Showing 99001 words to 102000 words out of 112099 words
Chapter 34 - KASHE FITILA Book Complete by Batul Mamman.txt
wannan rana ta kafa tarihi a rayuwarsu wanda bazasu taba mantawa ba.
*****
"Sleeping beauty asuba tayi" shine abinda Rumana taji yana fada mata a cikin kunne. Motsin da tayi ne ya tuna mata da wahalar da tasha daren jiya ta sake kudundune jikinta tana hawaye.
Dama sai da ya dawo daga masallaci ya tasheta don ko ba'a fada ba yasan yau kam akwai daru shi da Rumanansa. Dagata zaune yayi yana cewa ta tashi tayi wanka ga ruwan zafi can ya tanadar mata.
Idanu a kumbure saboda tasha kuka bata ma san lokacin da tayi bacci ba ta mike sanye da rigar baccinsa wadda bata san lokacin da ya saka mata ba ta dan saci kallonsa suka hada ido. Murmushi yayi ta maka masa hararar da batayi niya ba a hankali tace " kuma na dena yi maka Son So"
"Wanda nake miki ya ishemu"
Baki ya rike yana kallo ta shige bandakin tana ta tura masa baki yabi bayanta tayi saurin saka mukulli ta rufe. Yace ta bude zai taimaka mata ne kawai tace ita ya barta zata iya. Dariya yayi yace mata yau zai karbi kowane hukunci amma tayi masa sassauci. Daga haka tashi yayi ya gyara gadon ya zauna jiranta.
Tafi minti ashirin a ciki tana gasa jikinta kamar yadda Anti Umma yayar Mamanta ta fada mata ya kamata tayi. Da ta fito ko kallonsa batayi ba ita a dole tana fushi. Duk irin kukan da tayi masa bai tausaya mata ba bare ya kyaleta.
A zaune tayi sallah tana idarwa taji yana dariya yana cewa aiki ya sami mata. Wani kukan ta soma ya zagaya gabanta ya zauna. Kunnuwansa ya rike yana kallonta
"Tuba nake my sweet Son So bazan kara saki kuka ba. Kin hakura?"
"A'a nima ba nayi ta rokonka ba kaki hakura"
Shiru yayi kamar me tunani yace "to kada ki damu ki dauka kin kawo karar Son So wurin Uncle Awaisu ne zan miki maganinsa. Bulala nawa kike so ayi masa"
Murmushi tayi saboda yadda yake tsokanarta. Wani baccin taji yana neman daukarta tace masa sai ta tashi zata fada masa. Akan abin sallan ta soma gyangyadi ya mayar da ita kan gado ya soma shirin fita. Yaso kwarai ace yau ba ranar aiki bace ya zauna ya kula da ita don niyyarsa sai ta gama jarabawa gabadaya ma zata zama cikakkiyar amarya sai kuma ya kasa. Bayan ya gama shirinsa takarda ya samu yayi rubutu ya ajiye mata a gefen pillow sannan ya fita.
******
Karfe goma ta dan wuce ta tashi jikinta ya danyi sauki ba kamar dazu ba. Ganin rana ta fito ta san ya tafi ko abinci bata bashi ba. Takaici ne ya kamata ta fara neman wayarta zata kira shi tace yau kada ya aiko mata da abinci zata dafa. Takardar da ya ajiye mata ta gani ta dauka tana karantawa tana murmushi son Uncle Awaisu yana kara shigarta. Sake karantawa tayi ta rungume takardar tana dariya ita kadai.
*_I love you so much. Thank you for being mine._*
Tashi tayi ta gyara dakin tas ta fita falo nan ma ta share tayi mopping musamman inda manja nan ya zuba. Dadinta daya ba kafet a wurin da tasan da wuya ya fita gabadaya.
Tana aikin Gimbi ta fito dauke da handbag mai dan girma cikin shiri. Wani mugun bugun zuciya taji ganin Rumana da rigar Awaisu.
Tunawa tayi da nasihar Awaisu da kuma rashin maganar da yayiwa Gimbi wanda ta tabbatar yana da dalilinsa na yin hakan sai kawai ta gaisheta.
Ga mamakinta fuska a sake Gimbi ta amsa sannan tace mata ta tabbatar ta mori zamanta da Awaisu kafin ta dawo daga tafiyar nan da zata yi. Rumana bata fahimci kan zancen ba tace adawo lafiya ta cigaba da aikinta.
Gimbi na fita ta dokawa maigadi harara ya matsa ya bata wuri yana daga mata hannu "a sauka lafiya Hajiya"
Tsaki tayi ta wuce shi ta tsayar da taxi ta tafi tasha. Hankali kwance motar da zata Damaturu ta shiga tana kara rungumar jakarta. Babu komai a ciki sai kaya set biyu, kudin mota da takardun wani fili da Alh Mudi ya saya mata a Kano. Idan bokan Dr. Yana zaiyi mata aiki shine kadarar da zata iya bashi domin biyan bukata. Ita dai Awaisu ya sota ko da zai cika gidan da mata ya dauko duk danginsa na Fika.[28/08, 19:16] +234 813 154 5123: *KASHE FITILA*💡50
*Batul Mamman*💖
*_A zaman tare yau da gobe sai Allah. Amma ina so a yau duniya ta shaida I realy appreciate duka matan Fikra musamman shugaba mai jajircewa Safiyya Ummu Abdoul_*
*Masoyan KF a duk inda kuke wannan page din naku ne. Jazakumullah bi khair*
Kafin azahar Rumana ta gama girki da gyara kitchen. Gidan ne taji yayi mata shiru da yawa kewar mutan gidansu ta kamata. Wayar Abba ta kira aka rinka zagaye sai da ta gaisa da kusan kowa har tana rokon Maamu akan ta dawo su zauna tare. Ta matsu lahadi tayi Awaisu ya dauko su Daula gidan ya dan farfado. Gashi sun rabu da Yusra kawarta bata da waya lokacin bare ta kirata yanzu.
Awaisu ne ya kirata bayan ta gama waya da Iman yace zai turo dreba akwai kudi a dakinsa zaa kaita saloon a sake wanke mata kai sai tayi kitso. Godiya tayi masa kafin ya iso ta shirya. Wani hadadden wuri ya kaita duk ta tsargu saboda rashin sabo. Haka dai ta zauna aka gyara mata kan akayi mata kitso mai kyau. Sai laasar Gambo ya mayar da ita gida.
******
Kamar ta karbi motar tayi saurin kaisu Damaturu haka Gimbi ta rinka ji. Abin takaici sai magaribar fari suka isa. Daga tashar kai tsaye asibitin su Dr. Yana ta wuce tayi sa'a tashinta kenan zata tafo gida wata mai aikin shara ta rakata office dinta saboda tayi musu karyar yar uwarta ce ita kuma ta kasa samun wayarta.
Dr. Yana tana kama hannun kofar office din Gimbi ma ta kama suka bude tare. Wata muguwar razana tayi cikinta ya duri ruwa ta koma ciki babu shiri. Gimbi kuwa tayi murmushi tare da shiga ta rufe kofar.
"Wannan karon rayuwata kika zo nema ko me?" Dr Yana ta fada tana dan dakewa.
Gimbi ta zauna ta dora kafa daya kan daya tana karkadawa "ko daya, kawance nake so mu kulla. Nasan komai game dake Doctor saboda haka mu manta da komai domin karuwarmu mu duka"
A tsaye Dr. Yana take don bata san da me Gimbi tazo ba. Addu'a take yi kala kala a zuciyarta na neman tsari.
"Ban fahimci me kike son fada ba"
"Doctor kenan, kina zaton bansan ke kika turo min Gogojiya ba...sunan aljanar da take min aiki kenan idan banyi kuskure ba."
Dariya tayi ganin Gimbi tazo mata da rainin hankali sai dai kuma tabbas tasan daga ina Gogojiya take.
"Kina zaton kowa ma irinki ne mai nema daga wanin Allah?"
Tebur din Gimbi ta dafa da hannuwanta biyu fuskarta a tamke "kinga kada ki munafurceni don nazo neman taimako wurinki. Idan ma aikin da nasa akayi a kanki ne ya bata miki rai ke kika shiga gonata gashi kinyi sanadin sake rabani da mijina. Yanzu haka Rumana yake aure wannan 'yar budurwar da sukayi zaman asibitin nan da babarsa"
Sai a lokacin Dr. Yana tayi murmushi tana cewa ikon Allah yanzu Rumana tayi aure. Ashe hasashenta ya zama gaskiya.
"Idan kin gama murna da bakincikina sai ki saurari me ya kawoni"
"Baki isa na saurareki ba malama. Ni da kikayi sanadin rabani da abinda yafi komai soyuwa a gareni"
Gimbi tayi dariya "munyi draw inji 'yan ball. Anyi 1-1."
Ranta ya soma baci tace "kanki daya kuwa? Ki sa nayi barin cikin da na kwashe shekaru ina jiransa sannan kice wai munyi draw?" Hawaye ne ma ya sauko mata.
"Kizo ki fita kafin na kira miki security"
Jikin Gimbi ya danyi sanyi jin cewa bari Dr. Yana tayi ta dan sassauta murya "kiyi hakuri nayi zaton kema rabaki akayi da mijinki kamar yadda akayi min. Yanzu da kika ganni babu wanda yasan na taho. Mutumin da yake min aiki yace Gogojiya tafi karfinsa kuma ta hana ayyukana kama Awaisu. Shine nake so ki kaini wurin naki. Da shirina nazo ko me yake so zan bayar a mallaka min mijina"
Ga mamakin Dr. Yana takardun fili Gimbi ta nuna mata. Tsoro ta bata don tasan lallai tayi nisan da sai anyi da gaske zata ji kira. Wayarta ta dauka ta turawa Mujahid dogon text tana masa bayanin Gimbi. Lokacin yana tare da Haj Fanta. Ganin ya tashi a firgice ta tambayeshi lafiya shine ya fada mata abinda Yana tace. Ta jinjina lamarin sosai tayi murmushi sai tace yaje ya daukosu da kansa a kawota Gimbi. Dan makotansu yasa ya dauko shi a babur tunda Yana da mota taje asibitin yaje ya daukosu.
Sai lokacin da suka isa gidan hankalin Gimbi ya kwanta tana ganin hakkanta ya kusa cimma ruwa.
******
Da tunanin halin da ya bar Rumana a gida yake ta sauri ya kammala aikinsa. Ba don shine Manaja a bankin ba ya tabbatar yau da sai dai ya buga waya ya nemi alfarmar bazai je ba. Biyar saura ya fito yana ta sauri Gambo ya taso zai bude masa mota aka kira shi. Ko da ya duba DPO din da yake kula da case din wadanda aka kama da motar Gimbi ne. Ya sanar dashi cewa anyi nasarar cafkesu a hanyar zuwa kasuwa inda suke son ganin mai sayen sarkar Gimbin.
Ba yadda zaiyi dole ya wuce station din bayan ya kira Rumana ya sake bata hakurin jinkirin da zai yi.
Su Ovi ana zaune tsuru sun kasa gane mene ne yake faruwa sai ga mai sayen mota da Awaisu sun shigo. Yana ganin Rita ya gane fuskarta. Shi dama tuntuni ma ya tsaneta bare da ya dawo hayyacinsa ya tabbatar akwai abinda take yiwa Gimbi shiyasa ta barta a gidan.
Kowa cikinsu yayi bayani inda su Ovi su so nuna taurin kai, sai dai bayan jikinsu ya fara fada musu sunci duka suka tabbatar wa 'yan sandan cewa motar suka sace Rita harda karawa da cewa akwai sarkarta a jakarsu saboda kada a sake dukanta. Ovi kuwa ta rinka harararta. Da sarkar da motar duka an bawa Awaisu kayansa sannan kudin mota kuma ance su Ovi zasu biya mutumin da ya saya tare da kara masa wasu kudin na tara saboda sun janyo masa zaman cell.
A gajiye sosai Awaisu ya isa gida ga bacin rai sai dai yana ganin Rumana yaji hankalinsa ya kwanta.
A bakin kofa ta tsaya da murnarta tun da taji ana bude gate. Tana ganin ya fito wata kunyarsa ta kamata sai ta tuna ai fushi takeyi dashi shine ta juya ta koma dakinta ta kwanta. Tsoron hada ido take dashi gara tace masa kawai tana fushi don ya kyaleta.
"Son So rigima" taji yace bayan ya ajiye jakarsa yana sassauta daurin necktie.
"Na dawo shine kika kwanta harda juya min baya ko"
"Ban huce bane. Kuma na dena yi maka magana" ta fada har lokacin bayanta yake gani.
"Yau a shirye nake kizo ki rama bazan ce komai ba...amma kafin nan a taimakawa bawan Allah da ruwan wanka na gaji."
A hankali yake jan maganar ta sake lafewa taki tashi a shagwabe tace "ni ba cewa nayi zan rama ba"
Shima muryarsa kamar zaiyi kuka yana kwaikwayonta yace "ni dai sai kin rama"
Kamar ta shige cikin gadon don kunya sai murmushi kawai take yi. Shi kuwa don ta taso ya tuna jarkar da ya dauka a fridge dinta yayi murmushi zai tsokaneta
"Naga wata jarka a fridge me kike yi da ita?"
A gigice ta tashi jikinta yana rawa. Dama tsoron da taji kenan kada ya gani yace ko itama tana amfani da kayan asiri. Idonta har ya ciko da kwalla har ya soma zubowa
"wallahi Son So matar abokinka ce ta bani kuma ko sha banyi ba. Nima nasan babu kyau"
Daure fuska yayi ya zauna akan gadon
"wato duk abinda na fada miki jiya kin watsar ko. An baki abu baki fada min ba"
Kara tsorata tayi amma wannan Anti Kubra bata kyauta mata ba. Haka kawai zata janyo mata zargi. Durkusawa tayi a kasa kusa da kafafunsa tana share hawaye da bayan hannu
"ba rokonta nayi ba, ban san ko na meye ba haka kawai ta bani. Amma yanzu zanje na zubar"
Tashi tayi da sauri ta bude fridge ta nemi jarka sama da kasa ta rasa. Hankalinta ya sake tashi tana juyowa ta fada hannun Awaisu da yake tsaye kusa da ita.
"Shikenan na yarda amma kada ki kara, muje ki tara min ruwa nayi wanka"
Ba musu tace to don sauri ta rigashi zuwa dakin nasa ma. Yana biye da ita yana ta dariya a hankali. Tana fitowa daga bandakin ya sake daurewa
"mata kuyi ta daukowa kanku abu mara amfani...anyway ki fiddo min kaya sannan ki jira idan na fito ki shafa min mai"
Yadda hankalinta ya tashi sosai bata son fushinsa to ta sake cewa jikinta duk yayi sanyi. Indai zai hakura ko me yake so zatayi.
Tana zaune ta rafka tagumi ya fito ya kusa kwashewa da dariya ganin yadda tayi saurin tashi tayo kansa da karamin tawul.
"Bari na tayaka goge jikin nasan ka gaji"
Kansa ta goge masa sannan ta dauko man zata shafa masa hannunta yana ta rawa ta kasa taba shi. Tausayi ta bashi ya dagata ya sauke akan gado. Hancinta ya ja yana kare mata kallo tayi kyau sosai cikin riga da skirt na atampa da ta saka
"matsoraciya nima na rama abinda kika yi min shekaranjiya akan attaruhun indomin azaba"
"Da gaske wasa kake yi?" Ta tsare shi da idanunta suna kyalli har yanzu da kwalla.
"Tarkacenku ne na mata ta baki ko shima sai nayi miki bayani?"
Kunya taji ta rufe idonta. Amma gaskiya ya tayar mata da hankali sosai don ba karamin tsorata tayi ba. Kafafunta ta fara bugawa tana masa shagawaba wadda take kara tafiya da hankalinsa
"Ni sai na rama"
Bakinsa ya kai saitin nata "dama ramuwar nake so kiyi tun dazu kin kasa fahimta" daga nan ya hanata tashi.
******
Suna isa gidan Dr. Yana da Mujahid suka yiwa Gimbi jagora zuwa dakin Haj Fanta. Tuwo take ci suka yi sallama ta amsa amma hankalinta yana kan Gimbi.
"Sannu da zuwa Gombo"
Gimbi ta kalli Dr. Yana ta murmusa
"wato ke taki a gida take ma. Lallai kin ma fini. Gashi har sunana ta sani"
Dr. Yana bata amsa mata ba don gani take da kyar idan Gimbi tana da hankali. Gaisawa suka yi da Hajiya sannan tayi musu alama su fita.
Hankalin Gimbi a kwance tana ta jira matar ta bata damar fadin abinda ya kawota taji shiru sai cin tuwonta take yi.
"Doctor tayi miki bayanin me ya kawoni ne ko har kin sani?"
"Na sani shiyasa gobe da sassafe zamu wuce Maiduguri. A nan ne nake da wanda zaiyi miki maganin matsalolinki"
Kayataccen murmushi Gimbi tayi
"dama kuwa ina jin labarin Maiduguri suma ba daga nan ba wurin irin wannan taimakon. Yanzu ke sai a goben zan biyaki ko inda zamu je din zasu sallameki a abinda zan bayar?"
Haj Fanta tace mata kada ta damu yiwa kai ne. Abinci tasa Dr. Yana ta kawowa Gimbi taci tuwo zuciyarta fes tana jiran gobe tayi maganin makiya.
*****
Awaisu da Rumana na kwance tana ta shagwaba yana biye mata tace su tashi suci abinci. Kimtsawa sukayi zuwa falon ma tace ita bata da lafiya duka jikinta na ciwo sai kawai ya dauketa.
A kujerar dinning table ya ajiyeta sannan ya zauna ta zuba musu farar shinkafa da ta dafa da sauce din hanta wanda yaji kayan lambu. Awaisu ya zuba santi don babu yajin nan irin na girkinta na farko.
Lokaci lokaci tana kallon kofa ganin har tara ta wuce Gimbi bata dawo ba. Tana son fada masa amma tana tsoron kada ya zama gulma tayi kila ya riga ya sani ma. Bayan sun gama ya zauna yana kallon news tana kwance a jikinsa yana cewa ita da school sai monday ta zauna rabon kwana taki karatu. Dariya tayi amma hankalinta ba a kwance yake ba.
"Son So me ya sameki ne? Da safe kinyi min gardama zaki iya kula da jikinki amma na kula kamar jan kafa ma kike yi. Tashi mu tafi dama nasan ba wani iya kula da kanki zakiyi ba"
Da sauri tace
"ni lafiyata kalau dama naga Anti bata dawo bane kuma ina tsoron yi maka magana ko gulma ce" ta tashi zaune.
"Gimbi ta fita?" Ya fada ransa ya soma baci har muryarsa ta canja.
Tsorata tayi dama haka take gudu. To amma dare yana kara yi shiyasa tayi tunanin fada masan shi ya fi.
Fita yayi waje ya tambayi maigadi wanda ya tabbatar masa tun goman safe ta fice. Nan da nan kan Awaisu ya dau chaji. Wai me Gimbi take nema a rayuwarta ne? Ya tabbatar wurin wani bokan kila ta tafi saboda ta bari shaidan ya gama fitsare mata kai tayi nisa bata waige.
Rumana na zaune ya dawo yace ta fada masa yadda sukayi da zata fita. Ita duk ta tsorata ma da yanayinsa ta fada masa abinda Gimbin tace.
"Shikenan kije ciki ina zuwa" yace mata kawai bayan ta gama fada masa.
Magana taso yi ya sake cewa ta tashi da dan karfi.
Jiki a sanyaye ta tashi ga ciwon jiki da yake damunta wanda ya kara mata. Dakinta ta wuce ta je ta sami ruwa mai zafi ta zauna a ciki ko zata ji saukin jikinta. A hankali ta soma kuka tana tausayin kanta.
Awaisu yayi ta buga wayar Gimbi tana shiga bata dauka ba. Hankalinsa ya kara tashi ya kira Alh Mudi ya fada masa. Ce masa yayi su jira zuwa wayewar gari. Tunda rayuwar da ta zaba kenan lokaci yayi da duka har shi zasu zare hannuwansu daga kanta. Shi dai haka ya ajiye wayar zuciyarsa tana zafi. Me zaice da 'ya'yansa nan gaba gamw da mahaifiyarsu don ya tabbata bazai taba bari ta kusance su yadda zasuyi sabon da zata koya musu mugun hali ba.
Sai kai kawo yake yi a falon wayarsa tayi kara. Yana dubawa yaga Gimbi ce ya amsa da sauri.
Lokacin ma Haj Fanta ce tace ta kira maigidanta ta fada masa tana lafiya tunda da bakinta tace mata babu wanda yasan inda take.
"Naga kana ta wani kirana har amarcin ya kare ne? Kada ka fara murnar na tafi zaku sha iska dawowata daidai take da saituwar lamurana yadda nake so. Wannan yarinyar kuma