Showing 39001 words to 42000 words out of 98809 words
Chapter 14 - TAZARA COMPLETE by UMMU-ABDOUL & KHADIJA SIDI.txt
wai ki kai ma Yaya Saifullah abincinsa ɗaki, kin ji yanda ya kira sunanki, Aamat ya ce, wallahi Yaya Saifullah ɗan gayu ne..."
"Dilla rufe ma mutane baki, ba ɗan gayu kaɗai ba" Amatullah ta katse ta cikin tsawa, ba ta ga dalilin da zai sa ya nemi ta kai masa abinci ba.
'Zai so ki fa, kuma ki saki jiki ki sabar masa da jikinki, da farko a kwai wuya amma shine soyayya' ta tuna kalaman maman Jaafar. Nan sai ta ji sanyin jiki.
Kenan har ya fara sonta tun da har ya nemi ta kai masa abinci.
'da farko a kwai wuya'
ya sake faɗo mata a rai, nan ta tsorata ainun don in akwai abin da ta tsana abin da zai sa ta ji zafi a jikinta. Ta tuna a littafan da ta karanta yanda aka sa amare na sumewa in aka kai su. Ba ta san lokacin da hawaye su ka soma gangaro mata ba, kawai ɗuminsu ta ji.
"Amatullah haramun ne tsaurara kiyayya, balle wannan mijinki ne wanda Aljannarki ke tafin ƙafarsa. Ga abincin sa can maza ɗauka ki kai masa" Goggo mairo ta faɗi bayan ta sa hannu ta goge mata hawayen. Cikin sanyin jiki ta ɗauki abincin ta kai masa ɗaki.
Film yake kallo ƴar America, ganin ta bai sa ya kashe ba duk da kuwa abin da ake haskowa ya saɓa ma shari'a. Duƙar da kai tayi don tun da take abin da bata taɓa gani ba kenan.
"Daga kai ki gani, ki ga yanda su ka dace da juna, shin ni ɗin ya dace na gauraye gumi da bagidajiya irinki? Kalle su fa, wai ke har kina tunanin kin kai mace da za a gani a so?
Na so tsine ma ranar da aka ɗau cikinki don ranar bai zama mai adalci a rayuwata ba"
yace yana mai jan farantin da ta shigo da shi ya soma cin abincin da hankali kwance.
"Hijabin nan naki ƙarni ya ke yi, ki yi hakuri ki bani waje ko iskan zai yi daɗi" ya ce yana nuna mata hanyar fita.
Tsoro ya hana mata fita tun a farko, don ta san yana iya ƙulla mata wani sharrin, ga shi ta zauna, amma zaman bai mata amfani ba.
Kuka ya taso mata bayan fitowarta daga ɗakin, tsayawa ta yi ta tattaro duk wani natsuwa nata kafin ta isa ɗakin Baban Sasa, nan hira sosai su ka yi, sannan ya bata tukuicin hira da sanya tariyarsu sati biyu masu zuwa.
Yana faɗa mata lokacin za ta tafi ne, take ta ji duk wani natsuwar tafiya ya ɓace.
"Baban Sasa zan yi missing ɗinka don Allah kara lokaci" ta samu kanta da faɗi.
Kallonta yayi cikin dariyar su ta manya ya ce
"Ai muna tare, ki yi hakuri kuma ki bi mijinki, Allah ya sanya alkhairi ya muku Albarka, Nan da sati daya Saifullahi zai haɗo mana lefan ki bisa al'ada, kasancewar tsatso ɗaya kuka taso ba zai sa a toye mi ki hakkin ki na lefe" ba ta amsa ba anan ta sanya kuka mai tsuma rai, gaba ɗaya ta haɗa masa tun daga wanda ta ƙunso daga ɗakin Saifullah har zuwa na Tariya ga fuskar Dee Yusuf da ta gani a gate sai mata gizo ya ke a idanu.
***
Baban Sasa ne ya ruguzawa Saifullahi shirin shi na zuwa Kano a washagari, maganar tarewa nan da sati biyu, da na lefe da gidan da za su zauna ne gaba ɗaya ya ɓata masa lissafi. Yayi kokarin ɗaga tariyar ta hanyar ba da uzirin rashin kammala ginin sa da ya fara, Amma Baban Sasa ya ce wannan ba wani abu ba ne, zai iya zama ɗaya daga gidadan shi, ya zaɓi duk wanda ya masa a fara gyara. Haka ya kasance cikin bakin ciki da dana sanin biyewa Aysuh da yayi su ka dawo.
Magungunan mata da su tsumin da 'yan uwan Gwaggo ke angaza mata ba karamin tayarwa da Amatulah hankali su ke ba, tun tana musu alkunya ta na karɓa in ta shiga bandaki ta zubar har ta gaji ta fili ta ce musu su daina ɓata lokacin su, ita ba sha ta ke ba kuma ba ta ga dalilin sha ba. Haka kuma baccin ran da su ka nuna bai sa ta canza ra'ayin ta, har su ka gaji su ka bar ta da halin ta.
Satin biyun nan sun zo masu ne kamar kyaftawar ido, ba ta wani wahalar yin gayya ba sai su zulaikha da ya zama mata dole. Ana saura kwana uku aka nuna lehenta, wanda ya fi na duk wata ya mace da aka aurar a gidan.
Ranar bikin ta ci leshin ta masu kyau da atamfa ta dinga canzawa kowanne da hijab da ya shiga da shi.
Wannan shigan ya fi komi ɗaga hankalin Saifullah don a rayuwarshi bai taɓa fuskantar tozarta wa irin sa ba, wai shi kamar sa ana bikin sa duk da auren suna kawai ya tara amma a ce matarsa zulum zulum cikin Hijabi.
[3/2, 10:52 PM] +234 703 484 8802: TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼♂🤦🏿♀
✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL
BABI NA GOMA SHA TARA
Rana ɗaya aka yi komai aka gama. La'asar na yi Baban Sasa ya ce a shirya amarya a kai ta ɗakin mijin ta. Nan fa amarya kuka har da majina, musammam da aka ce ta zo ta yiwa Gwaggo sallama.
Hannayen ta biyu ta sa ta riƙe ƙafar Gwaggo da kyar aka iya bambare hannun aka wuce da ita ɓangaran Hajiya.
Nan kuwa ruwan habaice habaice su ka sha daga dangin Hajiya. Haka ma Hajiya wacce ta dubi Amatullah da ke tsugunne gaban ta fuskar ta rufe da lafaya, buɗar bakin ta sai cewa ta yi
" Toh mu dai babu abin cewa tunda ta faru ta kare ramamme ya zagi maye, Allah dai ya sa za ki iya kula da mijin na ki, dadin ta dai namiji mijin mace hudu ne....."
"Bare ma ɗiyar ta mu ai san kowa kin wanda ya rasa ce, wajan kula da iya zaman duniya ba a ce mata komai, uwar gida sarautar mata ba, kowa ya zo bayan ki ya ke...."
Cewar kanwar Gwaggo yayinda yan uwa Gwaggo su ka kara karfafa mata gwiwa da guɗa.
"Toh ai sai ku tashi a kai ta, Allah ya sa a dace"
"Allahumma amen"
Cewar dangin Gwaggo, in da su ka tayar da Amatulah. Kamar yanda su yan uwan Hajiya da yayyan Saifullahi ba su fasa yada habaici ba haka su ma dangin Gwaggo ba su fasa guɗa ba.
Ɗakin Baba Sasa aka kai Amatullah, nan aka tarad da Mahaifin ta tare da su Baba Zubairu da Baba Anas. Daya bayan ɗaya haka duka su ka mata faɗa tare da sanya albarka, ko da aka zo kan Mahaifin Amatullah sai cewa yayi
"Tashi ki tafi dakin mijin ki ɗiyar albarka, duk abinda za ki yi ki yi da halin ki, ba ni da haufi kan ki, kin haifu Amatullah, Allah ya sanya mi ki albarka"
Ya karasa maganar ne yayinda yar kwalla ke shirin fita daga idanunsa. Nan ma fa Amatullah ta ce ba ta tashi, aka yi aka yi, ta cije kuka ta ke harda wayyo Allah.
Mahaifin ta ne da kan sa ya riko hannun ta, sannan ta yarda ta mike, har mota ya kai ta sannan ya barta hannun manya ya koma ciki. Yan uwa da abokan arziki su ka shige mota, aka dauki hanyar gidan amarya.
***
Tafiya ce ɗoɗar daga Amaru zuwa filin mallawa da ke sabon layi, filin cikin na gadon su Baban Sasa ne ya mallaka, sanda ake yanka filayen ana siyarwa ya so ya siyar sai kuma ya yi tunanin gine shi.
Babu laifi gidan ginin zamani ne, flat ne, drive in mai dauke da daki uku kowanne da bandakin shi ciki, da kuma madaidaicin kitchen, sai kuma katon falo guda. Su Zulaikha ne su ka yi kokarin zauna mata kafin ango ya zo kar a barta ita kadai. Amma shiru babu Saifullahi babu alamar shi, dan haka sallama su ka mata, ta na ji ta na gani su ka barta ita kaɗai duk magiyar ta da su zauna amma umurni ne daga baban Sasa cewa kada wanda ya kwana a gidan duk da hakan al'adar mutan zaria ne.
Amatullah gwanar tsoro, suna fita ta sa mukulli ta garkame ɗakin ta, ta shige toilet ta dauro alwala bisa dadduma ta shiga jera salloli ta na rokan Allah sauki bisa lamarin ta, nan bacci mai nauyi ya sace ta.
Yunwa ne ya tada ita da asubar fari. Sai da ta yi sallar asuba, ba tare da ta cire hijabin da ta yi sallah da shi ba, a hankali ta bude kofar ɗakinta ta ɗan leƙa falon, duhun da ta gani ya bata karfin gwiwar fitowa ta na mai haska falon da wayan ta domin neman hanyar kitchen.
Babu shakka su Gwaggo sun tsantsara mata falon na ta da kayan alatu, kujerun ta ruwan zuma da kanana filullukan da aka jera ba karamin shiga yayi da labulen falon ba. Ganin kofofi hudu daya ya ɗan yi kusa da dakin ta, sai kuma ɗayan bangaran yamma kusa da kofar shigowa falon, sai kuma ɗayan wanda ke can gefe guda ya sa Amatullah ta yi turus, dan kuwa ba ta san wanene wanne cikin su ba, gashi yunwa ta ke ji kamar ta yi ihu.
Lissafin ta wannan na kusa da ita zai iya kasancewa dakin mai gidan, wancan na kusa da kofa ya zama na baki, dan haka na can gefe shi ne kitchen, kai tsaye to nufe shi.
Zuciyar ta daya ta kama mubudin kofar ta bude ta na mai tura kan ta ciki. Hasken wutan lantarki ne ya fara ziyarta idanun ta, kafin idanun ta ya gane mata wanda ke tsaye gaban fridge daga shi sai gajeran wando, ya bata baya hannun sa dauke da gorar ruwa. Da sauri ta juya cikin rawar jiki, wayar da ke hannun ta ce ta sullube ta faɗi kasa. Karar faduwar wayar ya sanya shi jiyowa fuskar shi cike da mamaki. Bacin rai ne ya maye gurbin mamakin da ya bayyana fuskar shi ganin Amatullah, cikin sauri da tsungunna ta dau wayar da niyar ficewa, ya dakatar da ita cikin tsawa ya ce
"Ke wace irin bagidajiya ce wai? Zo nan Malama!"
Tsayawa ta yi cak idanun ta kasa, ita ba ta fita ba, haka kuma ba ta karasa in da ya ke cikin kitchen ɗin ba.
"Ba da ke na ke magana ba! Ki zo na ce!"
Ya kara daka mata tsawa a karo na biyu in da ta tsinci kan ta tana mai karasawa gaban sa, da kyar ta yi karfin hali ta kai kallan ta ga fuskar sa ba tare da ta kalli kirgin sa ba, yanayin kallan takaici da ya ke mata ya sa ta sake yin ƙasa da na ta idon ka na ta furta
"Ban san kana kitchen ɗin ba......"
"Iya ka tarbiyar da aka koya mi ki kenan? Ba ki iya gaisuwa ba? Ga gidadanci ga rashin tarbiya...."
Lebben na kasa ta cije cikin takaici da jin zafin furucin Saifullahi, kafin ta kai ga ba shi amsa sai ji ta ya ce
"Bani hijabin nan!!!!!"
Jin maganar kamar kunnen ta ke mata zagi ya sa ta ɗaga kai da sauri ta na mai fidda idanu. Kai ya girgiza ya ce
"Yes kin ji ni da kyau, ki ciro hijabin jikin ki ki bani yanzun nan!!!!"
Baya ta ja tana mai girgiza kai yayinda zuciyar ta ke dukan uku uku ta furta
"Dan Allah dan annabi ka yi hakuri....."
"Dalla malama hakurin me ki ke bani, just do as I said ko kuwa ni na cire mi ki! you are so irritating!!!!"
Hawaye ne ya fara zuba daga idanun ta, ganin ba ta da niyar bin umarnin shi ya sanya shi tinkarar ta, ganin haka itama ta fara ja da baya tana fadin
"Menene haka wai ya Saifullahi?"
"Just remove the damn thing and give it to me!"
Jiki na rawa ta ciro hijabin, ta rike hannun ta idanun ta kallan kasa yayinda hawaye daya ke bin daya. Kallo ya bita da shi, kasancewar ba shiri bacci ya sace ta daren jiya, atamfar da aka kai ta da shi ne jikin ta. Kai ya girziza ya na mai nuna ta da hannu tun daga sama har kasa ya ce
"Just imagine! Na tabbatar da wannan atamfar a jikin ki ki ka kwana tsabagen gidadanci! God you're so local Amatullah!!!"
Ya sa hannu ya fizge hijabin daga hannun ta ya yi wulgi da shi cikin kwandan sharan da ke cikin kitchen, in da Amatulah ta bi shi da kallo, kafin ta dawo da kallan ta ga Saifullahi. Ya na nuna ta da dan yatsa ya ce
" Ni Saifullahi, wanda aka ɗaura min auran ki akan dole, daga yau har ki karaci zaman ki gida, na umarce ki da ki dena saka waccan abu, Kar na sake ganin ki da hijabi Amatullah! Na haramta mi ki saka hijabi cikin gida na!!! Bagidajiya kawai!!!"
Ya na gama magana ya fice yana huci kamar zaki. Ya bar Amatullah zube a kasa ta na sharbar kuka, shin ashe akwai ranar da za a haramta mata sanya hijabi? Kuma mijin ta? Wannan masifa har ina!
"Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun"
Furucin da ta ke yayinda tsanar Saifullahi ke kara ratsa zuciyar ta.
[3/5, 8:50 PM] Safiyya Ummu-Abdoul Writer: TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼♂🤦🏿♀
✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL
BABI NA ASHIRIN
Sannu sannu har mun yi sati goma a cikin wannan tafiya tamu, godiya ta Musamman ga duk wanda idonsa ke kan saƙon nan, mun gode, Saifullah da Amatullah na gaida ku cikin kwando. Dee Yusuf da mimi na muku fatan Alkhairi..
Baban Sasa na jiran ku kai masa farfesun Hanta.
Muna ƙaunar ku Fisabilillah.
Umdija😍😘🌹
***
Jan jiki ta yi zuwa ɗaki bayan ta nemi abin da za ta riƙe hanjinta da shi. Allah ya isa kuwa ta masa ya fi sau a ƙirga don ba ta ga dalilin da zai sa ya haramta mata sa hijab ba, haka kawai ta dinga tallan jikinta gareshi kamar wacce ba ta da kishin kanta. Da ire-iren tunanin nan ta kammala cin abincin, miƙe kafafu tayi ta jingina nan ma wani sabon bacci yayi awon gaba da ita.
Hayaniya ya tayar da ita sa'ilin da yan gidansu su ka iso wainda mafi akasarinsu innoninta ne, bayan ta gaida su, wasu na mata tsiya ne su ka sanya ta je ta yi wanka saboda masu shigowa ganin amarya.
Atamfarta ta sanya ɗinkin riga da skirt, sosai ɗinkin ya zauna a jikinta, golden color din da ke jikin atamfar wanda ya sakaya cofee da peach ya fito da kalarta tare da bayyana madarar kyawun da ta mallaka.
Hijab golden ta ɗinka ma kayan har ta ɗauko za ta sanya
"A matsayina na mijinki, na haramta miki sanya hijabi a cikin gida" take wasu hawaye su ka zubo mata, jujjuya hijabin ta ke a hannun ta hawayen ba su daina zubar mata ba, takaicin ta yanda cousins ɗinta maza ke kaikomo a cikin gidan suna taimakawa wajen ƙara kimtsa gidan.
"Ga wannan ki yafa" cewar innarta Aisha, kallon gyalen ta yi, kamar ta ce A'a amma shakkar Innar tata da take yi yasa ta amsa. Ana faɗin matar soja sojace bata yarda ba sai akan innarta Aisha, don in ta rikide musamman akan abubuwa da ya jiɓinci ado da kwalliya sai ka rantse wani hafsin soja ne a fagen yaƙi.
Gyaran da aka ma fuskarta da yanda ta yane jikinta da gyalen ya fito da ita ainun.
"MaashaAllah! MaashaAllah!!"
kawai ake faɗi, nan sai ta hau Saman gado fuskarta lulluɓe da gyalen amma tana iya hango su.
"Ai ni jiya hankali na ya ɗauke wajen hidimar yaya mairo, a ce amarya da hijabi, kai ke kuwa izalarki ta yi yawa wallahi" inna Aisha ta faɗi tana mai yaba kyawun yar tata.
Zamanta a legas ya sanya duk wani darun da aka yi ba ta da labari, itace ke bi ma Goggo Mairo, sun yi aure da mijinta tun tana shekaru goma sha huɗu shi kuma an yaye su a depot din zaria. Allah cikin ikonsa ya haɗa mijin nata da oga nagari ya masa hanya ya tura sa makarantar horar da sojaji ta NDA yayi shekaru biyar ya fita da anini. Yanzu har ya kai ga Jan wuya a aikin soja.
"Ai yaya indo ni na rasa kamun jiki irin na Amatullah, su ne yan fatawar ko hoda mace ba ta sawa, amma wainda su ka san darajar mata sun san su ake kira first class ladies" faɗin Inna Hafsatu kanwar su goggo mairo ce, hakan ya sanya yan uwan hajiya da su ka shigo fita cikin sanyin jiki, da sun shigo suna musu yatsina ne. Suna fita kannen Goggo Mairo su ka sanya shewa.
Haka su ka yini suna gyara da taya Amatullah zama sai da aka kira magariba sannan duk su ka watse a gidan, suna mai masu fatan Alkhairi.
Kamar juya Amatullah ba ta jira shigowar Saifullah ba ta kulle ɗakinta, sai dai ta iya canza kaya zuwa na bacci kafin ta bi lafiyar gado.
***
Washagari da misalin karfe goma sha biyu Saifullahi ya isa Kano gidan su Ayush. Kamar yanda aka saba karɓar shi cikin mutunci da girmamawa haka yau ma aka masa. Duk da kasancewar ba wannan ne zuwan shi gidan na farko ba bai hana shi bin gidan da kallo ba tamkar bakauye tsabagen tarin dukiyar da ke gidan.
Falon baki aka sauke shi, in da ma su aiki su ke ta kai kawo wajen kawo masa abinci da kayan marmari. Sai bayan sun gama da minti ashirin sannan Ayush ta shigo ta na taku ɗai ɗai da rangwaɗa, baki da hanci da idanu gaba ɗaya Saifu ya saki ya na kallon ta.
Sanye ta ke cikin doguwar riga ja, rigar ta kamata kwarai ta zauna jikin ta, ko mayafi ba ta saka ba, sai daurin da ta yi da kallabin kayan, irin wannan daurin da ake kira ture ka ga tsiya.
Kusa da shi ta zauna kamar wacce za ta shige cikin sa. Tuni kamshin turaren kamafanin the body shop ya mamaye hancin sa. Fuskarsa cike da fara'a ya ruko hannun ta ya