Showing 93001 words to 96000 words out of 112099 words
Chapter 32 - KASHE FITILA Book Complete by Batul Mamman.txt
shiyasa kika amince kika dawo gidan nan. Tun motarsu batayi nisa ba kice su dawo su daukeki kafin jikinki ya gaya miki. Abban Haris bazai taba zama dake ba. Yarinya baki fi cikin cokali ba na tsaya ina magana dake saboda wulakanci. Ki bani numbar uwarki da bata san ciwon haihuwarki ba inyi da ita"
Rumana taji haushi kamar tayi kuka ta daure ta tattaro duk wata dakiya da take da ita ta yiwa Gimbi wani kallo shekeke
"Anti kenan ni din dai cikin cokalin da na sace zuciyar Son So nice daidai dake."
Zuciyarta har tsalle take yi kada Gimbi ta kai mata duka tayi saurin fara tafiya sai kuma ta tsaya "Anti dama ina son muyi maganar rabon kwana. Idan Son So dina ya kiramu nasihar kishiyoyi ni dai kwana uku-uku zan ce ina so saboda gaskiya biyun nan da aka saba yayi min kadan. Ukun ma dai maneji zanyi kada na shiga hakkinki." Kafin ta amsa da sassarfa ta bar wurin kada ta saki fitsarin da ya kamata na tsoro.
Tamkar an kafe Gimbi da guduma haka taji. Wai ita Rumana take yiwa zancen rabon kwana. Tashin hankali da ba'a saka masa rana. Gumi ne ya rinka tsatstsafo mata ta rasa me zata yiwa yarinyar nan ta huce.
Tafi taji daga bayanta ta juya taga Awaisu yana dariya. Ashe duk abin da sukayi akan idonsa ne. Shi ya taho da sauri ya rarrashi Rumana ne ya samesu a wannan yanayin.
A harzuke tace "Ka jawa yarinyar nan kunne wallahi bazan dauki raini ba."
"Tsuntsun da yaja ruwa.."ya fada ya yana wuceta.
Tsoro ne ya kamata kada zuciyarta ta fashe saboda bakin ciki sai ta koma dakinta kawai.
Rumana najin an murda kofar dakinta hantar cikinta ta kada tsoro ya cikata tana tunanin Gimbi ce. Ganin Awaisu ta tashi da gudu taje ta rungume shi tana ajiyar zuciya.
"Yaya akayi Son So?"
Har lokacin jikinta na bari tana jin kamar Gimbi zata zo ta sameta nan "Uncle kasan me nayi kuwa? Taba zuciyata kaji ina jin jinina ne ya hau"
Dariya sosai ta bawa Awaisu yana rungume da ita ya dagata yana tafiya hanyar gadonta "ba rabon kwana kike so ayi ba Son So, nima kwana biyun gaskiya sunyi min kadan"
Kokarin sauka daga hannunsa tayi jin abinda yace. Wannan karon banda tsoro harda kunya. Jikinta sanyi kalau lokacin da ya kwantar da ita akan gadon.
"kaji abinda nace?"
Yayi murmushi yana zama a kusa da ita.
Tashi tayi zaune "to wallahi wasa nake yi kuma...kuma ma...kuma ni ban san meye rrrabbbon kwanan ba"
Janyota yayi tana ta zillewa "ki nutsu ma'anar rabon kwanan zan fada miki"*KASHE FITILA*💡48
*Batul Mamman*💖
*_Kin cancanci fiye da haka Aisha Maman4H....Gaisuwa tare da fatan alkhairi._*
Faduwar gaban Rumana ta tsananta ganin yadda Uncle Awaisu ya riketa ga abinda bata taba tsammanin faruwarsa ba wato hada wurin kwanciya dashi. Shiyasa gabadaya ta rikice har take ganin gara ace a gaban Gimbi take a tsaye tana jiran ta kai mata duka da wannan katuwar kunyar da ta lullubeta.
Idanunta ta runtse sosai tana fitar da numfashi da sauri shi kuwa ya danneta da rabin jikinsa saboda ta dena kokarin tashi yana kallon fuskarta. Murmushi yayi ya ja hancinta da yatsu biyu
"Wai waye ya firgita min amarya ne na kula tun safe yau wani tsorona ma kike ji"
Shiru tayi kirjinta yana dukan uku uku saboda numfashinsa da take ji ya kara yin kusa da fuskarta.
"Kinga ni kawo kunnenki yadda na fada miki wacece kwaila zan fada miki meye rabon kwanan da kike so ayi kwana uku na maneji"
Jin yayi saitin kunnenta ta dago hannu a tsorace ta dora akan bakinsa saboda ko kadan bata shirya jin me zai fada ba. Har yanzu bata manta kunyar da ya bata ba da ya fassara mata kwaila a Fika.
Cikin sarkewar harshe tace "na tuna ashe ma na sani ba sai ka fada ba"
Lumshe ido yayi yana shakar kamshin tafin hannunta mai laushi akan bakinsa ta kula da yadda yake yi ta zame hannunta a hankali zata tashi ya kara sakin jiki ta danyi kara cikin sanyin murya mai dadi tace.
"Wayyo Son So zan karye fa"
Har kasan zuciyarsa maganar ta shige shi ya rinka jin sonta yana kara fizgarsa ya rungumeta sosai a jikinsa yana mamakin wannan so da yake mata.
Ita kuwa kara tsorata tayi ta rasa yadda zatayi tasa ya tashi kawai sai tace masa tana jin yunwa. Tashi yayi zaune ya dagota a jikinsa.
"Me kike son ci?"
"Su Anti sun ce akwai komai na girki a fridge da store bari naje na dafa mana" tana magana tana sauke kafafunta daga kan gadon.
Wata irin janyowa Awaisu yayi mata ta fado cinyarsa ya kalleta fuskarsa kamar zaiyi mata kuka yace "ki rufa min asiri Son So har yau bakina bai manta yajin nan da kika gasa shi dashi ba"
Dariya sosai Rumana ta rinka yi harda rike ciki shi kuwa yana binta da kallo cike da jindadi.
Idonta harda hawaye don mugunta ta dan bata rai "kowace amarya mijinta yana son cin abincinta amma ni tsoron nawa ma kake yi. Nasan ma cewa zakayi ban iya girki ba"
Hawayen dariyarta da ta mayar kamar tana kuka ya hargitsa masa lissafi ita kuwa tana ta dariya a ranta.
"Waye yace miki amare suna girki? Daga gidan su miji ake kawo fa. Tunda mu munyi nisa na yarda zan siyo miki har ki gama kwana bakwai dinki a fara rabon kwana" ya kashe mata ido yana murmushi.
Sake bata rai tayi bakin nan ta turo shi gaba tana wasa da yatsun hannunta kamar da gaske bata ji dadi ba "Iman jiya ta koya min wani girki tace yana dadi aci as breakfast. Ko yi banyi ba kana cewa zaka siyo bayan na iya"
Ajiyar zuciya yayi shi dai gaskiya baya marmarin sake cin abincin Rumana nan kusa sai ya tabbatar da iyawarta.
"Fada min naji irin abin da ta koya miki din sai na rakaki kitchen din ma muyi tare"
"Yeeeyyhh" ta tashi daga cinyarsa dama a dofane take ta danyi tsalle tana dariya.
"Sunansa Indomie mai romon dadi"
Awaisu ya koma yayi kwanciyarsa yana tunanin sawa ta hakura don dole. Ko ta iya girki yafi son su yini tare ba wai ta tafi kitchen ta barshi ba.
"Kiyi hakuri Son So ni ba mai son Indomie bane dama."
"Wannan fa mai dadi ce...nama ake yankawa kanana sosai amma da yawa sai yayi laushi a jajjaga attaruhu da albasa...... "
Zama yayi ba shiri jin ta ambaci attaruhu "ina jinki Iman din nan da gani ta koyi mugunta a zaman boarding da tayi. To kuma attaruhun nawa ake sawa? "
Ba karamin dakewa tayi kada ta fashe da dariya ba saboda yadda yayi da fuska.
Da yatsun hannunta take masa lissafi "tace idan guda daya ce karama attaruhu biyu da rabi sai rabin albasa. Idan biyu ce kuma attaruhu biyar cif da albasa madaidaiciya daya. Soyawa ake fara yi sai a hada a ruwan naman a saka indomie din. Amma tace idan superpack ce guda hudu ake sawa a daya"
Daga labarin kawai yaji kamar dakin ya fara daukar zafin yaji ya taso gabanta ya tsaya. Kasa cigaba tayi saboda yadda yayi mata kwarjini sai ta ganta ta koma yar karama a gabansa. Kafadunta ya dafa tare da daidaita fuskarta da tasa
"Zanyi komai domin faranta miki Son So amma wannan romon azabar ba dani ba...naga alama a gadon asibiti kike so muyi amarcin nan"
Tun kafin ya daga kansa Rumana ta soma dariya harda kyakyatawa. Sosai taji dadin yadda ta ruda Uncle Awaisu ya mika hannu zai kamata ta zille ta haye gado. Ganowa yayi tsara shi kawai tayi don tsokana ya rinka binta yana cewa zaiyi maganinta tunda ya zama abin tsokana. Da kyar ya damkota suka fada kan gadon tuni idanunta suka raina fata da yace mata ya tuna yana da maganin yaji. Bai sake bari tayi magana ba ya hade bakinsu wuri daya yana jin yadda zuciyarta ke tsananin bugu. Don kansa ya kyaleta yana son su hada ido taki.
"Ashe ma duk cika baki ne tsokanar taki. Nafi so idan kinyi tsokana ki shiryawa abin da zai biyo baya. Muje kitchen din nima ina jin yunwa idan mun dawo zaki fada min me da me aka fada miki da yasa kike tsorona haka har nake jin bugun zuciyarki yana neman fin karfin kwailan kirjin nan naki"
Da muryar shagwaba tace "Ni dai ba kwaila bace"
"Mu gani" ya fada yana dago hannu ta tashi a guje ta fita.
Dariya yayi yabi bayanta sai dai dakin Gimbi ya fara wucewa.
*****
Waya take yi yana tura kofar tayi saurin katse kiran. Tabe baki yayi yana girgiza kai. Tunda Rumana ta tare lafiya lokacin da zai mayar da yakinsa kan Gimbi yayi. Shi kadai yasan me yake kudurawa a ransa game da ita.
Kallon banza tayi masa ta watsar duk kuwa da yadda zuciyarta take tsallen murnar ganin sa da jin kamshin turarensa mai sanyaya mata rai.
"Uhmmmm angon kwaila me ya fito da kai? Nayi zaton ni da sake ganinka sai zaku asibiti nakuda ta kamata. Ko ka fito da ita goye a bayanka"
"Me kike ci na baka na zuba. Muna nan dake wannan da abinda ya fishi duka zaki gani."
"Ka dai ji kunya auren yarka...woooooo" ta rinka masa ihu.
"Ke kinfi kowa sanin Rumana *halal dina* ce. Anyway nazo fada miki ne gas cooker dinki da wasu cikin kayan girkinki suna nan a gefe daya a kitchen. Kina da damar daukar duk abinda kike so a store ki dafa amma iya cikinki ke kadai. Ina rokonki tun muna fahimtar juna kada ki kuskura ki taba komai na Rumana"
Wani daci taji a wuyanta na bacin rai. Ita da ta taba yiwa Rumana iyaka da kitchen dinta yau itace akayi mata iyaka dashi.
"Dama maza da dama baku san adalci ba musamman idan kuka dauki budurwa. Kai naka gigin yafi na kowa ma tunda an hadaka da kwaila"
Rike baki yayi tamkar baiji haushin kalmar da ta fada ba "Me? Idan ma Son So kike yiwa kallon kwaila kije a wanke miki ido. Matata duk inda ake bukatar mace ta kai har da kari...ai kin gane me nake nufi" ya daga gira yana mata murmushin mugunta.
Ta kuwa hau ta cika fam ranta ya sake baci. Ta rasa yadda zatayi rayuwarta ta koma daidai. Hawaye taji ya sauko mata ta sharesu a fusace. Ta tsani Awaisu yana ganin hawayenta tamkar ta gaza ne
"Kaga Malam kaje ka dafata ka cinye karewar soyayya amma ka dawo min da 'ya'yana gabana. *Banda rashin adalci da rashin sanin darajar haihuwa* me zai sa ka rabani dasu"
Tafi Awaisu ya rinka yi ya shigo dakin sosai ya dawo gabanta ya tsaya "Gimbi ashe kinsan meye darajar haihuwa? Nayi zaton kinyi nisan da bakya jin kira. To bari kiji na fada miki " ya nuna ta da yatsa wanda ya kusa shigar mata ido "ni Awaisu Kabir Fika nasan daraja da kimar da Allah Yayiwa mahaifiya. Shiyasa dana dauke yaran na kaisu gidan iyayenki. Gimbi ko a lahira bana fatan su Haris su taba sanin matar da tafi kowacce mace daraja a rayuwarsu ta taba yin shirka, ta taba taka kafafunta taje gidan boka. Ni shaida ne kina cikin matan da suke matukar wahala wurin haihuwa musamman ta Mu'allim na kuma gode Allah babu haihuwar da kikayi ina nesa. Ciki da rainonsa da haihuwa duka babu wanda bansan yadda kika yishi ba. Wannan darajar ita tasa har yanzu kike amsa sunan matar Awaisu dan Maamu. Ke da na kai naki wurin naki iyayen kike jin haushina ki tuna abinda kika yiwa matar da baki san da yadda ta haifi nata dan ta raineshi ba."
Idanunsa a lokacin sun kada sosai sunyi ja yana kukan zuci saboda tuna halin da Maamu ta shiga bai sani ba. "Har yau ban ga alamun nadama ko dana sani a tattare dake game da hakkin uwa da danta da kika daukarwa kanki ba. Bana jin zaki taba fahimtar halin da kika jefamu sai kin wayi gari matar daya daga cikin yaranki ta gasa miki wulakanci kwatankwacin yadda kika yiwa Maamuna"
A zafafe tace "Allah Ya kiyaye wallahi wannan mugun fata naka ka gani a kanka"
Lebensa ya dan cije "ai na riga na gani Gimbi tunda na aureki. Ke naki jiyewa dai kinsan duniya tamkar gona take. Abinda ka shuka shi zaka girbe. Mutum bazai shuka dusa yazo ya girbe ciyawa ba....kiyi tunani"
Daga haka ya fita daga dakin yana tuno wasu lokuta da yake ganin Maamu a wulakance amma baya iya magana bare daukar mataki saboda an kawar masa da hankali.
Gimbi kuwa jikinta ne ya hau bari babu gaira babu dalili ta kama kofar dakin ta rufe tana fizgar kanta saboda yadda taji duniyar tayi mata zafi. Ina zata ga Anti Bebi ne?
*****
Rumana tana blending din kayan miya Awaisu ya shigo sai dai babu wannan fara'ar a fuskarsa saboda yadda ransa ya baci. Daga bakin kofa ya tsaya ya harde hannuwansa a kirji. Kallonsa tayi ta kula da yanayinsa wanda ta tabbatar dakin Gimbi da yaje ne ya mayar dashi haka. Tana son tambayarsa me ya same shi ta tuna da nasihar Mama da take cewa kada ta taba saka kanta a tsakiyar matsalarsa da Gimbi. Komai wuya komai dadi uwar 'ya'yansa ce saboda haka duk abinda ba'a saka da ita ba ta dauke kai sai taji dadin rayuwar gidan miji.
Shiru duka suka yi na yan mintuna har ta juye kayan miyar a tukunya ta dora akan gas cooker dinta. Hantar da ta fitar daga freezer ta dauka zata yanka sai ta sake kallonshi ta dora hannuwa biyu a kanta.
"Nayi mantuwa"
Karasowa yayi cikin kitchen din yana kallon yadda take bata rai.
"Me kika manta? Mu gyara kafin ki hada mana jagwalgwalo"
"Attaruhu goma Iman tace na saka na manta na sa tara yanzu yaya zanyi da dayan?"
Yana kallonta tana gimtse dariya yayi murmushi "Son So kin mayar dani kakanki ko amma nasan maganinki. Shi guda dayan da kika manta na yarda ki tauna ki zuba shi a ciki....bude bakin...haaaa" ya nufota da shi a hannu ba shiri ta fara bashi hakuri tana neman hanyar fita ya tare. Cikin dan lokaci ya ware suna dariya wayarsa ta soma ringing. Nuru ne yake kiransa ya sanar dashi suna hanya da matarsa Kubra zasu zo.
"Baki zamuyi su Nuru da matarsa kin ganesu ko?"
Ta gyada kai tana murmushi.
"Sun kusa isowa kije ki dauko hijab ki ajiye a kusa"
Fita yayi tabi bayansa da kallo tana jin wani irin yanayi mai cike da ni'ima idan tana tare da shi. Bata taba zaton hankalinta zai kwanta da auren nan ba sai gashi tun ba'aje ko'ina ba zuciyarta tana son tabbatar mata da cewa Uncle Awaisu ya cancanci ta kira shi Son So ba don ya dage sai ta kira shi da sunan ba. Kirjinta ta dafe saboda yadda zuciyarta take bugu da karfi. A hankali tace
"Washhh zuciyata....Uncle kada kasa min heart attack"
Juyo da ita taji anyi har ta firgita saboda tasan ita kadai ce a kitchen din. Fuskarta yake kallo yana kokarin kallon idanunta ya soma magana a hankali yana rungume da ita
"Me ya sami zuciyar taki?"
Kasa bashi amsa tayi saboda matsananciyar kunyar da take ji ta soma sunne kai.
"Umm Ruman ki bani amsa please....kin bani wurin da nake son samu a cikinta ne?" Fuskarta kawai yake kallo ya sanya hannunsa a saitin zuciyarta mai bugu da mugun sauri. Hannunta ya kama ya dora a nasa kirjin har lokacin idanunta a rufe amma tana jinsa.
"Idan baki yi min magana ba ni a yanzu heart attack din zai kamani"
Zancen zuci ta kama yi tana yiwa kanta fada yaya akayi tayi magana da karfi har yaji. Suna wannan yanayin sai kaurin kayan miya suka ji ya saketa da sauri taje ta kashe. Zai sake magana suka ji kararrawa tana cewa _assalamu alaikum_.
Sai da yaje bakin kofa ya juyo "Ina binki bashi"
Ya kuma juyawa Rumana tace "Uncle..." ya sake waigowa sai kawai tayi masa wannan alamar ta _I love you_ da hannuwanta hagu da dama. Baki bazai iya kwatanta yadda yaji a zuciyarsa ba wannan lokacin. Yayi taku biyu da nufin dawowa gareta kararrawar gidan ta sake sallama yayi guntun tsaki su Nuru dai basu iya zuwa ba.
Sai da taga ficewarsa hankalinta ya kwanta ta bi bayansa tana dafe da kirji. Dakinta ta wuce ta sako sabon dogon hijab ruwan kasa mai hannu har kasa ta sake komawa kitchen.
******
Da sallama ta shiga falon dauke da tray wanda ta doro musu juice mai sanyi da cake.
Kanta a kasa ta gaishesu don duka kunyarsu take ji musamman Uncle Awaisu. Su Nuru kuwa suna janta da tsokana ta kasa sakewa.
Awaisu ya kula a takure take yace su shiga dakinta da Kubra. Da saurinta kuwa ta mike suka tafi.
A dakin ma dai a saliharta ta fitowa Kubra. Da yake babba ce kusan sa'ar Gimbi tasan yadda zata bi da Rumana. Da wasa da dariya ta rinka janta har ta sake. Kusan minti ashirin sukayi sannan Nuru ya kira wayarta yace ta fito su tafi. Ledar hannunta ta mikawa Rumana.
"Ga wannan amarya ki tabbatar yau kika fara sha. Yana da kyau sosai in sha Allah zan rinka baki abubuwa masu amfani. Ki daukeni kamar Antinki ko yaya kinji"
Rumana hannu na rawa ta karba tana ji Kubra na cewa ta saka a fridge dinta tunda akwai a dakin. Jikinta a sanyaye suka rakasu har bakin mota tana tsoron me Kubra ta bata. Dama saboda sakon Kubra ta nace sai taje gidan a ranar. Itama saya tayi wurin kawarta Maman Farida shine ta kawowa Rumana don tausayinta take ji. Yarinya karama girma ya hauta.
Awaisu na rike da hannun Rumana ya kira drebansa ya bashi kudi ya siyo musu abinci. Suna gama cin abincin wanda ya siyo har Gimbi aka kira shi ba don yaso ba ya fice bai dawo ba sai da akayi Isha.
*****
Kafin lokacin Rumana ta sake fitowa dora abinci ta ga Gimbi ta dasa kujera a kitchen din ta zauna. Ko bari ta ganta bata yi ba ta lallaba ta koma dakinta. Duk abinta tana tsoron duka wanda ta tabbatar idan Gimbi ta damketa to kashinta ya bushe.
Awaisu kamar ya sani ya dawo gidan da abinci. Dakin Rumana ya ganta a kwance yayi mata murmushi.
"Sorry na barki ke kadai uzuri ne ya taso min"
Tashi tayi tana masa sannu da zuwa yace ta kashe komai na dakin ta taho