Showing 6001 words to 9000 words out of 98809 words
Chapter 3 - TAZARA COMPLETE by UMMU-ABDOUL & KHADIJA SIDI.txt
mu! Bana na san kauyanci! Ba na san gidadanci!! Kinga malam Sambo da ya kika yi allo a wajensa, shi yafi dacewa da ke not an engineer" Yana gama faɗi ya tsidda miyau ya wuce ya barta a daskare. Da kyar ta iya jan kafafun ta ta shige gida, idanun ta cike da kwallar bakin ciki, shin ita bagidajiya ce? Toh me mai ta ma sa na kauyanci da gidadanci?. Abun da ta ringa jinjinawa cikin ranta kenan.
***
Tun daga ranar ba su sake haɗuwa ba, ta kiyaye haɗuwarsu ta maida hankali a karance-karancenta.
Yau ma kamar kullum zaune take tana karatun "You can be the Happiest woman in the world" na Dr. Aid Al-Qarni, ta baje a falonsu, sanye take da riga da skirt dinkin zamani da ya ɗame ta, nan ta jiyo sallamarsa, bai jira amsarta ba ya kutso ciki, wani irin tsalle tayi ta jawo hijabinta da ta sarkafa a jikin ƙofa ta shiga kokuwan sawa, da ya ke hankalin sa na bisa wayar sa da ya ke ta faman dannawa nan ta ci sa'ar sanya hijabin kafin ya ankara da ita, har dan nufashi ta ke mayarwa cike da godiyar Allah. Kallon ta ya ke cike da kyama ya furta "Ina goggon"
"Suna wajen baban Sasa" tace masa. Har ya juya zai fita sai kuma ya sake dawowa, idanun sa kan ta ya kira sunan ta
"Amatullah!"
Daga idanun ta ta yi ta dube shi ba tare da ta amsa ba, irin kallan wulakancin da ta gani a idanun sa ya sa ta yi saurin kawar da kai. Bai gushe ba, ya cigaba da magana cike da nuna isa.
"Ina so ki fahimce ni, ba na son ki ba na kaunar ki, sam ba ki min ba, akwai yarinyar da na ke so....."
Kamar takobi haka ta ji maganar ta shi ta soki kirjin ta. Shi kuwa ko a jikin sa ya kara da "dama biyayya ya sanya da zan yi jihadi na aure ki, toh amma sam ban yi tsammanin haka ki ke ba, ni wayayye ne, ina bukatar wayayyiyar mace cikin rayuwa ta!! Na tabbatar cikin samarin unguwar nan ba za a rasa local champion da ke son ki ba, ki rufa ma kan ki asiri ki fito da shi, na tabbatar idan su ka ga dukkannin mu da wanda mu ke so, Baban Sasa zai janye wannan alkawari na shi mai muni, kin gane ko?"
Har ya kare maganan shi idanun Amatullah na kan ƴan yatsunta da ta ke wasa da su, tun da take a rayuwarta ba'a ta taba wayan gari ta na ƙin wani ko wata cikin ran ta ba, sai na wannan bawan Allah da ake shirin ɗaura ma ta aure da shi, ba don komai ba sai don kyama da ya nuna kiri kiri gare ta.
"Ba da ke na ke magana ba?"
Shiru ta masa kamar ma ba ta san yanayi ba wanda hakan ba karamin sosa ma sa rai yayi ba, Wai yarinya bagidajiya bakauyiya sai shegen girman kai da jin kai. A fusace ya furta
" Wato ki na ji na ba za ki tankaba ko? Toh ki saurare ni da kyau! Muddin ki ka bari aka ɗaura wannan aure tsakaninmu, ki ka shigo gida na wallahi sai na lahira ya fi ki jin dadi!!! Bagidajiya sakarya kawai!!!!!!!"
Ya na gama magana ya fice a fusace, nan Amatullah ta kwantar da kan ta bisa kujera yayinda kwallan da ta yi kokarin rikewa su ka shiga gasar kwarranya daga idanun ta, fadi ta ke
"Inna lillaahi wa inna ilaihi rajiun, ya Allah ban iya ba, ya Allah ka iya min! Ya Allah min takangar karfe da wannan bawa na ka Agithnee Yaa mugithu!"
A wannan halin Gwaggo ta same ta, cikin tashin hankalin ganin halin da Amatullah ta ke ciki ta shiga tambayar ba'asi. Duk zurfin ciki irin na Amatullah ba ta boye mata ba, ta kwashe duk yanda su ka yi da Saifullahi tun daga ranar da su ka fara magana har zuwa yau. Jikin Gwaggo yayi sanyi, ta na mai duban Amatullah wacce in banda sauke ajiyar zuciya babu abin da ta ke yi tsabagen kukan da ta sha. Cike da tausayawa ta ce
" Amatullah ni na haife ki, ba zan so na cutar da ke ba, Baban Sasa mai kaunar ki ne, ba zai cutar da ke ba, ina mai baki shawara ki karfafa addu'a ga ubangijin ki, Allah zai fishe ki alkhairi. Amma ko da wasa kar ki tunkari Baban Sasa da wannan batun, shi Saifullahi da ya ke ganin an ma sa ba daidai ba shi ya je ya same shi ........."
"Wallahil azim Gwaggo ba na san shi nima!!"
Amatullah ta katseta cikin kuka.
"Shhhhh! Kar na sake jin kin furta haka, ki dai yi addu'a, ki rufa mana asiri kar a ji wannan magana daga bangaranmu, ki bari shi can ya je ya shaida mu su, kin ji ko?"
Kai ta gyada alamar "eh"
"Tashi ki yo alwala ki yi sallah na san ko azahar ba ki samu kin yi ba, Allah ya yi miki albarka, kar da ki yarda maganar ta dame ki, idan ya rasa ki shi yayi rashi babba, babu kauyanci ko gidadanci tattare da ke Amatullah, sai tarbiya, kunya da yakana. Allah wadar wayewar ta shi da ya ke so. Inshallahu Allah zai shige mana gaba"
Da haka ta sami kwarin gwiwar dauro alwala. Nan ta kalli gabas ta shiga kai kukan ta ga mai duka.
***
Amatullah ba ta sake jin dadin gidan nan ba sai ranar Allah ya sa ta koma makaranta. Duk yanda kalaman Saifullahi su ka so tunzurata ta sami Baban Sasa ta akan rushe maganar auren su abin ya ci tura, ta yi kokarin jurewa ba dan komai ba sai dai alkawarin da daukarwa kan ta da Gwaggo, na duk kiyayyar da take ma Saifullahi ba dai a ji maganar daga bakin ta ba kamar yadda ya ke da buri, sai dai aji daga wajansa. Sati biyun da ta yi a gida har ta rame, ta rage walwala da kuzari. Kullum cikin tunani ta ke hatta lectures ma ba ta samu ta mayar da hankali ta gane a cikin aji. Tun Zulaikha na tambayar abin da ke damun ta, har ta gaji ta zubawa sarautar Allah ido.
Yanzun ma daga aji su ka fito, tun da Lecturer ya shiga har ya fita babu abin da ta gane, gaba daya hankalin ta ba ya ajin. Tunanin lafazin Saifullahi na cewar idan ta sake aka aura ma ta shi sai na lahira ya fi ta jin dadi ne ya addabi rayuwatar.
"Haba mana Amatullah!!!"
Zulaikha ce ta faɗa ta na me jijjaga kafadar Amatullah, wacce ta yi firgit ta dawo daga kogin tunanin da ta tsunduma. Ajiyar zuciya ta saki ta na mai duban Zulaikha ta ce
"Afuwan yar uwa, me ki ke cewa?"
Cikin damuwa Zulaikha ta furta
"Wai me ke damun ki ne Amatullah? Yau sati guda da dawowar mu na lura gaba daya kin canza, kai wannan damuwar da ki ke ciki har tafi sanda ki ka mari Dee Yusuf....."
"Dee Yusuf....."
Amatullah ta maimata, ikon Allah ashe akwai damuwar da zai sa ta manta da Dee Yusuf duk tsoran sa da take ji, abun da ta fada cikin ranta kenan, ta tsinci kan ta tana kewan ganin shi, a zahiri kuma cewa ta yi
"ke ni na sha'afa da lamarin wannan mutumin shaf, Allah ya amsa addu'a ta ya min katangar karfe da shi"
"Idan ba Dee Yusuf ba menene damuwar ki Amatullah"
Zulaikha ta sake tambaya. Kallon Zulaikha ta ke cikin nazari, kamar yanda ta ke sanye da hijabi, ita ma Zulaikha hijabin ne jikin ta, har kasa kuwa. Kai ta girgiza ta na mai fadin
"I'm very fine, kar ki damu dani kawata, bari na je KIL akwai wani littafi da na ke nema, daga nan sai na bi wannan course din da mu ka yi wallahi, wallahi sam ban gane shi ba"
Cikin nuna rashin gamsuwa Zulaikha ta amsa ma ta da "Ba dai za ki faɗa min abin da ke damun ki ba, ai shikenan duk sanda ki ka shirya magana ina nan Amatullah, adawo lafiya, Ni ban zuwa KIL daga dawowa ta makaranta"
Dariya Amatullah ta yi jin furincin Zulaikha na ba za ta je library ba. " Dama ai na san ba zuwa za ki yi ba shi ya sa ban mi ki tayi ba, kin ga tafiya ta, sai na dawo"
"Allah ya raba ki da ganin Dee... " Cewar Zulaikha cikin zolaya, juyawa Amatullah ta yi ta na murmushi, akaro na farko da ta ke jin da za ta gan shi ma ai ba wani abu ba ne, duk kauyancin ta ya na jure tsayuwa da ita, ba kamar Saifullahi ba ....
Nan ta kwabi zuciyar ta daga tunanin Dee Yusuf har tana gama shi da Saifullahi. Cikin sauri kan ta a kasa ta nufi hanyar da za ta sada ta da KIL. Ta gaban library ta hangi taran samari, dan haka ko da ta zo dab da su sai ta yi kasa da idanun ta, kafafun ta har hardewa su ke tsabagen tsarguwar kar dai kallon ta su ke, musammam yanzu da ta san ita ɗin bagidajiya ce yar kauye a cewar Saifullahi. Ilai kuwa ashe tun tahowar ta ya kafa mata idanu, gaba ɗaya hankalin sa na kan ta yana mamakin yanda a duniya ya sha ganin mata ma su saka hijabi ba wai a ABU kadai ba, amma bai taɓa ganin wacce shigar ke mata kyau ba kamar Amatullah. Ta gaban su ta gifta, ya tabbatar ba ta lura da shi ba, hankali kwance ya daɗa gyara tsayuwa, cikin ran sa faɗi ya ke
"Amatullah! Amatullah!! ina nan biye da ke, na yi kewan ganin ki Mama nah"
[1/8, 11:26 PM] Safiyya Ummu-Abdoul Writer: FIKRA WRITERS ASSOCIATION
TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼♂🤦🏿♀
✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL
BABI NA HUƊU
"Guys bari na ɗan shiga library kaɗan, I will catch up with you ko zuwa anjima ne, yeah?"
Cewar Dee Yusuf yayinda abokan Alutan na shi su ka zuba ma sa idanu cike da mamaki, ɗaya daga cikin su ne ya ce
"Dee kai fa ka takura lalle sai mun haɗu akan wannan maganar, hakan nan kuma ka ce za ka shiga library bayan ba a kashe ta ba?"
"Abi o help me ask him abeg!! Me ma za ka yi a library? Kowa dai yasan ba wajan ka ba ne, rannan ma da ka shiga raban shan mari ne ya kai ka!"
Hamza abokin Dee Yusuf ke magana, wanda dama cikin su shi kaɗai ne ajin su ɗaya, ɗakin baccin su ɗaya, sau da yawa mutane na musu kallon yan uwa ko aminai, tun zuwan su aji ɗaya dukkansu aka basu gurbin karanta Human anatomy a maimakon MBBS da ya ke zaɓinsu, tun a lokacin suke tare saboda su duka biyun masu nacin karatu ne da hazaƙa, kuma duk shaƙiyanci tare su ke yi hakan bai hana su samun lamba ta ɗaya (first class) a duk jarrabawar da su ke yi. . Jin batun Hamza ya sa su kwashewa da dariya, shi kuwa Dee murmushi kawai ya yi, ya na ɗan sosa ƙeya ya ce
"Ina wannan course din? Amatology da na ce maka na kasa gane shi? Ka tuna shi? Shi na ke so na je na duba ASAP ko Allah ya sa a dace"
Cikin ɗaukan haske Hamza ya dara, ya na mai bashi hannu su ka tafa ya furta
"Oya na go kafin ka jawa kan ka spill over, ka san dai final year mu ke, kuma second semester, in dai ba ka dace ba you better change the course, ka yi add and drop kawai a wuce wajen...."
"Kai karya ne wallahi Sec Gen guda da spill over!!!!!!"
Daya daga cikin su ya fada cikin kuranta Dee Yusuf, shi kuwa gogan hannu biyu ya tusa cikin aljihun wandon sa. Yau ma sanye cike cikin kananan kaya, bakar riga mai karamar hannu, da shudin wando. Juyawa yayi sai da yayi taku hudu sannan ya sake juyowa fuskar sa dauke da murmushi ya ke kallan Hamza, ya ce
"Baba in dai kan Amatology ne ba spill over 1 ba ko idan har spill over 2 ne sai dai na yi, ba zan yi add and drop ba, na rantse ma ka da Allah!!"
Ya na gama faɗi yayi gaba, ya na jiyo ihun su wanda hakan ya tabbatar ma sa cewa Hamza ya fasa kwai, sauran abokan siyasar na su sun fahimci wannan course din da ya ke magana ba kowa ba ne face yar budurwa.
***
Amatullah kuwa ko da ta shiga library, maimakon ta duba littafin da ta zo nema kamar yanda ta faɗawa Zulaikha, sai ta tsinci kanta da neman wannan wajen da ta fara haɗuwa da Dee Yusuf, nan ta samu ta zauna, cikin ran ta kuwa ta na karyata yakinin wani ɓangare na zuciyar ta na ina ma Allah ya sake haɗa ta da shi, ko babu komai duk gidadancinta shi ya nemi yayi abota da ita, duk da dai ta sha maimatawa zuciyar ta da ahir babu abota tsakanin namiji da mace.
Littafin da ta ke rubuce rubuce ta dauko, daidai shafin course din da su ka gama ba da dadewa ba, wato CHEM 132 ta buɗe, da ke ita theory na ba ta wuya, gashi wannan duk structures ne gaba ɗaya sanda malamin ya ke mu su bayani hankalin ta ba ya wajen. Tagumi ta yi ta na mai karewa rubutun na ta kallo, rubutun dai ita ta yi shi, amma gaba ɗaya kan ta ya kulle sai kawai ta kifa kan ta bisa teburi idanun ta rufe, littafin bude gaban ta.
Bai yi mamakin ganin ta inda zuciyar shi ke da yakinin taradda ita ba. Yanayin da ya ganta ciki ne ya sanya shi zama a kujerar da ke kallan na ta a hankali gudun kar ya tada ita, littafin na ta ya ja gaban sa. Wato yanda Allah ya ma Amatullah kyau da tsari haka ma rubutun ta ya ke. Dee ya tsinci kan sa da shafa rubutun da ɗan yatsa yayinda murmushi ya maye kyakkyawar fuskar shi mai cike da kwarjini, ba dan komai ba sai don ganin course din da Amatullah ke karantawa course ne da ya ke kwararre akai.
Kamshin turaren kamfanin Tomford ya bakunci hancin ta kuma ya kasa gushewa ya sanya ta bude idanu, nan su ka yi ido huɗu. Tuni ta yi zumbur ta tashi zaune ta na mai gyara hijabin ta da ya dan kwanta mata a jiki sanadiyyar kwanciyar da ta yi kan sa.
"Uhum" Yayi gyaran murya cikin zolaya sannan ya kara da
"Sallama gare ki Mama nah, salamu alaikum"
"Waalaikumus salam!! Ni ba Mamarka ba ce ba!!!! Sunana Amatullah!!!"
Amatullah ta tsinci kan ta tana mai amsa sallamar Dee Yusuf a karo na farko a rayuwatar ta duk da a tsiwace ta amsa masa. Cike da jin dadi ya ce
"Kai yau kin amsa sallama ta? Wannan farin cikin ina zan kai shi Mama nah?"
Kwayar idanun ta ta kada, irin sai kuma ka ta yi. Hannu ta mi ka da niyar karɓan littafin ta daga hannun shi, ganin ya janye littafin ya ɓoye a bayan shi ya sanya ta yin karfin halin kai idanun ta cikin na shi wanda karfin idanun shi ya haifar ma ta da faduwar gaba, da sauri ta yi kasa da na ta idanun ta na mai tasbihi cikin zuciyar ta. Shiru ne ya biyo baya, ita dai ba ta kara ɗaga ido ta kalle shi ba, shi kuma ya zuba ma ta na mujiya.
Jin shirun yayi yawa ya sanya ta furta
"Wai me ka ke so ne? Na fada ma ka babu abota tsakanin mace da namiji....."
"Amma akwai soyayya ko Mama nah?"
Ya katse ta, maganar ta sa ta zo mata a bazata, ta ma kasa ba shi amsa kallan sa kawai ta ke. Hakan ya ba shi damar sake furta
" Ba ki amsa min ba, akwai soyayya tsakanin Mace da Namiji?"
Da kyar kamar mai rada ta furta
"Akwai......"
"To ki zaba ko dai ki yi abota ko soyayya...."
"Ina da mijin da zan aura!"
Amatullah ta tsinci kanta ta na mai bashi amsa cikin faɗa faɗa. Hannu ya daga alamar kwantar da hankalin ki, kana ya ce
"Yi hakuri Mama nah ki fahimce ni, yanzu ina laifi idan ina so na kulla kyakkyawar alaka da mu'amala a tsakanin mu?"
"Me zai sa ka so kulla alaka da bagidajiya yar kauye kamar ni?"
Ga mamakin ta sai gashi ya murtuke fuska, cikin nuna rashin jin dadin maganar ta ya ce
" Saboda me ya sa? Saboda me ya sa za ki danganta kan ki da wannan sunaye?"
"Saboda haka wasu mazan su ka dauki mata ma su sanya hijabi irina, duka matan makarantar nan ba su ishe ka abota ba ko soyayya sai ni Amatullah yar kauye....."
"Shhhhhhhhhh"
Ya katse ta ta hanyar dora yatsan sa bisa leben sa, yana duban idanun ta wanda su ka cika da kwalla ya furta
"Hijabi ko suturta jiki abu ne mai muhimmanci ga addini, abu mai daraja shi ake suturtawa, fitar da tsaraici shi ne kauyenci da gidadanci Mama nah, hijabin ki abun sha'awa ne ga duk wanda ya san darajar diya mace....."
Baki ta buɗe ta na kallon shi, bai gushe ba ya cigaba
"Duk Namiji da ya dauki rufe jiki a matsayin gidadanci jahili ne Mamanah, da sutura ba ta da muhimmanci da dabbobi ma za su sanya ai, sutura ita ce banbancin mutum da dabba, hijabin ki shi ne banbancin ki da sauran mata....."
Ya na gama magana ya aje mata littafin ta, tashi tsaye yayi, ya na mai tusa hannun sa cikkin aljihu, ya fitar da yar takarda da biro yayi rubutu, kana ya ce
" CHEM 132 is my favorite, in ki na bukatar haske kan shi ga number ta ki kira ni, na barki lafiya"
Ya juya ya na wannan tafiyar tashi cike da takama, Bayan shi ta bi da kallo, mutanen da su ka san shi sai daga ma sa hannu su ke mata da maza, shi ma ya na mayar mu su, har ya fice. Kai bisa teburi ta kifa, yayinda zafafa hawayen da ba ta san na menene ba su ka shiga gangarowa daga idanun ta.
Kiran sallah ya nusar da ita zaman da tayi, ba ta yi mamakin ganin