Showing 18001 words to 21000 words out of 98809 words

Chapter 7 - TAZARA COMPLETE by UMMU-ABDOUL & KHADIJA SIDI.txt

ka da girma sai na jikin ka"


"Me ki ka ce?"
Ya tambaya cikin kokonton ko kunnan shi ke zagi.


"Babu komai"


Shiru ne ya biyo baya, har su ka isa makaranta babu wanda ya sake tankawa. Bayan sun isa, har ta bude mota za ta fita ya tsayar da ita ta hanyar fadin
"Amatullah aure na da ke ba abu ba ne mai yiyuwa ba, ki tabbatar ki gujewa faruwar shi......."


Kallan shi ta yi cikin ido wanda hakan ya sanya bugun zuciyar shi karuwa domin kuwa be taba sanin haka kwayar idanun Amatullah ke da kyau da karfi ba, a dake ta furta


"Kar ka damu, ni ma ba ka daga cikin mazan da na ke buri a ruyuwa ta, kai da zabin raina kamar haske da duhu ne, inshaAllah Allah zai min katangar karfe da kai!"


Ta na gama magana ta fice tare da mayar masa da murfin mota ta rufe. Yayi kusan minti biyar bai motsaba, shi kan shi ya kasa gane dalilin zaman na shi, tsiwar Amatullah ne ko kuwa idanun ta ne.


Amatullah kuwa tun da ta isa dakin su ta ke gwada numbar Dee Yusuf, dan Saifullahi ya dada tunzura ta, amma ina numbar ba ta shiga. Yanayin damur da ta ke ciki ya sanya Zulaikha fadin


"Amatullah na san ko na tambaye ki ba za ki fada min damuwar ki ba, zan iya cewa tun haduwar ki da Dee Yusuf ba ki kara samin nutsuwa ba....."


"Eh Dee Yusuf, shi ne damuwa ta Zulaikha, tun dazu na ke kiran wayar shi ba ya shiga, sati biyu Baban Sasa ya ba ni, I need to talk to him ASAP, yana ta ce min akwai maganar da ya ke so mu yi, na san ba zai wuce na soyayyar da ya ke min ba, Ni ma Ina san shi Zulaikha, gwara mu hadu ya faɗa min ko Allah zai kawo min mafita...."


Tana maganar ne kamar ta na faɗawa kan ta. Cikin rashin fahimta Zulaikha ta tashi tsaye, tana mai fad'in


"Wata magana kuma? Satin biyu na me Baba Sasa ya ba ki? Me ke faruwa ne Amatullah? "


Kai Amatullah ta girgiza, ta na mai sanya hijabin da ta cire tun shigowar ta dakin ta ce
"Zan mi ki bayani Zulaikha, bari na je na dawo...."


"Amatullah....."
Zulaikha ce ta yi niyar tsayar da ita, ita kuwa Amatullah tuni ta yi hanyar fita ta na mai faɗin
"Kar ki damu zan mi ki bayani anjima"
Ta fice. Bakin gado Zulaikha ta samu ta zauna, cikin ranta kuwa ta na addua'ar Allah ya sa ba abunda ta ke zargi ba ne.


***


Amatullah kuwa fitar da ta yi neman Dee Yusuf ta ke ruwa a jallo, duk da dai babu takamamman in da ta ke da yakinin ganin sa. Ba ta yi nisa da Queen Amina ba ta ji kamar ana bin ta a baya, ko da ta juya ta ga wanda ke biye da ita, yanayin da ta ke kallan shi ya sa shi fadin


"Malama Amatullah ina ta magana ba ki ji ba, ko dai ba ki gane ni ba? Hamza? Abokin Dee?"


Tuni ta faɗaɗa fara'ar ta, ta ce
"Haka fa, yi hakuri ai ban ji ka ba ne, ina wuni?"
"Lafiya lau Alhamdulillah, ko dan ba ki ga mutumin na ki ba ne?"


Tana mai murmushi cike da jin kunya ta ce
"Laa ko ɗaya, wayar shi ma ba ta shiga Allah ya sa lafiya"


"Lafiya lau ya ke, ai kin san yau Thursday suna evening service ne shi ya sa, amma ina ga ai sun kusa tashi yanzu, kuma ni ma ta wajan na yi yanzu, ko za ki zo mu je?"
Yayi maganar ne cikin ran sa ya fatan za ta amince domin ya sami damar hira da ita. Tsabagen idanun ta ya rufe ba ta da buri da ya wuce na ganin Dee Yusuf, sai ta amince, a na ta tunanin ba zai wuce in da su ka saba taran su na Alatu ba duk da dai ba ta gane menene service din da ya ke nufi ba.
Tare su ka dauki hanya ya na ta jan ta da hira, tambayar course din ta da level din da ta ke da sauran su. Ta na bashi amsa ne a takaice, in ban da sakar zuci babu abun da ta ke.
Ganin sun tsaya gaban katan Chochi da ke cikin makaranta, mutane na fitowa daga ganin alama sun tashi daga adduar yamma ne ta na mai waige waige ta ce


"Ya mu ka tsaya a nan? A nan su ke service din ne?"


"Eh mana, ai mostly nan su ka fi zuwa......yauwa gashi nan ma ya fito, Deee!"


Hamza ya kulla ma sa kira ya na mai daga masa hannu, fitowar shi kenan, sanye cikin bakaken kaya riga da wando hatta takalmin kafar shi baki ne. Tsayawa yayi in da ya ke, ganin Amatullah da Hamza mamaki ne ya bayyana a fuskar shi, kafin daga bisani damuwa ya maye gurbin mamakin yayinda idanun sa suka sauka bisa fuskar Amatullah da ke tahowa gare shi, Hamza biye da ita.


"Amatullah......."


Dee Yusuf ya kira sunan ta, ta na mai kallan littafin da ke makale cikin hammatar shi ta ce


"Yusuf......."


"David can you please come?"
Cewar wani Pastor da ya fito sanye da fararen kaya. Ga mamakin Amatullah sai ganin Dee ta yi ya juya ya na mai amsa da
"Yes Pastor"


Baki bude Amatullah ta ke kallon Dee Yusuf yayinda sunan da aka kira shi da shi ke ma ta ihu cikin zuciyar ta


"David!!!! David!!!!David"


Idanun ta kan Dee ta furta
"Dama Sunan shi David?"


Ta yi tambayar ne ciki ciki, amma hakan be hana Hamza ji ba wanda ya sha jinin jikin shi bayan fahimtar abin da ke faruwa, haka kuma ya kasa furta komai bare ya amsa mata tambayar da ta yi.

Bayan Pastor ya sallame shi, Amatullah ta nufi in da ya ke. A hankali ta ke tafiya yayinda bugun zuciyar ta ke karuwa duk sanda ta daga kafa ta ajiye, haka shi ma Dee wanda ya tsura mata idanu har ta karaso gaban shi.


"Yusuf menene addinini ka?"


Ta tambaya ta na mai duban fuskar shi.
"Amatullah da ma shi ne maganar da na ke so mu yi magana....."


"Menene addinin ka?"
Ta katse shi cikin kosawa.


"Christianity, I'm a Christian"


Ya fada cikin yanayi mai wuyar fasaltuwa.


Cikin sanyin jiki ta furta
" Ba ka fada min ba, all this while!!! God you should have told me......!"


"Ba ki taba tambaya ta ba, but I tried to, I wanted to tell you Mamanah duk dai ina tsoran kada hakan ya zame mana tazara a tsakanin mu. Ina son ki Amatullah! ina kaunar ki Mamanah, dan Allah kar addini ya zama tazara a tsakanin mu Amatullah"


Ji ta ke tamkar a mafarki, yau ga Dee ya na fada mata abin da take buri ta ji daga gare shi, sai dai kash ashe akwai tazara mafi girma a tsakanin su. Hawaye ne ya shiga zuba daga idanun ta, yayinda ta fara ja da baya ta na mai girgiza kai.
[1/29, 1:57 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: FIKRA WRITERS ASSOCIATION


TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀


✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL


BABI NA TARA

Ganin ya na tahowa gare ta ya sanya ta juyawa cikin sauri-sauri gudu-gudu ta ɗauki hanyar hostel, ta na jin muryar sa ya na ƙwalla mata kira.


Tsaye ya ke kamar gunki har ta ƙurewa ganinsa, Hamza wanda jikinsa ya riga ya gama sanyi ne ya matso gare shi tare da faɗin


"Dee I'm very sorry, na zaci ta sani ai...."


Hannu ya ɗaga masa alamar yayi shiru, kafin ya sauke hannun bisa kafadar Hamza, ka na ya ce


"Kar ka damu aboki, I understand"


Yana faɗin haka shi ma ɗin gaba yayi yabar Hamza nan tsaye.


Amatullah kuwa ba za ta iya kwatanta halin da ta ke ciki ba, gaba ɗaya ji tayi ta rasa duk wani lakka a jikinta tana mai tsanan kanta.
" Christianity, I'm a Christian"


kalamansa da ke yawo cikin kwakwalwarta, karin takaicinta ga mahaifiyarta na cikin matsanancin fushi da ita, ya za ta yi da iyayenta in su ka gano wanda ta ke so ɗin ba musulmi bane?


"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel" ta faɗi tana mai rike wani ƙarfe saboda jirin da ya ɗibe ta. Daidai lokacin Zulaikha ta taho daga famfo in da ta ɗebo ruwa, a kan idon ta Amatullah ta tashi faɗuwa da kuma wasu mata da su ka taro ta. Ita ta yi musu jagora har ɗakinsu don babu nisa da inda abin ya faru.


Ruwan sanyi zulaikha ta fita ta siyo bayan ta tabbatar da ta kwanta a kan gadonta, tare da kunna mata fanka. Duk a tunanin ta Baban Sasa ne ya cika.
Cike da tausayi ta miƙa mata tare da umurtanta ta shanye. Ajiyar zuciya kawai Amatullah ke yi tana zubar da kwalla mai tsananin ciwo.
"Kina tunanin Allah zai taɓa ɗaura ma bawa abin da ba zai iya ɗauka bane? Ina kika kai tawakallinki? Akwai wani rai da baya jiran mutuwa ne? Balle shi Baban Sasa ai kin san ko ba ciwo sa'o'insa nawa ke Raye?" ta faɗi cikin alhini.


"Zulaikha in Baban Sasa yajin abin da na aikata take bakin cikina zai kashe shi, ban san ya zanyi ba" tace cikin gunjin kuka.
Rungumo ta Zulaikha tayi tana shafa bayanta, tsoron tambayar ta me ta aikata tayi don ba ta son jin abin da ba ta taɓa tsammani ba. Shirun da Amatullah ta ji ne ya sanyata faɗin
"Ashe Dee Yusuf Christian ne" tace kamar tana tsoron faɗi.


"Na sani ai, menene abin damuwa? Ke dai ba ya koyar da ke bane?"


Zulaikha ta ce cikin basarwa kamar bata daɗe da lura da soyayyar da ke gudana tsakanin Dee da Amatullah ba, tun da Amatullah ba ta furta mata itama ba ta yi tajasusi ba.


"Ba kamar yadda kike tunani bane Zulaikha" nan ta faɗi mata duk abin da ke aukuwa tun da ga alkawarin aurenta da Baban Sasa ya ɗauka ranar da ta diro duniya har zuwa ga soyayyar ta ga Dee Yusuf, da kuma sati biyun da Baban Sasa ya ba ta ta gabatar da wanda ta ke so gare su.
"Zulaikha wallahi soyayya irin wacce kana hango ka da mutum a aljanna na ke ma Dee Yusuf, ashe Ahlil Kitab ne, ashe haramci akan haramci nake aikatawa, ashe babu aure a tsakanin mu" tace cikin hawaye da Dana sani.


"Kin san haramcin da kika aikata ɗaya ne, kin san haramun ne ciniki a cikin ciniki sai kika baje hajar da kin san an riga an siya" tace tana share kwallan da ya gangaro mata na tausayin kawarta.


"kin san jimlar da ta fi kowace jimla zama ƙarya?" Zulaikha ta tambaya a sukwane. Girgiza kai Amatullah ta yi don bakin ta ya mata nauyi, istigfari kawai take a cikin zuciyarta.
"Ina sonki/ka (I love you) Kinga kalmomin sun fi komi zama ƙarya, yau zaku wayi gari Kuna cikin soyayya kamar Romeo da Juliet gobe ku kasance kamar Saddam Hussain da George Bush. Saboda haka maza gyara kuskuren ki. Kin san illar da ke cikin fushin Gwaggo akanki? Kin san mahaifiya ko yaya ranta ya so su a dalilinka kamar zubar da Baraka ne a rayuwarka, san samu ki fara neman gafarar Gwaggo duk da dai ba da niyar ki bata mata hakan ya faru ba"
Kai Amatullah ta gyada cikin gasgata abun da Zulaikha ta ce. Cikin shasshekar kuka ta ce


" Na shiga uku Zulaikha, ya zan yi da wannan haramtacciyar soyayyar da ke cikin zuciya ta? Ko ina ba dadi, rana zafi inuwa ƙuna....."
"Ki roki Allah ya yaye mi ki, Allah ya kawo sauki cikin lamarin ki Amatullah, tashi maza ki yi sallah ki karanta qur'ani za ki sami sauki"
Da wannan Amatullah ta tashi, alwala ta ɗauro nan ta dukufa gaban Allah cikin namen ɗoki


***
Yanda Amatullah ke cikin baƙin ciki da alhani, ɓangaren Dee ma hakan ya ke, duk yanda ya so yayi magana da ita hakan ya gagara ba dan komai ba sai dan kashe waya da Amatullah ta yi, ya sha zuwa gaban Queen Amina ya zauna ko Allah ya sa ya gan ta, amma babu ita babu mai kama da ita, haka sati guda ya shude.
Amatullah kuwa tsabagen gudun haɗuwa da Dee ya sa ta koma saka nikabi da safa, ta sha wucewa ta gan shi gaban Queen Amina, ko dai ya doka tagumi, ko ya na raba idanu, kuma ta san tabbas ita ya ke nema. Amma gudun abin da zai je ya dawo ya sa ta ƙauracewa kan ta ganin shi duk da kuwa ta na kewansa, sau dayawa idan ta tuna shi har kuka ta ke. Ranar da za su tafi mid-samester break da sassafe ta haɗa na ta ya nata ta yi gida, duk da dai gidan ma wani masifan ke jiran ta, musammam idan ta tuna fushin da Gwaggo da ta ke yi da ita, da kuma Saifullahi, gashi cikin satin biyun da Baban Sasa ya bata sati daya kacal ya rage mata.
Kamar kullum, yau ma ya na fitowa daga lectures Queen Amina ya nufa. Kallo ɗaya za ka ma sa ka tabbatar da rashin kwanciyar hankalin da ke tattare da shi. Yanayin zirga zirgan dalibai ya ragu sanadiyyar hutun mako ɗaya da aka tafi, amma hakan bai hana Dee samun waje ya zauna ba idanunsa kan kofar Queen Amina. Kamar kullum yau ma Amatullah shiru, hannu ya sa ya ɗauko wayarsa, ya sake kira karo na ashirin kenan a ranar, abin da ya saba ji yau ma hakan aka ce, wato
"The number you dialed is switched off"


Cikin damuwa ya na shirin tashi ya tafi ya hango wata ta fito daga Queen Amina, idanun shi kan ta ya na mata kallon sani har ta motso kusa da shi, sai a sannan ya gane ta, ko shakka babu ta na daya daga cikin matan da ya taba ganin Amatullah da su. Cikin sauri ya tashi ya na mai fad'in
"Salamun alaikum, sannu ko Mamanah"


Ganin da ita ya ke ya sa ta tsaya cikin fara'a ta amsa da
"Waalaikumus salam, sannun fa"


Ta amsa a takaice.
"Ni kuwa kamar na san ki, na taba ganin ki da Amatullah, ke kawar ta ce ko?"


"Kwarai da gaske, ashe za ka gane ni, ina wuni ya karatu?"
Cewar Maman Jafa'ar wacce farin cikin Dee ya gane ta ya mamaye fuskar ta.


" Lafiya lau, mun gode Allah. Ina mutuniyar ne? Ina fatan dai ba har ta wuce gida ba"
Dee Yusuf ya tambaya ya na mai fatan samin hadin kai a wajen Maman Ja'afar. Maman Ja'afar kuwa wacce sam ba ta san halin da Amatullah ke ciki ba, zuciyar ta ɗaya ta ce
"Ai fa tun sassafe ta wuce dan ko nima ban same ta ba, ka gwada wayar ta kuwa?"
"Eh na kira a kashe, gashi kwatancan gidan na su da ta min ne ya dan kwanta min"
Cewar Dee, cikin ran sa roko yake Allah ya sa Maman Ja'afar ta bashi abinda ya ke bukata. Nan ta ke Allah ya amsa ma sa, jin Maman Ja'afar na fadin


"Ai fa gidan na su Amatullahi ne cikin lungu, bari in gwada sake yi ma ka kwatancen ko za ka gane......."


Nan ta kwantata masa gidan tsaf, Dee Yusuf na mai godiya su ka yi sallama. Maman Ja'afar kuwa cikin jin dadin ashe dai Amatullah da Dee soyayya ta habbaka har ya na neman gidan su shi ne ba ta fada mu su ba, Allah ya hada su kuwa za ta sha tsiya, ta tafi zuciyar ta cike da farin ciki.


****
Komawar Amatullah gida bai sa ta samu wani kwanciyar hankali ba. Sai da ta gaishe da Baban Sasa da su baffaninta sannan ta shige gida. Daga Baban Sasa har su Baba Zubairu babu wanda ya mata maganar auren ta, ko na wanda ake jira ta turo, wanda hakan ba karamin sauki ta samu ba. Gwaggo kuwa ba ta sake zani ba, har ila yau fushi ta ke da diyar ta ta, dan haka bayan ta gaishe ta dakin ta ta shiga ta yi gum kamar daddawar daka.
Da la'asar bayan ta idar da salla ne ta yanke hukuncin fita can babban tsakar gida ita ma ayi kai kawo da ita, duk da dai ta na tsoran abun da zai je ya dawo. Sanye ta ke cikin riga da siket dinkin atamfa, atamfar kore ne da ja. Sanin yanayin gidan na su ne ya sanya ta sanya hijabi.
Ta tarar da duka matan gidan zaune a tsakar gida bisa ga al'adar zamantakewar gidan, kowacce mata na hidamar gaban ta, wato kujiba kujibar daura na dare, Matar Baba Zubairu ce ke mai daka, sai kuma matar Baba Muhamadu wacce ke yin tankade. Sauran yanran kuwa tare su ke da Mahaifiyar Saifullahi wacce su ke kira Hajiya tare da Gwaggo, kowa da nashi tiren dauke da shinkafa yar hausa sun dukufa ana ta tsinta.
Ganin ta budar bakin mahaifiyar Saifullahi sai cewa ta yi
"Ah ah su amare ashe ana ganin ku a tsakar gida?"
Sai a sanannan kowa ya lura da ita, Gwaggo kuwa takaici ne ya sa ta dauke kai, dan tabbas ta san fitowar Amatullah tsakar gidan nan babu abin da zai jawo mata sai bacin rai.


"Sannun ku da aiki Hajiya"
Cewar Amatullah yayinda ta sami waje kusa da daya daga cikin kanan na ta, ta na mai sa hannu cikin tsintar ba tare da ta kula da kallon da Hajiyar ta bi ta da shi ba, cikin ran ta kuwa fadi ta ce ba a banza Saifullahi ke da hali irin na sa ba, gado ba karya ba ne.
Daga waje kuwa Saifullahi ne zaune bisa benci, abin duniya ne ya ishe shi, gashi dai sati ɗaya ya rage amma Amatullah shiru ta ki kawo wanda ta ke ikirarin masoyin ta ne, babban abin tashin hankalin sa bai wuce zaman Nigeria ba, Allah Allah ya ke ya hada 'yan komatsan sa ya tafi. Ya na cikin wannan zurfin tunanin sam be ji alamun mota ba, bare ma ya san da tsayuwar ta. Haka kuma jin an furta


"Kai yaro ya ka nan, nan ne gidan su Amatullah?"


Bai sa shi daga kai balle ya kalli wanda ke tambayar da wanda aka tambaya ba.


"Eh nan ne"


"Shiga ka ce ta zo ana sallama da ita"


Yaro ya amsa da toh, har yayi gaba ya dawo ya na mai faɗin


"In jiwa zance?"


Shiru yayi kamar mai nazari, kafin daga bisani ya furta


"Ka ce in

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login