Showing 15001 words to 18000 words out of 98809 words

Chapter 6 - TAZARA COMPLETE by UMMU-ABDOUL & KHADIJA SIDI.txt

murmushin mugunta, domin kuwa yau Allah ya bashi sa'a haƙon sa ya cimma ruwa. Takalmi ya sanya, cikin sakar zuci ya fita neman su Baffannin shi da ya tabbatar zai same su a tare a wannan lokacin bisa ga al'adar su.


Zaune su ke ta wajen masallacin ƙofar gidan Jamoh, gaba ɗayansu in ka cire baba Salihu kamar yadda yaran su ke kiran su, watau mahaifin Amatullah da yanzu ya ke babban hedkwatan gidan rediyo Nijeriya da ke babban birnin tarayya. Baya shigowa zaria sai ƙarshen mako hakan ya sanya babu shi a zaman da su ka maida al'ada duk bayan sallan isha'i. Su kan yi hira da ya shafi zumunci da ma siyasa da rayuwa na yau da kullum.


"Assalamu Alaikum" Saifullahi ya faɗi yana mai tsugunawa haɗe da sunkuyar da kansa kamar wanda yayi wa sarki ƙarya.


"Ango ne da kansa" Baba Hamza ya faɗi cikin barkwanci wanda hakan ɗabi'arsa ce. Dariya aka yi duka, kafin aka ba shi damar faɗin bukatar da ya kawo shi.
Kara sunkuyar da kai yayi sannan ya ce


"Don Allah Alfarma na ke nema a wajen ku a madadin Amatullah, ko babu alkawarin aure tsakanin mu kanwata ce da zan tsaya mata ta samu cikar burinta. Har ga Allah, na so haɗin nan Naji dadinsa ko don kaunar da Goggo mairo ke min amma tun da na faɗa mata musabbabin dawowata take kuka, tare da rokona na janye tana da wanda take so, Baba Zubairu kai ne sheda ai ka ganmu sanda mu ka dawo"


Ya ƙarasa domin kuwa yana da tabbacin Baba Zubairu ya kula da yanayin Amatullah ko da su ka shigo gida.


"Dalla yi mana shiru sakarai, har mu zaka zo ka yi ma halin yan duniya? Tun da ka tafi ƙasar waje ka waiwayota? Yarinyar nan kowa shaida ne babu wanda ya taɓa mata sallama ta fita"
mahaifinsa ne ya tareshi.


"Yaushe za a mata sallama tana abar kyama" Saifullahi ya fada a ransa yana mai takaicin mahaifinsa.


"A'a Anas, amma kuma duk sanda aka kira shi akanzancen auren haka ya ke tsallake kasashe ya amsa kiran ko, ita dai ce, ai tun da aka tura ta jamia nake tsoro"
Fadin Baba Idris wanda ya na cikin masu adawa da karatun ya mace, su yayansa a shekaru goma sha biyu yake aurar da su ko sakandire sai dai wacce ta yi a ɗakinta.


"A'a ban ƙi taka ba, amma ku duba ku ga, daidai da wasika yaron nan bai taɓa aiko mata ba, zai aiko sakwanni dubu daga Babanmu sai goggon sa mairo ke da tsaraba, ai zuciya tana tare da wanda ke kyautata mata ne. Zuwan da yayi ƙarshe sai da innarsa ta ce ba ta ga ya kira yarinyar nan ko sau ɗaya ba, ku duba fa"
Baba Anas ya sake fadi yana mai jin haushin Saifullah don shi ya sani sarai wannan duk shirin sa ne, ya ari bakin Amatullah ne don ya biya bukatar sa.


"Toh in haka ne ya kamata a bata damarta, a kira ta aji wanda take so in ɗan gidan mutunci ne sai mu roki Babanmu ayi abin nan cikin mutuntawa"
Baba Zubairu ya faɗi, take wani dadi ya cika Saifullah, yayin da baba Anas ya ji ba dadi don ba haka ya so ba.


"Na amince amma rana ɗaya za a ɗaura aurensa da Nusaiba tun da itama zaune ta ke taƙi boko kuma babu miji" Baba Anas ya faɗi yana mai mikewa, nan duk wani farin ciki da ya lullube Saifullah ya ɓace ɓat, Nusaiba dai Jikan kanwar Jamo ce aka ɗauko ta daga ƙauyen farin kasa. Tun da ta gama aji shida ta ki makaranta, kanzantar ta da muninta ya sanya babu namijin arzikin da ya taɓa tunkarar ta da sunan so.
"Saifullah ka je za mu nemi Amatullah ɗin" fadin Baba Mahmuda. Nan ya tashi jiki a sanyaye, don a take ya iske ƙoshi ga shi zai yi kwanan yunwa kuma.


***
Da asuba bayan ta idar da sallar asuba ta gaida mahaifiyarta sannan ta ɗauko littafin da ta riko ta fara bitar karatunta.
"Amatullah wai ki zo inji baban Sasa" Nasir Dan Baba Muhammad ya leko ya faɗi, hakan ya sanya ta ajiye littafin ta, ita kanta rashin ganin Baban Sasa tun dawowar ta ya tsaya mata a rai. Dakin Gwoggon ta ta shiga domin shaida mata kiran, amma sai ganin ta tayi sanye da hijabi, ta ce
"Ai har da ni kiran Amatullah, Allah dai ya sa lafiya"


Tare su ka tafi, da sallamar su suka shiga dakin nan su ka tadda babanninta zaune da Shi kanshi Baban Sasa sai daga gefe Saifullah ya natsu kamar mutumin kirki. Gaban Amatullah ne ya shiga faduwa yayinda ta sami waje gefe guda ta zauna. Shi kuwa Saifu kallon nan da ya ke mata na kyama shi din ta hango a idonsa.
Gaida iyayen ta yi ɗaya bayan ɗaya sannan ta gaida shi, don munafunci har da tambayarta ya ciwon kan da fatan ya lafa.
Sai ya juya ga iyayen ya ce
"Ai jiya ina rabuwa da ku na shiga na iske ta cikin matsanancin ciwon kai"


Mamaki ya cika Amatullah wani ciwon kai ta ke yi da yake maganar oho"
Idanun ta ta kai ga fuskar Baban Sasa, ganin yanayin da ya ke babu annuri ya sa ta yi saurin sunkuyar da kai, ko shakka babu akwai abun da ya faru, tunanin da Amatullah ke yi cikin zuciyar ta kenan.


"Amatullah ya mu ka yi da ke sanda za ki je Jami'a"
Baban Sasa ya tambaya kai tsaye hakan ya sanya Amatullah daga kai ta kalle shi cikin jinjina tambayar. Kai ta kara sunkuyarwa kafin ta bashi amsa da


"Alkawarin babu soyayya na ɗauka maka"


"Yanzu me ya faru?"
ya sake tambaya, nan ta yi shiru, zuciyarta na bugawa da sauri da sauri. Satar kallon Saifullah tayi, murmushin mugunta ya sakar mata.


"Ke mu ke sauraro"
Baba Zubairu ne ya yi magana. Baban Sasa ya kara da


"Amatullah ki fada mana gaskiya, zamu baki abin da kike so, duk so na da auren ki da Saifullah babu dole a ciki, da gaske kina da wanda kuka daidaita?"
Gaban ta ne yayi mummunar faduwa, kai shiga girgizawa alamar "ah ah" musammam da ta kai idanun ta kan mahaifiyar ta, ta ga irin kallan da ta ke aika mata cike da sakon magiya.
"Ki dena girgiza kai ki budi baki ki yi magana ke mu ke sauraro!"
Baban Sasa ne yayi magana cikin nuna kosawa.
Baki na rawa ta furta
"Ban karya alkawarin da na dauka ma ka ba Baban Sasa, babu wani da mu ka sasanta da shi...."


Daga Baban Sasa har su Baba Zubairu idanu su ka zubawa Saifullahi, Gwaggo kuwa sassanyar ajiyar zuciya ta saki.


"Menene ma'anar haka Saifullahi? Shin da ma batun da ka same mu da shi yasasshen zance ne? Mu za ka mayar sakarkaru?"


Mahaifin Saifu ne ka maganar a fusace. Shi kuwa gogan cikin rarrashi ya dubi Amatullah, budar bakin sa sai cewa yayi


"Amatullah ki fada mu su gaskiya, kamar yadda na ce mi ki babu mai mi ki dole, mu duka ma su kaunar ki ne, dama na san ba za ki iya fada mu su ba dan girman alkawarin da ki ka daukarwa Baban Sasa, ni kuma ina dan uwan ki ba zan bari ki cutu ta sanadiya ta ba, hakan ya sa na yi recording wayar da mu ka yi a daren jiya...."


Baki bude dan mamaki Amatullah ke duban sa, ba ta tsora ta sai da ta ga Saifullahi ya fito da wayar shi, ya shiga call recording ya kunna tuni muryar Saifullahi da Amatullah ya gwauraye dakin


"Dee Yusuf din, ki na nufin shi ki ke so?"


"Eh shi na ke so, shi na ke kauna, daidai da second daya ban taba jin san ka a rai na ba Ya Saifullahi, Dee Yusuf ya fi ka komai, mutunci, kima, daraja da kuma sanin muhimmancin diya mace.....biyayya shi ya sa na ke iya jurewa har na ke iya sauraran wula......"


"Kar ki damu Amatullah"


"Ni dan uwan ki ne ba zan so a cutar da ke ba, inshaAllah zan yiwa Baban Sasa bayanin ba kya sona, ba za su mi ki dole ba tun da ba kya sona"


Ana kaiwa hakan recording ya dauke. Shiru ne ya biyo baya, Amatullah kuwa da za a tsaka jikin ta lokacin da ba za a ga jini ba tsabagen daskarewa da ta yi zaune kamar matacciya.[1/29, 1:57 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: FIKRA WRITERS ASSOCIATION


TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀


✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL


BABI NA TAKWAS




Shirun da kowa yayi ba ƙaramin ɗagawa Amatullah hankali yayi ba, musammam da ta kai kallan ta ga Gwaggo, yanayin fuskar Gwaggo ne ya sanya hawaye zuba daga idanun ta. Cikin ranta fadi ta ke


"Allah ya sa za ki yafe min Gwaggo"
"Uhum"


Gyaran muryar Baban Sasa ne ya dawo da Amatullah cikin hayyacin ta, nan ta tsincin kan ta tana mai faɗin


" Wallahi Baban Sasa na rantse da Allah ban karya alkawarin da na dauka ma ka ba..... wallahi, dama shi ne kullum ya ke cewa ba ya so na....."


"Shi wa?"
Baban Sasa ya tambaya a dake, yayinda ya tsare Saifullahi da idanu.


"Yaya Saifullahi"


Ta bashi amsa cikin kuka.


"Biri yayi kama da mutum, Ni na ce mu ku wannan yaron da kuke gani zai aikata, dena kuka Amatullah, me ma zai sa ka dauki muryar ta haka ba tare da izinin ta ba? Ka mata adalci kenan? "
Cewar Mahaifin Saifullahi ya na mai nuna shi da danyatsa, Saifullahi wanda be taba zatan Amatullah za ta ma sa haka ba shi ma kai ya sunkuyar cike da fargaba.


"Saifullahi menene gaskiyar wannan maganar?"
Cewar Baban Sasa ya na mai kallan Saifullahi, wanda ya dukar da kai cikin ladabi ya furta


"Baban Sasa ni kuwa me zai sa na ki jini na? Me zai sa na ki Amatullah? Me zai sa na kasa son abin da ka ke so? Har ga Allah ina nan kan baka na na yi mu ku biyayya, shi ya sa ma na aje duk abun da na ke na taho daga uwa duniya domin cika ma ka buri, da wani ido zan kalle ka? Da wani baki zan furta kiyayya ga Amatullah gare ku?"


Idan aka ɗauke Mahaifin Saifullahi da Amatullah babu wanda be gamsu da jawabin Saifullahi ba. Musammam Baban Sasa wanda har gyada kai ya ke cikin gamsuwa da jin dadi, ya furta
"Na gode maka Saifullahi, yanda ka faranta min Allah ya faranta ma ka"
Saifu kuwa wani dadi ne ya sake rufe shi, in da Amatullah ke fuskantar kishiyar haka musammam jin Baban Sasa ya ce
"Ina Amatullah?"


"Na'am Baba"


"Na ji na amince ba ki karya alkawarin da ki ka ɗaukar min ba, Allah ya gani kauna ce ya sanya na so hadin auren nan tsakanin ku da ɗan uwan ki, amma yanayi ya nuna akwai dan targanda saboda haka ga umarni na gare ki......"


Ya dan takaita yayinda idanun sa ke bisa bangon dakin kamar mai nazari. In banda kukan Amatullah babu abin da ke tashi cikin dakin. Kana ya nisa yayinda ya mayar da kallan sa ga Amatullah sannan ya furta


"Ki shedawa ko shi wanene wanda ki ke biɗa, mun bashi sati biyu ya zo ya gabatar da kan shi a gare mu, daga randa sati biyun nan ya cika kuma babu wanda ya zo gare mu da batu na auren ki toh fa ku sheda ranar zan sanya auren Amatullah da Saifullahi wata biyu da izinin rabbil samawati......."


Yayin da hantar Amatullah ta kaɗa, shi kuwa shi kuwa Saifu bakin ciki ne ya sake lullube shi, wannan shi ne ga koshi ga kwanan yunwa, wannan masifa ta tsoho yaushe za ta kare ne haka! Mitar da ya ke ta yi cikin ran sa. Har Baban Sasa ya sallame su kowa yayi na shi wajan. Baba Anas Mahaifin Saifullahi ne ya kira shi daki domin yi masa nasiha akan abun da ya faru. Ita kuwa Amatullah dakin ta ta koma ta ci kukan ta ta koshi. Babban tashin hankalin ta shi ne shin ya za ta yi da fushin mahaifiyar ta da ta san ko shakka babu a kule ta ke d ita, sai kuma na tuggun da Saifullahi ya kulla mata. Tun da take a rayuwar ta ba ta taba soyayya ba, asali ma bata taba ji tana san wani da namiji cikin rayuwar ta ba face Dee Yusuf, shi kuma ba wai ya furta kalmar so a gare ta ba bare ta sa ran zai iya gabatar da kan sa cikin sati biyu domin kubucewa shiga hannun makirin namiji kamar Saifullahi. Abin da ke dan kwantar mata da hankali shi ne idan ta tuna Dee Yusuf ya na ta jaddada mata akwai maganar da ya ke so su yi, gwara ta koma makaranta idan ma son ta ya ke ya fada mata in ya so ta ce idan da gaske ya ke ya kawai ya zo ya gaida Baban Sasa, da wannan ta sami karfin gwiwar fitawo falo.
Kallon da mahaifiyarta ta bi ta da shi ne tun a ɗakin baban Sasa ya kashe mata duk wani kwarin guiwa da take tunanin ta na da shi. Saifullah ya shammace ta, ba ta taɓa jin kunya irin na yau ba duk da ba wani tashin hankali bane iyayen su ka nuna duk da ransu bai so hakan ba.
Tsoron keɓantuwarsu da mahaifiyarta take amma duk da haka ba ta fasa zaman jiranta ba tare da ɗauko mus'hafin da Dee ya bata ta shiga tilawa a cikin suratul Yusuf.
Tana kai Ayar "WA'UFAWIDU AMRI ILALLAH.." taji wasu hawaye na zubo mata tare da jin wani irin ni'imomi na ratsa ta jini da ɓargo. Lallai Allah mai lura ne a kan bayinsa ta fassara karashen Ayar.
'Gashi ya kawo miki ɗauki cikin ruwan sanyi, ku yi aurenku da Dee hankali kwance' zuciyar ta mai kaunar tarayyarta da Dee ta fadi mata.
'Amma ya za ki yi da fushin mahaifa? Shi Dee din ma ya fada miki yana son ki ne' ɗayan zuciyarta mai fidda gaskiya ta nusar da ita, hakan ya sanya ta ji kawai babu abin da ya fi mata fiye da ta isa makaranta ta ga Dee Yusuf.
Shigowar mahaifiyarta ya tsaida mata tunanin da take, bata ce da ita kanzil, amma kwatakwata babu wani rahama ko annuri a tattare da fuskarta.
"Ki yi hakuri Gwaggo shi ya tunzura ni na fadi haka ban san zai yi recording ba" tace tana mai kama kafar mahaifiyarta cikin kuka. Janye kafafunta tayi, tace mata
"Ai duk wanda yace shi bai haifu ba, zai yi fiye da wannan ma" ta janye jiki ta bar ɗakin.
Duk yanda Amatullah ta so ta bata hakuri kafin ta tafi ya gagara saboda gaba ɗaya ba ta dawo ɗakin ba. Haka jiki a saɓule ta yi shirin komawa maranta, cikin shigar ta da ta saba wato hijab.
A kofar gida ya ganta, ta tsayar da mai keke kenan domin fitar da ita titin da za ta hau Bus.
"Malam jeka abin ka"
ya faɗi yana kallon ɗan keke. Kallon sa take, in ba ƙarya idon ta ke mata ba farin ciki ne tsantsa a tattare da shi.
"Mrs Danliti Yusuf ya dai? Zo na taimaka na rage mi ki hanya"
yace yana mai buɗe mata motar, har ta yi niyyar wucewa ta hango Baba Muhammadu kuma idanunsa akansu. Murmushi ta sakar masa kana ta shiga ciki tana mai faɗaɗa murmushi ta.
Suna wuce harabar gidan su ta gimtse fuska tare da fad'in
"Menene amfanin hakan da ka ke yi? Menene afanin bata min suna a wajen iyayen mu? Menene amfanin mutum mai fuska biyu?"
Shiru ya mata kamar ba zai amsa ba, kafin daga bisani ya ce
"Kin san duk a cikin iyayenmu mata ban da sama da mahaifiyarki. Ba wai ina son bata ƙi a wajan iyayen mu ba ne, ba wai na ƙi ki bane fa. Akwai tazara a tsakanin mu, har ga Allah ke ba irin matar da na ke burin aure ba ce, you're too local for my liking, ina san wayayyiyar mace ta burgewa wanda duk wanda ya ganta zai san ta amsa sunan ta mata ga Saif."
Ya fada ne ya na mai kallan ta ta wutsiyar ido, ya kara da
"Kin ga wannan Danliti da ki ke so?....."


"A point of correction, ba sunan shi Danliti ba Dee Yusuf sunan shi!!!"
Ta katse shi cikin kuwa
"Dee din menene shi?"


Nan fa ɗaya dan kuwa ita kan ta ba ta sani ba, kuma ba ta damu da sani ba, ta dai fi dangata shi da Dauda, ko da yake maganar ce ba ta taba tasowa ba, amma kam yau idan ta ganshi za ta tambayi shi, da ma duk wani abu da ya shafe shi. Tunanin da take yi cikin zuciyar ta kenan.


"Kin yi shiru kar ki ce min baki san cikakken sunan wanda ki ke ikirarin ki na so ba?"


"Ina ruwan ka toh?"


Kai ya girgiza ya ce
"Babu fa, ruwa na shi ne ki lallabashi ya zo wajan Baban Sasa ko a samu a kashe maganar nan kowa ya huta, dan Allah ki taimake ni Amatullah"


ya ƙarasa cikin lallashi.
Bata iya ce masa komi ba, don ba ta da abin faɗa masa, bakin cikine ya tokare mata ƙirji ta ji ina ma kisa ya halalta da wuka za ta soka masa. Wa zai burge da matar da bai isa ya bada aronta ko dandanonta ga wani ba, watau shi zai yi aure ne ba don ibada ba sai don ya burge mutan duniya ko ina aka shiga a ce Saifullah Jamoh yana da haɗaɗiyar mata. Har ga Allah tsoran magana ta ke kar ya buye yana recording. Sai da ta ɓata fiye da minti bakwai kafin tace


"Menene dalilin ka na kai ni makaranta? Na ce dai ba wani recording ka ke so ka yi ba?"
Dariya ya saka duk da dai ba amsar da ya so ya ji daga bakin ta kenan ba. Kana ya ce
"Toh ke ai godiya ya kamata ki min, gashi sanadiyyar haka an baki dama ki gabatar da Danlitin ki? Ni dai ki min wannan alfarma shi ya sa ma na kaskantar da kai zan kai ki makaranta"


Ta na mai girgiza kai, kasa kasa ta furta
"Assha ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login