Showing 54001 words to 57000 words out of 112099 words
Chapter 19 - KASHE FITILA Book Complete by Batul Mamman.txt
ta sani ba.
Shi kuwa sai da ya kusa isa inda suke tare da su Daula sannan ya tsaya cak yana tunanin me Baaba tace. Rumanansa? Me take nufi da hakan? Daga ido yayi suka hada ido da Rumanan da yake tunani ta dan yi masa murmushin karfin hali a zatonta ko yaji haushin yadda ta nuna tsoron matarsa ne don tasan yana sonta sosai. Shi kuwa wannan murmushin jinsa yayi tamkar an *kunna fitila* a cikin zuciyarsa har abin ya bashi tsoro. Rumana ce fa 'yarsa.
A cikin sakin kuma cikin yarensu Anti Ummukulsum ta tambayi Baaba me take nufi da Rumanan Awaisu. Nan tayi bata bayanin sunyi ne kawai don bata ran matarsa. Maamu ta kafe Harisu da ido tace
"ni ba da wasa nake yi ba dana ka taimakeni ka kara yi min wannan alfarmar"
Baaba tayi saurin kallonta "Da gaske kike yi Awaisu kike son hadawa da Rumana?"
"Ba don na huce takaici ko bacin ran da matarsa ta saka min ba kawai na kula kamar shima yana son hakan"
A raunane take maganar ta rike Baaba Hure "kiyi hakuri idan na bata miki rai, ban ko yi tunani ba"
Baaba tace "da gaske kina son wannan hadin?"
Su Harisu duk suka zaro ido jin wannan maganar ta iyayensu. Maamu na cewa eh Baaba tace
"In sha Allahu anyi an gama alfarmar Manzon Allah SAW"
Dakin tsit yayi su Harisu an ma rasa me cewa komai. Gimbi tana tsaye suna yare bata fahimci komai ba sai dai zuciyarta ta bata akwai abin da suke kullawa jin an ambaci sunan Rumana da na mijinta. Wani zafi ta fara ji a jikinta tun daga tsakiyar kai har tafin kafa.
[15/08, 17:46] +234 803 272 5896: *KASHE FITILA*💡35
*Batul Mamman*💖
Babu wanda ya kula ta sai ma Harisu da ya fita don ya rasa abin cewa. Awaisu ya hango ya kusa karasawa inda su Rumana suke yayi saurin binsa ya tare shi. Rasa abin fada yayi don jin wannan hadi da bai taba tsammani yayi ba daga sama. Sai kuma ya daidaita kansa yace ya kamata yaran suci abinci a mayar dasu gida saboda sun sha hanya, gashi suna isowa an sake tahowa dasu asibiti.
Awaisu yayi na'am da shawarar "ni zan zauna a nan waje har su gama don raina bazai jurewa karairayin Gimbi ba"
Kafadarsa Harisu ya dafa "kayi hakuri Awaisu ni bana son wata rigima ta tashi a asibitin nan ba mutumcinmu bane. Duk abin da zamuyi ka bari a koma gida"
Daga nan Rumana ya kira ya umarceta da zubawa su Amir abinci. A dan tsorace ta shiga dakin kai a kasa taki bari su hada ido da Gimbi wadda take sankame a gefe guda zuciyarta tana ruri kamar ana hura mata wutar bacin rai.
Ganin Rumanan sai ta dan saita kanta ta rungumota. Tamkar mazari jikin Rumana ya hau bari saboda tsabar tsoro.
"Oyoyo Rumana kin tafi kin barni da kewa ganin Maamu yasa ban kula babbar 'yar Mummy ba."
Yawu ma kafewa Rumana yayi ta kasa daga harshe tayi magana sai murmushin yake. Gimbi na kula da yadda ta tsure a ranta taji dadi yarinyar nan bata isa ta kawo mata raini ba don ta riga ta dasa mata dafi a zuciya. Hannunta ta kama tayi hanyar fita daga dakin da ita tana dariya
"Shine kika biyewa Abbanku baku fada min Maamu babu lafiya ba ko? Muje waje dai musa labule akwai labari"
Rumana ido yayi kwal-kwal da hawaye ta juyo neman agaji wurin iyayenta tana so wani cikinsu ya hana Gimbi fita da ita daga dakin. Anti Suwaiba ce tayi yunkurin tashi ta hana Baaba ta girgiza kai. Bayan fitarsu ganin cewa akwai su Haris a dakin ta sake magana da yarensu
"Ku kyaleta hakan da tayi ya tabbatar min tayi zargin wani abu game da maganganun da mukayi dazu. Ga dukkan alamu tsorata ta zata yi."
"Kuma shine zaki hana a tsayar da ita? Kada ta cutar da Rumana" cewar Maamu tana sako kafarta kasa daga kan gadon.
Baaba ko a jikinta harda dariya tace "nafi so ta cigaba da tunanin tayi nasara wannan ne zaifi kona mata rai idan taji an shafa fatiha"
Abinci ta zubawa yaran da kanta tace su ci a kama hanyar komawa Fika su huta. Su Maamu duka hankalinsu a tashe tace kada su damu da kanta zata fita ta dawo da ita. Tafi so dai ta bata damar da zata ji kamar babu wanda ya isa sai ita kadai.
Wani dan wuri da babu kowa Gimbi ta kai Rumana ta sakar mata hannu tare da hade fuska sosai
"Rumana kin fadawa su Abban Haris wani abu ne?"
Hadiyar yawu tayi da kyar "Mummy wane abu?"
"Au har kin manta na fada miki ni ba Mummynki bace? Da kika dawo gidan ubanki baki hadu da taki uwar ba?"
Bata ce komai ba hakan ya kara tunzura Gimbi amma dole ta daure tana wurin da dolenta tayi a hankali saboda 'yan uwan Awaisu ne ko ta ina. Zaro idanu tayi tana mata kallon banza
"Akwai wani abu tsakaninki da Abban Haris? Naji ana ce miki Rumanansa"
Wannan karon ma kasa magana tayi sai ma tsoro da taji ya mamayeta tunda bata nan lokacin da Baaba ta fadi hakan.
Ta gama kidemewa karshe kamar daga sama taji muryar Awaisu ya kirata cikin sanyin muryar da ko kadan batayi kama da muryar da uba zai kira 'yarsa ba. Ita kanta Rumana ba don rashin sabo ba da ta dago cewa Uncle Awaisu fa wani salon shagwaba yayi mata.
"Umm Ruman kije ki gani idan sun gama cin abinci ku fito mu tafi dare yana yi kuma nima yunwar nake ji baki bani abinci ba"
Tirkashi, zuciyar Gimbi ta kumbura suntum da bacin rai mara misaltuwa. Kallon Rumana tayi wadda ta kara shiga cikin duhu saboda rashin fahimtar meyasa yayi magana irin haka. Ita ina ruwanta da cin abincinsa? Ko da can ma ai ba ita take bashi ba. Yadda ya tsareta da kallo yasa ta cewa "bari na duba idan akwai saura sai na zuba maka"
Kamar zata bi iska don sauri haka ta bar wurin. Bayanta yabi da kallo kuma yasan tabbas Gimbi shi take kallo yayi dan murmushi yayi gaba yana jin yadda take kiransa hankali a tashe.
Sai da ya koma wurin Harisu yake fada masa me yaji Gimbi na tambayar Rumana. Dama tare suka hango fitowarsu Awaisu yayi saurin tahowa don yasan bazaa kulla alkhairi ba.
Ita kuwa Gimbi da zaa aunata a lokacin tabbas jininta ya hau. Ta rasa gane meye yake faruwa. Tunda tazo fa ko kalma daya bata shiga tsakaninta da Awaisu ba. Abubuwa ke neman rikecewa ta zaro wayarta daga jaka ta kira Ovi. Kuka ne ya taho mata ta danne don kada wani ya fito ya ganta ta zayyana mata halin da take ciki.
"Ovi please kije wurin Boka ki sanar dashi. Idan abubuwa suka cigaba a haka ina kyautata zaton komai zai lalace zuwa matakin da bazaa iya gyarawa ba."
Ovi ta gimtse dariyarta tace "ki turo kudi yanzun nan zan tafi wurinsa. Ina muka ga ta zama ana neman bata shirin da aka jima ana yi. Dayan maganin nan dai da ya baki kiyi kokari ko ta wane hali ki shafawa maman tasa. Boka yace da kanta zata ce ya biyoki ku tafi kuma bata son kara ganinsa. Kinga daga nan kin huta"
Gimbi ta sauke ajiyar zuciya sai dai tana kokontan yadda zata iya shafawa Maamu magani babu wanda ya kula. Ta kula wani kallon tsana suke yi mata shiyasa take tunanin ko Rumana tazo ta fada musu irin zaman da sukayi. Sai kuma ta ga babu dalilin damuwa saboda idan boka yayi mata aiki a kansu babu wani wanda ya isa ya daga mata yatsa. A take ta turawa Ovi dubu hamsin sai dai tana jin faduwar gaba game da maganar Baaba Hure akan kiran Rumana ta Awaisu.
Tana nan tsaye suka fito tare da su Anti Baraka yau Anti Ummukulsum ce zata kwana. Babu wanda ya kulata taji jikinta ya danyi sanyi. Dakin ta koma tayiwa Maamu sallama harda alkawarin gobe da wuri zata zo don ita zata kwana da ita ma ta fita.
Motar Awaisu ta nufa domin tana son magana dashi akan abubuwan da ta gani daga zuwanta. Sai da Baaba Hure ta tabbatar nan ta taho har tana cewa su Haris su tafi motar da suka zo da ita kawai Baaba tace
"Rumana kin gaji ne haka kike tafiya da kyar? Awaisu bude mata gaba ta zauna kannenta sai su zauna a baya ku fara yin gaba"
Murmushi yayi ya bude kofar yana satar kallon yadda Gimbi ta kame kam a wurin tana kallon ikon Allah. Rumana itama tsayuwa tayi zata waiga ta ga yaya Gimbi tayi don tayi tunanin tare zasu tafi da Awaisu taji yace
"Shiga mana ko sai na dauke ki ne?"
Kunya taji tayi saurin shigewa yana yi mata dariya. Baaba Hure a zuci tace karen bana maganin zomon bana Awaisu kayi min daidai. Taji dadi da ta lura da yadda kalar fuskar Gimbi ta canja gabadaya.
Harisu dama ya riga ya tayar da tasa motar su Anti Suwaiba sun shiga. Baaba Hure suke jira ta tsaya ta karewa Gimbi kallo
"Kun zo mota a cike zaki koma ke kadai. Ko na dawo taku motar ne na tayaki hira?"
Duk yadda taso daurewa bata san sanda ta watsawa Baaba harara ba sannan tayi gaba kamar zata tayar da kura. Baaba tana dariya ta karasa motar Harisu suka tafi. Shima Awaisu jan tasa yayi yaransa suna ta yi masa hira yana amsawa cikin nishadi. Rumana kuwa shiru tayi jikinta ya kara mutuwa. Me zaisa ace ta shiga motarsa ga matarsa a wurin da ta gama bata tsoro dazu.
Gimbi na shiga mota sai hawaye ya balle mata. Tsawa ta dakawa dreban akan ya fita daga motar. Jiki na rawa ya fita tana kuka ta kira uwargijiyarta Ovi ta fada mata sabon lamarin da yake faruwa.
"Ovi cikin kankanin lokaci daga zuwana mutanen nan zasu kasheni da bacin rai. Ki fadawa Boka ko wane irin shiri suke yi ya wargaza zan bashi ko me ya bukata"
Kwantar mata da hankali Ovi tayi da kyakkyawan alkawarin cewa daga gobe idan taso duka gidan sai ta juyasu suga tsiya. Tayi wani mugun murmushin auno yadda zata fanshe bacin ran da Awaisu ya saka mata.
*****
Har gari ya waye bata ga Awaisu ba domin jiya sun rigasu isa Fika. Da suka iso kuma bata ma ga motarsa ba. Daki aka bata ta shiga tana tabe baki. Ta tsani zuwa garin nan domin a takure take jin kanta. Su Haris sun bi 'yan uwansu maza yaran Harisu a dakinsu suka kwana. Daula uwar iyayi ma wurin Rumana ta zabi kwana suka bar Gimbi ita kadai. Da aka bata abincin dare cewa tayi bata ci saboda tunani yayi mata yawa.
Shiyasa da safe Anti Amarya taki aika mata da breakfast. Shiru Gimbi na jiran abinci don ba karamar yunwa take ji ba taji shiru sai hayaniyar yara. Nata 'ya'yan da take ji kamar 'ya'yan gwal babu wanda ya leko dakin. Takaici ya sake kamata.
Sai wurin karfe goma Awaisu ya shigo gaishe da Baaba kafin ya wuce asibiti. Bayan sun gaisa yana cin abinci tasa aka kira mata Harisu.
Nutsuwa sukayi a gabanta tace tana fatan sun amince da maganar da akayi jiya na auren Rumana. Awaisu ya dago kai da sauri
"Aure kuma Baaba karatunta fa? Saura watanni ta gama secondary. Daga dawowarta ko wata biyar bata yi ba ta sami miji ne?"
Sai a lokacin ta tuna baya dakin suka yi magana a asibiti.
"Aure ne zaa hadaku Awaisu ina fata bazaka watsa mana kasa a ido ba"
Harisu yayi saurin kallo shi kuma ya kawar da nasa kan saboda har yanzu bai san yadda zai kwatanta yaya ransa ya karbi wannan hadi ba.
Baaba Hure ta lura dasu tayi murmushi
"wannan hadi wanda bamu taba kawowa ko da wasa zamuyi shi ba ina so ku dauke shi a matsayin rubutaccen al'amari. Bansan me Maamu ta gani ba amma ni dai tunda ta fada zuciyata ta aminta ta kuma sami nutsuwa sosai akan hakan. Ina so a matsayinku na 'yan uwa kuyi shawara da juna. Idan har wannan hadin zai taba muku zumunci kafin mu tafi asibiti yau ku yanke shawara ku fada min."
Babu wanda yayi magana a cikinsu Baaba Hure ta tashi ta fita. Sai suka koma yiwa juna kallon kallo. Awaisu kunyar Harisu yaji ta rufe shi. Shi da kansa yana mamaki tun zuwansa Fika yake yiwa Rumana kallo na daban. Yarinyar da aka haifa a gabansa har ya saka mata suna. Wannan abu da kunya sai dai ya rasa gane dalilin da yasa shima zuciyarsa take kwadaita masa da ya amince.
Harisu ya gyara zama yana kallonsa "nasan yadda nayi mamakin wannan magana kaima kayi. Ina so nace ban yarda ba domin Rumana 'yarka ce amma bazan taba yiwa iyayenmu musu. Abu daya zan tambayeka dan uwana....ka amince da auren nan da zuciya daya?"
Ya Ilahi sosai Awaisu yaji kunya musamman ganin yanayin Harisu ba yadda ya saba ba. Yasan ko shine zaiji kwatankwacin haka ko ma fi. Bai taba tunanin faruwar haka ba amma shima tasa zuciyar ingiza shi take yi akan kada ya cuci kansa.
Kansa ya sunkuyar "Yaya Harisu... " sai kuma yayi shiru saboda nauyin amsar da zai bayar.
Tashi Harisu yayi batare da ya saurari amsar tasa ba ya fita. Bai dade ba suka dawo da Baaba a gabanta yace ya amince. Awaisu ya kasa kallonsu duka su biyun saboda tsananin nauyi da yaji. Harisu yasan cewa duka su biyun abin yazo musu a bazata kuma baya ganin laifin kanin nasa sai dai har ga Allah yana tausayin Rumana.
Nasiha sosai Baaba tayi musu akan zumunci da fatan wannan hadi ya zame musu alkhairi mai dorewa.
Awaisu ne ya fara fita Baaba ta cigaba da yiwa Harisu nasiha don tasan sai a hankali zai nutsu da maganar. Ba kuma don baya son Awaisu ba sai dai ko waye yaji zaiyi mamaki duba da alakar dake tsakaninsu.
Ranar Gimbi kirikiri taki zuwa asibiti wai bata da lafiya saboda Ovi bata kira ba. Abinci kuwa sai da rana ta take Anti Amarya ta aika mata. Ba don gudun batawa Harisu rai ba ma ai so tayi ta gasa ta yadda ta yiwa Maamu.
Da Maamu taji sun amince duka su biyun tayi ta saka musu albarka shi da Harisu. Sai kuma ta bawa Awaisu shawarar ya koma bakin aikinsa tunda suna sa ran nan kwana biyu a sallameta.
Dr. Yana taji dadin yadda Maamu take samu sauki sosai idan ta gama round har hira take zuwa suyi.
Washegari Gimbi ta sami kuzarin zuwa asibitin saboda Ovi ta kirata ta fada mata Boka ya kwana aiki akan Awaisu da duk wani wanda zai iya kawo mata cikas. Yaranta tun safe suka bi 'yan uwansu da Abba ya cika a mota suka tafi. Rumana da yayyenta dake gidajen mazajensu suka tafi har yanzu ita da iyayenta mata babu wanda yake da masaniya akan hadin aurenta da Awaisu.
Hayaniya sosai suke yi a dakin Maamu kuma da ita ake hirar wani likita yazo yace ko su rage murya ko su fita. Harisu yace gara su zo su tafi kawai don hayaniyar tayi yawa. Yaran aka fara turawa suka tafi Rumana zata bisu Baaba tace ta zauna sai tabi Awaisu. Duk da tayi mamaki haka dai ta zauna.
Yayyenta basu kawo komai ba suka fita. Dakin ya rage Gimbi, Baaba da 'ya'yanta duka su hudun da Awaisu. Hirarsu suke yi babu wanda ya sakata ga Maamu tana ta jan Rumana da hira tana biye mata suna dariya.
Gimbi ta auna taga wulakancin yayi mata yawa kuma dai an tabbatar mata Boka ya gama dasu. Awaisu ta kalla tana wani kada kai tace
"Abban Haris ya kamata mu fara shirin komawa Abuja ko"
A dakile ya amsa mata "tare muka zo?"
Baaba tace ya kamata ya koma saboda aikinsa. Maamu ma tace dama tayi masa maganar jiya. A wautar Gimbi da mika wuya ga boka sai tayi tsammanin aiki ne ya soma ci shiyasa abin da ta fada duka suka bada goyon baya.
Tayi shu'umin murmushin nasara sannan ta kada kai ta kalli Harisu.
"Yaya Harisu ranar da nazo na taho muku da kayan abinci amma da kai da matanka babu wanda ya nuna ya gani bare ayi godiya. Ko ba komai nasan na rage maka wani nauyin"
Baki bude suka bita da kallon mamakin wannan furucin nata. Awaisu yaji ya mugun tsanar kansa da ya rasa matar aure sai Gimbi. Kafin yayi magana Anti Suwaiba rai a bace tace
"uban waye ya rokeki da har kike jiran godiya. Ke Gimbi! bari kiji in fada miki wallahi baki da arzikin da zaki kawowa iyayenmu abinci"
Baaba tace cikin bacin rai "Suwaiba bana son sakarci ki wuce ku tafi kawai ki kyaleta"
Dayake dama itama bata iya fushi ba sai ta kasa yin shiru
"Baaba wallahi shirun da ake yi mata ne yasa take tunanin ana jin tsoronta. Bayan kin kusa kashe Maamu da yunwa a gidanki shine don rashin kunya zaki zo ki taho da kayan abinci? Billahilzi Gimbiya idan zaki koma baki kwashe kayan nan ba sai na nuna miki ke karamar mara kunya ce. Ki dubemu da kyau gabadayanmu babu matsiyaci balle kice maula muke yi."
Gimbi ta rasa abin yi jin wannan magana ta tabbatar asirinta yana daf da tonuwa sai kawai tasa kukan munafirci
"Yaya Suwaiba me yayi zafi haka"
"Munafuka kada ki sake kirana Yaya. Da can kina kiran sunayenmu ne ma, sai yanzu don gulma tunda kika zo kike cewa kowa yaya"
Anti Baraka ta kama hannun Suwaiba tace tazo su fita daga dakin ta kwace. Ana ta yi mata magana amma ranta ya gama baci taki sauraron kowa
"Ku barni na amayar mata da abinda ke raina. Gara ta sake shiri idan tana tunanin tayi nasara ne. "
Jikin gadon Maamu ta karasa ta dafa ta "dubi yadda kika mayar mana da uwa. Ba don tsahon kwana ba da tuni bakinciki da ciwukan da kika kwasa mata sunyi ajalinta "
Rumana gani tayi dakin ya kaure Gimbi na kuka ana ta kokarin Anti Suwaiba tayi shiru taki sai ta tashi ta fita tana kuka. Awaisu na ganin haka baiyi tunanin komai ba ya bi bayanta yana kiranta saboda yadda ganin hawayenta ya tayar masa da hankali.
Kukan karyar Gimbi ta dena ta bisu da kallo tana