Showing 39001 words to 42000 words out of 112099 words

Chapter 14 - KASHE FITILA Book Complete by Batul Mamman.txt

23 Jun 2024

14007

da kallonta gareta.


Sai da ta zauna a kusa da Maamu sannan ta kwalawa Rita kira akan ta kawo abincinta na rana. Ragowar dankalin hausa ne da aka soya musu da yara da Awaisu suka ci da farfaesu da safe tasa aka kawowa Maamun. Sai dai ita nata banda bushewar da ya fara babu farfesun sai yaji aka dan barbada a gefe. Idanunta da basa rabuwa da hawaye taji sun soma cikowa ta sunkuyar da kanta.


Gimbi tayi murmushin keta ta janyo mata plate din tare da daukar daya ta dangwalo yajin.


"Bude na baki a baki kinji Maamuna. Ai cewa Rita nayi yau kada a baki shinkafar rana saboda kada dankanoma ko basir su kamaki"


Da yake hausar tayi mata tsauri da yawa bata fahimta ba ta bude bakin a dole saboda yadda take tsoron Gimbi. Dandanon yajin mai azababben fada ne ya fara sauka a harshenta kafin taji an tura mata dankalin dukkansa.


Kwarewa tayi ta soma tari sai ga Awaisu ya taho amma daga bakin kofa ya tsaya yana tsoron kada ya karaso Gimbi tayi fada. Zuciyarsa babu dadi don yasan ba'a kyautawa Maamu amma cikin lokaci kankani sai yaji ya manta ko abin ya dena damunsa a rai. Kasa jurewa yayi yadda Maamu take cin dankalin tana kwarewa ko ruwa babu a kusa. Juyawa yayi zai tafi Gimbi ta kira shi tana wani shu'umin murmushi


"Abban Haris yau ka ganmu a baki nake bawa Maamu abinci ko. Kasan nice 'yar gatanta kai ka nemi wata"


Maamu ya kalla ya ga ta tsira masa idanu tana yi masa kallon ka ceceni. Ji yayi kafafunsa har rawa suna yi ya fice batare da ya tankawa Gimbi ba.


Yana tafiya Maamu tasa kuka Gimbi tayi ta rarrashinta wai me take so. Da ta gaji ta fito falo suka kebe da Rita.


"Madam wai yaushe zaki mayar da matar nan garinsu tunda aiki yayi kyau ita da Oga duka a hannunki suke"


Dariya tayi "na fasa mayar da ita saboda wadannan munafukan dangin nasu masu sa ido. Gara mu zauna a nan tare irin haka bata isa tasa ko ta hana ba bare tayi min iko da gidan miji."


Rita ta gyada kai "haka ne kuma"


Bayan Gimbi ta shige wurin mijinta Rita ta tafi kitchen ta dauko robar ruwa ta kaiwa Maamu a daki. Tsayawa tayi a kanta tace ta sha ta bata robar kada Gimbi ta gani. Maamu sai da tasha rabin robar ta mika mata. Rita ta dan share kwalla. Daga ita har Ovi ba mutumci garesu ba amma ta fuskanci Gimbi lamba daya ce a rashin imani. Sosai take jin tausayin Maamu yana shigarta albarkacin yawan adduar da Maamu take yi na neman sauki.


*****
Washegari da wuri Harisu ya sanar da Awaisu zai taho da safe ya nuna masa farincikinsa sosai kuwa. Wurin azahar sai ga waya daga Katsina garinsu Baaba Hure yayanta da take bi ya rasu. Cikin gaggawa suka shirya kusan rabin gidan suka kama hanyar Katsinan. A hanya Harisu ya sake kiran Awaisu yana fada masa. Yaji mutuwar domin yasan mutumin dattijon kirki ne.


"In sha Allah ranar uku zai kama asabar zan taho Katsinan. Ka yiwa Baaba gaisuwa kafin na kira"


Yana ajiye wayar Gimbi dake zaune a cikin office dinsa ta hade rai "ina zaka je?" Ta tambaya a gadarance.


"Yayan Baaba ne ya rasu zanje Katsina"


Ta kyabe fuska zata yi masa kuka "kai da ayyuka suka yi maka yawa nake so weekend dinnan ka samu hutu shine zaka tsiri tafiya. Haba Abban Haris ka tayani kula da mijina mana. Kana bukatar hutu. Next weekend sai muje Katsinan tare"


"To" yace yana kallonta tana wani kwarkwasa kamar a gidanta. Ganin yana samun kudi sosai ga kasuwancinsa ko shi kadai suke dashi zasu wataya son ransu yasa ta ajiye aikinta. Amma kullum sai taje office din Awaisu kai masa abincin rana. Har an ganeta ana tsokanarsu da cewa soyayyarsu tana burge mutane. Ita kuwa mata ne bata so yayi mu'amala dasu don yadda ya kara kyau da haske saboda zaman naira kishinsa a ranta ya karu.


Su Harisu sun isa Katsina nan suka zauna har akayi sadakar uku babu Awaisu babu wayarsa. Idan ya kira shi ma baya dauka sai can dare yayi masa text wai aiki yayi yawa. Jikin Harisu yayi sanyi so yake kawai ya ganshi a Abuja. Abokansa har na Fika sun zo gaisuwa ga Alh Saminu na Kano dashi suke komai sai kaninsa ne zaice aiki yayi masa yawa. Duk hakuri irin nasa baiji dadi ba ko kadan.


Sun koma Fika da iyalansa ya bar Baaba cikin 'yan uwa tace sai tayi wata guda zata koma. Kwanansa biyu da komawa tunanin canjin da yake gani daga wurin Awaisu ya dame shi. Hada kayansa yayi ya kira babba cikin yaransa maza mai sunan babansu suna kiran shi Abba yayi masa rakiya zuwa Abuja.


Suna isa kamar ya kira Awaisu ya fada masa sun shigo sai kawai ya fasa suka wuce gidan. Maigadi ya gane shi babu shamaki ya barshi ya shiga.


Gimbi ta tafi park shakatawa da yaranta sai Rita a falo tana kallo. Sallama Abba yayi ta fito kofar wajen da dan skirt wanda da kyar ya rufe rabin cinyarta. Harisu ya sunkuyar da kai Abba yasa kai zai shiga ta hana wai bata sansu ba.


Harisu yace mata shi yayan maigidan ne daga garinsu. Sai ta danyi murmushi


"Kaine baban Rumana ko, duka sun fita mutan gidan amma Maamu tana ciki muje na kaiku dakin"


Abba na gaba Harisu na bayansa suna bin Rita har kofar dakin Maamu. Dakin duk yayi kura saboda shigowar sanyi da gani ba'a sharewa. Wani sauti mai kama da kuka Abba ya saki wanda ya kai hankalin Harisu kan Maamu da Abban yake kallo tana tsaye a bakin gado.


Wata tsohuwa ya gani tukuf don har tafi Baaba Hure nuna tsufa mai kama da Maamu. Sanye take da riga da zani amma saboda rama hannu daya ya sabule har kusan kirjinta. Fuskar nan ta koma tamkar kashi lullube da fata. Gabadaya ta rame sosai sai idanu sun firfito ga kasusuwan wuya. Zani ne a hannunta take kokarin daurawa yana ta sabulewa saboda rashin isasshen wurin da zai zauna. Kuka Harisu yasa tamkar karamin yaro yaje ya rike hannuwanta duka biyun ya durkusa yana bata hakuri.


"Maamu bansan zantukan Rumana gaskiya bane...., har raina naso ace karya take yi dan uwana bazai wulakanta aljannarsa ba. Ki yafe mana Maamu, ki yafe mana "
[15/08, 17:45] ‪+234 803 272 5896‬: *KASHE FITILA*💡 29


*Batul Mamman*💖




Kuka Maamu ta fashe dashi irin mai ratsa zuciyar nan. Duk wani bakinciki da bacin rai da take dannewa a lokacin ya bayyana. Kukan nata ya sake tayarwa da Harisu hankali. Abba yana tsaye daga gefe idanunsa shima sun kada sunyi jawur. Tsanar Kawun nasa Awaisu ce ta dirar masa a zuciya yana mai kara tabbatar da labaran da Rumana ta basu da ta koma.


Bayan tayi shiru Harisu ya soma kokarin taimaka mata ta zauna a bakin gado fafur taki.


"Maamu ki zauna muyi magana don Allah" ya fada muryarsa tana rawa. Yau da wani ya bashi labarin an ganta a wannan yanayin bazai taba yarda ba. Rama ce tayi tamkar ta shekara a kwance. Cikin muryar da ta dashe da kuka ta dafa kafadarsa


"Harisu ka mayar dani cikin 'yan uwana kafin ku fitar da gawata"


Agogon hannunsa ya kalla ya ga biyar ta kusa. Ya dan tausasa murya


"In sha Allah gobe war haka kina dakinki a Fika."


Hannu ya ga ta daga masa "Wallahi Harisu bazan kara kwana a gidan nan. Indai ina da sauran gata a duniya ko yaya ne kuma ina da kima a naka idon kayi min wannan alfarmar don Allah"


Ji yayi ta kara karyar masa da zuciya ya kira Abba da ke tsaye kamar dogari yace ya bude drawer ya hada mata kaya.


Kai ta girgiza ta dauko hijab dinta akan abin sallah.
"Ni da nake jiran lokacina yayi me zanyi da kaya Harisu?"


Maganar ta tsaya masa a rai sosai ta kara masa tausayinta. Wannan duniya ina zaki damu yake ta fada a ransa. Shi dai Abba ya rarumo duk kayan da hannunsa ya kai garesu. Haka suka fito suka nufi indai ya ajiye motarsa da ya tuko su. Itama Awaisu ne ya cika masa ya saya. Duk da cewa yayi matukar gajiya saboda baya dogon tuki haka ya sake shiga mazaunin dreba zai tuka su. Abba ne ya shiga rokonsa akan ya bari ya tuka yayi masa alkawarin bazaiyi gudu ba. Da kyar ya shawo kansa ya bashi mukullin bayan dogon gargadi. Da shigarsu gidan da sake kama hanyar Fika ko cikakkiyar awa daya ba'a samu ba.


Rita tana ganin sun fita daga gidan ta sauke ajiyar zuciya. Burinta su fita kafin uwar gayya Gimbiya ta dawo. Wannan tsohuwa ba karamar wahala take sha a gidan ba.
*****


Hayaniyar su Mu'allim ce ta sanar da Rita dawowarsu ta fito daga dakinta sanye da wani gajeren wando da riga damammiya mai karamin hannu. Gimbi ta saki baki tana kallonta kafin ta hau ta da fada


"Wani sabon iskanci ne zaki fito min a haka lokacin da mijina ya kusa dawowa? Common go and change."


Rita da bi jikinta da kallo sannan ta kalli Gimbi a yatsine sannan ta koma daki. Ita fa ba don Ovi ta nace tazo gidan ba babu abin da zaisa ta zauna ana mata cin kashi. Amma bari dai hakarsu ta cimma ruwa.


A falon suka bararraje ana ta ciye ciyen kayan kwalama da Gimbi ta saya musu. Binsu take yi da kallo dadi na ratsa zuciyarta saboda yadda take son yaranta. Daula wadda ta tafi fitsari tun shigowarsu ta kwala mata kira daga ciki. Yanayin kiran yasa ta tashi da sauri ta nufi dakin da take. A korido suka hadu Daula tana nuna dakin Maamu


"Mummy Maamu bata nan"


Tsaki ta ja da karfi tana hararar yarinyar "saboda haka kike yi min wannan mugun kiran? Daga zuwa fitsari me ya kaiki dakinta"


Daula ta sunkuyar da kai. Gimbi tayi gaba zuwa dakin Maamu tana ta surutai. Rashin ganinta a dakin bai dameta ba tayi tunanin bandaki ta shiga. Sai ta kula babu haske. Kamar ta fita sai ta koma ta buga kofar da karfi


"Maamu" ta kwala mata kira kamar sa'arta. Shiru taji ranta kuwa ya baci. Jiya ta sake zuba mata wani maganin kwantar da zuciya wanda zata mallaketa kamar yadda ta mallake danta. Shine kuma taki amsa kiranta? Lallai da sake. Tura kofar tayi inda taji tsamin abinci ya bugi hancinta. Da sauri ta kunna fitila sai ga kwandon shara ya soma cika da abinci ya lalace.


Baki Gimbi ta rike tana gyada kai "wato kwana ukun nan matar nan asara tasa na dafka. Kaddai ace bata cin abincin tun na ranar da na soma saka maganin"


"Mummy me kika ce?" Daula ta kura mata idanu.


"Babu komai kirawo min Rita"


Bata jima ba suka dawo tare harda su Haris ta tsegumta musu Maamu bata nan.


"Kinga fitar Maamu ne?"


Murmushi da soma yi domin duk yadda Gimbi taso boyewa kana kallonta kasan hankalinta a tashe yake. Boka yace kada ta bari Maamu ta fita daga gidan. A haka ne zata fi iya juya Awaisu hankali kwance.


"Anzo an tafi da ita"


"Me?"
"Waye yazo?"
"Ina aka kaita?"


A gigice take maganar Haris da yafi sauran wayo shima hankalinsa ya tashi. Amir kuwa kuka ya saka


"Mummy ko saceta akayi? Sai da nace miki mu tafi da ita Park din kika ki"


"Rufe min baki" ta daka masa tsawa sannan ta koma ga Rita ta sake tambayarta waye ya dauki Maamu.


"Baban Rumana ne fa."


"Harisu yazo gidan nan? Yaushe?"


Yau ko dan jarida ya shafawa Gimbi lafiya a tambayoyi. Rita ta fada mata cewa sun zo babu kowa suka fito da ita suka tafi.


"Haba Rita bayan kinsan komai yaya zaki bari su tafi."


Wayarta ta dauka ta tafi daki harda rufe kofa. Awaisu ta kira tana kuka ta fada nasa Harisu yazo ya dauki Maamu batare da saninsu ba.


Yana cikin office har lokacin ya nuna mata babu matsala zai kira shi dama sunyi magana.


A harzuke tace "da saninka dama yazo. Shine zai tafi da ita don a nuna ni ban iya kula da ita ko me?"


Jin ta fara fada ya soma bata hakuri. Haka nan ya hada kayansa ya tafi gida batare da yasan me zuciyarsa take ji game da tafiyar Maamu ba.
*****


Duka 'yan uwan Harisu mata ya kira a waya yace komai dare idan mazansu sun amince yana bukatar su zo gidansa. Kowacce hankali a tashe ta nemi izini ta tafi. Sannan ya kira wani cikin yaran kawunsa da ya rasu yace a bawa Baaba Hure waya. Bayani yake son yi mata sai kuka ya kwace masa. Me zai fada to. Ya ga Maamu a yanayin da zaka rantse ta fito daga kasashen da yunwa tayiwa kamun kazar kuku ne. Rama ce irin wadda ake nuna mutanen a TV ace a taimaka musu rashin kwanciyar hankali a kasarsu ya hade da yunwa.


Baaba ta razana sosai da jin kukansa. Mutum babba kamarsa yana kuka tasan babu lafiya.


"Harisu kaine kake kuka kamar ba namiji ba? Me ya faru?"


"Maamu ce"


Zumbur ta tashi daga zaune ta tsaya baki na karkarwa "wani abun ne ya faru?"


"Na daukota Baaba. Don Allah ki taho gobe"


Baaba duk ta tsorata ko rasuwa tayi ya boye mata ta soma kuka itama. Maamun ya kalla tana kwance a bayan mota inda yayi mata pillow da babbar rigarsa. Idanun nan duk sun.shige loko sai jirwayen hawayenta yake gani yana jika rigar tasa. Wayar ya dan kara mata a kunne tayiwa Baaba Hure sallama.


Ajiyar zuciya Baaban tayi tace mata gobe da asuba zata taso.


Matarsa ta uku wadda dama yau girkinta ne ya kira ya sanar da ita suna hanya ta fadawa kowa. Sannan ya umarceta tayi abinci mai rai da lafiya yana tare da Maamu. Jin sunan Maamu ta fita da sauri ta sanar da abokan zamanta. Rumana na jin haka tace a bata mukulli zata gyara mata daki.


Su Anti Baraka kusan tare suka shigo gidan da kannenta suna mamakin wannan kira na Harisu. kamar hadin baki ma da niyar kwana duka su ukun suka taho don sun san babu lafiya.


Shadayan dare ta wuce suka iso kusan duka gidan aka fito tarbarsu. Motar yarabsuka kusan rufewa suna ihun Maamu tazo. Sai dai me. A bayan mota take kwance kai kace karamar yarinya ce saboda yadda ta kankance. Anti Ummukulsum ce tace kowa ya matsa ta mika hannu ta riko Maamu. Ai tana fitowa da ta kare mata kallo bata san lokacin da kuka mai sauti ya kwace mata ba. Nan fa sauran suka matso kowa ya ganta sai kuka. Maamu sai murmushin yake take yi


"Ban mutu ba Kaltume, meye na kukan"


Rumana kusan bangaje iyayenta tayi tazo ta rungume Maamu. Sai a lokacin Maamun ta soma nata sabon kukan. Harisu kasa hanasu yayi shima zuciyarsa tayi rauni. Da taimakon Rumana Maamu ta soma tafiya zasu shiga cikin gida sai ga zaninta yana neman faduwa saboda yayi mata yawa da nauyi ta kasa daurawa. Duk wanda ya kula da hakan sai da kukansa ya karu don tausayi.


Suna shiga ciki dakinta aka kaita sannan aka kori yaran don sun cika dakin. Cewa tayi duk su dawo babu mai fita yau Allah Ya yaye mata kadaici.


Abinci aka jere mata tuwon semovita ya tuku da kyau an kulla a leda da miyar kuka wadda taji daddawa da wake da naman kazar da tsabar dahuwa yasa ya soma fashewa. A wani flask ga kunu mai zafi sannan ga kayan tea da ruwan zafi da bread.


"Idan akwai abin da kike so Maamu ki fada na dafa miki" cewar Anti wadda tayi girkin.


Godiya tayi mata tace wannan ma ya isa. Wai ita ce da wannan kwanuka a gabanta duk nata ne taci iya cinta. Lallai ashe da ranka da lafiya da kuma matsayi da mukami lomar abinci ma sai Allah Ya yarda zaka samu. Ita da arzikin danta ya isa ace tana daukar dawainiyar wani ma ta fanin ciyarwa ita ce ta koma haka saboda yunwa. Rumana ce ta zuba mata abincin har lokacin tana zubar da hawaye da takaicin me yasa ta gudu ta bar Maamu. Dama sun dade da ramewa su biyun tun kafin ta taho amma abin yayi muni yanzu da ta ga Maamu.


Abinci Maamu taci sosai ta kora da kunu sannan ta bukaci ruwan wanka don ko sallar magariba basuyi ba bare isha. Cikin 'yan matan kannen Rumana wata ta kai mata ruwa ta sirka mata. Mama ta kaita bandaki ta dawo suka hau maganar wannan abin al'ajabi. Harisu yana jinsu yace suyi shiru sai Baaba ta dawo gobe zaa san me ya kamata ayi amma tabbas zaman Maamu ya kare a Abuja. Suna wannan tattaunawar ne Rumana ta shigo a guje. Dama a kofar bandakin ta tsaya tana jiranta.


"Baba ga Maamu can tana ta amai"


A gurguje suka fito dukkansu suka nufi bandakin inda suka sameta a bakin kofar tana durkushe tana amai ta baki ta hanci. Cikin kankanin lokaci ta galabaita sosai tana neman fita daga hayyacinta. Abinka da mata sunfi yawa a ciki sai koke-koke da salati suke yi.


Harisu ya kinkimeta Abba ya fito da mota ya sakata a ciki suka fice sai asibiti.
*****


"So nakeyi ka kira Harisu kace ya dawo min da Maamu yadda yazo ya dauketa"


Gimbi ke wannan furuci tana karkada kafa daga zaune a gaban Awaisu. A ladabce ya ke bata amsa


"Kiyi hakuri nasan zai dawo da ita"


""Wai kai baka ji haushi bane yazo har gidanka don gadara ya dauke maka uwa. To meye nufinsa?"


"Naji haushi mana, tunda ranki ya baci nima naji haushi amma nasan baiyi da wata manufa ba. Don ma ina ta kiransa ne bata shiga da tun dazu na ce gobe ya dawo da ita"


Tsaki ta buga masa ta tashi. Gashi dai ta mallake shi amma ita bata jindadin yadda ya zama baya iya wani tunanin kirki akan komai sai tayi magana. Maimakon yaji haushi sai wani shirme yake yi mata.
[15/08, 17:45] ‪+234 803 272 5896‬: *KASHE FTILA*💡30


*Batul Mamman*💖




Wani asibiti suka nufa nan cikin garin Fika. Suna zuwa Harisu ya dauko Maamu ya shiga da ita. Likita aka kira yana ganin yadda take ya fara bawa nurses umarni. Haka suka rinka guje-guje a dauko wannan a dauko wancan. Ba su suka samu ta dan daidaita ba sai gabanin asuba don sumanta biyar. Likitan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login