Showing 27001 words to 30000 words out of 112099 words

Chapter 10 - KASHE FITILA Book Complete by Batul Mamman.txt

23 Jun 2024

14002

daidai bane iyalinka tayi maka laifi ka rasa wurin tsawatarwa sai bainar jamaa"


"Yaya wallahi tun ranar da kuka zo na rasa dalilin da yasa nake jin haushinta. Amma idan ka duba zaka ga da gaske laifin take yi. Gani nake kamar tana boye min wani abu"


Tausayi ya bawa Harisu hakan yasa ya dafa kafadarsa.


"Kada ka bari zamanku na shekaru ya baci a yanzu da kuka tara iyali. Idan Allah Yasa Maamu ta warke komai ya daidaita mun tafi ka samu kuyi magana ta fahimta."


Shawarwari Harisu ya cigaba da bashi ita kuma Gimbi tana gefe ranta ya gama baci. Ba komai ke damunta ba sai tunanin Harisu ne yake ingiza Awaisu yana mata wulakanci yanzu. Ji tayi komai ya dagule mata ta fice daga wurin. Balele ta kira zata yi korafin rashin ganin sakamakon aikin bokansa.


*****
Anti Bebi na mota tana jiran Balele da yake tsaye ana zuba mai taji wayarsa na kara. Daukowa tayi zata mika masa ta taga ta kula an rubuta *hajiya gimbi*.


Wata irin dariya ta fashe da ita daga Balele har mai zuba man sai da suka tsorata. Yana shiga motar ta bukaci ya fada mata meye hadinsa da Gimbi. Sanin hatsabibancin uwardakin nasa yasa ya fada mata komai.


Cinya ta daka tana tafa hannuwa "lallai Gimbi tana cikin matsi. Shine don wulakanci ka kaita gidanka. To bata ga yaranka ba gari guda."


Dukar da kai yayi kada tace ya dawo da kudin.


"Wannan kudi kaci rabonka a jikinta. Neman boka yanzu ta fara ma. Wani abin sai na kamata a hannu. Bari dai Shuhada ta gama idda "


Balele ya zaro ido "Hajiya me zaki sake yiwa Shuhadan? Da kin barta haka tunda auren ya mutu"


Yana tausayin yarinyar ganin yadda Anti Bebi ta juya musu rayuwa ita da iyayenta lokaci daya.


"Aure zanyi mata ba wata tsiya ba"


*****


Bayan Laminde ta farka kumburin bakinta ya hanata magana. 'Yan sandan suka ce zasu dawo washegari. Awaisu yasa Gimbi ta kira wadda ta kawo mata ita domin a sanar da danginta. Da ma bazawara ce, danta daya Nafi'u dan kimanin shekara sha bakwai saboda tayi auren wuri. A hannun kanin babansa yake tun bayan rasuwar mijinta. Da suka ji sakon Nafi'u ya sha kuka suka yi shirin zuwa Abujan shi da kawunsa. Kawun nasa kuma yayi alqawarin ta dena aiki kenan. Gara ta nemi wata sanaar a kusa da gida.
*****


Washegari har yamma Laminde babu bakin magana. Mutanen Fika sun je dubiya tare da Maamu wadda aka sallama a ranar aka bar Hinde a wurinta.


Mama itama ta kadu da jin wannan mummunan labari taje ta dubata tare da wata mai aikinta wadda zata rinka kwana da ita.


Nafi'u da Kawunsa sunzo inda Awaisu yayi ta basu hakuri. Suma a gidansa sukayi masauki. Kawun yace ana sallamarta gida zasu tafi da ita. 'Yan sanda kuma jira suke ta fara magana su dauki jawabinta.
****


Su Maamu na zuwa gida Baaba tace zasu koma Fika washegari tunda sun kwana biyu. Maamu ta rasa yadda zatayi. Tana son fadawa Baaba matsalarta a gidan Awaisu amma tana son rufa masa asiri. Da kunya ta kare rayuwarta a alfarma duk da sun dauketa tamkar jininsu. Ita da take burin Awaisu ya cigaba da kyautata musu ace kuma ita kanta ya gagara rikonta. Gashi bata da 'yar uwa mace da zata iya fadawa domin neman shawara. Tana ji tana gani washegari suka tafi. Tikeke da Hinde duk tijarar da suka tanada abubuwan sa suka faru a gidan suka sa su yin lakwas. Bomoi kuwa yayi alkawarin dawowa nan da dan lokaci cin arzikin gudan jininsa. Suna bakin mota Rumana tana ta kuka har Gimbi na zolayarta wai ta zama 'yar yaye. Ita wasan ma tsoro ya bata don bata saba ba.


Dayake tafiyar sassafe ce suna tafiya itama da yaran dreba ya kaisu makaranta. Bandaki ta tafi ta rufe kanta tana kuka. A nan Yusra ta sameta. Bayan tambayoyi da kyar ta sanar da ita komai game da zamanta da kawunta.


"Da nice ke Rumana da tuni kowa ya manta na taba zaman Abuja. Ai wallahi da haukan gaske da na karya zan gudu. Rannan Umma take cewa na tambayeki ko baki da lafiya kike ta ramewa ashe yunwa ce. Kuma kika ki fada min" ta kare da hararta.


Rumana bata amsa mata ba, hankalinta ya tafi tunanin maganar Yusra...anya ba haukan zatayi musu ba kuwa. Har fargaba take a tashi ta koma gida.
*****


A tsattseye suke gefen gadon da Laminde take tare da 'yan sanda biyu sai Awaisu da Gimbi da kuma Kawu da Nafi'u.


A hankali saboda kumburin bakinta Laminde ta tashi da salati. Tana hada ido da Gimbi ta razana ta fara cewa


"ruwan asiri"


Kasa kunne duk suka yi domin gane me take fada.
*KASHE FITILA*💡21


*Batul Mamman*💖




Laminde ta sake cewa "ruwan asiri"


Gimbi ji tayi kamar an sauke guduma a cikinta ganin Laminde zata tona mata asiri.


A daidai lokacin Mama ta shigo kuma ta ji abin da Laminde ta fada. Kawu ne ya kara matsawa bakin gadon zaiyi mata tambaya sai daya daga cikin 'yan sandan ya dakatar dashi.


Da sauri Gimbi ta kirkiro kuka harda hawaye. Ita kanta mamakin saurin zubar hawayen nata tayi. Kan Laminde ta fada tana rusa kuka


"Abban Haris kaji wata masifa, Laminde ba dai tabin hankali kika samu ba"


Nafi'u ya matso da sauri yana tambayarta ko ta gane shi. Gimbi ta samu yana tayata kukan duk ta cika dakin da karaji.


"Yallabai ku nemo mutumin nan da ya kadeta. Wallahi bazamu yarda ba idan ta haukace"


Tsawa Awaisu ya daka mata ganin itama ta zama kamar mahaukaciyar
"Meye yake damunki ne, dubi tana son yin magana kin hanata"


Ko motsi batayi ba domin tasan muddin Laminde ta fadi abin da ta gani kowa yarda zaiyi. Musamman Awaisu da ta kula yanzu kamar ma ya tsaneta da Mama da take saka mata ido.


'Yan sandan suka ce kowa ya fita zasuyi mata tambayoyi. Gimbi ta wani kankame Laminde
"Babu inda zani sai na tabbatar da lafiyarta. Laminde amana ce garemu. Ni satar da na kamata zatayi min na yafe. Ki yafe min, duk laifina ne da na kasa hakuri ban saurari dalilin da yasa kika shigarwa Abban Haris daki ba"


Maganar ta doki kunnen Laminde cikin kaduwa, _sata!_. Yanzu sharrin sata Gimbi ta kala mata. Hawaye ta soma yi tana kallon danta wanda aka zubar mata da mutumci a gabansa.


Sake bude baki tayi zata fadi gaskiyar abin da ta gani Gimbi kawai ta mike tsaye tana dafe kai
"Wayyo kaina, washhhh"


Sai gata ta fadi a kasa gaban Kawu. Duk abin Awaisu da gudu ya fita neman likita. Mama wadda tun shigowarta bata ce komai ba sai lokacin tayi wani murmushi mai ciwo. Iyakar abin da Gimbi tayi a gabanta yanzu ya tabbatar mata da gaskiyar Laminde. Fita tayi jiki a sanyaye tana bakincikin wannan al'amari. Tana shiga mota ta sanar da dreban inda zai kaita.
*****


Da gaske Gimbi taki farfadowa har kusan rabin awa. Likitan ya rasa gane mene ne yake damunta. Da ya auna jininta ya ga ya hau. Awaisu yayi wa bayanin cewa a kula da ita domin ciwon Laminde ya tsaya mata sosai. 'Yan sanda suka gama bincikensu suka tafi. Iya abin da Laminde ta fada bai wuce cewa ba sata tayi ba kuma bata shiga dakin maigidan ba.


Bayan fitarsu Kawu ya tilasta mata ta fada masa gaskiyar me ya faru. Tana fada tana kuka tace dole zata sanarwa Mama.


"Laminde mutanen nan ba sa'aninmu bane. Wannan matar idan har gaskiya kike fada tafi karfinmu ta ko ina saboda haka ki bar maganar nan"


Kokarin zama tayi Nafi'u ya tayar da ita sosai "iyalin mutumin nan musamman mahaifiyarsa suna cikin hatsari. Da ace kana ganin irin yadda uwar mijin take rayuwa a gidan bazaka ce nayi shiru ba. Ba sharrin sata ba ko me zata yi min sai na fadawa 'yan sandan nan gaskiya"


Kafin Kawu ya bata amsa yace Nafi'u ya basu wuri. Ya kama kofar zai fita Gimbi ta shigo fuska cike da hawaye.


"Laminde ki rufa min asiri. Abubuwan da kika gani sharrin shaidan ne. Kada ki tona min asiri ki raba sunnar Annabi SAW. "


"Kinga Hajiya daga nan garinmu zamu wuce da ita. Ina rokonki da kiyi hakuri ki janye satar da kika dora mata. Daga yau kin dena ganinta ma"


Farinciki ne ya bayyana a fuskar Gimbi har ta kasa boyewa Kawu. Kudi ta debo a jakarta ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu.


"Bama neman komai daga gareki. Kina iya tafiya amma kada ki taba mantawa rana dubu ta barawo...."


Dan dakatawa tayi tana auna maganarsa sai kuma tayi saurin fita saboda Awaisu yana wurin likita ta fito daga dakin da aka bata. Laminde ta kalli Kawu zata yi magana yace ta bar komai a hannunsa. Irinsu Gimbi baka musu fito na fito lokaci guda, musamman idan baka da shaida. Zaiyi iya kokarinsa wurin taya Awaisu da mahaifiyarsa da addu'ar neman tsari.
*****


Naman kaza take ci tana kurbar juice a kofin glass taji an banko kofar dakinta. Duk gidan hatta Shuhada da take iya yi mata rashin kunya wasu lokutan bata isa tayi mata haka ba. Shiyasa tana jin karar kofar ta zabura ta tashi. Kusan karo suka yi da Mama kafin taji saukar mari zazzafa a kuncinta.


"Bebi sai Allah Yayi mana shari'a ni da ke. Me nayi miki haka kika lalata rayuwar 'yata"


Duk da radadin da kumatunta yake yi bai hanata dariyar keta ba.


"Su Aminatu salihan bayi. To ai kinsan ba'a daya a dangi. Wannan Gimbiyar taki kina ganinta haka ba karamar fitinanniya bace."


Mama ta kara harzuka "kada kiyi tunanin zan bar maganar nan haka. Naji komai daga wurin Laminde. Nasan kece kika kaita wurin shaidanun bokayenki."


"Kin kuskuro 'yar uwa. Wannan karon Gimbiya gaban kanta tayi. Shawara ta daya gareki shine ki nemi Awaisu ya mayarda uwarsa garinsu. Idan ta cigaba da zama to ina mai tabbatar miki yanzu ta fara kwanciya a asibiti. Gimbi ba karamin tsana tayiwa wannan matar ba"


Kallonta Mama tayi sosai. Anti Bebi ko kadan zuciyarta bata rissina ga abin da tayi niyya. Idan aka cigaba da haka watarana ba auren Gimbi ne kadai zai mutu ba. Su ma iyayenta mutumcinsu sai ya zube a idanun al'umma.


"Bebi ki dubi Allah ki kyale Gimbi tayi rayuwarta. Idan tazo gidanki kici mutumcinta ki koreta. Ke kin sani bin boka da malaman tsibbu haramun ne amma kike takewa. To akan mene ne sai kin hada da 'yata?"


"Masu 'ya manya, abin da nake so ki sani shine yaran yanzu idanunsu a bude suke. Kowa ya waye da sanin rayuwa. Idan baki nemi taimako ba kina kallo bakincikin da namiji zai kasheki a banza. Ko zaki ce kin manta irin bacin ran da Innarmu tasha wurin Baba? Tun lokacin nasan cewa namiji zuma ne sai da wuta. Ban ga wani shegen da zan ragawa ba yazo yana cin zarafina"


Mama ta saki baki tana sauraron kanwarta da tayiwa duniya gurguwar fahimta.


"Ba duka aka zama daya ba Bebi. Yanzu kina jindadin zama da mijinki ya zama kamar hoto sai yadda kika juya shi?"


"Wannan ne mulkin, ko da wasa bai isa ya takani ba. Gimbiya kuma ki dena ganin laifina ita ta kawo kanta. Mata da dama a zamanin nan sai da haka suke samun damar cimma burinsu a wurin mazajensu. Me za'ayi da uwarmiji banda takura da sanya idanu"


Anti Bebi tayi nisa. Mama gani tayi cigaba da yi mata magana bacin lokaci ne sai kawai ta juya ta fita daga gidan. Ba abin ta fadawa Innarsu ba tasan babu wani mataki da zata dauka. Komai Anti Bebi tayi daidai ne. Tana zuwa gida ta kira Alh Mudi a waya ta fada masa. Ya rinka fada kuwa kamar ya ari baki. Allah Yasa yana gari yace ta kira masa Gimbi kafin ya karaso gidan.
*****


Sai yamma Gimbi ta sami damar amsa kiran Alh Mudi. Lokacin ta tabbatar Laminde da 'yan uwanta bazasu cigaba da zama barazana a gareta ba. Shi kuma Awaisu ya wuce kasuwa.


A tsorace ta shiga gidan domin tun fitar Mama daga dakin asibitin jikin Gimbi ya bata akwai matsala. Sama ta hau dakin Alhajin ta samesu duka su biyun babu wanda yayi mata kallon arziki. Haka ta sami wuri ta zauna can gefe. Alh Mudi ne ya fara magana


"Gimbi ki fada min tsakaninki da Allah mijinki yana tauye miki hakki ne?"


A hankali ta girgiza kai alamun a'a. Ya sake tambayarta


"Ita Maamu ko sau daya ta taba nuna bata sonki da danta?"


Wannan karon ma girgiza kai tayi. A take ta ji Alhaji ya daga murya ya soma fada.


"Bakin gwargwado Gimbi mun baki tarbiya daidai iyawarmu. Mun baki ilimi domin ki bambance daidai da abin da yake ba daidai ba. Amma sai kika zabi biyewa son zuciya da hudubar shaidan. To ki sanu komai ka shuka da sannu zaka girbe duk daren dadewa"


Da yake ba kunya gareta ba sai ta dago kai tana tambayarsa me yake faruwa ne.


Hakan ya kara batawa Mama rai ta tashi zata kai mata duka. Alhaji yace ta zauna


"Bar ta Amina, Gimbi duk abin da kike yi domin ganin Maamu ta bar gidan danta mun gane. Banyi zaton akwai ranar da zan wayi gari 'yar cikina tana mu'amala da malaman tsibbu ba. Saboda haka na shirya sanar da Awaisu halin da ake ciki zan kuma umarce shi da ya sakeki muddin baki chanza hali ba"


Da sauri ta dago kai tana kallon iyayenta.


"Alhaji saki fa kace."


"Rufa min baki mara kunya, har kina da bakin magana. Alhaji kace ya saketa kawai ya huta. Idan kina son shi da gaske babarsa ko musaka ce wallahi zaki taya shi kyautata mata" cewar Mama


Gimbi ta matso kusa da Mama jin abin da tace tana kuka "don Allah kuyi hakuri bazan kara ba."


Fada sosai suka rinka yi mata tare da cigaba da barazanar zasu saka Awaisu ya saketa. Da suka ga hankalinta ya tashi sosai shawarwari suka bata da nasiha akan hukuncin da zata tarar nan gaba a lahira. Ita dai rokonsu takeyi kada Awaisu yaji maganar. Da ta fito daga gidan ko tunanin kirki batayi ta wuce gidan Anti Bebi.


Da kuka ta shiga ta fada jikinta. Anti Bebi ta tureta tana fadan me ya kawota gidan.


"Ki taimakeni Anti Bebi kada su Mama su kashe min aure. Awaisu shine farincikina. Komai nawa ya rikice tun bayan rabuwarmu a asibiti."


"Gimbiya kenan, ai nayi zaton karanki ya kai tsaiko har zaki iya hada kafada dani"


A ladabce ta kalli Anti Bebi "kiyi hakuri, bana son duk wani abu da zai gifta tsakanina da Awaisu mara dadi. Yanzu baki ga irin wulakancin da yake min ba. Gashi su Mama sun gano"


Anti Bebi tayi murmushin samun nasara akan Gimbi. Lallai Wangesi ibilishi ne. Cewa tayi kawai yayi duk yadda zaiyi Gimbi ta dawo karkashin ikonta. Gashi ta gani kuwa.


"Yanzu me kike so ayi?"


Da yatsu ta fara kirgawa


"so nake Awaisu ya koma kamar mijinki, kada ya rinka min musu ko gardama, Maamu ta koma garinsu ko kuma ya fita harkarta ni kuma zanyi yadda na ga dama har sai ta tafi don kanta, su Alhaji su dena yi min fada duk abin da zanyi babu ruwansu, sannan a wurin aiki kowa ya rinka shakkata hatta oganmu"


Ita kanta Anti Bebi ta jinjinawa dogon burin Gimbi. Shiyasa baa so mutum ya fara shige shige. Idan akayi rashin sa'a imani yayi karanci shikenan kuma an soma kenan. Ko don ta rama marin da Mama tayi mata zata karbi Gimbi hannu bibbiyu. Amma kuma tayi alkawarin sai itama tayi kuka a gaba. Bata ga wanda ya isa ya takata ta kyale ba.


Bayan tafiyar Gimbi dakin Alh Maitama ta shiga. Yana zaune shi kadai a takure a gefen gado kamar wanda akace kada ya motsa. Yana ganinta ya sake gyara zama. Sakin fuska tayi bayan yasan dazu ya bata mata rai saboda ta nemi kudi yace ta jira ayi albashi. Shine tace ya zauna a daki. Sassauta murya tayi tana masa murmushi


"Alhajina yaushe Shuhada zata tafi ne?"


"Ke nake jira dama ki fadi rana sai na sanar da ita. Kamar yadda kika nema na hanata fitar"


"Na samar mata miji ne. Idan ta gama idda sai ayi auren."


Kamar yayi magana sai ya kasa saboda bakinsa da yayi masa nauyi


"Baka ce komai ba, ko banyi gwaninta bane?"


Dolensa ya kirkiro murmushi "kinyi min komai Bebi, nagode sosai."


Tashi tayi har ta fita tana jiyo muryarsa yana mata godiya. Tana zuwa daki ta dauki waya ta kira Wangesi. Duk bukatar Gimbi ta zayyana masa sannan ta kara da cewa bata so Alhaji Maitama ya bar Shuhada ta tafi. Kuma tana gama iddah ayi aurenta da Awaisu ko ta wane hali ne.


*KASHE FITILA*💡22


*Batul Mamman*💖






*Bayan sati uku*




Babu kowa a ajin kasancewar ko bakwai da kwata batayi ba. Rumana ta shigo kayan makarantarta kamar an kwato a bakin kare. Sun yamutse gashi da alamun ko wanki basu samu ba. Zama tayi akan kujerarta ta hada kai da teburin gabanta tana kuka. Tunda take a gidan kawunta Awaisu bata taba ganin wulakanci irin na safiyar yau ba. Ji take yi kirjinta kamar ya fashe don bakinciki. Shi kuwa Awaisu ya fice fit daga ranta bata ko kaunar ganinsa.


Tana wannan kukan wasu mutum biyu suka shigo taki dago kanta balle a ga idonta. Yusra ce ta hudun shigowa ajin. Ko ba'a fada ba tasan aminiyarta ce a zaune shiyasa tana ajiye jakarta ta kai mata dundu a baya. Maimakon ta dago tace zata rama yadda suka saba sai taji shiru. Dago kan Rumana tayi da karfinta sai ga hawaye suna sintiri a kumatunta.


"Rumana kiyi hakuri, ko zaki rama ne?" A zatonta dundun da tayi mata ne yasata kuka.


Ganin an fara kallonta yasa ta fice daga ajin Yusra na bin bayanta. Bayan SS3 da babu kowa saboda daliban sun gama WAEC suka je. Nan Yusra ta rinka rokon Rumana da kyar ta fada mata irin zaman da takeyi a gidan kawunta da kuma sabon salon wulakancin da ake yiwa Maamu.


"Yanzu ita matar Uncle din naki don wulakanci idan ita ce aka yiwa haka zata ji dadi?"


Rumana ta goge idonta da yake faman radadi saboda kuka
"Don ma ba a gabanki akayi bane Yusra."


"Ni shawara daya zan baki wallahi ku tattara ku koma gida. Ki fadawa Maamu tace zata koma Fika. Idan kuma taki Allah kiyi tafiyarki. Ga yunwa ga wulakanci....tabdi, wallahi da nice watarana sai na zuba mata miyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login