Showing 93001 words to 96000 words out of 98809 words

Chapter 32 - TAZARA COMPLETE by UMMU-ABDOUL & KHADIJA SIDI.txt

dana wuce shi" yace yana mai rage murya zuwa na mai roƙo.


"Allah" tace a mamakance.


"Wallahi kinji na rantse miki" yace yana yar dariya, itama taya shi dariyar ta yi kana ta ce.


"ni kuwa sai nake ganin kamar warin nan ya fi komi tafiyar da tunani na, amma dai ka bani lokaci zan yi istikhara akan aurenmu. Kuma ka ga jarrabawar mu na kusanto mu, zuwa dai ƙarshen semester dinnan sai mu tsayar da magana. Bari na koma aji kar na rasa da yawa" Juyawa tayi tana kai aya.


Farin ciki sosai ya shiga yi, don gaba ɗaya ya hango nasara ne a cikin haka. Tayi dan tafiya kaɗan ya ɗan ɗaga murya ya ce


"Don Allah a dinga ɗagan waya"


Kai kawai ta ɗaga ta wuce abin ta. Addu'a ta ke ta sake ganin Dee don tun da ya kirata din nan ba ta sake ji daga gare shi ba, ya kan aiko mata da kyaututtuka da gaisuwa daga Mimi amma bai kira ta ba balle ya nemi ganin ta.


Addu'ar ta bata amsu ba don bata ganshi ba, aji ta wuce ta iske malamin ya fita, Mimi kuwa kallon tuhuma take ta mata, sai ta bata dariya.


"Kin san tun last week yake zarya"


Mimi tace tana yamutsa fuska. Dariya Amatullah tayi ta ce


"Wallahi ba ki da kirki, baban babyn naki"


"A'a fa shi da kanshi ya ce ba na shi bane, atoh!" nan din ma dariya Amatullah ta yi sosai, ita kuwa mimi cunkus tayi kamar za ta fashe.


"Wai har period nawa ake a gama waiting period din ne" Ta tambayi Amatullah cikin tuhuma, dariya tayi ta ce.


"Wani waiting period kuma, ba ki ga sai samari nake yi ba, ai yanzu yanda kika san iska haka nake free" tace tana mai shagala hannu ta wuyan Mimi. Ita kuma ba ta ce komi ba sai wayar da ta kara a kunne.


"Kasan Allah Dee ta gama, ka tsaya kana kallon har kwaɗo ya maka ƙafa"


ta ce tana katse wayar, ba ta ce ma Amatullah komi ba, ta haɗe littafanta ta saka a jaka, ta fice daga ajin a nufin ta yi fushi. Cikin sauri ta bi ta, tana mata magiya.


"Ai na ga baki da kirki ne, and I wanted telling you something, shike nan kowa ya riƙe sirrin sa" tace tana fisge hannun ta da ta kamo.


"Nooo Mimi, wallahi ba haka bane, kiyi hakuri, kin san dai a kan Dee na san soyayya, kuma so ɗaya shi na ba, Haba ƙanwata" tace tana mai rungumarta.


Dariya Mimi tayi kana ta ce
"Laa ilaha illah Allah Muhammad Rasulullah, tabbas babu addinin gaskiya sama da musulunci, na yi imani da Allah ɗaya ne kuma Annabi Isah Annabin Allah ne ba ɗansa ba"


Kuka Amatullah ta saki, kuka sosai take tana rungumar Mimi.


"Muje Mimi kiyi wanka, Mimi kin musulunta, Mimi yanzu duk wani zunubi da kika aikata an yafe miki, Mimi littafinki sabo ne dal babu datti ko ɗaya a ciki"


Amatullah tace kamar mai sumbatu, abin da bata taɓa tunani ba, bata taɓa taya ma Mimi musulunci ba tana dai ƙokari wajen haska mata ni'ima da ke tattare da musulunci.


"Wai tun yaushe kika niyyata" tace mata yayin da su ke tafiya.


"Tun bayan musuluntar Dee, sosai yake bani littafai na musulunci ina ganin babu addini da ya daraja mutum sai musulunci, it's a religion full of humanity. A musulunci fa na ga in kana son ka ci nasara sai ka sa wani yayi nasara, a musulunci na ga yanda ake bayani akan duk abin da ya shafi rayuwa, daidai da yanda za a zauna a toilet. Maman Emjay sai in na yi comparing da halin musulmi sai naga gaba ɗaya ya sha bambam da abin da ke littafansu.
Dan zaman da muka yi da ke, naga yanda kike da tsantsan amana, idanunki basu taɓa rufewa akan abin da zaki samu ba balle ki hillace mutane ki samu, naga abubuwa da dama kina kamanta yanda aka siffanta manzo SAW ne, sai na yarda da cewa, lallai musulunci ba halin musulmai kaɗai za a duba ba, a karanta a Santa sai a kamanta.
Dee ya taɓa ce min in duniya sun haɗu suna aikata abu, ba zai taɓa canza haram ya zama halal ba, abubuwa dai da dama mai cike da jinkai na gani a musulunci"




Tun da ta fara Amatullah ta ke kallonta, zuciyar ta fal da farin ciki, godiya take ma Allah har su ka isa.


***
Ayush ta gama amincewa da kalaman Saifullah, hakan ya sanya gaba ɗaya ba ta tuna ta nemi Jamila ba har sai da ta ga an yi satin da ya ce aiki zai masa yawa, an yi na biyu ana sati na uku sannan hankalin ta ya tashi.


"Saif ni kam wai me muke ciki ne" tace bayan ta tsaya jiran sa har ƙarfe sha biyun dare da ya kan shigo mata gida.


"ki duba ki ga fa yanzu nake dawowa, na gaji aiki ne sai godiya wallahi, amma ki shirya jibi inshaAllah sai mu je" yace yana wuce ta zuwa ɗaki.


Bata musa masa ba ta amince. Haka su ke rayuwar su, ba a sake jin su ba amma kuma ba wai suna cikin jin daɗi bane. Ko da ta ga an ƙara kwana huɗu sai ta kira jamila, ba ta ɓoye mata komi ba ta faɗa mata.


"Amma ban san ke ɗin wata bi can bace sai yau wallahi. Aka ce miki zai amince ne, kuma kin san ƙarin sati huɗun nan ƙarin wata ɗaya kenan. Gobe zan aiko miki da maganin nan" tace a hasale.


"nagode Jamila you are indeed a savior" tace cikin farin ciki.


Washe gari ko da aka yi azahar an Kira ta saƙonta da aka sa a filin parking ya iso zaria, cikin murna ta figi motar ta taje ta amso. Sai da ta karanta takardar maganin sannan ta haɗiye guda biyu ta je ta kwanta.


Tun tana tsumaye ta ji shiru ba ta ga komi na fita daga jikinta ba. Haka ta yini kwance tana jira, da ta gaji da jira kuma ta fara dubawa nan ma shiru ba komi.
Ganin har an kwana an tashi cikin bai motsa ba ya sanya ta ɓalle kwayoyi huɗu ta jefa a baki bayan ta gama cin kalaci.


"in aka yi azahar baka fita ba don uban ka sauran huɗun zan haɗiye" tace tana ajiyewa kusa da ita.


Bacci ne yayi awon gaba da ita, cikin bacci ta fara jin murɗawan ciki kaɗan kaɗan, ta ɗauka duk wasan yara ne sai da taga gaba ɗaya ta kasa motsin kirki, ga jini ya ɓalle mata ga bayanta ya riƙe sosai.
Da kyar ta ɗago wayarta ta kira saif yana ɗaga wa tace


"zan mutu Saif zan mutu"


"Hello! Hello!!" yake faɗi amma ina bakin nata ya ɗauke gaba ɗaya. Hakan ya sa shi zuwa gidan cikin sauri, ko da ya ido a sume ya ganta cikin jini, ɗaukan ta yayi ya fice ba tare da nemi ɗaukin kowa ba.
Asibiti mai zaman kanta nan kusa da su ya kaita, babu ɓata lokacin aka fara dubata.


Addu'a sosai yake yi da fatan Allah ya sa ta tashi don bai san me zai ce ma iyayenta ba in ta mutu.


Awa uku yayi zaune yana jira kafin likita ya fito ya nemi ganin sa a ofishin sa.
"Gaskiya akwai abin da ta sha da ya nemi ɓarar da cikin jikinta, an yi hoto cikin na nan ɗan sati goma sha biyu da kwana uku. Sai ta huta sosai, sannan sai ta kiyaye abin da za ta dinga kaiwa bakin ta saboda lafiyanta da na yaron" yace masa bayan sun gaisa


"Na gode Dr." Saifullah yace yana miƙa masa hannu.


Sai yamma lis suka koma gida bayan ta sha ledan ruwa ta dawo da ƙarfinta kaɗan.
"Don Allah Ayush kiyi hakuri, kinga garin gajen hakuri kin sa rayuwarki a hatsari. Gobe nake da niyyar kaiki fa, amma kin kasa yarda da ni, yanzu Dr yace any attempt is a threat to your life" yace yana share kwalla, shi hawayen farin ciki yake na yanda Allah ya kare masa ɗan cikin sa, ita kuwa gani take hawayen so da tausayin ta yake yi.


"Naji, amma gaskiya mu bar gidan can, na tsani gidan ni shine kawai damuwata da kai" tace a wahalce.


"daga kin haihu zan kama mana haya, it's a promise. Yanzu kiyi hakuri, ko don samun masu miki hidima ki yi hakuri" haka ya dinga bata baki har su ka isa gida.


Nan ya shiga ɗakin hajiya ya tasa su Najaatu ya sanya su gyara gidan da sanya turare. Suna kammalawa ya sa su yin girkin da za su ci.


Ba su suka samu kansu ba sai wajen bakwai na dare sannan suka sallame ta ba tare da sun bata ki cokali ta lasa ba.


Tun daga ranar Ayush ta maida Najaatu mai aikin ta Sam babu kyautatawa balle tausayawa. A rana sai ta mata girki kala biyar, kala shida ita ba a bata taci ba sannan Ayush ba lallai ta ci ba, a ƙarshe sai ta iske a wanke wanke an ajiye ta wanke raguwa.


Ba ta taɓa fadi ba amma ta fara ba almajirai raguwan abincin da ta gani cikin wanke wanke.


Haka ya faru yau, ta yi farfesun kifi, tun yanka biyu da Ayush ta ci ta ajiye saura, Saifullah da ya zo ya dan taɓa kaɗan aka bar kifi cikin tukunya.


Ko da Najaatu ta ga tukunyar a cikin wanke wanke sai ta fita ta nemi Almajirai ta basu da sauran cuscus su sake.
Ta shigo da tukunyar kenan Ayush ta fito inda take wankewaken ta ganta da tukunyar abinci. Ba ta tambayi ba'asi ba kawai ta fara dukanta, duka sosai ta ko ina.


"Shegiya ɓarauniya meye na kwasan min abinci ki kai ma mayunwaciyar uwar ki, ba cewa nayi ki wanke ba? Ko baki nayi?"


tace cikin hayagaga wanda hakan ya tunzura Najaatu ta tunkuɗeta da faɗin


"uwar ki dai na aika mawa" hakan yayi daidai da shigowar Saifullah da Hajiya da aka je aka faɗa mata kamar dukan Najaatu ake.


"Baki da hankali ne Naja, uwar wa kike kira haka, da kika tunkuɗeta in wani abin ya same ta fa?" ya ce yana taro Ayush.




"ai ba laifin ta bane, ka ga wacce ke aiko min ita nan, kai ba zaman gidan nan kake ba, ni kuma bana son ka dinga ganin bakinsu wallahi kashe ni suke da niyyar yi" Ayush ta ce tana rushewa da kuka.


"Ke Naja me ya haɗa ku" faɗin Goggo da ta shigo Sasan don a idon ta Najaatu tayi rabon abincin.


Tiryan Tiryan ta faɗi masu buɗe bakin Saifullah sai cewa


"Toh in ba sata ba me kika yi? cewa aka yi ki ba almajirai, don ta ce uwar ki kika kai ma abincin ƙarya tayi? Ko ba ɗan kuka ke jawo wa uwarsa jifa ba" ya faɗi yana yunkurin marin Naja.


"Saifullah a kan ido na ta sake ma Almajirai" Goggo ta faɗi tana mai janye Najaatu.


"Toh Goggo in ba hajiya ta kai mawa ba ai hajiya ta sanyata, gaskiya hajiya ki fitar da idon ki akan iyali na, ke kenan ki rasa wacce za kiyi gasa da ita sai matar ɗanki? Ina aka ce dole se na ciyar da ke tunda kina da miji, in dadin kike son ci mijinki ya miki itama mijinta ke mata Haba " yace cikin tsawa tsawa, Hajiya mutuwar tsaye tayi tana nuna shi da yatsa.


" Ni Saifullahi, ni ta kan mace? Allah ya isa nono... "


" A'a hajiya kar ki masa. Yi hakuri, muje don Allah " Goggo tace tana kamo ta, sai a lokacin hajiya ta tuna goggo fa mahaifiyar Amatullah ce, kuma yanzu ita ce ke tallafo ta a lokacin da rayuwa ke shirin kayar da ita.




***


Ayyiriri!!!


Ga biki zuwa maza nemo zanin ɗaurawa


Kun taɓa jin labarin Diamond package?
Idan ba ku da labari ku zo ku ji da ɗumiɗuminsa.


Ba komi bane face DANGARTAKARMU mai cike da SARƘAƘIYA wanda ke haddasa AUREN SHEHU.


Package ne da Ummu-Abdoul, Aisha Yau Kura da Khadija Sidi suka haɗa don Ilmantar da mai karatu gami da Nishaɗantarwa.


Tikitin Karanta littafan nan guda uku Naira dubu ɗaya ne kacal, za a fara siyar da Tikitin 4 ga watan shawwal 1441 in da za a rufe siyarwa 24th ga watan shawwal..


Biki ne na wance da wance, ku hanzarta nemo kuɗin zanen ɗaurawa don kar a bar ku a baya.
[4/23, 10:08 PM] +234 809 229 4372: TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀
✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL


BABI NA TALATIN DA SHIDA


"ki yafe min, ina Amatullah ita ma na yi mata ba daidai ba, a yafe ni"


Cewar Hajiya ta na mai share kwalla. Kai Gwaggo ta girgiza ta ce


"ah ah sam ban taɓa rike ki cikin rai na ba, balle kuma Amatullah da take ɗiyar ki, Allah ya yafe mana baki daya"


"Aameen ya Allah, na gode Allah ya saka da alkhairi, ya bawa Amatullah miji na gari"


Gwaggo na mai darawa ta ce
"Ai kuwa dai Allah ya riga ya bata, sai dai fatan Allah ya ara mana rai mu sha biki"


Cike da mamaki Hajiya ta ce
"Toh madallah, Aameen, ko gun su Baban yaran nan kin ga kuwa ban ji ba"


"Eh ai dazun nan shi Baba Anas da Baban ne tare da mahaifin Amatullah su ka yanke hukuncin, idan Allah ya tabbatar nan da wata daya ma su ke so a yi auren"


Gwaggo ta karasa maganar daidai lokacin da su ka zo mararrabar bangaran na su. Nan ta yiwa Hajiya sallama tare da bata shawarar fita sabgar Saifullahi da matar sa. Ta bar Hajiya cikin tunanin ko wanene mijin da Amatullah ta samu haka?


***
Dee Yusuf kuwa tun da Mimi ta faɗa masa Amatullah ta fita idda ya ke mata naci, yayi yayi Amatullah ta dinga zuwa office din sa, ta ƙi, dan haka in dai ba shi da aji toh lalle za ka ga motar shi department din su Amatullah, ko kunya ba ya ji a matsayin shi na malami cikin makarantar. Duk in da aka gama lectures kuwa shi ne ke mayar da su gidan daliban da Mimi ta ke.


Kamar yanda su ka saba, zaune su ke dan harabar gidan Mimi, kasancewar waje ne mai sirri. Tun da ya ɗauko su daga makaranta ya lura da yanayin Amatullah, kamar ta na cikin damuwa. Amatullah ta na zaune da shi ne, Amma zuciyar ta tunanin wayar da ta yi da Baba Anas a safiyar ranar ne, maganar sa ke ta dawo mata cikin ran ta,


"Amatullah na kira ne a matsayin waliyin auren ki da Baba ya bani, ya ba ni wuka da nama akan hukunci da hidimar auren ki, shin akwai wanda kuka sasanta? Idan akwai ki sheda masa muna so mu gan shi gobe idan Allah ya kai mu, bayan magariba in Sha Allah....."


"Amatullah!"


Da sauri ya dago ta na kallon Dee da ya kira sunan ta a karo na uku.


"Wai menene?"


"Babu"


Ta bashi amsa a takaice. Shiru yayi ya na nazari akan ta, ita kuwa rasa yanda za ta tunkare shi da maganar Baba Anas ta ke


"Maman Emjay stop behaving like a chikala! Please kin riga kin wuce wajan!"
Abin da Mimi ta ce mata kenan lokacin da ta faɗa mata yanda su ka yi da Baba Anas, ta kuma ce mata ba ta san yanda za ta faɗa masa ba. Kamar wacce ake zaro maganar daga bakin ta ta ce


"Baba Anas ya kira ni, ya ce ya na so ya gan ka gobe after magrib"


"A haba da Allah?"
Cewar Dee ya na mai washe baki, cike da ɗoki ya ce


"Halan cewa zai yi ya bani ke for better for better"


"In sha Allah"
Cewar Amatullah ba tare da ta san sanda kalmar ya fito daga bakin ta ba. Hakan ba ƙaramin burge Dee yayi ba, ya ce


"Iyye ashe dai ana so ake ta ja min aji har haka"


"Ayya mana Dee"


Cewar Amatullah ta na mai rufe fuskar ta da tafin hannun ta. Ita dai duk sanda take tare da Dee ta kanji ta kamar ƴar budurwa, ta kasa gane yanda aka yi ya ke saka ta cikin wannan yanayi.


"Oh ba ki Sona?"


Ta girgiza kai alamar ah ah, Dee ya ce
"no ban yarda da maganar kurame ba, tun da mu ke da ke ba ki taɓa furta kalmar so gare ni ba Amatullah, do you even love me?"


Amatullah ta sunkayar da kai, ta ce


"Yes I do"


"Yes you do what? Look at me Amatullah"


A hankali ta ɗago kan ta su ka haɗa ido. Idanun shi cikin na ta ya ce


"Say you love me"


Murya can kasan makogaro ta ce


"I love you......"


Idanu ya lumshe sannan ya sake buɗewa, wani kyau da kwarjini ya ƙara a idanun Amatullah da ya sanya ta kasa daina kallon sa, wanda hakan ya sanya shi shagala da kallon kwayar idanun ta da ke sheki. Ya kara faɗin


"Kara faɗa min dan Allah, Say you love me...."


"I love you Dawood, I will always do with all my heart"


Idanun sa cike da kwallar farin ciki ya ce


"Na sha mafarkin wannan ranar, kullum cikin kewar ki na ke, daidai da sakan daya ban daina son ki ba Amatullah duk da TAZARAR DA KE TSAKANINMU a lokaci"


Kasa ta yi da na ta idanun ta cike da nishadi da jin dadi. Ta ce


"Thank you"


"For what?"
Fuskarta ɗauke da murmushi mai kayatarwa ta amsa masa da


"For not giving up on me"


Kallon juna su ke yi cike da so da kauna, haka su cigaba da soyayya cikin Jin dadi da annashuwa kamar ba za su rabu da juna ba a ranar.


***


Washagari Dee ya amsa kiran Baba Anas in da ya umarce shi da ya turo iyayen sa a yi maganar aure. Ranar Dee har sujjada yayi ya godewa Allah. Mahaifiyar shi ya fara shaidawa kafin ya nufi Haɗeja gun dangin Mahaifin sa.


Sun so ace Amatullah budurwa ce kasancewar Dee bai taba aure ba, Amma haka babu yanda za su yi su ka niki gari sai ga su a birnin zazzau, in da aka yi maganar aure, aka sanya wata ɗaya kacal ranar daurin aure.


Tun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login