Showing 45001 words to 48000 words out of 98809 words
Chapter 16 - TAZARA COMPLETE by UMMU-ABDOUL & KHADIJA SIDI.txt
da ke jikinta.
Ya shigo daga rakiyan su Yunus inda su ka shiga Congo ya siyo fura don ya lura tana so.
Bai san iya lokacin da ya ɗauka yana ƙare mata kallo ba, karshe dai tsintar kansa yayi lullube da ita.
Cikin mafarki ta ji alamun mutum tattare da ita, a hankali da baƙin abubuwan da ta ke ji ya sanya ta tabbatar da gaskiya ce ba mafarki ba. Buɗe baki ta yi don yin ihu take ya liƙe mata shi da nasa.
Ba ta san yanayin ba, wannan shine mafari, ba za ta iya tantance me take ciki ba ta ji gaba ɗaya an ɗaga ta. Bai ɓata lokacin kauda doguwar rigar ba balle aika mata sakwanni hakanan bai ɗauki doguwar lokaci ba ya gauraya kwayoyin halittarsu su ka tabbata ɗaya.
***
Kiran Sallar magariba yayi daidai da samun natsuwarsa, kallon ta yake cikin mamaki da takaici. Tsaki ya ja kana ya tashi ya shige banɗaki in da yayi wanka ya fice masallaci.
Sai a lokacin Amatullah ta saki kukan da ta dinga maƙewa, kuka sosai ta ke yi duk da cikin ranta ta gode ma Allah da ya bata ikon rike mutuncin ta har sai da ta miƙa shi ga mijin aure ba mijin dandi ba.
Tunawa da littafan da ta karanta tayi, ta tuna yanda miji ke surar matarsa zuwa banɗaki ya mata wanka ya bata kyaututtuka amma ita ba ta tsira da komai ba sai tsaki.
'Ai ke ma ba ki suma ba, ance ana suma ne' wata sashi na zuciyarta ta faɗi mata hakan..
"Toh ai bai dade ba, su an ce ana yin awanni, toh ko bai da lafiya ne" ta faɗi a sarari sai da ta fadi sanan ta ji kunyar kanta.
A hankali ta isa banɗaki ta yi wanka, ta lallaba ta bada farali. Nan ma godiya ta yi ga Allah da ya tsare ta sannan ta roke shi da ya ƙara kare ta daga afkawa sharrin zina.
***
Kwana uku aka ɗauka duk dare sai ya zo gare ta kuma duk zuwa kyautan tsaki ya ke bin ta da shi. Washegarin na huɗu ne ya tsare ta ya ce
"Wai ke ina iliminki yaje ne, ko yarinya yar shekara goma sha biyu aka aura ta san yanda za ta yi sarrafa amma ke kin wani baje kin bar mutum da aiki, mtswwwww" ya fice ya barta cikin ƙunan rai da tunani.
Wannan wani irin abu ne, kullum ya je sai ya dawo amma kuma bai hana a bi ta da tsaki ba. Ta tuna littafin da ta karanta ƙarshe auren dole aka musu amma tun da ya tara da ita sau ɗaya ya bata kyaututtuka haɗe da yi mata alkawura, ba za ta manta labarin ba don ganin kamanceceniya da yake da su amma ita ga shi ta ga akasin haka.
Shima ranar da takaici ya fita, haduwar da yayi da su Yunus ne ya sa ya faɗi masu damuwar shi.
"Kun sa na kula yarinyar nan amma in ban da takaici ba abin da take cusa min, in kana neman bahar maliya ka sameta ka gama samun komi amma wallahi yanda kuka san sanda haka fa take min" yace cikin takaici.
"Hahahhhhhh wayyo Saif, kace a gajimare kake yawo, ai daga ganinta ka san can wajen natural spice gareshi" Yunus ya ce cikin shakiyanci.
"Natural spice din banza, ai bai kamata ta maida min shi abu mai wahala ba" ya kara faɗi a ƙufule.
"Kaga Saif, duk ba wani tashin hankali bane, Kaga am very sure ita ba kallon porn take ba, ita ba karanta explicit abubuwa take ba, ita kuma ba wai yar hannu bace wai ba za ka gode Allah ba. Ka dena haɗa aure da duniyanci Saif, koya mata ka mori ƙuruciyarta ni dai shawaran da zan baka kenan. In ba ta iya ba ai kana da Ayush, ita sai tayi maka abin da Amatullah ta kasa maka" Salis ya ce masa yana mai tabo kafadunsa. Da wannan tunanin ya dan ji salama har ya cire alwashin da ya ɗauka akan ba zai sake kallon ta ba.
[3/12, 11:55 AM] Safiyya Ummu-Abdoul Writer: TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼♂🤦🏿♀
✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL
BABI NA ASHIRIN DA ƊAYA
Kalamansa sun tsaya mata a rai, duk iya tunanin ta rasa gane mai hakan ya ke nufi, ita dai ta san ba ta ji azaban da ake lissafawa a littafan hausa ba duk da dai ba za ta ce babu zafin ba, sannan bata ga an yi tun dare har asuba ba, sannan kwatakwata mintunan da yayi bai kai wanda ta karanta ba. Ita ba ta abin daɗi a ciki ba.
"A haka kuma wasu ke kwasan zunubi da shi" ta ce tana mai ƙarasawa da jan tsaki.
Wayarta ta ɗauko tana mai tunanin ko ta kira goggonta ne, amma kunyar da ya rufe ta bayan ta tuna haka ya sanya ta yi ma kanta dariya.
"Inna Hafsatu"
tace a bayyane tana tunawa da kanwar goggo Mairo, wacce ita ce karamar su baki ɗaya. Sau da yawa idan inna Hafsatu na bukatar shawara, Amatullah ta ke nema su ci su suɗe tsakaninsu.
Latsa lambar ta yi, bugu biyu a na uku ta ɗauka
"ɗiyata amarya!"
tace cikin dariya da farin ciki. Ita kanta Amatullah dariya ta yi sannan su ka gaisa, bayan nan sai ta yi shiru tana tunanin ta ina za ta fara.
"Darling Daughter ko dai in zo ne" Inna hafsatu tace ganin da alamu Amatullah na da magana a bakin ta.
"A'a fa, dama, Hmmmn dama shine wai ban iya komi ba" tace kamar ta sa kuka don ji tayi ta gama tona asirin ta watau dai yanzu innarta ta san me suke yi.
" Ai shi kuma dai, ai a hankali ne abin, ba wanda aka haifa da iyawa" tace mata, jin haka Amatullah ta samu ƙarfin cigaba da faɗin
"kuma fa Shima ɗin baya kai asuba fa, kwatakwata 20min fa, sannan wani kyauta wani alkawura duk baya yi ko duk rashin iyawan ne"
Dariya sosai inna Hafsatu tayi kana tace
"A ina kika ji anayi tun dare har asuba, sannan wani kyauta kuma za a baki"
"Kai inna ai na karanta littafan hausa da dama na ga duk haka ake yi" tace iya gaskiyanta.
"Toh ke girki kala nawa kike masa kafin ya farka baccin" inna ta tambaya, shiru Amatullah tayi, don duk tunanin ta akan yin girki kala kala kafin ya farka ya kan kulle, ta kan masa farfesu dai duk rana breakfast ko dinner amma ba ma za ta iya yin girke-girke da taga ana lissafa wa ba.
"kin yi shiru Darling" inna ta katse mata tunanin ta.
" Kinga Amatullah ki ajiye rayuwar novel ki rungumi rayuwar zahiri. Mijinki mijinki ne, in ba mai shan magani ba babu mai lafiya da zai yi awa yana abu ɗaya, sannan ai ke ba injin ba ce, zancen kyaututtuka in ya baki ci da sha, bai wulakanta ki ba, bai barki cikin tsumma ba ai gama miki duk wani soyayya.
Aikin me yake yi da zai baki mota ko wani ubansu kyauta kawai don kin rike mutuncin kanki?
Ai kyautan kenan ya ƙara daraja ki, sannan duk wulakancinsa ba zai taɓa danganta ki da matar banza ba. Zancen baki iya ba, ki duba ki ga abin da ya miki ki kwatanta hakan, kina lakantar me yafi so. Sannan kar ki manta Addu'oi. Ina
Littafin Gidan Aurena, ki karanta it can serve as a guide Kuma da Addu'oi a ciki don samun kan mijinki" haka inna Hafsatu ta dinga mata nasiha da bayanai har sai da ta tabbatar da ta fahimta sannan su ka yi sallama.
Da karfinta ta tashi ta shiga kitchen nan ɗin ma abincin da ta san yana so ta shiga haɗa masa, farar shinkafa da miyar ganye amma maimakon taushe sauce take masa ya ji nama da hanta.
Duba fridge ta yi ta ga suna da sauran kankana ta yi haramar yi masa lemun kankana da madara.
***
Cikin ikon Allah sai da ta kammala komi har ta yi wanka kafin ya shigo bayan la'asar, sanye ta ke da doguwar riga ta atamfa amma gaba ɗaya bai wuce guiwanta ba.
Dinkin ya kamata daga sama sai ƙasan aka yi mata kamar lema hakan yayi daidai da zamansa a kan mazaunanta ya fito da kyawu ta.
Hoda kawai ta sa a fuskar ta, kanta kuma da ya ji kitso ta barshi a buɗe. Babu abin da ke fita daga jikinta sai ƙamshi.
Tun da tace masa sannu da zuwa uffan bata sake haɗa su ba, amma tana zaune a kujera ya natsu yana cin abinci haɗe da kora lemun.
"akwai saura da yawa" yace bayan ya idar da na gabansa, shiru tayi kamar hankalinta na ga talabijin sai da ya sake maimaita mata sannan ta yi firgigit ta amsa da akwai.
"Zuba ma Baban Sasa ki zo mu je mu kai masa" yace yana mikewa. Wani murna ta ji bata san lokacin da ta rungume shi ta baya ba, shi kuma a hankali ya juyo da ita, kallon da yake mata duk ya tafi da imaninta.
"Kin san ban masa godiya daga ƙasan zuciya ta ba, yau zan masa, don ba ƙaramin gata ya min ba, Ubangiji Allah ya miki Albarka Amatullah"
ya faɗi yana mai haɗa laɓɓansu. Yanda ta saki jiki ya bashi mamaki, ita kanta sai a lokacin ta san garɗin abin. Bayan yan mintuna su ka je don su shirya zuwa ga Baban Sasa.
***
"Yaya Amatullah oyoyo!" da yaran gidan ke faɗi ya isa ga kunnuwan matan gidan, sosai mahaifiyarta ta shiga farin ciki haka baba Anas da ke zaune yana sauraron radiyo France shirin almuru.
Tare su ka shigo tamkar wasu taurari, sanye yake da shadda wanda ya ji aikin hannu ruwan samaniya, hulansa yayi daidai da kalar aikin jikin shaddan. Ita kuma Amatullah sanye take da material fari mai adon fulawa na kaloli, ta ɗaura hijabi ja wanda ya shiga da jan da ke cikin fulawar, kafunta sanye da takalmi ja mai tsini.
Babu wani ado a fuskarta face hodar da ta sanya don rage maiƙon fuska. Fuskar nan tata cike da annuri, ji take kamar ta sheƙa a guje ta ga goggo maironta.
Sanin da ta masa na son aji ya sa ta danne murnarta har su ka isa ɗakin Baban Sasa a tare.
Shima zaune ya ke yana kallon Aljazeera su ka yi sallama su ka shiga. Wangale bakin da ya yi kaɗai ya isa ya bayyana farin cikin da ya ke ciki.
Nan su ka zube su ka gaishe shi, ya amsa yana mai shi masu albarka. Kwandon abinci da Saifullah ya riko ya ajiye gabansa yana mai cewa
"Kaci ka ji irin daɗin da ake ciyar da ni, kai Tsohon nan ka fi kowa iya match making" ya ƙarasa cikin tsokana.
Zama su ka gyara da su ka ga da gaske baban Sasa santi yake bayan Saifullah ya zuba masa abincin.
Suna cikin masa shaƙiyanci su Baba Anas su ka shigo, nan Amatullah ta ji duk wani kunyar duniya ya rufe ta.
Gaishe su tayi ta tashi sum za ta fice, take Saifullahi ya tashi ya bi bayanta, ya bar iyayensu da mamaki.
"Allah ya saka da Aljanna Babanmu, ka gansu ko" Baba Anas yace cikin murna, nan saura su ka shiga farin ciki suna fadin yanda Saifullah ya yi ƙiba.
"Ai tsatson Mairo gwanaye ne a mallaka, ku duba ku ga, yaron nan ba so yake ba amma yanzu ya zama bindi. Kaico!" Baba mahmuda ya faɗi wanda hakan ya ɗanyi tasiri a zukatan wasu daga cikinsu.
"Ko me zata yi ta daɗe bata yi ba, balle wannan girki haka, kai ko zaku ɗanɗana ne" Baban Sasa yace yana tura musu raguwar abincin nan sai su ka yi shiru.
***
A cikin gida ɗakin Hajiya ya ja ta, bayan sun gaida matan da ke wajen gida, ji tayi kamar ta rusa kuka ganin yanda ya hakince a kujera.
Hajiya ma da ke zaune in ban da tururi babu abin da zuciyarta ke mata ganin fara'ar da Saifullah ke ma Amatullah da yanda ya ke sako ta a cikin hirar su.
Rasa yanda za ta yi ta cusa ma Amatullah haushi bayan ta fito da turarruka biyu ta ba hajiya a sunan nata da na Baba Anas, Saifullah da bai san da turare ba ya dinga shi mata albarka ba tare da ya ba hajiya damar cewa uffan ba.
"Hajiya wallahi turarruka ne masu shegen tsada kin gansu, ni ban ma san ta riko muku ba, ke abin da kike da pocket money dinki Kenan"
ita dai Amatullah murmushi kawai ta ke yi, duk da bata san darajan turaren ba, zuwan da mahaifin ta yayi ne ya bata da umurnin duk ranar da ta je gida ta kai a hajiya da baba Anas.
"Toh ni in ba don ka faɗi ba ai sai in ce yan uku da hamsin ne" tace tana yatsina.
Dariya Saifullah yayi ba tare da ya auno komi ba. Su ka cigaba da hira, anan ne Hajiya ta ce.
"Ni kuwa ina Ayush ne? Yaushe za aje gaisuwa ne?" tace tana tsare shi da ido, kallon Amatullah yayi cikin sauri ya ga babu wani sauyi a fuskar ta, haka kawai ya tsinci kanshi da jin haushin hajiya, bai ce da ita kanzil ba, sai da ta sake maimaitawa.
"Hajiya da kin manta da Ayush da duk yafi, ba ta ban damar yi mata bayani ba, ta daina ɗaukan wayata, ni bata sake nema na ba sai ɗazu, na ga kiranta sau uku duk ba wanda na ɗauka" yace kai tsaye.
Duk da Amatullah ta ji ɗacin zancen sa ta ɗaure ba tare da ta nuna masu ba, tashi yayi yana riko ta kamar mai koyon tsayawa tare da faɗin
"Muje wajen goggona sharp sharp mu wuce"
Kamar jela haka ta bi shi tana mai ma hajiya sallama.
Takaici bai rufe ta ba sai duk yanda ta so su keɓe da mahaifiyarta bai bari ba, zama yayi ya dinga janta da hira kamar Saifullah kafin dawowarshi daga Rasha.
Nan su ka ci abincin dare ba su suka bar gidan ba sai bayan sallan magariba.
Tun da su ka dauki hanya maganar Hajiya ce ke damun zuciyar ta, dan haka ta yanke hukuncin tarar aradu da ka, ta mai nisawa ta furta
"Yaya Saifullahi wacece Ayush?"
Kallon ta yayi na wani ɗan lokaci, har ta fitar da ran jin amsa daga gare shi ta ji ya ce
"Budurwa ta ce........."
Gaban Amatullah ya faɗi, shi kuwa gogan na ta ko a jikin sa bai gushe ba ya cigaba da faɗin
" ita na so aura kafin Baban Sasa ya aura min ke, kuma har yanzu ban fitar da ran za ta zama mata a gare ni ba"
Ya karasa maganar ya na duban ta da wutsiyar idanu. Daurewa ta yi duk da bakin kishin da ya tukare ta a kirji, ta na mai murmushin ya ke ta furta
"Ai namiji mijin mace huɗu ne, Allah ya tabbatar mana da alkhairin sa"
Shi ma din murmushin ya sakar mata yayinda da ya saki numfashi da shi kan sa bai san ya rike, kana ya ce
"Dadi na da ke hankali Amatullah, Aameen dan rasulillahi"
Haka su ka cigaba da tafiya, ya na ɗan jan ta da hira amma ita Allah Allah ya ke su isa gida ko ta samu ta shiga dakin ta yi kuka ko ta ji sauki a ran ta.
Ko da su ka isa dakin ta ta shige, cikin bandaki ta sha kukan ta, sai da ta yi mai isar ta sannan ta yi wanka da alwala. Da wuri ta kwanta dan kada ma Saifullahi ya rabe, shi ma Saifullahi da tun a mota ya gano halin da ta ke ciki, daren ranar sarara mata yayi, ya na mai fatan daga ranar dai ba za ta dauki sarar hana shi hakkin sa ba, dan kuwa in dai wannan ko gaban Baban Sasa sa je.
***
Rayuwar su suke gwanin ban sha'awa, in da ta yi watsi da maganar Ayush ta mayar da hankalin ta wajan kula da mijin ta. Ba ta wasa da cikin sa, tana masa biyayya sosai sannan ta fannin ƙishinsa kullum cikin koyon salon da za ta kashe masa ƙishinsa ta ke, shi ma baya gajiya da koyar da ita.
Ranakun karatun ta shi ke kaita ya ɗauko ta, sannan duk wani abin da ba ta fahimta ba duk da aji biyu karatun fannin kwas dinsu ne mafi akasari yana kokarin nuna mata.
Lokaci ya ware mata wajen karatu, ya kan fita ya bar mata gidan tayi karatun ta, lectures ko ƙarfe bakwai aka sanya sai ya tabbatar da ba ta makara ba.
Uwa uba baya gajiya da gayyatarta makwanci, ba ta san lokacin da ta zama majuniniya a soyayyarsu ba.
Duk kulawar da ya ke nuna mata bai hana masa yin waya da Ayush ba, wacce daga baya da kan ta ta kira Saifullahi ta ba shi hakuri, ta kuma amince da auren ta da zai yi a matsayin mata ta biyu, Amma fa da sharaɗin tun da auren dole ya ce aka ma sa, kada ya kuskura ta ji sun hada shimfiɗa da matar shi bare ta ji tana da juna biyu.
Jin ta kawai Saifullahi yayi dan kuwa aikin gama ya gama, bare kuma babu yanda za a yi yana ganin mace kamar Amatullah ya zuba mata idanu, shi ma ya san da Ayush ta san wacece matar da aka aura masa da ba ta yi wannan yasshesshen zancen ba.
Ya kan kai mata ziyara lokaci zuwa lokaci kuma ya mata alkawarin zai aure ta matsayin matarsa ta biyu kuma ta ƙarshe nan da shekara daya da rabi, yanda Babab Sasa ba zai hana shi kara aure ba.
Bai ɓoye ma Amatullah ba don a cewarsa kar ta yaudari kanta.
Sannu a hankali su ka cika shekara da aure, a ranar ya mata kyautan zinari na naira dubu dari biyu da hamsin.
"Kinga kin zama min haske tun cikin 2009 har 2010, ina fatan ki zama tauraruwa, wata kuma ranar da zata dinga haska rayuwata har ƙarshen ta. Amatullah ke ɗin Alkhairi ce, na gode"