Showing 48001 words to 51000 words out of 98809 words

Chapter 17 - TAZARA COMPLETE by UMMU-ABDOUL & KHADIJA SIDI.txt

yace yayin da yake miƙa mata.


Ji tayi gaba ɗaya ba ta da wani damuwa, nan ta ƙara son mijinta, ta kuma so Baban Sasa don shi ya zama silar samun gatanta.


"Na Gode Saahib, Ubangiji Allah ya bar mu tare har a Aljanna" tace tana mai rungume shi.


Sati uku bayan cikar su shekara ɗaya yayi daidai da lokacin ganin baƙon watanta, amma shiru ake ji, ga duk wani alamu na zuwansa ta gani amma shiru babu shi babu alamunsa.


Inna Hafsatu ta kira ta faɗa mata, nan ta mata alkawarin biyowa in ta taso daga aiki.




"Alhamdulillah!!! Amatullah addu'ar mu ta amsu, bayan shekara ɗaya fa, Alhamdulillah!!" tace bayan ta ɗaga tsinken gwajin cikin da ya nuna Amatullah na ɗauke da shi, rufe fuska Amatullah tayi cike da jin kunyar innarta.


" Daina kunya, ciki da ubansa, kar na zama babbar kwabo da na yi ma Saifullah albishir" tace cikin dariya.


Nan ta bata shawarwari tare da mata addu'ar samun sauki wajen rainon ciki da haihuwa sannan ta tafi.


***


Faɗin irin ƙosawar da Amatullah ta shiga akan dawowar Saifullah wanda ya je Kano wajen Ayush. Ji tayi kamar ta masa waya don ta hango farin cikin da zai yi in ta faɗa masa.


Tashi tayi ta kimtsa tare da shirya masa abinci, sannan ta samu waje ta zauna tana duban agogo.


Biyar da minti shida ya shigo, nan ta rungume shi cikin tsantsan farin ciki.


Kallon ta yayi cikin murmushi yace
"Hala mafarki kika yi bazan dawo ba"


"Haba Saahib, kawai dai farin cikin samun ka a matsayin miji nake kullu yaumin" tace tana kanne masa idanu.


Sai bayan ya gama cin abinci ya miƙe ƙafa yana bata labari ne ta ɗauko masa tsinken da ba ta yar ba.


Kallon ta yake a sheƙe, cike da tuhuma da son musanta zargin sa, ganin yayi shiru ya sa tace


"Saahib duba fa, kyautar Allah bayan shekara ɗaya" tace tana mai tsananin farin ciki.


"Ni wallahi ban taɓa ganin Jarababba irin ki ba, har yaushe aka yi auren da za ki ƙunso ciki" yace a hasale wanda hakan ya sa ta yin mutuwar zaune.


"Saahib shekara ɗaya fa, ba wayonmu ko dabara fa" tace a marairaice.


"will you shut up!" yace cikin tsawa.


Hango ta haihu yake yi shike nan yan biyunsa zubewa za su yi, ita kanta buɗewa za ta yi, ba zai sake jin daɗin da yake ji ba, ga Alkawarin da ya tabbatar ma Ayush ita za ta fara haihuwa a gidansa.


"Allah ya isa! Allah ya isa Amatullah!! Me ya sa kika bari ciki ya shiga, muna zaman lafiya abun mu why? Why Amatullah" ya ce a rikice yana mai jifa da kofin tangaran din da ke kusa da shi.


Take ya tarwatse gaba ɗaya. Riko ta yayi idanunsa cikin nata ya ce
"kina so na?" bata iya amsawa ba sai gyaɗa kai da ta yi.


"Muje a cire abin nan, mu cigaba da rayuwar mu hankali kwance kinji" ji tayi gaba ɗaya ba za ta iya masa musu ba. Ta gwammace ta zubar da cikin, ta gwammace ta jira har zuwa lokacin da zai shirya haihuwa su haihu.


Ba musu ta tashi ta shiga daki ta ciro hijabinta.[3/15, 11:41 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀
✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL


BABI NA ASHIRIN DA BIYU


Ko da ta fito tashi yayi tsaye su ka fice, a mota ya kira Salis ko yana asibitinsa kasancewarsa likita ma'aikaci a asibitin gwamnati na Gambo sawaba, mahaifin sa kuma ya buɗe masa nashi a cikin GRA, mutane na son asibitin saboda kwarewarsu da kula da marasa lafiya.


Minti Ashirin ya ɗauke su kafin su ka isa Umjad clinic and maternity. A dirare Amatullah ta gaida Salis don cike take da waswasi duk da cewa a shirye take da ta yi komi don farin cikin mijinta. Ai ko ba komi Aljannarta na ƙarkashin ƙafafunsa ne, da wannan take ba kanta haƙuri da ƙwarin gwuiwa.


"Bari mu yi scan mu ga girman cikin don kamar ya fi wata ɗaya fa" Salis ya ce bayan ya ɗan dudduba ta.
"Kai likita ban son shegantaka, watan nan ne kawai ta yi ɓatan sa amma duk saura suna zuwa" Saifullah ya ce a ƙufule, shi kawai so yayi a mata allura ko ya bata kwaya ta haɗiya cikin ya zube.


"Engr. Ai wasu ma har su haihu su na yi, wasu in sun kammala wata ukun farko, wasu sai ya kai shida, amma mafi akasari daga ciki ya shiga wata ɗaya ko sati biyu yake ɗaukewa"
Da haka ya tura ta scanning wannan ake yi a wani sashi na asibitin. Saifullah bai yarda ta tafi ita ɗaya ba, tare su ka je bayan an tabbatar da a matse take aka sa ta hawa gadon gwaji.


"yaushe kika ce kin ga hailan ki ƙarshe, first date of your last period" ya ƙarasa cikin turanci ganin bata fahimci hausar ba, bai san cewa tsananin tsurewa ne da tunane tunane ya cika mata ciki.


" 5th August" tace kai tsaye


"Wow, Kuna cikin ƴan baiwa" ya ce yana kallon allon kwamfutarsa yana cigaba da dudduba ta, bayan ya gama ya fitar da sakamako ya basu don maida ma Salis.


"Ai na faɗi maka, kallo ɗaya na mata na san ya wuce haka, cikin ta satinsa goma sha biyar da kwana uku ko ba kwana uku (15weeks +/- 3days)" Salis ya faɗi yana mai addu'a a ranshi ko Saifullah zai canza shawara.


"Sai a burge shi kawai Salis, ni dai ya fita, ban shirya zama uba ba, beside kwatakwata yaushe aka yi auren, ace mace daga an kalle ta se ciki" ya ce cikin fushi yana mai bankawa Amatullah harara. Ganin haka Salis ya bashi takarda ya sa hannu, itama ta sa hannu akan da amincewarta za ayi.


"Za ka iya zama da ita sanda za a cire....."


"Ina ba zan iya ba, just let me know idan ka gama"


Yana gama fadin haka ko kallan Amatullah wanda idanun ta su ka ciko da hawaye bai yi ba, ya sa ƙafa ya fice.


Dakin da aka tanada na musammam Wanda ake kira da Gynae Emergency Room Dr Salis ya shigar da ita, hankalin Amatullah bai tashi ba sai da ta ga wani gado dan siriri, gefe da gefen sa wasu karafuna ne. Dr Salis na mai duban Amatullah ya ce


"Madam zan ba ki dama ki shirya kafin nan an gama sterilizing kayan aikin, wannan gadon za ki hau, and remove your pant please"
Ya na gama maganar ya juya ya fice.


'and remove your pant please'


Maganar da ya tsaya mata a rai kenan, kallan gadon ta ke cikin tashin hankali, komai na dakin ma abin tsoro ne. A sanyaye ta zame pant din ta, ta ninke ta sa a jaka. Amma sai ta kasa hawa kan gadon, hawayen da take ta kokarin rikewa tuni suka fara gangarowa bisa kuncin ta, yayin da ta ke gogewa da bayan hannun ta.


Bayan minti goma Dr Salis ya shigo dauke wani ɗan tire. Amatullah ta bi tiren da idanu in da idanun ta su ka yi kacibus da kananan karafuna, wasu kamar aska, sai mai ɗan lankwasa kamar kugiya, sai wasu kamar kananan wuka, da wasu ma su zubin almakashi.


"Madam da fatan kin shirya, before then zan mi ki allura, ta Pentazocine domin kashe zafin wajan ko?"


Cewar Dr Salis ya na mai sanya safa a hannun shi. Sai da ya mata allurar kafin ya sake cire safar hannun ya fita. Kusan minti biyar ya sake ɗauka kafin ya dawo, ganin har lokacin Amatullah ba ta hau gadon ba ya ce da ita


"bisimillah madam, ki cire zanin ki ki hau gadon"


"Shin ba ku da Doctor mace ne?"


Cewar Amatullah cikin tashin hankali. Murmushi Dr Salis yayi, kana ya ce
"Unfortunately babu, Amma kar ki damu ai duk cikin neman lafiya ne, ni ma ina da iyali kamar ke a gida"


"Za ka bari a yiwa iyalin ka abin da za ka min yanzu? Za ka bari a zubar mata da ciki? "


Ta sake tambayar sa. Ya na mai yamutsa fuska ya ce
"Idan iyalina ba ta da lafiya kuma babu Doctor mace sai namiji why not? But batun bari a zubar da cikin wannan ra'ayin ki ne ke da mijin ki ai"


Shiru ta yi tana mai duban gadon, hannun ta bisa cikin ta.


"Idan kin shirya please"


Dr Salis ya sake maimaitawa a karo na biyu. Jiki sanyaye Amatullah ta cire zanin jikin ta ya rage sai under siket, yayinda da ta tattare hijabin ta zuwa wuya. A hankali ta haye bisa gadon. Ganin Dr Salis ya gyara karafunan da ke gefe da gefen gadon yayinda da ya umarce ta da ta sanya kowacce kafa bisa karafunan yanda kafafun ta za su bude sosai ya sanya Amatullah girgiza kai.


Cikin kokarin ganar da Amatullah ya ce
"Madam in ba ki saka kafafunki na ɗaure su jikin karfen nan ba, za ki iya zube kafafun ina cikin aiki kuma hakan zai iya jawo matsala......"


Ga mamakin shi sai ganin Amatullah yayi ta diro daga gadon ta na mai sakin hijabin ta, ta ja zanin ta daura. Hannun ta rike da jakar ta ta dubi Dr Salis ta ce


"Ka kira shi ka sheda ma sa na ki baka haɗin kai, dan kuwa wallahi babu wanda ya isa ya min abin da ka ke shirin yi min!!!!"


Ta na gama fadin haka ta fice, shi kuwa Dr Salis har cikin ran sa ya ji dadin maganar Amatullah.


'ashe dai da sauran wayon ta'


cewar Dr Salis cikin ransa. Hankali kwance ya kira Saifullahi ya shaida masa halin da ake ciki. Kamar zai yi hauka dan bacin rai inda ya zo ya tadda Amatullah tsaye bakin kofar Dr Salis.


"Malama me ki ke yi anan? Me ya sa ba ki tsaya an cire mi ki wannan abin ba?"




Kallan sa ta ke cikin Ido, duk wani shakka na shi da ta ke ji ya gushi, cikin dakewa ta ce


"Kai na ke jira ka kai ni gida, wannan abin da ka ke so a cire ba zai yiyu ba, ina san abu na idan kai ba ka so......."


Takaici ya sa ya kasa ba ta amsa, cikin bacin rai ya shiga zirga zirga, ya kai ya kawo. Ita dai Amatullah ta zubawa sarautar Allah ido. Cikin wannan hali Dr Salis ya fito ya same su


"Ya za ka min haka Dr Salis bayan na saka hannu a cire mata wannan jarabar?"


"Ya ka ke so na yi bayan Madam ta ce ba ta so? I can't force her you know, Zai dai fi kyau ku kara shawara......"


"Malama wuce mu tafi!"


Ya katse Dr Salis, ya wuce fuuu, in da Amatulah ta bi bayan shi. Yanda ya ke tuka motar kamar zai tashi sama, ita dai adduar ta su isa lafiya. Gashi allurar da aka mata ya dan fara saka ta jiri, haka kuma duka jikin ta ya mutu. Suna isa tun kafin ta fito daga mota ya riga ta fita, a falo ta taddashi ya na ta kai kawo kamar wanda ya hadiyi gatari. Sim sim ta shige shi za ta wuce dakin ta ya daga ya tsayar da ita ta hanyar daka mata matsawa


"Malama ji mana!!!!!"


Amatullah ta tsaya, gaban ta ya sha ya na mai nuna ta da dan yatsa ya ce


"Wato komai aka haɗa da jaki sai ya ci kara, so ina so ki zaɓa ko ni ko cikin da ke jikin ki!!!!"


Kasa magana ta yi, kai kawai ta ke girgiza masa yayinda hawaye ke gudana daga idanun ta.


"Malama dallah ki amsa min!!!!"


"Ya Saifullahi dan Allah ka yi hakuri....."


"Ni ko wannan abin da ke cikin ki?"


Hannu ta kai ga cikin ta, ta dago idanun ta ta sanya cikin na shi, murya a sanyaye ta ce


"Ciki na, na zaɓi ɗan da ya ke ciki na...."


Kallan ta ya ke tsana karara cikin idanun sa


"Amatullah yau kin tabbatar mi ni ke butulu ce! Kin zaɓi cikin ki? Fine! Very fine ki je ki auri cikin na ki!! Shashasha bagidajiya!!!!"


Ya juya ya fita a fusace. Baki buɗe ta bi bayan shi da kallo, a karo na farko ta nemi kuka ta rasa, fadi ta ke


"Inna lillahi wa inna ilaihi ilaihi rajiun"


Ta fada ta kara maimaitawa. Jikin ta babu nauyi saboda allurar da aka mata, haka ta lallaba ta shiga daki, ba ta san sanda bacci ya sace ta ba.


***


Washagari kamar yanda ta saba ta haɗa masa karin kumallo, amma shiru ya ki fitowa daga dakin sa. Gashi lecture din sassafe gare ta, na 8:30, kuma test za a mu su. Saifullahi da idan ta na da lecture din safiya karfe bakwai shirya tsaf sun ɗauki hanya. Ganin shirun yayi yawa ta je ta buga masa kofa, har ta fitar da rai za a bude kofar, sai gashi ya bude, sanye cikin singileti da gajeran wando. Kallan banza ya bi ta da shi, ya na mika ya furta


"Malama lafiya?"


Tana inina dan shakkar amsar da zai ba ta, ta ce


"Dama school...ka manta ..dama ina da lecture din safe"


"Oh toh shi cikin na ki ba zai kai ki makaranta ba?"


"Ya Saifullahi........."


Hannu ya daga mata tare da faɗin


"Shut up!!! Duk sanda ki ka shirya zubar da wannan abin da ki ke dauke da shi toh sai ki tafi makarantar, but for now ki saka a ranki cikin ki ki ke aure, kuma wallahi ki ka saka kafa ki bar gidan nan wallahi sai na lahira ya fi ki kin daɗi! Bagidajiya kawai!"


Ya na gama magana ya ja kofa ya mayar ya rufe. Kuka Amatullah ta saki mai karfi har da shashsheka, da sauri ta koma ɗakin ta, in da ta ɗauki wayar ta, numbar Baban Sasa ta shiga kira, bugu na uku Baban Sasa ya dauka ya na mai faɗin


"Amaryar yau kewata ake da sassafe?"


Maimakon ya yaji muryar Amatullah cikin walwala kamar yanda ya saba ji, sai ji ta yi tana kuka har da shashsheka, ta ma kasa magana.


"Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun!!! Lafiya Amatullah? Ina Saifullahi? Me ya same shi? Wani abu ne ya same shi"


"Dama shi ne ya ce ba zan je makaranta ba ...."


"Akan wani dalilin kuma????"


Baban Sasa ya tambaya cikin nuna bacin rai
"Wai dan na ce.....Wai dan ina dauke. . wai dan...."


Amatullah ta tsinci kan ta tana mai kame kame, jin haka Baban Sasa ya ce


"Wai dan me Amatullah?"


Wuf Saifullahi ya fuzge wayar, dama tun da ya juyo kukan Amatullah ya san za a rina, hankalin sa ya kasa kwanciya ya biyo bayan ta, ya kuwa tadda ta tana shirin shaidawa Baban Sasa halin da su ke ciki.


"Baban Sasa, shagwaba ce irin na Amatullah"


"Shagwaba irin na Amatullah? Me ya sa ka hana ta zuwa makaranta?"


"Ba hana ta zuwa makaranta na yi ba, yanzun haka ma shirin kai ta makarantar, ka san halin matar ta ka ne sai a sannu"


Shiru Baban Sasa yayi kafin daga bisani ya ce ya bawa Amatullah wayar. Maimakon ya bata wayar, sai ya saka ta handsfree, ya na mai yi mata gargadi ta san amsar da za ta bawa Baban Sasa.


"Amatullah shin akwai wani damuwa na bayan zuwa makarantar?"


Idanun ta kan Saifullahi ta ke girgiza mata kai, Amatullah ta ce


"Ah ah Baban Sasa, dama shi ne kawai"


"Kin tabbatar? Kar ki boye min komai"


"Babu komai Baban Sasa"


"Maza ki shirya yanzu zai kai ki, Allah ya mu ku albarka"


Ta amsa masa da amen. Saifullahi na kashe wayar maimakon ya bata, sai ya tusa shi aljihun sa, baki bude Amatullah ke duban shi. Ganin ya juya ya fice daga ɗakin ta biyo shi da sauri zuwa falo, ko a jikin sa ya wuce zai shige dakin sa ta yi saurin tsayar da shi


"Wallahi Yaya Saifullahi test gare ni, idan na yi missing carry over ce......"


Ya na murmushin mugunta ya ke kallan ta
"Toh ke a na ki wautan makarantar zan kai ki? Saurare ni da kyau, Wallahi! Wallahi! Wallahi! Babu ke babu makaranta matukar ba ki yarda an zubar da wannan abin da ke cikin ki ba!!!!"


Yayi maganar ne ya na mai nuni ga cikin ta, bai gushe ba ya kara da


"Ba ke mai Baban Sasa ba? Sai ki je gida ki fada ma sa ai, shashasha, ba carry over ba, Allah ya sa spill over ne!!! What a local human being!!!!!"


Fuuu ya wuce dakin sa, in da Amatulah ta bishi da kallo, hannun ta bisa kirjin ta tsabagen zafi da zuciyar ta ke mata.
[3/18, 11:07 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀
✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL


BABI NA ASHIRIN DA UKU


Ɗakinta ta koma, ta ɗauko jakar ta da take ɗan ajiyar ta, ko da ta ƙirga chanjin da ke ciki ko makaranta ba zai kai ta ba, balle ayi maganar dawo da ita gida. Bakin gado ta zauna tana zancen zuci. Ta san duk abin nan da Saifullahi ke mata dan cikin da take ɗauke da shi ne, cikin da ba ita ta sakawa kan ta, tsabagen rashin adalci irin na mijin ta. Nan ta sha alwashin hafe cikin ko da kuwa hakan na nufin karshen zaman ta da Saifullah ne.


Wasa wasa Amatullah na ji ta na gani ya hana ta zuwa makaranta, wayar ta kuma ya kashe, Su Gwoggo kuma ya tsara mu su karyar wayar Amatullah ta sami matsala, idan kuma suka kira daga ya ce ta na makaranta nan za ta wuni, sai ya ce ta na bayi. Tun abin ba ya damun Gwaggo har ta fara tunanin ko lafiya.


Gashi ko abinci idan ta girka ba ya ci balle a kai ga magana mai daɗi ta shiga tsakanin su. Duniya ta yiwa Amatullah zafi, ji ta ke kamar ta na gidan kurkuku har tsawan kwana uku. A na hudun ne da safe Saifullahi na fita, itama ta sanya hijabin ta. Dan kudin da ke hannun ta ta biya kudin mota ba ta zame ko ina ba sai gida.
A zaure ta tadda Baban Sasa zaune bisa tabarma tare da Baba Anas. Yanda ta shigo mu su afujajan kamar an koro ta ne ya sa suka tsora, in da a tare su ke tambayar lafiya? Gaban Baban Sasa ta zauna ta na kuka hawaye ɗaya na bin ɗaya, ta ce


"Baban Sasa ya hana ni zuwa makaranta, kwana uku

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login