Showing 81001 words to 84000 words out of 98809 words

Chapter 28 - TAZARA COMPLETE by UMMU-ABDOUL & KHADIJA SIDI.txt

ta ba shi ba ƙaramin sosa masa zuciya ta yi ba. Ya ɗaure ya amsa mata da


"Alhamdulillah, ya Emjay? I missed you guys .."


"Lafiya lau Alhamdulillah, sai anjima ko?"


"Ina za ki je ne, ai sai na ajiye ku kin ga yamma na yi"


Cewar Saifullahi ya na mai fatan Amatullah ta yarda ya ajiye ta, dan har ga Allah ba ya so ya dena magana da ita.


Kai Amatullah ta girgiza tare da faɗin
"Thank you, we are very fine, we can manage"


Ta na faɗin haka ta yi gaba. Nan ya tsaya ya na duban ta, har sai da ta ƙurewa ganin sa sannan ya hakura ya shige gida.


Ɗaki ya tarar da Hajiya tana matse kwalla, ganin Saifullahi ta fashe masa da kuka, wai ta na da ɗa kamar shi a cikin gidan nan sai dai ta ga kaza ɗakin matar shi, ya na neman albarka kuwa?


Saifullahi kallon ta kawai ya ke har ta gama kukan ta, ta share hawayen ta dan kan ta. Sannan ya ce


"Hajiya da kin san abin da ke damuna da kaza ba ta saki kuka ba Hajiya, tun ba a je ko ina ba, zuciyata ta fara konuwa da barin Amatullah, Allah ya sa ba dana sani zan yi ba Hajiya!"


Nan fa ta haushi da faɗa, ta in da ta ke shiga ba nan ta ke fita ba, ta kare da


"Idan ni na haife ka Saifullahi maganar wannan bakar yarinyar ta fita bakin ka! Ina tunanin dai ba haka uwar ta ta bar ka ba!"


Saifullahi ya tashi zai fita ba tare da ya sake furta komai ba, har ya kai kofa Hajiya ta tsayar da shi ta hanyar faɗin


"Kuma ka tabbatar kazar yau da ni za ka siya! Na dai faɗa ma ka! Wanda ba ya neman albarka!"


Takaici ya sanya shi girgiza kai ba tare da ya furta komai ba. Ya wuce bangaran sa.


***


Sai da Baban Sasa ya kwana biyar kafin ya dawo cikin hayyacin sa, babu wanda bai zo ya duba shi ba, hatta Saifullahi ya samu ya lallaɓa ya je ya duba shi, Amma ban da Aysuh. Dee Yusuf kuwa duk sanda ya je wajan supervisor din shi ya kan yi kokarin leƙa Baban Sasa, duk da har lokacin ba su gana ba, kullum ya zo sai su Baba Hamza su ce bacci Baban Sasa ya ke, ba ma sa bari ya shiga.


Shi kuwa dama ya na zuwa ne saboda Baba Salihu, waje su ke zama su ta hirar mahaifin Dee, kasancewar ya faɗa masa makaranta daya su ka yi. Hakan ba karamin fahimtar juna da sabo su ka yi ba cikin kankanin lokaci. Baba Salihu kan yi tunanin ina ma Dee musulmi ne da tabbas sai ya ba shi auren Amatullah, dan kuwa ya yaba da nutsuwa da hankalin Dee, babu shakka ya gaji mahaifin sa, haka kuma bai fidda ran zai musulunta ba dan hakan ma ya sa ya ke jan sa a jiki sosai.


Kamar yanda su ka saba, yau ma da yammaci, sun shafe wajan awa ɗaya suna hira da Baba Salihu, kafin Dee ya ma sa sallama, ya ce ya na so ya koma gidan sa. Baba Salihu ya ce


"Ka tafi hakan nan ba ku gaisa da Baban ba?"


Ya na mai sosa kyeya ya furta
"Ai ina ce har yanzu bai tashi ba Baba, wani karan na zo ma gaisa"


"Ah ah yau kam za ku gaisa, mu je ku gaisa"


Ba a san ran shi ba, amma ba ya so yayiwa Baba Salihu musu haka ya bi shi. Baba Salihu na tafe, Dee na biye da shi har su ka isa dakin kwanciyar Baban Sasa.
Baban Sasa kishingide kan gadon shi, Alhamdulillah jiki yayi kyau, a kasa kan tabarma Baba Anas, Baba Hamza, Baba Idris da Baba Muhmuda ne zaune, in da su ke zantawa Baban Sasa na ɗan sa mu su baki jifa jifa. Ganin Baba Salihu da wanda ke biye da shi tuni kowannen su ya tsuke fuska. Baba Anas ne ya yiwa Dee iso cikin sakin fuska.


Gaban gadon Baban Sasa Dee ya tsuganna, yanda Baban Sasa ya haɗe rai bai hana Dee murmusawa ba, cikin girmamawa ya furta


"Baban Sasa sannu da jiki? Ya saukin jiki?"


Da kamar ba zai amsa ba, dan har Dee ya fidda rai, sai kuma ya amsa masa da
"Lafiya, asibitin ma sai ka biyo ni yaro? Wannan naci har ina?"


"Yo ai Baba tun randa ya ba ka jini kullum sai ka gan shi asibitin nan, na kasa ganewa ko jinin na sa ya ke so a biya sa......"


Cewar Baba Idris cikin dacin rai. Maganar ta shi ce ta firgita Baban Sasa, ya na mai rike kirji ya ce


"Waye ya ba ni jini? Eye?"


Shiru ne ya biyo baya, dan kuwa takaicin furucin Baba Idris ne ya hana su magana. Baba Anas na mai duban Baba Idris ya ce


"Yanzu Idris menene amfanin kalaman ka?"


"To to ai gwara ya sani, dan dai kun san da Baba ya na cikin hayyacin sa ba zai yarda a kara masa jinin arne ba!"


Baban Sasa da hankalin sa ya gama tashi ya kara da


"Yo 'ya'yan nan kwa min shiru? Na ce jinin wa aka karamin!"


"Jini na ne Baba, kuma har leda uku ma kuwa!"


Cewar Dee cike da tsokana, dan kuwa ya gane Baban Sasa irin wannan tsofaffin nan ne ma su kafiya, tun kalaman na sa na bata masa rai, har ya dena.


"Jinin ka aka kara min yaro?"


Cewar Baban Sasa ya na mai fidda idanu, Shi kuwa Dee ya gyada masa kai alamar "eh".


"Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun! Shikenan ni Jamoh yara sun kashe ni da rai na! Yanzu Anas ka na ina aka karamin jinin arne! Yanzu da ku za a ci amana ta?"


Kunya ne ya cika Baba Anas da Baba Salihu, su Baba Idris kuwa da ma abin da su ke so kenan, Baba Sasa ya san abin da aka masa dan an ga ya na kwance rai a hannun Allah. Ganin yanda Babab Sasa ya rikice, idanu na fidda kwalla hannu bisa kirji ya na faɗin


"Jinin arne ke gudana a jiki na, an ci amana na, an cuce ni!"


Dee ya ce
"Kwantar da hankalin ka Baba, ni ma ɗin aro na ba ka ai ba kyauta ba, ka dawo min da kaya na, shi yasa ai kullum na ke zuwa duba ka, in ba haka ba ina ruwan arne da kai"


Jin haka Baban Sasa ya tsaya ya duban Dee, irin wannan kallon na kar ka maida ni shasha mana. Su kuwa Baba Anas da Baba Salihu dariya ce fal bakin su ganin kallon da Baban Sasa ya ke yiwa Dee, amma su ka kunshe gudun bacin ran Baban Sasa.


"Ku ji mu da yasasshen zancen! Ta yaya zan dawo ma ka da jinin na ka?"


"Ai wannan abu ne mai sauki, da ka warke duka jinin jikin ka za a zuke, in ya so sai a tace min nawa daga na ka, dan ko nima ba na son jinin tsoho ya gwarwaya da nawa, hakan nan da kuruciya ta!"


Cewar Dee da mayar da zafafan maganar Baban Sasa zolaya. Baban Sasa na mai duban Baba Anas ya ce


"Anas ka ga ɗan butan tsiya! Da ka samu ma aka sanya jinin ka jiki na mai daraja! Sai ka zo ka zuke jinin na ka na gani! Dan tselan uwa kai!"


Daga Baba Anas har Baba Salihu kasa rike dariyar su ka yi, dariya su ke sosai, cikin wannan yanayi likita ya shigo. Ganin yanda su Baba Anas ke cikin nishadi ya ce


"An ya kuwa Baba ana bari ka huta?"


"Ina za su bari na huta bayan sun kashe ni da rai na? Sun gaji da ni so su ke na mu su huta! Jinin arne su ka ƙaramin, gashi nan gaban ka ya na faɗa min wai biyan sa zan yi bayan na warke?"


Ya na maganar ne ya na mai nuna Dee da ɗan yatsa. Ko da Doctor ya kalli Dee su ka hada ido sai ya fadada fara'ar dan kuwa ya san Dee tun suna makaranta.


" Ah Dee Yusuf! Har da kai ake daga hankalin Baba?"
Dee na murmushi ya tashi ya na mai bawa Doctor hannu su ka gaisa, kana ya ce
"Dr Abba Ai tsohon nan da ka ke gani ran karfe gare shi, mun yi kaɗan mu daga ma sa hankali, kawai dai jina na ne sai ya biya ni!"


Dr Abba shi ma ɗin dariyar ya ke yiwa Baban Sasa ya ce


"Dr kada ka daga ma Baba hankali, Baba rabu da shi, shakiyanci ne irin na jikoki....."


"Kai ni ba jika na ba ne! Ina ni ina jika da arne ne!"


"Toh Allah ya ba ka hakuri Baba, Dee ko za ku fita daga waje? Ina so na duba Baba"


Kai ya gyada, in da yayiwa Baban Sasa sallama, maimakon ya amsa masa sai ma kawar da kai gefe yayi. Aka bar Baban Sasa da Doctor.


A waje Baba Salihu yayiwa Dee godiya, tare da bashi hakuri bisa lafazan Baban Sasa. Dee ya ce da shi kar ya damu, ai babu komai shi ɗin yanzu ya gama fahimtar Baban Sasa, ai shekaru sun ja. Cike da sha'awar hali irin na Dee Yusuf su ma yi sallama, bayan tafiyar sa Baba Anas ya ce da Baba Salihu zai so ace Dee musulmi ne, ko zai musulunta, da ko shakka aure tsakanin shi da Amatullah alkhairi ne, ya kare da


"Ka ga fa yanda ya iya tafiya da Baba cikin sauki da lumana, duk da cin fuskar da mu ke masa, ina ma Saifullahi ke da wannan halin"


Kai Baba Salihu ya gyada tare da faɗin
"Yusuf sak, haka uban sa marigayi ya ke wallahi, Allah ya masa rahama"


Baba Anas ya amsa da Aameen. Su Baba Idris kuwa ba su fasa tuhumar su Baba Anas ba, dan kuwa wannan karan laifin biyu ya zama, wai har da na rashin kunyar sa su ka bari Dee yayiwa mahaifin su. Haka kan baffanin Amatullah ya rabu biyu, masu son Dee, wato Baba Zubairu, Baba Anas da Baba Salihu, sai kuma masu nuna masa kiyayya karara, Baba Hamza, Baba Mahamuda da Baba Idris.


****
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, sai da Baban Sasa yayi sati uku kwance gadon asibiti kafin a sallame shi, cikin satin ukun nan kuwa Dee Yusuf na yawan kai masa ziyara, acewar shi dubawa ya ke ya ga ko ya warke dan kar Baban Sasa ya warke ya cika rigar sa da jinin sa. Tun idan ya zo ya na kin amsa gaisuwar shi, har ya zo ya na amsa sama sama, Har dai ya dan saba da ganin sa. Haka duk sanda Dee ya tashi zuwa ya kan zo masa da kayan marmari, kamar 'ya'yan itatuwa haka. Amma fa duk ran da ya zo ba sa wanyewa lafiya, hakan ya sa Su Baba Idris su ka yi kokarin hana shi zuwa ba tare da sanin Baban Sasa ko su Baba Anas ba.


Ganin an sallame su, kuma kusan kwana uku kenan bai ga Dee Yusuf ba ya sanya Baban Sasa raba idanu. Kayan sa ake kwasa ana sanyawa cikin mota, cikin masu kwasar kayan har da Saifullahi. Baban Sasa zaune kan kujera, tun da aka sallame su aka ce ya zo a kai shi mota, ya ce ah ah a fara kwashe kayan tukun. Amma a zahiri jira ya ke ko Dee Yusuf zai zo. Baba Anas da Saifullahi ne su ka dawo tafiya da shi bayan Baba Hamza yayi gaba da ragowar kayan.


"Wai lafiya yaron nan ya daina zuwa?"


Cewar Baban Sasa yayinda Baba Anas da Saifullahi su ka riko hannun sa suna mai sanya shi tsakiya.


"Wani yaro fa Baba?"


Baba Anas ya amsa masa da tashi tambayar.
"Wannan arnan mana! Dan Yusuf"


Gaban Saifullahi ne ya faɗi jin Baba na maganar Dee Yusuf, shi kuwa Baba Anas darawa yayi ya ce


"Ah Baba yau kuma kewan sa ka ke kenan?"


Shiru yayi, sai da su ka isa mota kafin ya shiga ya amsa masa da
"Ka san zuciya ba ta da kashi Anas, yaron nan duk da arne ne na gane ya na da hali mai kyau"


"Ko dai kana jin tsoran kar ya zo a zuke masa jinin sa da ya ba ka ne"


Cewar Baba Anas cikin zolaya yayinda ya taimakawa Baban Sasa ya shiga mota ya zauna. Shi kuwa Saifullahi wani malulun kishi ne ya taso ya tokare shi a kirji jin ana yaban tsohon saurayin Amatullah, dan kuwa duk duniyar nan idan akwai wacce ya ke so ta bi bayan Amatullah, so ya ke Baban Sasa ya sami sauki sosai ya lallaba shi ko Allah zai sa a mayar da auren su. Wai kuma har jinin sa aka sanyawa kakan sa! Wannan abu ya tsaya masa a rai, ya na kuma daga masa hankali.


Daga cikin mota Baban Sasa ya dan leko, kana ya ce


"Anas ba na son shakiyanci, amma dan Allah idan da hali a shaida masa an sallame ni, ka ga yana yawan zuwa duba ni, kar ya zo ya ga ba na nan"


"Toh Baba za a sheda masa kuwa"
Baba Anas ya amsa zuciyar sa ɗaya ba tare da ya lura da halin tashin hankalin da Saifullahi ke ciki ba. Haka su ka koma gida Baban Sasa na yaban Dee Yusuf, ihu ne kawai Saifullahi bai kurma mu su cikin motar ba tsabagen kishi.


*****
Ranar da Baban Sasa ya koma gida murna gidan kamar sallah. Ayush kuwa ranar wuni ta yi cikin taikaci. Ko da Amatullah ta je gaishe da Baban Sasa, nan ma sai da ya mata maganar Dee Yusuf, cewar shi


"Jinin Dan Yusuf aka kara min Amatullah, kin ga rayuwa kenan, na ki hada jini da shi sanadiyar sabanin addini, ashe akwai lokacin da jinin sa zai ratsa nawa, har ya ke gudana a jiki na!"


Mamaki ne ya cika Amatullah, dan kuwa ko da wasa ba ta ji maganar nan ba, ba ta ji ko Mimi ma ta sani da ta fada ma ta. Haka su ka sha hirar su, nan ya jara jaddada mata ta shedawa wannan yar uwar Dan Yusuf din, cewar an sallame shi fa, dan Allah ta fada masa dan kwana biyu ya rabu da lekowa. Amatullah ta amsa da toh. Da haka su ka yi sallama.


***
Sai da Baban Sasa ya kwana uku a gida su Amatullah su ka fara Lectures gadan gadan. Jin Dee shiru Baba Anas da kan sa ya tambayi Baba Salihu number Dee, dan ya tambayi Amatullah ta ce ma sa ba ta da shi, kuma da gaske ba ta da shi din.
Kamar daga sama Dee ya ji kiran Baba Anas, ko da ya gane Baba Anas ne sai gaishe shi cike da girmamawa, in da Baba Anas ya ce ya Kira yayi biko ne, kwana biyu sun ji shiru, ko dai ya fasa karbar jinin na sa ne? Baban Sasa ma ya na kyewar sa. Dee ya masa alkawarin zuwa tare da bashi uzurin komawar makarantar da dilibai su ka yi ya sanya hidama su ka yi masa yawa, ba tare da ya sheda masa su Baba Idiris ne su ka ja masa kunne akan zuwa gun Baban Sasa ba, a cewar su ya na hana shi samun kwanciyar hankali.


Kamar yanda yayi alkawarin washagari sai gashi kofar gidan su Amatullah. Baban Sasa bai iya ɓoye farin cikin ganin sa ba, duk da kuwa har lokacin bai fasa zolayar sa ba. Dee sanye ya ke cikin shadda ruwan toka dinki buba, kan sa dauke da hula zanna bukar mai ratsin ruwan toka da kore. Waje gaban sa Baban Sasa ya bashi ya zauna, ya na mai duban sa ya ce


"Kai Dan Yusuf sai kawai ka ɗauke kafa mu dena ganin ka haka ake yi?"


"Sunana Dee Yusuf Baba, ka ce Dee ba Dan ba"
Cewar Dee cikin zolaya.


"Kai tafi can! Wannan ruwan ka ne ba nawa ba! Yaro na gode fa, ashe dai za ka min rana? Allah ya saka maka da alkhairi"


Cewar Baban Sasa idanun sa na mai kawo kwalla. Ganin haka Dee ya ce
"Ah ah Baba godiyar me ka ke min? Sai fa ka biya ni jini na? Haka za ka zauna da jinin arne?"


"Yo to da haka sai ka kashe ni ai ka huta!"


Dariya Dee ya saka. Nan su ka cigaba da hirar su tamkar jika da kaka, dan kuwa wasa da tsokanan shi da Dee ya ke ko Saifullahi ba ya yi. Sai da su ka gaisa da Baba Anas da Baba Zubairu sannan yayi musu sallama.


Ya na shirin shiga mota ne sai ga Amatullah dauke da Emjay sun dawo daga makaranta. Ganin ta ya sanya Dee tsayawa ya na kallan ta yayin da zuciyar sa ke dada kamuwa da soyayyar ta. Sai da ta zo dab da shi sannan ya mayar da kallan sa ga Emjay wanda ke kwance kan kafadar ta. Kamar kullum yau ma hijabi ne jikin ta, fari kal.


Zuciyar ta ke harbawa tun da ta yi tozali da Dee bai hana ta murmusawa ba yayinda da ta furta


"Sannu da zuwa, ashe ka zo"


Shi ma dai murmushin ya ke, ya na mai mayar da kallan sa ga fuskar ta, in da ta yi kasa da na ta idanun. Shi kan shi ya san Amatullah ta canza, Amma ba ya ce menene takamamman canjin ba.


"Amatullah how are you? Ya babyn ki!"


Ya tsinci kan sa ya na fada, dan kuwa ya biyewa zuciyar sa zai shagala ne nan tsaye ya na kallan ta.


"Alhamdulillah, gashi nan bacci ya ke yi ya gama rigima"


Ta juya masa fuskar Emjay, hakan yayi daidai da fitowar Saifullahi. Ran shi idan yayi duba ya baci ganin Dee da Amatullah, musammam yanayin da Dee ke kallan ta fuskar shi ɗauke da murmushi. Bai san sanda ya tunkare su ba, kamar daga sama sai gashi gaban su.


"Amatullah ba ni yaron nan ba ki ga ana rana ba za ki tsaya da shi haka?"


Cewar Saifullahi ya na mai kokarin karbe shi daga hannun Amatullah ba tare da ta ankare ba. Ganin haka babu shiri ta sakar masa Emjay, fuu ya wuce ciki. Daga Amatullah har Dee bin sa su ka yi da kallo cike da mamaki, musammam Amatullah da ta san tun da ta bar gidan Saifullahi bai taɓa nuna wani kulawa ga Emjay ba.


Kallon Dee ta yi ta na mai murmushin yake dan kuwa hankalin ta na kan Emjay,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login