....."
Cewar Mimi, kafin ta juya ta na kallon Dee, cikin neman bayani ta ce
"Menene dangantakar ku? What was she to you? Me ya sa mijin ta zai zarge ka da neman matar shi na aure? What is happening Dee?"
Ajiyar zuciya ya saki, ya na mai wasa da sitiyarin motar ya ce
"It's a long story Mimi, Zan ba ki labari. Amma zancen neman matar shi wallahi sharri ne irin na namijin da bai san ciwon kan sa ba, Amatullah is the most decent person I know in my life, please mu tafi kafin wannan jahilin mijin na ta ya dawo, wallahi zan iya bugun shi...."
"Ya sake ta!"
Cewar Mimi ba tare da ta kalli Dee Yusuf ba. Ji yayi kamar kunnen sa ne ke masa gizo.
"I beg your pardon!"
Cewar Dee cikin kaɗuwa. Mimi na mai jinjina kai yayin da hawaye ke zuba daga idanun ta
"Ka ji ni da kyau, an saki Amatullah, that useless person accused her of sleeping with you, kuma hatta Emjay ya ce ba ɗan sa ba ne, ɗan ka ne......"
"Waiyazubillah!"
Cewar Dee ya na mai doka hannu kan sitiyari. Mimi ba ta gushe ba ta kara da
"Ya ce kar ya dawo ya same ta, Amma ta ki yarda mu kai ta gida, Ni damuwa ta a yi clearing wannan misunderstanding ɗin kar ya je ya maimaitawa iyayen su abin da ya furta mata, I'm feeling very bad Dee, Ni na jawo mata, da na sani da ban ce mu je asibiti ba, da mu ka kira wayar shi bai ɗaga ba da mun hakura ta koma gida, da ban kira ka ba....."
Ta karasa maganar cikin shashshekar kuka. Motar ya kunna ba tare da ya tankawa Mimi ba, zuciyar shi ke tafasa yayinda ya ke Jin duk duniya babu jahili mara ilimi kamar Saifullahi ba. Motar ya ja, Mimi na tambayar shi ina za su je bayan sun bar Amatullah cikin halin haula'i, ya mata shiru. Tun ta na tambaya har ta gaji ta ma sa shiru ta zubawa sarautar Allah ido.
***
Saifullah kuwa ko da ya fice Amaru ya wuce, zuciyar sa in ban da ƙuna babu abin da take yi, hango Amatullah da Dee ya ke a shimfiɗa, tiryan tiryan idanunsa ke masa gizo da abin da kwakwalwarsa ke sauwara masa. Da haka ya isa gidan Jamoh.
Kamar yadda yake al'adar su yau ɗin ma zaune suke, su takwas ciki har da mahaifin sa da mahaifin Amatu. Bai tsaya rufe ƙofar motar sa ba ya isa garesu a firgice.
"Lafiya? Me ya samu Amatullah?" Baba Anas ya tarye shi cikin matsanancin tashin hankali.
"Baba Amatullah ta cuce ni, shege ta kawo min... " wawan marin da ya sauka a fuskar sa ya sa ya kasa ƙarasawa.
"Ko mutuwa na kunyan idon mahaifa balle kai sakarai gaja, kalli nan mahaifinta ne, kalle mu nan mu bakwai duk ba wanda zai yarda a ci zarafin Amatullah" Baba Anas yace cikin Dana sanin tambayarsa.
"Baba wallahi bata rabu da Arnen nan ba, yau a kan ido na ya sauke ta a ƙofar gidan aurenmu" yace yana sunkuyar da kai, nan gaba ɗaya su ka ɗauki salati.
"Saifullahi shin wani laifi Amatullah ta yi ma ka da za ka jefe ta wannan mugun zargi haka? Idan mai magana wawa ne ai majiyinta ba wawa ba ne"
Cewar Baba Zubairu cikin adduar Allah ya sa dai Saifullahi bai san abin da ya ke fada ma. Shi kuwa mahaifin Amatullah mutuwar zaune yayi duk da kuwa ko duka jikin shi kunne ne ba zai taɓa yarda da wannan maganar ba.
"Allah ya wadar na ka ya lalace! Saifullahi sakayyar da za ka yiwa zumunci kenan?"
Cewar Baba Anas wanda kunyar mahaifin Amatullah ya rufe shi, ji ya ke kamar kasa ta tsage ya shige.
Motar Dee da ya faka daga gefen su ne ya ja hankalin su, kallan motan su ke cikin jiran tsammani. Shi kuwa Saifullahi da ya san motar Dee ne, tsabagen idanun sa sun rufe be ma iya gane daga Dee sai Mimi ne tafe cikin motar ba, cikin farin cikin Allah ya kawo ma sa sheda har gida ya ce tsaya,
"Kun ga ni ko Baba, ga shi dai kun ga zahiri ya kawo ta har gida dan rashin daraja!"
Duka motar su ke kallo, da ya ke fitilar kofar gidan Baba Sasa ba ta da haske sosai dan haka ba su iya tantace wacce ke zaune gaban motar ba, shin Amatullah din ce kamar yanda Saifullahi ya ke jaddawa? Tambayar da ke yawo cikin kwakwalwar Baba Anas kenan. Shi kuwa mahaifin Amatullah adduar neman tsari daga abin da ke shirin faruwa ya ke, dan kuwa idan ya kasance Amatullah ce da tsohon saurayin ta zaune cikin motar nan, to lalle diyar shi ba ta ma sa adalci ba.
Mimi da tun isar su ta ke duban Dee ta ce
"Dee ina ne?"
"Gidan su Amatullah..."
Ya amsa mata a takaice, kai Mimi ta jinjin kafin ta ce
"Da gaske ne kenan you guys had a relationship? Oh Lord Jesus!"
Cewar Mimi ta na mai dafe kai, ba ta gushe ba ta kara da
" Ohh She is the one! That Muslim girl that made you......"
"Mimi babu lokaci, please za mu yi magana, for now you have to this for Amatullah, you call her a friend, da ke aka yi komai, kin ga wannan mutanen da ke zaune?"
Ya nuna in da su Baba Anas ke zaune
"I'm very sure uncles din ta ne, or maybe da Baban ta, ina wayar ki?
Jiki sanyaye ta ce
"Ga shi nan"
"Ina receipt din hospital bill da ki ka biya?"
Ta na mai dafe kai ta ce ya na jakar Maman Emjay.
"Na so ya na gun ki, but wannan ma zai yi, I know you're smart, I trust you, only you can clear Amatullah, please go and explain everything to them!"
Cikin karfin hali Mimi ta girgiza kai, kana ta ce
"Tare za mu?"
Dee ya girgiza kai tare da faɗin
"I don't need to be there, you can do it"
Kai ta girgiza alamar toh, kana tayi yunkurin buɗe motar.
" kun gani ko, har yanzu ta kasa fitowa tsabagen borin kunya" Saifullahi ya faɗi yana tashi kamar wani sabon hauka ya dumfari motar Dee.
"Idan ka ƙara taku ɗaya Allah ya tsine maka Saifullah" Baba Anas ya ce, wanda hakan yayi daidai da fitowar Mimi. Nan Saifullahi ya tsaya ya na raba idanu domin ganin Amatullah ta fito bayan Mimi, amma babu ita babu alamar ta.
Baba Anas kuwa da Mahaifin Amatullah ajiyar zuciya su ka saki a lokaci ɗaya, su na mai godewa Allah ganin watan Amatullah ce ta fito daga motar, maimakon Amatullah da Saifullahi ya ce.
"Haba Anas, wai duk gaskiyan nan da ke bayyane, me ze sa makamashin nan dawowa kofar gidan nan in ba dai akwai kamshin gaskiya a maganar Saifullahi ba? Ku duba da kyau ku gani wannan arnan nan ne dai cikin motar can" Baba Mahmuda ya faɗi cikin hasala.
Sallama Mimi ta musu duk da kuwa gaban ta na dukan uku uku, cikin girmamawa ta gaida su, su ka amsa suna kallon ta a kyamace.
"Yarinya ke kuma daga ina?"
Ba ta kai ga amsawa Baban Sasa ya aiko Hafiz da ya kai masa rahoton abin da ke faruwa da duk su shiga ciki. Dan haka duka su ka garzaya, Baban Anas ne kafin ya tashi ya dubi yarinya ya ce
"Za ki iya jiran mu yarinya?"
Mimi ta ce
"Eh Baba, dama na zo ne kan batun Amatullah ta nan can gida yanzu haka ba lafiya....."
"Amatullah ki ka ce?"
Mahaifin Amatullah wanda shi ma ɗin tsayawa yayi dan sauraron Mimi.
"Ai ina ga zai fi ita ma din ta biyo mu"
Cewar Baba Anas, ya na mai kallon Mimi ya ce za ki iya shigowa daga ciki. Baba Anas da Mahaifin Amatullah tafe, Mimi na biye da su haka su ka shiga ciki gurin Baban Sasa.
Nan su ka tadda su Baba Zubairu zaune, Baba Anas yayiwa Mimi wacce tun shigowar su Baban Sasa ya bi ta da kallan tuhuma, wuri da setin in da Saifullahi ke zaune taje ta ɗan raɓe. Su ma din waje su ka samu su ka zauna.
Baba Mahmuda da Baba Idris ji suka yi kamar su hau mimi da duka saboda kafiɗirinta.
"Me ke faruwa da kuke min tallan martaba a idon duniya, a'a kai!" Baban Sasa ya ce cike da takaici yana mai bin su da kallon tuhuma.
"Baban Sasa, ashe ɗan can ba nawa bane, ashe Amatullah ta daɗe tana cin amanar aure na Ban tashi sani ba sai yau, ashe shi ya sa lokacin da na ce a zubar da cikin ta ƙi amincewa saboda riban soyayya ne" ya faɗi ba tare da tunanin abin da yake faɗi ba sai da ya ga kallon da baba Anas ke watsa masa, bai gushe ba ya cigaba da fadin.
"Tun la'asar nake makarantar su don ɗauko su aka ce min ta tafi, wasu suka ce ba ta ma zo ba, na dawo gida shiru shiru kawai na fito na sanar da ku sai na ga wannan tsinannen tsohon saurayin ta kawo ta, yau dubun su ya cika" ya karasa maganar ne cikin dacin kishi. Salati Baban Sasa ya saka, ya na mai dafe kirji ya ke faɗin
"Kai Amatullah ta ba ni kunya, Amatullah ta cuce mu ta ci mutuncin aure!"
Mahaifin Amatullah ya sunkyar da kai cike da kunya da takaici. Ita kuwa Mimi jikin ta har rawa ya ke tsabagen yanda ta ke so a bata dama ta yi magana.
"Baba ban tari numfashin ka ba, zai fi kyau a bi wannan lamari daki daki a yi bincike