Showing 24001 words to 27000 words out of 98809 words

Chapter 9 - TAZARA COMPLETE by UMMU-ABDOUL & KHADIJA SIDI.txt

da ƙara masa gishiri da Magi.


***
Da Sallama Amatullah ta shiga ɗakin, hawayen da ke zubo mata bai fasa zubowa ba tashin hankalinta ya ƙaru ganin mahaifinta zaune a wajen.
"Baba gani" tace bayan ta bi su ɗaya-ɗaya tana gaida su.
"Yauwa! Amaryas, ko da yake an ce wannan da zai min kwace ya zo ko" ya faɗi cikin sigar tsokana. Girgiza kai ta shiga yi tana so ta yi magana amma halshenta ya mata nauyi.
"Baban Sasa wallahi ban karya alkawarin mu ba, zaɓinka shine zaɓina" ta kokarta ta fadi nan ta saki sabon kuka a wajen, wanda ya taɓa zukatan baban Sasa da baba Anas kaɗai. Mahaifinta da ke wajen ji yayi kamar ya mauje ta yanda take kuka. Su baba zubairu kuwa da su ka shigo bayan fitan Hajiya ma duk takaici ta basu.
"Toh shi wancan da ya zo wanene shi?" Baban Sasa ya tambaya a dake. Baya son tausayin ta ya ci galaba akansa.
"Dee Yusuf ne" ta ce a can kasan muryarta.
"Ba shi ne Saifullahi ke magana ba" cewar Baba zubairu a harzuke. Shiru tayi ta kara sinne kanta.
"Wanene shi Dee Yusuf din? Me nene ma'ana Dee ɗin" Mahaifinta ya tambaya cike da addu'ar amsar ta ya karyata Hajiya Sadiya. Don duk yadda ya so ya duba bai hango dalilin da zai sa yarsa mai ilimin addini da kokarin kiyaye dokokin Allah ce da soyayya da wanda ba musulmi ba.


"Sec Gen din SRC ne, shi ke mana tutorials din chemistry, past question papers ya kawo min" ta samu kanta da fadi, amma sanin da su ka yi ita ba mai karya bace take su ka ɗago ta.


"Dauda yake ko Dahiru" Baba Mahmuda ya faɗi ganin ta kife su akan asalin sunansa.


"David Yusuf" ta fadi a hankali. Take ɗakin ya kaure da salati, baba hamza ya taso zai kai mata hannu take Baba Anas ya tare shi.
"Fisabilillahi karya kuke so ta muku? Bata ɓoye alakar su ba, koyar da su karatu yake, sannan ina ce Saifullahi ya fara kawo zancen Dee din sannan innarsa ce ta fara kawo zancen shi din ba musulmi bane. Haba ku duba mana"
Baba Anas ya ce yana kare ta, sauran in banda masifa babu abin da su ke tare da aibata ta.
"Babanmu ka duba lamarin nan da kyau, tun kafin a haifi Amatu babu macen da ke daraja ku kamar Mairo, tun da ka ba da ita ga Saifullah ba a taɓa ganin ta da waninsa ba duk da ba a ganta da shi ɗin ba. Duk zamanta a jami'a bincike na ya tabbatar min ba ta fita zancen da wasu ɗalibai ke yi, Babanmu Amatullah ba ta saɓa alkawarin ku ba, kar ka yi mata hukunci akan laifin da ba ta aikata ba" yace yana mai gurfanawa gaban Baban Sasa, hakan ya kara tsinka zuciyar Amatullah tare da ganin rashin kamatan abin da zuciyarta ta aikata na son Dee.
"Kai Anas in an yi magana ka dinga kare Mairo da iyalinta kenan, ni ban san me su ka baka ka sha ba, Salihu ka yi magana mana ka yi shiru kana kallon mu" Baba Idris ya faɗi a harzuke.
"ni kuwa mai zan ce bayan ku ne iyayenta" Baba Salihu ya ce yana mai mikewa da barin falon. Nan su ka haɗu su na ta masifa tare da aibata karatun ƴa mace da nuna laifin Baba Salihu da ya gagara nuna fushinsa akan abin da yarsa ta aikata.
"Baba ba ka ce komi ba" Baba Anas ya ce da Baban Sasa yana mai sunkuyar da kansa.
"Amatullah kin ce Alkawarin mu na nan ko" yace yana mai kallon ta cikin tausayawa, kuka take bilhaqqi kamar ranta zai fita.
"Ehhhh!" tace tana mai jan majina.
"Anas ka amince da bamu ƴarka a matsayin mata" Baban Sasa ya sake fadi yana mai kallon Baba Anas, hakan ya dawo da hankalin sauran da ke falon garesu.
"Baba Zaɓinka shine namu ko ƴar Albarka" yace yana kallon Amatullah. Gyaɗa kanta sama tayi, tana mai share hawaye.
"Toh ku kawo kawo sadakin Dan ku, gobe bayan sallahn Asuba za'a ɗaura aure, sati mai zuwa kamar yadda nayi alkawari zan sanya ranar tariya a maimakon ranar aure" Baban Sasa yace yana kallon sashin da su Baba Zubairu ke zaune. Da haka ya sallame Amatullah.
Cikin sanyin jiki ta ƙarasa ɗakin su, a falo ta zauna amma tana jiyo muryar mahaifinta da goggonta abin da ba ta taɓa ji ba.
"me ya sa kike mahaifiya in ƴar ki ba za ta samu Rahma daga gare ki ba? Kin bincike ta kin ji gaskiyar lamarin ko dokin zuciya kawai kika hau? Amanar da na baki kenan"
Yace, yana fitowa, ganin da ya mata cikin hawaye ne ya sa ya riko hannunta su ka fita, ko da su ka iso tsakar gida kallon ta yayi ya ga hawaye kawai take yi hakan ya sanya shi sa hannu tare da share hawayen da su ka zubo ma Amatullah.
Chan gefen gidan su ka je inda ɗakin kannen Amatullah maza yake, ciro makulli yayi ya bude su ka shiga.
Gefen katifa su ka zauna, ya ciro hankici ya bata ta share hawayen da ya take yi sannan ya ce
"Amatullah!!!"
Ba Ta amsa ba sai ɗago idanunta tayi ta kalle shi.
"Faɗa min gaskiyar abin da ke faruwa, na yarda dake, na san ba zaki taɓa manta inda kika fito ba, faɗa min and I will give you 100% support" yace yana riko hannayenta biyu. Nan ta samu ƙwarin gwuiwa ta faɗi masa duk abin da ya faru tun daga farkon haɗuwarta da Dee Yusuf zuwa abin da ya faru zuwan shi.


"Wani amsa kika bashi bayan ya faɗi miki uzurin sa?"
"Idan za ka karbi addinin ba dan ni ba, ba dan soyayya ta ba, domin soyayyar dan adam abu ne mara tabbas, idan za ka karba domin soyayyar Allah da manzon sa, Ni ma na daukar maka alkawari ba zan cuce ka ba, ba zan bari a cuce ka ba, Zan kare duk wani hikki na ka a matsayin ka na miji na...."
Amatullah ta maimaitawa mahaifin ta. Kai ya ke girgizawa cike da dana sani
"kin san da na shigo aka faɗi min, na ji tsoro a raina saboda ina tsoron kar ace hakkin Binta Sule ne ya kamani"
Ya ce cikin sanyin jiki. Kallon sa tayi cikin neman ƙarin haske. Be gushe ba ya cigaba
"Ajin mu ɗaya da Binta Sule, duk mun shaida soyayyarta da Yusuf Haɗeja. Muna cikin wainda ke mata kallon tubabbiya, muna da hannu a komawarta Christianity. Amatullah Al'ummar musulmi Hausawa na da wannan nakasun, ni ma a lokacin ina da ita. Kwanakin baya mun haɗu a taron yan jarida, na yi kokarin neman gafaranta amma tace min abin da mu ka Aikata ya zama mata gobarar titi a jos"
Numfashi ya sha cikin dana sani ya cigaba da fadin
"Ta so MSS su kula da ita, ta so zama cikin musulunci amma alakar da muka nuna mata mai rauni ce, da shi wannan David din na ki zai karbi musulunci ko shakka babu ni mahaifin ki zan ba ku kowacce gudunmawa, duk da dai zan fi so ki auri dan uwan ki wanda ya ke tsatson ki..."[2/2, 4:48 PM] Safiyya Ummu-Abdoul Writer: FIKRA WRITERS ASSOCIATION


TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀


✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL


BABI NA GOMA SHA DAYA


Shigowa ya yi don amsar abincin dare duk da hakan ba al'adarsa bace amma yanayin da yake ciki ya isa ya hana masa cin abin da yafi soyuwa a gare shi da dare. Har yayi hanyar ɗakin gwaggo Mairo kamar yadda ya saba sai ya canza don baya fatan abin da zai haɗa shi da bagidajiyar yarinyar nan, ya ayyana a ransa.


"Amma dai an yi sakarai wahalalle ya rasa wacce zai ci burin sakawa a motar nan sai bagidajiyar yarinyar nan" ya fadi ya na mai dafa bango jin wani abu ya tokare shi a ƙirji.


"2008 Suzuki SX4 ce fa" ya faɗi tunawa da cewa a ƙarshen shekarar da ta gabata a ka fitar da motar, yayi maitan mallakar ta amma shi a karan kanshi ya san motar ta girmi duk wani ahlin gidan Jamoh a wannan lokacin, sai gashi wacce ya fi gani a kaskantaciya da bai yi tunanin mamallakin keke zai kalle ta da soyayya ba mamallakin dream car dinsa ya zo afujajajan idanunsa dauke da tsantsan soyayya gareta.


Sai da ya kwashe kusan mintuna goma sha biyar yana maida numfarfashi da tattaro natsuwa kafin ya karasa cikin ɗakin mahaifiyar sa
.
"Ku tashi ku bamu wuri" hajiya ta faɗi ma kannensa ganin suna zaune ba mai shirin fita duk da ba wai don sun saba fita bane in ya shigo ɗakin.
"Saki Ranka yayansu, ashe yaron nan da Amatullah ke so arne ne, in faɗa maka ina ji na yi wuf na iske baban Sasa na faɗa masa" tace cikin raɗa, fuskar ta cike da annuri, rasa me zai ce mata yayi, ya rasa yanayin da ya tsinci kansa haka yake kallonta sheƙeƙe bai ga ta in da tayi gwaninta ba balle ta birge shi.


"Kin ga matsalar shegiyar al'adar nan taku ta banza wai kunyar ɗan fari ko, ni na ce miki ina son Amatullah da har za ki taya ni kishi" ya ce yana kokarin saita fushi da ya ji yana taso masa da ga kasan zuciya.


'watau ba ma musulmi bane balle a ce shima ustaz ne yana son ustaziyya' zuciyar sa ta dinga nanata masa.


"Na ga dai duk gidan nan babu wacce ta kamo kafafunta ne a haɗuwa boko da islamiyya, in ka aureta zan tabbata na zarce duk wata mace a gidan nan" ta katse masa tunani, magana take ƙasa-ƙasa gudun fitar da wani gun, duk da ta san ana faɗin bango na da kunnuwa.


"A tunanin ki hajja zan auri wacce ta taso a cikin manyan biranen ƙasar nan ne balle kuma wacce ta taso a cikin zaria, matan da ba su san komi ba sai lulluɓe jiki kamar sauran kuturta. Hajja ki min jagora kar a aura min bagidajiyar can, zan auro miki wacce ta haɗu, wacce duk ta wuce sai an saki baki an bi ta da idanu, ki amince min Hajja" ya ƙarasa rauni cike da muryarsa, shiru ta yi ta lula mafarkin ido biyu, babu abin da ta ke hangowa sai surukar da sanadin ta za ta dinga zuwa haji duk shekara.


"Amma kuma mahaifin ka fa? Ɗazu fa kiris ya kwaɗe ni gaban su Baban Sasa" tace sa'ilin da ta tuna babu wanda zai kawo masu cikas sama da shi.


"Hajja matarsa fa kike, kiyi amfani da damar nan" yace mata kai tsaye. Tunawa da tayi da Madina, kanwar mijinta kuma aminiyarta wacce ba ta san wa yafi tsanar Goggo Mairo ba cikin su biyun.
"Zan nemi madina gobe inshaAllah, duk abin da ake ciki za ka ji" da haka su ka yi sallama, ya wuce ɗakin sa ya rufe, baya ko fatan abin da zai sa ya haɗu da mahaifinsu hakan ya sa ya kuduri niyyar ba zai fita sallan asuba ba.


***


Kwance ya ke bisa gadon sa, duk yadda ya so ya cire tunanin Amatullah da maganganun da su ka yi abin ya gagara. Hamza yayi kokarin jan shi su fita amma hakan ya ci tura, rokan sa yayi da dan Allah ya rabu da shi sam ba ya jin dadi dan haka ba ya san damuwa.
Sanye ya ke cikin farin singileti da gajeran wando. Tun yana juye-juye har ya tashi yana mai lalubar wayar shi da tun dawowar shi daga wajan Amatullah ta ke kashe. Kunna wayar yayi, idanun sa kan fuskar wayar in da agogon kan wayar ya nuna karfe goma sha daya da rabi na dare, lalle ya daɗe kwance domin kuwa Allah kaɗai ya san awanni nawa ya ɗauka nan kwance. Ba tare da ta san abin da ya ke ba ya tsinci kan sa ya na mai danna number Amatullah, ta yi ringing har ta katse ba ta ɗaga ba. Ajiyar zuciya ya saki, yayin da ya furta


"Oh lord I'm so confused I'm going crazy!!"


Number Mahaifiyar shi ya shiga kira ba tare da yayi la'akari da lokaci ba, har sai da wayar ta kusa tsinkewa sai gashi ta daga a tsorace ta furta


"Dan albarka lafiya kuwa ka kira cikin dare haka?"


"Mummy.........."


Dee ya amsa mata yayin da ya nemi abincewa ya rasa. Jin haka Mahaifiyar shi wacce wayar Dee din ne ya tashe ta daga bacci, tashi ta yi gudun kar ta tayar da mijin ta daga bacci. Sai da ta koma falo ta sami waje ta zauna sannan ta ce


"Owk David, yanzu ina jin ka, me ke faruwa? Ba ka da lafiya ne?"


"Lafiya lau Mommy, kawai dama na kasa bacci ne....."


"No David, na san ka kamar yunwar ciki na, hakan nan dan ka kasa bacci ba zai sa ka kira ni cikin dare haka ba, me ya faru my baby?"


Ta katse shi ta na maganar ne cikin nuna damuwa. Numfashi ya sauke sannan ya furta
"Mommy idan har addinin musulunci ya yarda namiji musulmi ya auri mace Christain ko da kuwa ba ta musulunta ba, me ya sa kika musulunta?"


Shiru ne ya biyo baya, domin kuwa tambayar da Dee ya mata ya zo mata a bazata, har yayi tunanin wayar ya katse, ya sake furta
"Hello Mummy? Hello?"


"Yes Son, I can hear you....well kyawawan halin mahaifin ka da kaunar da na ke ma sa ya sanya na ga hasken da ke cikin addinin sa, ya sa min kwaɗayin shiga addidnin, duk da ya ce zan iya addini na ba tare da mun bari dangin sa sun sani ba. Your Father was very kind, da haka duka musulmai su ke da har yanzu ban bar musulunci ba"
Ta amsa masa ta na mai jin dacin rashin mahaifin Dee da har yanzu be bar zuciyar ta ba. Jin Dee yayi shiru ta kara fadin


"Oya it's your time to answer me now, me ya sa ka ke min wannan tambayar? Na san hakan nan baza ka kira ni cikin dare ka na min wannan tambayar ba tare da wani dalili ba, so tell me what is going on, I mean tell me everything kar ka ɓoye min komi"


Shiru Dee yayi yana mai muhawara cikin zuciyar shi na fada mata ko rashin fada mata.


"David......"


"Na'am Mummy"


"Start talking, your Mommy is here for you"


Cikin sassanyar murya ya furta
"Mummy Amatullah ce......"


Sai kuma yayi shiru, ya kasa cigabawa. Cikin bashi karfin gwiwa ta ce
"Ina Jin ka, wacece Amatullah? A ina ta ke? Wani irin dangantaka ce a tsakanin ku? Me ya faru?"
Tambayar da Mahaifiyar ta jero ma sa ne ya sanya Dee bude mata cikin sa, tun daga haduwar shi da Amatullah har izuwa ranar yau in da ya je gidan su Amatullah. Ya kare maganar ne da
"Wallahi Mummy ina kaunar Amatullah, babu abin da ba zan iya yi ba a dalilin ta, ko da kuwa hakan na nufin zuwa Hadejia ne....ki taimaka min Mummy....."


"David ka san me ka ke faɗi kuwa? Ka na tunanin dangin mahaifin ka za su karɓe ka ne after all this years? Ka na jinjiri, innocent child ba su karɓe ka ba sai yanzun da ka zama saurayi ka tashi cikin addinin da ba na su ba? Ka na tunanin za su karbe ka ne ka na Christain? "


Cewar Mummy cikin nuna bacin rai Jin Dee na zancen zuwa Hadejia, dan kuwa idan akwai wainda ta tsana su na bayan dangin mahaifin Dee. Ga mamakin ta sai ji ta yi ya ce


"Mummy in dai zuwa Haɗeja gun dangin baba na shi zai sa su yarda su nema min auren Amatullah, Mummy zan yi, ko da kuwa za su min korar kare......"


Shiru Mummy ta yi na ɗan wani lokaci, daga bisani ta furta


" Oh Lord Jesus! This is history repeating itself!!!"


"Mummy please understand me, Ina son Amatullah, ban taba son kowace ɗiya mace ba kamar yanda na ke son Amatullah..."


"Ita Amatullah ta na son ka ne? Ya za ka yi da tazarar da ke tsakanin ku? Shin kana tunanin iyayen ta za su yarda su aura ma ka ita ka na Christain? Ko ba ka san addidinin su ya hana ba?"


Mummy ce ke maganar cikin faɗa
-faɗa. Shi kuwa Dee daɗa sassauta murya yayi kamar ya na gaban ta ya ce


" Mummy na sani, I mean ta fada min a addidinin su haramun ne mace Musulma ta auri Christain, Amma idan na musulunta shikenan......."


"Za ka musulunta ne David saboda yarinya da soyayya? Shin rayuwata ba zai zame ma ka makaranta ba David?"


"Mummy..... please try to understand me, please!"


Ya faɗa cikin rauni. Shirun da Mummy ta yi ba karamin tayar ma sa da hankali yayi ba. Idanunsa na fitar da hawaye ya furta


"It's not just about Amatullah kawai, har da mahaifina wanda ki ke kauna har gobe, da kyawawan halin sa da ya kwaɗaita mi ki son shiga musulunci, Mummy ina laifi idan ɗa yana so ya gaji uban sa? Ina laifi dan ina son kasancewa kamar mahaifi na........?"


"David......."


Mummy ta yi kokarin katse shi, Dee wanda ke gudun jin abin da za ta ce ya tari numfashin ta


"Mummy kasancewa na musulmi zai zama abin alfahari ga mahaifina, abin kaunar ki.....kar ki manta addinin musulunci addidinin shi ne, please Mummy understand me...."


" I understand David, na fihimce ka, you have my blessings son today and always addini ba zai taba zama tazara a tsakanin mu ba, a Musulmi ko Christain you will always be my blood and flesh"


Cike da murna wanda ya ke bayyane cikin muryar sa ya ce
" Na gode Mummy, na gode, I love you so much"


Tana murmushi ta amsa da
"I love you more son, but David?"


"Na'am Mummy"


"Shin ka faɗa mata za ka musulunta? Ita Amatullah ɗin ta ka? Ka ga ka ce ana shirin ɗaura mata ɗan uwan ta nan da one week, kar fa ka makara"


Nan gaban shi ya faɗi, yana ɗan sosa kyeya ya ce


"Ah ah Mummy ban faɗa mata ba, dama I wanted to tell you first, bari in je faɗa mata yanzu....."


"Toh Alhaji ɗan gidan Yusuf, ka duba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login