Showing 69001 words to 72000 words out of 98809 words
Chapter 24 - TAZARA COMPLETE by UMMU-ABDOUL & KHADIJA SIDI.txt
ta karbi Emjay daga hannun Baba Mahmuda ta shige ciki ta na takawa da kyar. Hajiya ma Baban Sasa ne ya sallame ta, ta na kukan takaici ta shige gida. Ɗakin kaf idan aka dauke Baba Anas babu wanda bai ga bakin Baba Salihu mahaifin Amatullah ba, ba dan komai ba sai dan furucin da ya yi yana mai kare Amatullah, a na su ya nuna san diyar shi karara bai yi kara ba. Baban Sasa wanda ya fi kowa jin zafin Baba Salihu ne ya ce
"Toh kai Saifullahi ka dai ji abin da yarinya ta ce, ka kuma ji hukuncin da uban ta ya yanke, ba ka kyauta min ba, duk yanda na so na haɗa wannan zumuncin, a yau an ruguza shi, dan haka sai ka sa a ran ka aure tsakanin ka da Amatullah ya kare....."
Wani irin yanayi mai kama da tashin hankali da bakin ciki na babu gaira babu dalili ne ya lullube shi, a da yayi zaton rabuwa da Amatullah zai zama tamkar an ɗauke masa dutse mai nauyi daga kan kirjin sa, ga mamakin sa sai gashi ya ji sabanin haka
"Baban Sasa a duba ......"
"Ka yiwa mutane shiru!"
Baba Zubairu ya dakatar da shi. Baban Sasa bai gushe ba ya cigaba da faɗin
"Bayan wannan danyan aikin da ka aikata ga yar uwar ka jinin ka, ka sani wasi wasi shin za ka iya ruke gidan ka kuwa? Wannan auren na ka da za a yi nan da wata biyu shin ba wani zanin za ka kwance mana a kasuwa ba?"
Cikin kaduwa bai san sanda ya furta
"Na yi kuskure Baban Sasa, a gafarce ni kar ka hana ni auren nan!"
"Aure babu mai hana ka, mu ɗin ba kanana mutane ba ne ko sakarkaru kamar ka! Duk abin da ya faru har da laifin mu, da mu ka yi sake mu ka bari ka bar gaban mu, ka tafi can uwa duniya ka ci karen ka ba babbaka, da ka na gaban mu duk abubun nan da su ka faru da ba su faru ba! Wancan dakuna biyu na kusa da bangaran mahaifiyar ka, in da ta ke kiwon kaji nan na ke so ka gyara ka saka matar ta ka ciki"
"Allahumma ajirni fi masibati!"
Cewar Saifullahi ya na mai goge zufa. Ya kara da
"Afuwa Baban Sasa, wallahi wancan gidan kiris ya rage a gama gyarawa....."
"Ba dai gida na ba ne? Na karɓe kaya na! Haka wanda tsohuwar mata ke ciki a da, kudin da ka kashe wajan gyara ka lissafa min zan biya ka in ya so ka gyara dakunan da shi. Yanda iyayen ka ke zaune cikin gidan nan haka kai ma za ka zauna da mu!"
Baban Sasa ya karasa maganar cikin jaddadawa. Shi kuwa tunanin yanda za a yi mace kamar Ayush yar gayu diyar masu kudi ya iya zama gidan nan na su babban damuwarsa. Wani Sabon zufa ne ya sake karyo masa, bai san sanda ya ya ja rigar sa ya shiga gogewa da shi ba.
Babu wanda ya kula shi, a haka suka watse taro zuciyar kowa babu daɗi.
***
Cikin wani irin yanayi Amatullah ta shiga ɗakin mahaifiyarta wanda Hafiz ya gama feshe musu mummunar labarin sakin Amatullah.
Tafiyar ta Goggo Mairo ke kallo cike da tsusayawa, so take ta rungume ƴarta ta lallashe ta amma kawaicin da aka tayar da ita ana ma ƴan fari ya sa ba za ta iya hakan ba.
Siddiƙa ce ta tashi ta amshi Emjay a hannun yayarta, kallon yaron take cike da ƙauna da soyayya.
"idanunki kenan? Shi kenan son miji da boko su rufe miki ido, ko yawon Arba'in ki gagara yi" Goggo ta ɓige da faɗa ba tare da nuna ta san wani abin ya faru ba. Murmushi Amatullah ta yi don ta daɗe da sanin salon soyayyar Goggo gareta kenan yi mata faɗa da basar da ita.
"Goggo yanzu ai komi ya zo ƙarshe, zan zauna nan babu mai hana mini zuwa ganinki" tace cikin danne kukan da ke neman zuwa mata. Sai da idon ta ya sauka akan Goggo sannan ta ji ɗacin sakin da aka mata.
Tsawon zaman ta a gidansu babu ƴa macen da ta taɓa yin aure ta fito a dalilin saki, sai gashi ta zama farau a gidan.
"Assalamu Alaikum! Ina Amatullah ɗin take" Hajiya Zainab matar Baba Hamza da yaran gidan ke kira da Mama ce ta shigo cike da tashin hankali. Rungume Amatullah ta yi tsam cike da hawaye ta ce
"Bamu kyauta miki ba Amatullah, wallahi bamu kyauta ba, muna mata muka shashantar da ke a lokacin da kika fi buƙatar mu, kaico!" tace tana share hawaye da gefen zanenta.
"Yanzu Babansu ke faɗa min, sakin bai min zafi ba kamar ɗinkinta da aka ce sai da aka sabonta Mairo ki duba ko sabo ya mutum ke yi balle a ce sai an kankare wajen kafin nan fa" tace tana magana cikin tausayawa da jinkai ga Amatullah.
Zama su ka yi nan Amatullah kamar wacce aka buɗe ma baki ta shiga faɗin abubuwan da ta fuskanta na cin kashi a gidan Saifullah daga lokacin da ya ce ta je a cire cikin.
"Kin ga ni ba, barewa zai yi gudu ne ɗansa yai rarrafe, ai duk abin da ya fito daga tsatson Sadiya zai aikata fin haka don an samu ma Baba Anas na ɗan sirka su da halin kwarai" Mama ta faɗi cikin takaici.
Duk wanda ke gidan ya san yar tsamar da ke tsakanin Hajiya da Mama. Tare a ka yi aurensu kasancewar mazajensu sa'annin juna ne, Mama yar gidan matawallen Zazzau ce ta wancan lokacin saboda haka garanta da jerenta ya sha bambam da na Hajiya, ba'a shafe shekara ba hajiya ta siyar da nata tas, ta sa irin na mama hatta kala ɗaya, bayan sun haifi yaya uku Matawalle ya biya ma Baba Hamza da Mama aikin haji su ka je su ka dawo, tun kafin su dawo Hajiya ta sa yaranta su koma kiranta Hajiya ba innarmu da suke cewa ba.
Kasancewar Mama ta iya faɗin gaskiya ya sa mafi yawan matan gidan ke tare da Hajiya a ƙulla sharri a kwance a alkhairi. Shekara na zagayowa Hajiya ta siyar da gidan gadon ta ta biya kujerar haji itama ta dawo liƙe da haƙorinta biyu a Saman dasashi.
Bayan auren Baba Salihu da Goggo Mairo da irin ladabin da take ma surukanta da kula da su da ya sanya su ka so ta fiye da saura, duk matan gidan sun tsane ta in ka cire tsirarunsu kamar su Mama. Ita kuma mama ba ta girkin gaba ɗaya, bata wani shiga taron facaloli hakan ya san ba kasafai ake ganin ta cikinsu ba. Ita ce kaɗai sasanta ke kewaye a gefe, duk da ta aurar da duk yaranta mata hakan bai sa ta nema a cikin gida ba.
"Kinga Sasarmu za ki koma, duk mai son ganinki ya biyo ki, sabon jego za mu fara" tace tana mai ɗaukan Emjay ta fice don ta san Amatullah na da bukatar ganawa da iyayenta.
Sosai Goggo Mairo ta ji sanyi a ranta, don tun da Hafiz ya faɗi mata take tunanin yanda za ta yi, duk da a lokacin ta sadakar za ta zaƙe ta kula da ƴarta.
Bayan shigowar Baba Salihu ya iske su jigum jigum kamar ma su makoki ne Goggo kefaɗi masa yanda su ka yi da Mama.
"Ke ba za ki iya kula da ƴar ki bane Maryam" ya tambaya yana mai tsare ta da ido.
Sunkuyar da kai tayi tace
"Ka dai san zuciyar Hajiya Zainab mai kyau ce, ina laifi ta fitar da ni tsaka mai wuya. Yar fari ce fa Babansu" ta ƙarasa tana rausayar da kai gefe.
"ƴar fari ko? Sannu mai ƴar fari, al'adar da ta sa kika kasa gane ukubar da ƴar ki ke ciki, ba damuwa kije Amatullah, amma ko kallon banza ta miki ki dawo kina da ɗakin uba, Nima zan maida hankali mu koma ginina, na gaji da wannan koma bayan gidan gandun nan" yace yana jan tsaki.
Tare duk su ka ci abinci kafin saddika ta raka ta sashin Mama, inda su ka iske ta ware mata ɗaki ɗaya, ta sa ma ɗakin rushi kamshi na tashi daga ɗakin, ga makewayi maƙale da ɗakin.
"InshaAllah gobe mai hidimar ki za ta iso daga gidanmu tun da ba zan iya wahalar ɗaura ruwa" mama tace cike da ƙauna. Wani irin farin ciki ne ya mamaye zuciyar Amatullah, jin kaunar mama na ratsa take, nan ta tabbatar lallai ko me ɗan Adam ke yi yana da dalili. Ta san dai Mama bata nan aka yi rikicin auren su amma da ta dawo ko sau ɗaya bata taka gidansu ba. Kenan da ta ɗauki zafi da ta sha kunya.
***
Jumma'a na zuwa Baba Anas da kanshi ya tuƙa ta zuwa zana test ɗin da za su yi, ta matsu ta ga Mimi ko don ta gode mata, lokacin da mahaifinta ke faɗa mata ƙoƙarin da Mimi ta yi ba ƙaramin jinjinawa soyayyarta da amanarta ta yi ba.
"Sai a ce Ahlil Kitaab ba masoya bane" ta faɗi a ranta, duk da ta san ba za ka saki ɗan uwanka musulmi ka riƙe su ba amma tabbas annabi ya zauna da su cikin zama na amana da jin ƙai, tana mamakin musulmi mai taƙamar koyi da karantarwar Manzon tsira SAW amma ya zama mai rashin kyautata mu'amala da wainda ba musulmi ba.
Tara da minti ashirin su ka isa Faculty of pharmaceutical sciences inda za su yi test ɗin da ƙarfe goma.
"Nagode Baba Allah ya ƙara girma da ɗaukaka" tace cikin jin nauyi da farin ciki.
"zan jira ki kammala sai mu wuce inshaAllah, Allah ya bada sa'a" yace mata yayin da take ficewa da ga motar.
Tun bayan hargitsin sakin ta wani girmansa da ƙaunarsa ya ƙaru a zuciyar ta. Tabbas Baba Anas ya kasance cikin mutane ƙalilan masu ƙin nasu su so gaskiya, sannan ya kasance mutum mai riƙo da igiyar zumunta, har abada ba za ta daina gode ma Allah da ya yi Baba Anas ya kasance kaka ga gudan jinin ta.
Rungume Mimi ta yi tsam da su ka haɗu har wasu yan ajin na masu tsiyan kwana ɗaya kawai da ba su haɗu ba. Dariya kawai su ka yi amma ita Mimi kanta ta hango soyayya da kaunar ta mai matsanancin yawa a idanun Amatullah. Hannun ta taja su ka zauna a kujera,
"Na gode Mimi, Ubangiji Allah ya baki Alkhairin duniya da lahira" Amatullah ta faɗi cikin nuna alamun ƙarancin kalaman da za su bayyana godiyarta. Amma tun ranar ta ke ma Mimi addu'ar jinkai da samun rabon imani.
"Common Maman Emjay, what are friends for" ta faɗi mata cike da ƙauna. A takaice Amatullah ta faɗi mata halin da ake ciki wanda hakan ba ƙaramin faranta ran Mimi yayi ba.
Daga nan su ka duƙufa bitar karatu, har zuwa shigowar malamin. Ba za su ce ya musu sauƙi amma kam sun ji dadin sa sosai, don Allah ya basu sa'ar amsa duka don haka sun fito suna gode ma Allah.
"Abuja zan je mid semester tare da Dee. In na ce in je Yola yanzu wahala zan yi" Mimi ta ce mata sa'ilin da su ke sallama.
"Allah ya kaiku lafiya, ki masa godiya don Allah" tace cikin sanyin jiki.
"Ki sani fa maman Emjay, babu wanda zai so ki sama da ke kan ki, sannan babu wanda zai wahala in kika yi sakaci da kanki sama da ke kanki. Duniya wani na tayaka son ka ne, sannan waninka iyaka ya yi imagining pains ɗin da kake ciki amma kai ke da wahala.
Use this break wisely, breakups should not crash us, they are meant to make us stronger" Mimi ta ce mata tana riƙe da hannunta. Tare su ka fito Facultyn, har zuwa inda Baba Anas ya ke jiranta, nan Mimi ta gaida shi cike da ladabi suka yi sallama su ka wuce.
[4/13, 8:29 AM] Zuraiyah Zuzu 🌟: TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼♂🤦🏿♀
✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL
BABI NA ASHIRIN DA TARA
"Abuja zan je mid semester tare da Dee. In na ce in je Yola yanzu wahala zan yi"
Maganar da ke ta shawagi cikin zuciyar ta kenan.
'Shin bayan dangantakar jini akwai dangantakar zuci tsakanin Dee da Mimi ne? Kamar dai akwai, toh idan ma akwai ni tawa a wa? Ko ba komai ai addini ya riga yayi tazara a tsakanin mu.. .. '
Da wannan muhawarar cikin ran ta su ka isa gida. Godiya ta yiwa Baba Anas sannan ta shiga ta gaida Baban Sasa wanda har lokacin ya na da burin komawar ta gidan Saifullahi. Gwaggo kuwa gaisuwa ke haɗa ta da Amatullah, da ta gaishe ta ɓangaran uwar jinyarta ta ke wucewa.
Ba ƙaramin kula da gyara ta ke samu wajan Mama ba, duk ta na ji a jikin ta dan kuwa in dai wajen gyara ne Mama ba ta tausaya mata.
Yau ɗin ma gaishe da Gwaggo ta yi in da ta aje mata Emjay kafin ta wuce wajen Mama. Ferfesun naman rago mai romo da kunun gyada Mama ta ajiye mata, Sai da ta tabbatar ta ci da shanye roman tas sannan ta ce maza ta shirya ta zo ta zauna ruwa mai dan zafi da ta tanadar mata domin a samu ɗinkin ya fara haɗe kan sa.
Saifullahi a na shi bangaran tun bayan da Amatullah bar gidan sa gaba ɗaya gidan ya daina masa daɗi, wani sa'in ma kukan Emjay har gizo ya ke masa a kunne.
Tsananin yanda ya ke kewar su ya sanya ya ke Allah Allah ranar auren sa da Ayush ya zo, kila idan ya ga masoyiyar ta shi kusa da shi ya manta da batun Amatullah. Toh amma sharaɗin da Baban Sasa ya yanke ba ƙaramin damuwa ya ƙara masa ba, kullum da tunanin yanda zai bulluwa lamarin ya ke kwana ya ke tashi har dai ya yanke hukuncin tunkarar Ayush da maganar a yi ta takare ko zai sami sauki cikin ran sa.
Sati biyu kenan da yanke ɗanyen hukuncin dole ya ajiye ta a gidan wanda yayi daidai da saura sati shida ɗaurin auren su. Shiryawa yayi asubar fari ya nufi hanyar Kano.
Kallo ɗaya za a gano tsananin damuwar da ya ke ciki, duk yanda ya so ya ɓullo ma Ayush da zancen ya kasa ga bikin sai matsowa yake yi.
Kamar ko yaushe tarbo ya samu cike da maƙulashe, Ayush ta cika shi da kwalliyan ta mai rikita shi, ga ƙamshin da ke fita daga jikinta na ƙara narkashi duk da ba su yi tasirin cire masa firgicin da ke ransa ba.
Hira su ke jefi - jefi yana mai kara bayyana mata sirrin zuciyar sa da kuma tarin burikan da yake da na rayuwar auren su. Sai da ya gama samun ta, ya tabbatar da ta gama natsuwa da Kalamansa haɗe da yarda da dacen da tayi na samun sa a matsayin miji sannan ya ce
"Aisha...."
Har cikin ranta ta ji muryar ta shi musammam yanda ya kira ainihin sunan ta, kallon shi ta ke ba tare da ta amsa ba, ganin haka ya cigaba da faɗin
"Ban san yanda zan mi ki bayani ki gane ba, amma zan yi iyakar kokari na, kuma kin san dai ba zan taɓa cutar da ke ba ko?"
Ayush da gaban ta ya fara faɗuwa ta ɗan gyara zama sannan ta ce
"Ina Jin ka, Baban Sasa ya ce ba za ka aure ni ba ne?"
Kai ya girgiza ya na mai mamakin yanda ta kama sunan Baban Sasa haka, ya ce
"Ya sallam! Ko kusa! Me zai sa ki yi tunanin haka?"
Cikin yatsine ta ce
"Toh ai yanda na ga ka na ba da labarin kakan na ka ne ai komai mai ma zai iya faruwa, bare kuma ka ce shi ya aura maka matar ka"
"Auren ya mutu....."
"Sorry?"
Ayush ta faɗa domin son Jin ya sake maimaitawa, dan gudun kar dai kunen ta ke zagi. Shi kuwa Saifullahi ya girgiza kai sannan ya kara da
"Na sake ta"
"Ka sake ta fa ka ce? Saboda me ya sa? Kar dai saboda auren mu ne?"
Cewar ta, ta na mai fatan hakan ne, shi kuwa Saifullahi nan ya sami hujjar da zai fake, ya tsinci kan sa ya na faɗin
"Na so jurewa na haɗa ku ba don komai ba, sai dan biyayyan iyaye, Allah na gani yanda na ke kaunar ki ban ji zan iya adalci tsakanin ku ba, saboda haka sai na sauwake mata"
Wani irin daɗi da annushuwa ne ya mamaye Aysuh duk da kuwa ta so ta ɓoye shi, amma hakan ya gagara. Ta na mai danna fara'a ta ce
"Ayya Honey pie ai da ka barta, ko dan gujewar fushin su Baban Sasa"
Ta tabuwa Saifullahi in da ya ke masa kaikayi, ya na mai share zufa ya ce
"San ki da na ke ya sa idanuna rufewa Ayush, yanzu haka ina kan fuskantar fushin na su, saboda na saki yarinyar nan yanzu sun ce a lalle sai dai mu zauna cikin family house din mu......"
"Allah ya sauwake na zauna gidan gandu in yamutse se kace dambu!"
Ayush ta katse shi cikin tsawa, ta kara da
"Ka san me ka ke faɗa kuwa Saif? Kamar ni? Ni Ayush ka ce na zauna family house din ku? Dama hakan nan zaman family house masifa ne bare kuma a ce ka saki cousin ɗin ka saboda ni? Na zauna a kuntata min kenan? Wallahi ba ka isa ba! Ko dai ka aje ni gidan da ka ce ka gyara min, wanda shi ma din ka san is not up to my standard, ko kuwa a fasa auren nan!"
Ta kare maganar cike da tsiwa. Jikin Saifullahi yayi sanyi hankali tashe jin Aysuh na batun fasa aure
"Ayush kar ki min haka, ki rufa min asiri ba zan iya rayuwa babu ke ba, ba kuma zan iya bijirewa maganar iyaye na ba, ki tuna fa kasa jure soyayyar ki ya sanya na saki Amatullah, su kuma dan su kuntata min ya sa suka bijiro da wannan hukunci....."
"Malam ni ina ruwa na! Ba zan zauna family hause ba!"
Ayush ta kara jadadda masa. Juyin duniya da rarrashi babu