Showing 54001 words to 57000 words out of 98809 words

Chapter 19 - TAZARA COMPLETE by UMMU-ABDOUL & KHADIJA SIDI.txt

ba ƙaramin batawa Saifullahi rai ta yi ba, a fusace ya ce


"Idan ba ballagaza ba wace mace za ta yi tunani irin na ki? Mijin ki ya dena cin abincin ki maimakon ki duba dalilin yin haka ki bashi hakuri ina ke lasisin dena girkin gaba daya ki ka samu ko?"


"Ayya mana ya Saifullahi, me ya sa ba ka min adalci ne saboda Allah da manzan sa? Kullum fa ina ma ka girkin nan kafin na je makaranta na aje maka, Amma haka zan dawo na kwashe kaya na, hakan kuma ba zai hana na maka na dare ba, shi ma haka zan kwasa da safe ba tare da ka taba ba, dan yau daya ban iya yi ba saboda ba na jin dadi sai ya zama matsala? Wani dalili zan tambaye ka bayan na riga na san dalilin na ka ba zai wuce na cikin da na ke dauke da shi ba?"


A fusace ya na mai nuna ta da dan yatsa ya ce
"Ni ke mayarwa magana haka? Har kin iya tsaurin idanun da za ki iya mayar min da martani?"


Amatullah na mai dafe kai tsabagen yanda ta ji ya na sara mata ta ce


"Auzubillahi minan shaidanir rajim!"


"Ni ne shaidani Amatullah? Ni ne shaidanin na ki?"


Cikin sanyi ta na mai kaskantar da kai ta ce
"Allah ya ba ka hakuri, dan Allah ka yi hakuri wallahi ba na jin dadi Ya Saifullahi, Allah ya huci zuciyar ka"


Ya na mai huci kamar maciji ya ce
"Malama ba hakurin ki na ke bukata ba! Ki tashi ki shiga kitchen ki dafa min abinci, tuwon shinkafa na ke so da miyar bushesshen kubewa"


Kallan sa ta ke cike da mamakin rashin imanin sa, a hankali ta ce


"Wallahi ban da lafiya...."


"Ina ruwa na? Ba ke ki ka zabi ki yi rashin lafiyar ba! Ki tashi ki dafa min dinner jor!"


Ya koma kujera ya kame ya na hura hanci. A daddafe Amatullah ta tashi ta shiga kitchen jiri na dibar ta haka ta kokarta ta daura tuwan nan. Kafin ta gama ta zauna a kasan kitchen din ya kai sau goma.


Ko da ta gama ta shiga falo ɗauke da kula sai ganin shi ta yi da robar take away gaban shi, ya hakimce ya na cin fried rice da kaza. Idanu cike da kwalla ta ce


"Ayya mana ya Saifullahi, duk wahalar nan da ka bani ashe ka na da abin da za ka ci dan Allah? Me ya sa haka?"


"Saboda na isa, dole sai na ci abin da ki ka dafa ne? Ina da damar canza shawara"


Kular ta aje in da ta saba ba tare da ta sake tanka masa ba ta shige dakin ta. Shi kuwa dadi har ran shi dan ko shakka babu ya san yau ba karamin kuntatawa Amatullah yayi ba.


Ta na yin sallar Isha'i ta yi wanka ta bi lafiyar gado tsabagen yanda ta ke jin jikin ta, gashi gobe ta na da sammako lecture din safe gare ta. Ba ta yi cikakken awa da kwanciya ba bacci ya dan sace ta sai ji ta yi mutum kusa da ita. Hankali tashe ta ce


"Ya Saifullahi lafiya?"


Dankuwa ba ta yi zatan zai shigo mata ba. Cike da takama ya na mai jawo ta jikin sa ba tare da ya damu da kunna wutar dakin ba ya ce


"Hakki na za ki bani"


Hankalin Amatullah ba karamin tashi yayi ba jin abun da ya zo da shi, kana cikin magiya ta ce


"Dan girman Allah ka yi hakuri, wallahi, wallahi ban da lafiya ya Saifullahi, ka bari na sami sauki...."


"Ki na nufin na bari ki haihu? Wa ya ce mi ki za ki sami lafiya muddin ba haihuwa ki ka yi ba ko zubar da cikin nan? Ba zan iya jira ba, hakki na nake so yanzu ma kuwa..."


Ganin abin da ya taka ya sanya Amatullah ta yi shiru ba ta sake tanka masa ba, kyele shi ta yi yayi kidin sa yayi rawan sa, sai hawaye da ke bin kuncin ta daya bayan daya. Sai da ya gama biyawa kan sa bukata ba tare da ya tausaya mata ba sannan ya ja gefe yayi kwanciyar shi.


Tsanar da ba ta taba yiwa wani ɗan adam ba haka ta ji na Saifullahi na ratsa zuciyar ta. A daddafe ta shige bayi domin ji take ba za ta iya kara minti biyar ba ba tare da ta yi wanka ba. Ta yi wankan ne tana mai fatan ba za ta fito ta tadda shi a dakin ba, Amma abin takaici haka ta fito ta ga ya kunna wutar dakin in da yayi rashe rashe bisa kan gado ya na waya. Kallan sa ta yi cike da takaici Jin ya na furta


"Haba mana Ayush kin san yanda na ke san ki kuwa? Ke kaɗai ce macen da na ke kauna, sauran mata ai suna su ka tara...... "


Amatullah na mai kawar da kai ta bude wardrobe din ta domin neman wata rigar baccin, tsabagen tsanar Saifullahi ya sa ba ta san mayar da wanda ta cire, Jin Saifullahi ya ce


"Albishirin ki toh? Baban Sasa ya amince next week za su zo kawo kudin aure gidan ku......."


Cak Amatullah ta tsaya yayinda wani sabon jiri ya shiga kwasan ta har sai da ta sami waje gaban wardrobe din ta zauna dirshen. Saifullahi kuwa da ya lura da halin da maganar ta shi ya sanya Amatullah ciki tuni ya cigaba da jaddada soyayyar shi ga Aysuh. Zafafan hawaye ne su ka shiga fita daga idanun ta, ta na mai neman taimakon ubangiji ta samu ta ja wani doguwar riga da Allah ya sa ta kai hannun ta kan shi, tana rike da rigar ta bar masa dakin.


A falon ta sanya kayan ta, kan doguwar kujera ta kwanta, maganar Saifullahi ke mata yawo a kunne


'Albishirin ki toh? Baban Sasa ya amince next week za su zo kawo kudin aure gidan ku'


Duk da dai ta san yayi ne dan ya bakanta mata, kuma ya ci nasara kwaran gaske. Ta na mai tuhumar Baban Sasa akan amincewa da yayi akan auren Aysuh, duk da dai ba za ta yarda ba sai ta tabbatar da maganar tukun, dan kuwa idan haka ne da Baban Sasa bai kyauta mata ba cewar Amatullah cikin ran ta in da Tasha kukan ta ta koshi, ta na ji Saifullahi ya koma dakin sa amma ta kasa tashi ta koma na ta, sai wajan ukun dare bacci barowo ya sace ta.


****
Washagari ta nemi izinin zuwa gida idan ta tashi daga makaranta, ya hana ta. Dan haka sai a waya ta samu ta yi magana da Gwaggo. Yanda Gwaggon ta ke mata hanya hanya na game da batun auren Saifullahi ya tabbatar mata da maganar hakan ta ke. Gaba ɗaya ta rasa nutsuwa, hatta lectures din ranar kasa gane su ta yi. Gashi Saifullahi ya fito mata da saban salo na neman hakkin sa duk dare, kuma bayan ya gama kuma ya kira Aysuh a waya Amatullah na ji ta na gani, idan ta yi magana ya ce matar da zai aura ne ko za ta hana shi abin da Allah ya halatta ma sa ne.


Ranar da abin ya ishi Amatullah ta yanke hukuncin zuwa gida gun Baban Sasa sai ta taradda Saifullahi ya riga ta, ya je wai Baban Sasa ya kira Amatullah ya mata nasiha, jin zai kara aure gaba daya ta tayar da hankalin ta, shi tsoran sa kar wani abu ya same ta ko ɗan da take ɗauke da shi. Dan takaici ma kasa magana ta yi sai hawaye kawai, shi kuwa Baban Sasa da ya hau magana ya yarda da shi musammam ya san yanda mata ke daukar maganar kishiya tuni ya shiga mata nasiha da rarrashi, har da kada ta bashi kunya yana yaban ta sallah ta kasa alwala. Hajiyar Saifullahi kuwa ko da Gwaggo ta takura Amatullah ta je ta gaishe ta sai ta hau ta da faɗa , har ta na fadin da ba a auren a auri Amatullah.
Wannan tashin hankalin da kuma ɗan laulayin da Amatulah ke fama da shi ya sa ta zama koma baya a makaranta, gaba ɗaya ta zama mara nutsuwa dan ko tayi karatun ma ba koda yaushe ya ke shiga ba, haka kuma ta na yawan fashi saboda rashin cikakken lafiya. A wani asibitin na gwamnati Saifullahi ya mata rigista na awo, cewar shi abubuwa sun masa yawa ba zai iya kai ta na kudi ba, aure ne gaban shi dan kuwa ba gaisuwa ba, hatta ranar auren shi da Ayush an saka, wata tara cif. A wannan hali jarabawa ta gabato har ta yi yi ta gama a daddafe.


***




Cikin Amatullah na wata takwas aka kafe mu su result din first semester, haka kuma ana saura sati biyu su fara exam din second semester.
Da in ta ji mutane na kiran sakamakon jarrabawa da dodon bango dariya ta ke yi, amma wannan karan ta tabbatar da zancen su zahir ne.


A daddafe ta iso inda ake manna sakamako da sanarwa (notice board) Bayan sun ji labarin an manna.
"Wannan ai mugunta ce, a rasa yaushe za a manna sai ana sati biyu mu fara jarrabawa" maman Jaafar ta faɗi cikin mita, da isar su kowa ya shiga duba na shi.
GPA dinta ta duba kafin komai, wanda hakan ya girgiza mata kayan ciki don kuwa 1.26 ta gani, tana matsawa Ramin gaba na CGPA ta iske 2.13, motsin da yaron cikin ta ke yi bai sa ta duba sashin darrusa nan ta iske duk sun dawo mata.
"Inna lillaahi wa inna ilaihi raji'un" ta ce tana mai zama a ginin da aka ma fulawowi da ke gefen su.
Ko wancan jarrabawar ta fita da 4.51 dinta, duk wanda ya Santa ya san ta a matsayin ɗaliba mai daraja ɗaya (first class student). Addu'a ta shiga yi a zuciyar ta don neman ɗauki da agaji wajen Ubangiji.


"muguntar ABU akan ki yau Amatullah, ba fa zai yiwu ba" cewar Maman Jaafar da itama sakamakon ya rikita wa hankali.


"Kin manta C courses uku muka yi kuma duk Kinga ban zarce 47 ba" Amatullah tace cikin ƙarfin guiwa.


"Even though, mu ka dai samu B balle ke, ni takaici na ba wai kasancewarsu C courses ba, kowannensu lamba uku (3 credit unit) gareshi, sannan chain prerequisite ne fa taso Amatullah mu je mu ji ina matsalar take" Maman Jaafar ta ce tana kamo hannunta, bata ce komi ba sannan ba ta Mike ba.


A cikin darrusa bakwai ta ci guda biyu, ta faɗi biyar. Wanda duk son mai sonta bai da abin da zai ce da ita da ya wuce za ta sake maimaita aji uku.
A rayuwar ta Sam ba ta san wani abu wai shi damuwa ba sai a Yan watannin baya. Shafo cikin ta tayi cike da so da kaunar abin da ke ciki duk da tana da masaniyar yana da hannu a faduwar ta jarrabawa.
"Allah ya fi mu sanin daidai maman Jaafar" tace tana mai murmushi.


Ba kawayenta kaɗai ba gaba ɗaya faculty of pharmaceutical sciences an girgiza da sakamakon Amatullah S. Jamoh, maluma da dama sun girgiza saboda an jinjinawa kokarin ta a shekaru biyun farkon ta a jamiar.


***


Sai dare ta samu ta kira mahaifinta, bayan ta kammala duk wani abin da ta san Saifullah na bukata sannan ta shige ɗaki.
Kuka sosai ta sanya masa tana faɗi masa sakamakon ta.
"Babanmu Saura sati biyu jarrabawa, ko na yi ba zan gyara ba sai ma in ɓata, wallahi komi ban iya ba, Babanmu kar a yi withdrawing ɗina" tace cikin Kuka mai tsuma rai. Shiru yayi yana sauraren ta don shi Sam bai san ta inda zai kamo zaren ba. Ya dade da sanin tana cikin damuwa ɓoye masa ake hakan ya sanya shi mata aiken kudi lokaci zuwa lokaci.


"a ina kike zuwa awo" ya samu kansa da tambayar ta. Shiru ya biyo baya don bata son yi masa ƙarya kuma ba ta son sa shi cikin damuwa.
"ki samo medical report Sai ki yi deferring semester ɗin, inshaAllah shekara mai zuwa zaki dawo kan digadiganki" yace ganin ta yi shiru. Nasiha ya cigaba da yi mata yana mai faɗi mata mahimmancin da ke tattare da lafiyarta fiye da komi. A haka su ka yi sallama.
[3/26, 10:18 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀
✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL


BABI NA ASHIRIN DA BIYAR


Cikin iko na Ubangiji da taimakon wata malamarsu Dr. Mu'azatu Usman El-Yakub ta samu tayi differing semester ɗin nata, hakan ya sanya ta daina fita makaranta.


Cikinta kullum girma ya ke ƙarawa yayin da motsinsa ta zama mata abokin hira abokin ɗebe kewa. Idan ya motsa har shafo shi take cike da ƙauna ta ce "Ubangiji Allah ya nisanta ka da mummunar halin mahaifin ka" wani lokaci kuma ta shagala wajen ba shi labarin duniya.


"ka ga rayuwar duniya da daɗi amma cike yake da ƙalubale, kar ka damu ina son ka, ba zan taɓa juya maka baya ba, come sun come rain" ire-iren hirarrakin da ta ke yi da ɗan Cikinta kenan. Wani lokaci ta bashi jinsin mace wani lokaci na namiji.


Banda pad, zaitun, sai riga ƙwaya ɗaya bata ta siya komi ba, su ɗin ma da kyar ta iya fitar da kudin su saboda gaba ɗaya ba ta da hanyar samu.


Saifullahi kuwa sashin da aka tura shi aiki babu wani tsauri, ya kan yi sati biyu bai je Abuja ba in ya je kuma baya wuce kwana biyu zuwa uku.


Ko da cikin ta ya cika wata tara babu abin da ta ke sai addu'a, sosai ta rike YAA HAYYU YAA QAYYUM BI RAHMATIKA ASTAGITHU saboda samun sauƙin haihuwa. Yanda Saifullahi ya maida hankali wajen kammala gininsa a cewarsa nan Ayush za ta tare har mamaki ya ke ba Amatullah, ganin gaba ɗaya bai wani hoɓɓasa ba wajen tanadar mata abin haihuwa tun daga kanta har zuwa na jaririn ya sanya ta sadakar da cewa tabbas Saifullah ba ƙaunar ta yake ba.


Duk halin da take ciki baya dubawa yake kwasan romon sadakinsa. Bata taɓa hana masa ba, ta yanke ƙauna daga sake samun jin dadin aure, ta kaddara a ranta kila cikin ya zama ajali a gareta.
"Ki dage da Addu'ar sulhu da ƙulla soyayya tsakanin mutane" shine shawarar da goggonta ke bata a duk lokacin da ta kai mata kokenta ya sanya ta ke barin ma cikin ta. Hakan bai hana mata yawaita faɗin

ALLAHUMMA ALLIF BAYNA ƘULUBINA, WA ASLIH ZATA BAYNINA WAHDINAL SUBULA-S-SALAM. ALLAHUMMA ALLIF BAYNA ZAUJIE WA IYAYYA BI SHAFAQATIN WA RIDAAN WAL WI'AAM.


Tana yi don samun salama da soyayya a gidan aure, ta san Alƙalamin kaddararta ya riga da ya bushe amma wani sa'in ta kan ji ni'ima da rahman Ubangiji ya lulluɓe ta.


***
Ana saura sati uku su koma makaranta sabon shekara ta fara naƙuda. Da farko ba ta ɗauka da gaske ba sai da ta fara jin ba za ta iya jure zafin ba. A hankali ta isa ga Saifullah wanda ya zauna ya tasa kallo a gaba yana yi yana kyakyata dariya shi kaɗai yana jefa ci cin ɗin da ta masa a baki.

"Ya Saifullah taimaka ka kai ni asibiti, inaga haihuwar ce ta zo" tace cikin cije leɓe. Kallonta yayi a sheƙe wanda hakan yayi daidai da ƙarar wayar sa, bai kula da ya bata amsa ba ya ɗaga wayar.


"Babe how far" ya faɗi wanda hakan ya tabbatar ma Amatullah Ayush ce ta kira. Nan ta ji wani murɗawan ciki da bata san lokacin da ta tsuguna tana mai ambatan "Wash!" ba. Maimakon ya kula ta sai tsallake ta yayi ya fice daga gidan.


Hawaye mai zafi ya zubo ma Amatullah, gaba ɗaya ta sadakar a wajen za ta cika don ba ta da mai taimakon ta sai Allah.
Tana cikin mukurkusun ta jiyo sallama, hamdala ta yi don ta san in ba Allah ba babu wanda ya turo mata ɗauki.
Makociyarta ce ta shigo sa charji, nan ta ganta cikin naƙuda.


"Subhanallah! Pharm kashe kanki za ki yi?" tace tana tallafo ta zuwa kujera.


"bari na ma Baban Huda magana ya kaimu Layin sarki" tace tana mai ficewa.
Ba tare da ɓata lokaci ba ta dawo ta kamo Amatullah ta taimaka mata zuwa cikin mota, sannan ta koma ɗauko kayan da Amatullah ta faɗi mata in da ta ajiye.


Asibitin primary health care da ke Layin sarki su ka nufa, da kyar aka amince da ta haihu a wajen saboda ƙaida ba sa karɓa haihuwar fari da na wacce ta yi fiye da biyar.


Bayan doguwar naƙuda na kusan awa uku Amatullah ta sambaɗo ɗanta da daga faɗowarsa ya karaɗe asibitin da kuka.
Nan aka kimtsa ta, aka ɗinke ƙarin da ta samu, sannan aka kai ta ɗakin hutu.


***
Saifullah kuwa fitan da yayi saƙo ya amso na wani leshi da Ayush ta sanya ya siya mata don sawa a akwati, leshin yayarta ke siyar da shi Dubu ɗari da hamsin.


Saman gadan ɗanmagaji yaje ya same su in da za su wuce Abuja daga Kano su ka tsaya su ka bashi. Tun a hanyar dawowa halin da ya bar Amatullah ke masa gizo, nan ya tuna da zancen
"mai naƙuda ƙafarta ɗaya na duniya ɗaya na lahira ne"


Hakan ya ƙara masa matsanancin tsoro ya ƙara gudun motarsa zuwa gida.
Kamar yadda ya sa rai tana ciki, ya zata ganin gate ɗin gidan kamar yanda ya barshi.


Cikin sassarfa ya isa cikin gida amma babu ita a falo da ya barta tana muƙurƙusu, ya shiga ɗakuna babu ita, ya duba bayan kitchen babu ita, take ya ji wasu zufa su ka fara keto masa.
"Inna lillaahi wa inna ilaihi raji'un" yace yana mai kai komo a cikin gidan ko tana wani lungu ne cikin rashin hayyaci.
Wayar sa ya ɗauko ya kirata sai jin ƙarar wayarta yayi a ɗaki.


Addu'a yake ba kakkautawa don baya son abin da zai haɗa shi da Baba Anas a wannan Marra. A haka ya fito zuciyarsa na bugu da niyyar zuwa Amaru don yana da yaƙinin can ta nufa.
Ya fito kenan ya iske makocinsa na shirin shiga motarsa.


"Engineer ashe kana gari"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login