Showing 42001 words to 45000 words out of 98809 words
Chapter 15 - TAZARA COMPLETE by UMMU-ABDOUL & KHADIJA SIDI.txt
na mai faɗin
"Ayush mine, queen of beauty"
Idanun ta kaɗa ta yi fari, cikin kissa ta ce
"Saif Man, wallahi na yi kewan ka ina fata dai ka zo min da sakon turo iyayen ka su kawo gaisuwa, tun da dai ka ki yarda mu yi maganar a waya"
Hannun ta ya saki, yayinda ya shafa kyeyar sa cikin kame kame ya ce
"Haba mana ke kuwa, daga zuwa babu sannu bare ya hanya?"
Kunya ne ya rufe ta, kana ta ce
"Afuwan, Dad ne ya ke ta min maganar wallahi. Ya hanya? Hope ka iso lafiya"
"Lafiya lau Alhamdulillah, dan bani ruwa ni zafi ma na ke ji'
"Kai Mine duk AC da ke busowa ka ce zafi? Ko dai ba ka da lafiya ne?"
Cewar Ayush yayinda ta zuba masa ruwan ta mika masa. Sai da ya sha kofi biyu, ga mamakin Ayush har zufa ya ke.
"Lafiya lau na ke, oya gist me, have you missed me?"
Nan ya fara Jan ta da hira, tun tana biye ma sa, har ta gaji ta sake tambayar abin da ke ran ta.
"Aisha......"
Jin ya kira ta da sunan ta na ainihi ya sanya ta dagowa da sauri ta na duban shi.
"Ki yafe min na zo mi ki da labari mai muni, wallahil azim ba da san rai na aka yi ba, kuma na mi ki alkawarin hakan ba zai sa a fasa auren mu ba......"
"What are you saying ne? Ka yi min gwari gwari dan Allah"
Ta katse shi cikin nuna gajiyawa. Hannun ta ya sake rikowa sannan ya ce
"An daura min aure da yar uwa ta....."
"Hahahahahahaah"
Ayush ta katse shi da dariya mai cike da keta. Cikin yanayin firgici da tsoro ya ke duban ta, sai da ta yi dariyar mai isar ta har da kwalla sannan ta furta
"You must be kidding me, Kai amma Mine ka iya zolaya wallahi, dan kuwa wannan wasan na ka ai tsokana ne"
"I'm serious Ayush, wallahi I'm serious..."
"Bura uban nan kayyasa!!!!! Ni za ka kalla ka yiwa wannan maganar Saifullahi? Ka kalli tsabar idona ka ce min an yi maka auren dole? Do you think I'm stupid?"
"Ayush calm down, ina san ki, ina kaunar ki, wallahi ba zan iya zama da bagidajiyar da aka aura min ba, I want to marry you....."
"Get out!!!"
Cewar Ayush yayinda da ta tashi tsaye, hanyar fita ta masa nuni da shi tare da sake faɗin
"Get out!!!!??"
Jiki sanyaye ya tashi, a hankali ya furta
"Ayush, listen........"
"Damn you!!!!! Fitar mana daga gida Malam"
Jiki sanyaye Saifullahi ya fice. Sai da ya fita sannan ta saki kukan da ya tsaya mata can karkashin makogoro, duniyar nan babu wanda ta tsana kamar Saifullahi.
Saifullahi na fita daga gidan masallaci ya nufa yayi sallah ko zuciyar sa ta dan yi sanyi. Yana idarwa ya shiga Kiran wayar Ayush amma ta ki dagawa. Haka ya ɗauki hanyar Zaria ba tare da ya tsaya neman abinci ba, yayinda tsanar Amatullah ke kara ratsa zuciyar sa.
***
Ranar da Amatulah ta cika kwana biyar gidan miji Maman Jafa'ar da Zulaikha suka kawo mata ziyara. Ranar Amatulah murna kamar ta goya su. Daki su ka zauna, Zulaikha ce ta takura ita lalle sai ta ga ango, Amatullah ta Kira shi su gaisa. Amatullah da ta yi kokarin buye mu su halin da ta ke ciki, tuni ta fashe mu su da kuka, nan takwashe komai ta fada musu, ta kare da
"Kuma rabona da ganin shi cikin gidan nan kwana uku kenan....."
"Ki na nufin ba gidan ya ke kwana ba?"
Cewar Maman Ja'afar cike da jimami
"In ma nan ya ke kwana ban sani ba, babu abin da ke hada mu"
"Toh ai Amatullah laifin ki ne wallahi, mace kamar ki, mace har mace akwai namijin da ya isa ya wulakantaki Amatullah? Wai tsaya duk tarin littafan da na haɗa ki da shi karatunsu ya tashi a banza kenan?"
Maman Ja'afar ta faɗa cikin nuna ɓacin rai, ita kuwa Zulaikha tagumi ta yi ta ma rasa na cewa.
"Ba dai ya haramta mi ki saka hijabi ba? Toh ai kuwa ya tsokanowa kan sa rashin kwanciyar hankali daga yau Amatullah kanana kaya shi ne kayan sakawar ki, ki karkada masa kugu a sannu zai dawo tafin hannun ki sai yanda ki ka yi da shi...."
"Ayya mana Maman Ja'afar...."
Cewar Amatullah, kunya ne ya rufe ta. Ita kuwa Zulaikha shewa ta yi tare da faɗin
"I trust you Maman Ja'afar, Amma fa mutuniyar ban ji ta na da kananan kaya fa"
"Kar ki damu, gashi ai dama na ruko guda biyu, short gown ne duka, kuma in sha Allah ni da kai na zan shiga kasuwa na karo mata"
Jakarta ta bude, ta fito da kayan ta mikawa Amatullah tare da faɗin
"Oya tashi ki saka mu gani"
"Caf wannan mitsitsiyar rigar zan saka?"
"Eh yanzu ma kuwa Amatullah"
"Gaskiya ba zan iya ba sai ka ce wata yar iska?"
"Ni da na kawo mi ki halan ni ce yar iska"
Cewar Maman Ja'afar cikin gatse, in da Zulaikha ta kwashe da dariyar mugunta.
"Ni ah ah ba haka na ke nufi ba Maman Ja'afar, kayan ne....."
"Idan ba haka ki ke nufi ba toh ki saka kayan mu gani"
Amatullah na gunguni ta shige bayi, sai da tai kusan minti goma da saka kayan amma ta kasa fitowa, Zulaikha ce ta buɗe bayin ba ta san sanda ta saka ihu ba, kunya ya rufe Amatullah kamar ta nitse. Riga ce koriya, mai dan ƙaramin hannu iya ka gwuiwa, duk da dai ba wani kama ta yayi ba amma yanayin dirin Amatullah ya sanya rigar kayatuwa jikin ta.
Da zuga suka sanya ta sake gwada dayar, wacce ta ke jar body fitting gown mai tafiya da hankalin duk wani mai kallo, rigar mara hannu ce kuma bata karasa gwiwa ba. Ba ƙaramin kyau Amatullah ta yi ba kamar aljana.
"Tsira da aminci ya tabbata ga mahaliccin wannan halitar"
Cewar Maman Ja'afar, in da Zulaikha ta kara da
"Wow, wallahi kin haɗu Amatullah babu karya!!!"
Ita dai Amatullah ta kasa sakewa gaban su ma, bare kuma uwa uba uban gayyar.
"Fisabilillahi wannan ba sutura ba ce....."
"Ai dai yau dinnan za ki saka, yamma na yi ki wanka na tsantsara mi ki ado Amatullah, sai Mijin ki ya kasa gane ki"
Maman Ja'afar ta faɗa cikin jaddadawa.
"Yo ina ma zai ganni, na manta rabon da na ji motsin shi"
"Yau kuwa za ki ji"
Duka suka sa dariya, ita kuwa kayan ta cire cikin ranta ta na faɗin sa ga wacce za ta saka kayan. Sai da su ka yinan mata, bayan la'asar kamar yanda Maman Ja'afar ta ce , wanka ta tursasa Amatullah ta yi, sai da ta yi mata kwalliya kafin su yi diramar sanya kaya.
Ganin an fi karfin ta Amatullah ta sanya yar karamar jar rigar da Maman Ja'afar ta zaba ma ta, ta na mai kudirin cire kayan da sun tafi. Ita kanta ta san ta yi kyau na burgewa da ban sha'awa. Ga body komai cif cif da ta taka sai komai ya motsa.
"Big sai bigi babban goro sai magogin karfe.."
Zulaikha ce ta ke mata kirari.
"Bari Zulaikha, irin su Amatullah ake kira da zaratan mata...."
"Ni dai ku bar zigani haka dan Allah"
Amatullah ta katse ta tana mai tifke gashin ta da ribon. Nan fa baki su ka ce za su yi halin su. Amatullah ta ja hijabi za ta saka domin rakiya Maman Ja'afar ta kwace tana faɗin
"An dai haramta mi ki sanya hijabi cikin gida"
Baki bude Amatullah ta bata amsa da
"Haka zan fita na raka ku toh? Kai jama'a Allah ya sauwake na fita haka"
"Ke Malama wa ya ce fita za ki yi? Iyakar ki bakin kofar falon ki ko gate ba za ki kai ba, dan haka mayar da wukar"
Akwatin lafen ta ta bude ba tare da basu amsa ba, kayan kwalliya ta dauka har da body spray da sabulu, ta zuba a leda. Ba su fasa tsokanar ta ba har ta raka su, kayan ta ba su tare da godiya, ji take kamar ta bi su kawai su koma makaranta ta huta. Ran ta ba dadi su ka yi sallama ta rufe kofar falon.
Har za ta shiga ɗakin ta ji an kwankwasa kofa, zuciyar ta daya su Zulaikha ne su ka yi mantawa ta koma ta na faɗin
"Na face duk wacce ta yi mantuwa ya zama nawa"
Yayin da ta bude kofar, ganin wanda ke tsaye gaban ta ya sanya ta mummunar faduwar gaba. Saifullahi ne sanye cikin kanana kaya, farar riga mara hannu da bakin wando. Kallan da ya bi ta da shi tun daga sama har kasa ne ya sa ta tuna da yanayin shigar da ta yi,
'Kai amma su Zulaikha sun cuce ni!' abin da ta ce cikin ran ta kenan yayinda ta juya ciki da sauri da niyar komawa dakin ta, nan Saifullahi ya sami damar karewa bayan ta kallo, sai da ya bari ta kai dab da kofar dakin ta ya ce
"Malama tsaya!"
Turis ta yi ta tsaya, dan kunya kamar kasa ta tsage ta shige. Ta kasa juyowa ta kalle shi, In da ta ke ya karasa duk ya bi ya susuce. Cikin kame kame ya ce
"Ba ki iya sannu da zuwa ba ko? Haka aka koya mi ki?"
"Sannun da zuwa"
Ta furta da sauri ba tare da ta juya ta kalle shi ba.
"Ba za ki juyo ki kalle ni ba iye Amat? Haka mace ta ke yiwa mijin ta sannu da zuwa a garin ku?"
Jikin ta ne ya fara rawa, yayin da ta juyo a hankali. Ganin yanda idanun Saifullahi su ka fara juyewa cikin wani yanayi ya sanya ta saurin yin ƙasa da idanun ta.
Muryar shi ƙasa ƙasa ya kai hannun shi ga na ta, ya ce
"Bari na koya mi ki yanda ake yiwa miji sannu da zuwa Amat"
Ba ta ankara ba sai ga ta jikin shi, ba karamin firgita ta yi ganin yanda ya kamkame ta ya na mayar da numfashi.
Kuka ta sakar masa mai karfi ta na faɗin
"Dan Allah Ya Saifullahi ka yi hakuri, wallahi ba zan sake ba"
Maimakon ya sake ta, sai ji ta yi ya fara shafa bayan ta, nan fa Amatullah ta yi kicin kicin ta shiga ture shi, har Allah ya ba ta iko ta kwaci kan ta, Saifullahi yayi baya kamar wanda ke shirin faduwa.
Cikin zafin nama ta shige dakin ta tare da sa mukulli ta kulle. Ta faɗa kan gado ta na kukan da ita kan ta ba ta san dalilin sa ba.
Kamar wanda kwai ya fashe haka Saifullahi ya ja jikin sa ya zauna kan kujera. Ya san Amatullah ta na da diri amma bai taɓa tsammanin za ta iya rikita shi haka ba, ace kamar shi Saifullahi bagidajiya irin Amatullah ta sanya hankalin shi ya gushe haka!
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil"
Cewar shi a sarari, ya kara da
"Kai dama hajar da Baban Sasa ke hango min kenan, gwara na kwashi rabo na na mure tunda kuwa halak dina ce, kan uba Amatullah mace ce!!!"
Kai ya ci gaba da jinjinawa dan kuwa dai jikin sa ya mutu murus, gashi Ayush ta dena daga wayar sa, ta kuma ki ma sa reply na sakonnin alkawarin auren ta da ya ke tura mata kullum bare ya kira ta ko a waya ne ya rage zafi. Nan yayi kwance inda surar Amatullah ke ma sa gizo.
Sai da aka kira magariba ta iya tashi ta yi sallah. Bayan ta idar ne ta kira Maman Ja'afar ta na mata mitar masifar da ta jaza mata ranar. Ta kare da
"Dama Ya Saifullahi dan iska ne Maman Jafa'ar!!!"
Dariya ta yi mata, ita lamarin daidai ya mata sannan ta yiwa Amatullah faɗa da Kar ta sake ture mijin ta, haramun ne, itama ai mai sani ce ta san tsinuwar malaiku dai babban lamari ne. Nasiha ta mata sosai, ta kara jaddada mata gobe goben nan za ta aiko da sauran kayan. Ita kuwa Amatullah ta ce Allah kashe ta ba za ta sake saka irin kayan ba. Da haka su ka yi sallama Maman Ja'afar na murna ta kira Zulaikha ta labar ta mata.
Amatullah ba ta kara yarda ta fita daga dakin ta ba bare ta haɗu da Saifullahi, daren ranar haka ta kwana da yunwa.
****
Washagari da safe, sai da ta tabbatar ba ta jin motsin Saifullahi ta fito kitchen sanye da material shudi, riga da siket ne ya karbe ta kwarai. Yunwar da ta ke ji ya sanya ta yagar buredi ta na ci hakan nan kafin indomie din da ta daura ya nuna. Daf da kunen ta ta ji ya furta
"Ni ki ke gudu ko Amat?"
Da sauri ta ja gefe, yayin da da hanjin cikin ta ya kaɗa ganin Saifullahi tsaye gaban ta, kamar ranan yau ma daga shi sai gajeran wando. Idanun ta a kasa ta ce
"Ina kwana?"
"Lafiya lau, ki dafa da ni ina jiran ki falo"
Ya na gama magana ya fice. Bin shi ta yi da kallo cike da mamaki, yau kuma ita ce za ta dafa ma sa abinci? Yau ga saban salo barawo da sallama.
Ruwan indomie ɗin ta kara, ta dafa da shi din, tare da soya kwai. Ko da ta kai ma sa sai ya dage sai ta zauna sunci tare. Kai ta girgiza ma sa ta ce
"Nawa ya na kitchen ai"
"Toh dauko ki zauna ki ci anan ina kallan ki"
Hakan kuwa aka yi, ita kan tun abin yana ba ta mamaki har ya fara ba ta tsoro. Saifullahi kuwa jikin Amatullah ya ke yiwa, babu abinda ke burge shi nan duniya kamar sura da diran Amatullah.
Sama sama haka ta caccaki indomie duk ta kasa nutsuwa, gashi Saifullahi bai sa ka riga ba haka ya zauna mata hankali kwance ya na yi ya na kallan ta ta wutsiyar ido. Ta shi ta yi za ta shiga kitchen, ya tsayar da ita tare da tambayar
"Ina za ki? Har kin yi me?"
"Na koshi ne ......"
"Gudun mijin ki ke Amat?"
Shiru ta masa tana jinjina maganar cikin ranta. Jin ba ta da niyar amsa masa ya kara da
"Je ki aje plate din ki dawo"
Da sauri ta wuce kitchen. Maimakon ta yi yanda ya ce mata sai ta bige da wanke wanke da gyaran kitchen, tun ya na sa ran komawar ta ya gaji ya bita kitchen din. Ganin ta na tana aiki na ba gyara ba dalili ya rabu da ita, ya san duk daren dadewa za ta shigo hannu,
'duk wayon amarya sai an sha miyar ta'
Da wannan tunanin ya shirya ya fice yana mai saƙe-saƙe a zuciyar sa.
Kwanakin da su ka biyo baya rashin ji daga Ayush da kuma wasan ɓoyo da Amatullah ke yi ya sanya shi ɗaukan alwashin kyale ta har iya adadin zaman ta a gidanshi kafin yacillar da ita ya auro Ayush dinsa.
Nan ya shiga takaicin kansa da ba kansa laifin cin amanar Ayush na kallon watan ta a matsayin abar marmari.
***
Kwanci tashi asarar mai rai, auren Saifullah ya cika wata biyu ras, wanda duk an yi shine cikin hutun karshen shekara na su Amatullah. Duk zaman nan shi ma Saifullah yana gida, sau da yawa ya kan baje a falo yana kallo ne.
Babu abin da ke haɗa su da ya wuce gaisuwa, ta yi girki ya ci, ya gayyato abokai su zauna su ci.
Tun ranar da su ka fara zuwa Amatullah ta koma a guje ta sanya hijabi bai sake yarda ta fito ba, ya gwammace ta yi abincin ta bar shi a kitchen ya je ya ɗauko da a ce matarsa ce ta zo ga abokansa bulum bulum cikin hijabi.
Yau ɗinma kamar kullum, fankasau ta yi masu da miyar hanta. Bayan dawowarta daga makaranta in da su ka fara registration ɗin sabon Zango.
"Baaba kai dai ka mana zarra Billahil lazi, kai mace har mace, ga kyau ga diri ga iya girki. Wallahi ka more aure, na san a can wajen ma abin ba kanta wannan teɓa da ka fara ajiyewa" cewa Yunus abokin Saifullah na tun sakandire.
"Ka san abin da ya ke ƙara birge ni, yarinyar nan ustaziyya ce, jiya na ganta a Samaru wallahi ta rufe masa kayansa amma wallahi tafiyarta ma cikin hijabi abin sha'awa ne. Saif ka gode Allah, Sadiya na nan nayi nayi ta dinga sa pashmina ma gyalen ta ƙi tana tafe ana bin ta da heys! " Salis ya ce yana mai jan tsaki.
Wani loma da su ka sake kaiwa baki ba su san sanda su ka ce
" Allah ya ma Amatullah albarka" sai da su ka faɗi sannan su ka kwashe da dariya.
"Ba fa santi bane, amma girkin nan ya kai kololuwa wajen shiga kwanya" Yunus ya faɗi.
Shi kuwa Saifullah wani yanayi ya shiga yan mai jin kansa na ƙara girma, murmushi yayi yana mai kallon abokansa. Duk sun san Ayush, sun san tsakanin sa da ita, amma ba su yarda da alkawarin da ya ce ya ɗauka mata ba, gani su ke yayi ne kawai don jin dadin bakinsa.
"Kun ci amanar Ayush! Duniya babu wani nawa da ta aminta da shi sama da ku biyun nan amma kuma nan ku ke koɗa wata" yace yana taɓe baki haɗe da girgiza kai.
"Jamoh!!!" Salis ya kira shi da sunan da in ana zancen gaskiya yake kiransa da shi.
"Ka san Allah ɗaya! Amatullah ce full option amma Ayush tsohuwa da ina mai yakinin in baku zo sa'a ba toh tabbas ta girme ka.
Ita auren Jari za ka yi da ita, wannan kuma matar da za ta tarbiyyantar da yayanku. Ko ba komi ai zaka ci abinci mai gina jiki" yace yana kai lomar karshe tare da kora ruwa.
Nushi Saifullah ya kai masa amma ya kauce.
"Ku taso mu fita in kun gama ci" Saifullah ya ce a dake. Nan su ka shiga bambamta masa Amatullah da Ayush tun zuciyar sa na ƙaryatawa har ta gaji ta yarda gaskiyar kenan.
Tun bayan fitar su ta kimtsa wajen ta sanya turaren wuta tare da kunna kallo. Tashar Iqra TV ta kunna tana sauraron shirin da ake akan da'awa. A nan wajen bacci yayi awon gaba da ita.
Sanye take da doguwar riga mara hannu, gaban rigar an masa kwalliya da duwatsu masu kyau. Kallar rigar na ruwan ƙasa ya kwanta sosai a jikinta, ɗame ta da rigar tayi ya bayyana halittar Allah