Showing 105001 words to 108000 words out of 112099 words
Chapter 36 - KASHE FITILA Book Complete by Batul Mamman.txt
rabo?" Zuciya a karye take magana cikin kuka.
Haj Fanta ta janyota jikinta itama tana kukan. Shi kuwa Malam bai barsu haka ba ya rinka janyo hadisai da ayoyi yana cika musu zukata da tsoron shirka.
Sunfi awa biyu a zaune sannan yace zai tafi. Gimbi ta rarrafa ta dan matsa kusa da kujerarsa "Malam yaya zanyi da iyayena, mijina da Maamu? Na yarda na rasa komai a duniya indai zasu yafe min na rabauta ranar lahira...wayyo ni na cuci kaina"
"Ki kwantar da hankalinki ki yiwa Allah kirari da yabo da godiya sannan ki tuba. Gafarar Allah yawa gareta har Yake cewa da bawanSa zaizo masa da zunubi kamar kumfar teku kuma ya tuba , to da Zai zo masa da gafara kwatankwacinta. Mu duka masu laifi ne mu yawaita tuba ko zamu dace da gafarar Allah. Mu kiyayi manya da kananun kaba'ira bakin gwargwadon iyawarmu Shi kuma Allah Zai kiyaye mana imaninmu Ya tsaremu Ya saka mana da rahamarSa da muke rayuwa a duniya domin nemanta. Allahumma innaka afuwun kareemun tuhibbul afuwa fa'afu anna."
Gabadayansu suka amsa da Amin suna goge hawaye. Malam ma yana fita nasa hawayen suka sauko na tsoron Allah yana mai jaddada addu'a akan yin nasara a zuciyar Gimbi.
Haj Fanta kuwa hannun Gimbi ta kama ta kaita uwar dakin Yakura sannan da kanta taje ta zuba mata abinci ta kawo mata. Tana zuwa ta sameta a nan inda ta barta tana ta kuka har tana neman shidewa. Tunda tazo duniya bata taba jin tsoron azabar Allah kamar yau ba. Jin kanta take kamar wadda ta rayu cikin mafarki yau ne ta farka. Kusa da ita Haj Fanta ta zauna jiki a sanyaye
"Gombo kici abinci sai mu fara tunanin komawarki gida"
"Hajiya wane gida zani a yadda nake jin kaina lullube da kazanta? Kin san sau nawa kafafunnan suka kaini gidan boka? Sau nawa hannuwana suka yi amfani da magungunan bokaye domin cimma burina? Ku taimaka min muje na roki Maamu gafara wallahi idan ta yafe min nasan Awaisu zaiyi saurin yafe min shima. Ga iyayena sun dade da yin fushi dani. Ga Anti Bebi da nasa aljanu suka mayar da ita tamkar mahaukaciya" wani kukan ta saka Haj Fanta tayi ta bata hakuri.
******
Tun fitar Awaisu da safe Rumana ta gama gyara gida sannan tazo tayi girki saboda yace mata gida zai dawo yayi shirin zuwa sallar juma'a. Tana tsaye a gaban wardrobe dinsa tana neman kayan da zata dauko masa taji ya bude kofar dakin da sallama.
A hankali ta amsa amma bata juya ba. Tana nan tsaye har yazo ya rungumeta ya rankwafa ya doro kansa a kafadarta.
"Duk fushin ne my sweet Son So, gaskiya na kula mijin nan naki sarkin laifi ne amma nasan maganinsa"
Juyawa tayi har lokacin yana rungume da ita ta turo baki. Tun asuba da ta tashi tana sallah ta tafi hada masa abinci duk da bacci da muguwar gajiyar dake damunta. Amma da ya fito kurba daya yayi wa tea tare da mata kiss ya fice yace yana sauri.
Waya ce ya samu daga DPO cewa anyi masa waya daga sama ance ya saki Ovi da kanwarta. Ita kanta Ovi bata san hakan zata faru ba ta dai gwada sa'arta ne ta kira wani mai babban mukami da sukayi hulda a baya ta nemi alfarma shine yace a saketa. Ko da yaje sun gama rufe case din DPO ya bashi hakuri. Ransa a bace ya wuce office sai yanzu da ya dawo ne yaji dadi da yaga Rumanansa.
Kallonsa tayi tana dan murmushi "to yaya aiki?"
"Lafiya kalau sai gajiya da yunwa"
Cikin shagwaba tace ita dai daga yau ya dena fita bai ci abinci ba. Yana rike da hannunta suka fita falo ta zuba masa yana ci suna hira.
"Kinga dai korafi da mita ta kare na dawo naci abinci gashi har ina da sauran lokacin yin wasu abubuwan kafin nayi shirin masallaci"
"Wani aikin zaka yi kuma daga dawowa?"
Kashe mata ido yayi yana wani murmushi "eh mana..aikin kula da amaryata"
A tsorace ta mike don ta fara fahimtar inda ya dosa. Ya damko hannunta kafin ta gudu
"Ina zaki kuma muna hira matsoraciya?"
Fuskarta kamar zatayi kuka tace "Son So bani da lafiya ne"
Hannu yasa a kasan habarsa "ohhh yarinyar nan ba dai fassara ni kikayi ba. Don da kin fara kiran rashin lafiya nasan me kike gudu" yana mata dariya
Tuni kunya ta kamata ta daure tace "ni dai babu abinda nake nufi, bance komai ba"
Dariya yake sosai ya tashi tsaye yana shafar fuskarta da bayan hannunsa ya soma magana kasa-kasa "ni din me kike tsammani ina nufi uhmm?"
Duk ta rikice ta rasa amsar bashi ya cigaba da tsokanarta har ta fara masa kuka.
"Idan kaga amarya na kuka fa rarrashi take so, bari ki gani" daukarta ta ga zaiyi ta gudu daki tana dariya.
Soyayya sosai da kulawa ya nuna mata sannan ya tafi masallaci. Da ya dawo a kwance ya sameta tayi sallah bacci ya dauketa. Shima kwanciyar yayi ya rungumota suka yi baccin tare.
******
Da kyar Gimbi ta iya shan tea da su Yakura suka takura mata sannan ta roki alfarmar a bata kudin mota Fika zata wuce. Sai lokacin Haj Fanta ta tuna da jakarta da tasa Bukarti kwacewa a hannunta ta mika mata sannan tace mata zasu tafi tare da ita saboda kada a ki gaskata ta. Murna Gimbi tayi ta rinka godiya kalmar da ta dade banda boka da Ovi babu wanda take fadawa.
Daga nan ta roki su kaita wurin wannan malamin kafin ta tafi. Sai bayan masallaci suka je gidan nasa. Yana ganinsu yayi hamdala domin yasan canjin ra'ayi daga wurin Gimbiya shi kadai ne zai kawota gidansa.
Shima godiya tayi masa sosai yayi ta mata addua har yake bata labari akwai kaninsa limami ne a Abuja kwana biyu kenan da ya kirashi yana bashi labarin wata matar manajan banki da abubuwan da tayi. Ya kare da cewa yanzu kanwar babarta kamar dai naki lamarin ita yake nema saboda itace ta koya mata bin bokaye. Ya kira ne dama yana neman shawarar yadda zaiyi mata nasihar da zata shigeta.
Wani sabon kukan mai taba zuciya Gimbi ta soma tace "wallahi mijina ne, Malam ashe har yanzu bayan abubuwan da nayi Awaisu yana sona da alkhairi. Na cuci kaina na cuci mijina kuma naci amanar zaman tare da soyayyarsa gareni..gabadaya lamarin nan babu ta inda matsala ta taso min ni kadai na rinka kidana ina rawata gashi komai ya baci"
"Kuma komai zai gyaru da izinin Allah. Kin dai ga yadda ikon Allah yake wanda kika so cuta yana binki da kishiyar abinda kika yi masa. Ina jin har duniya ta tashi baza'a dena samun sabani tsakanin surukai ba amma ki tuna Manzon Allah SAW yace kada mu cuci kowa kuma kada mu bari a cucemu. To idan har daya zai faru gara ki jewa Allah a matsayin wadda aka cuta akan kije a macuciya. Komai runtsi komai wuya kiyi kokari kiga baki cutar da dabba ba ma balle dan Adam kuma musulmi. Wanda duk ya cuceki Allah zai isar miki ko a gaban idonki ko bayan kin koma gareShi. Allah Yayi miki albarka Nana mai sunan manya"
Tana kuka sosai tace Amin suka shiga motar Mujahid wannan karon harda Yakura suka nufi Fika.
[28/08, 19:17] +234 813 154 5123: *KASHE FITILA*💡52
*Batul Mamman*💖
Wuraren uku da rabi wayar Awaisu ta soma ringing. Saurin amsa kiran yayi tare da kwantar da kan Rumana a kan pillow ya fita don kada ya katse mata bacci. Ganin sunan Harisu da yayi yasa shi murmushi ya amsa suka gaisa. Zai fara jansa da hira ya katse shi ta hanyar sanar dashi zuwan Gimbi gidan tare da Dr. Yana da mijinta da wasu mata biyu. Mamaki ya kama Awaisu sai Harisu ya ce masa yayi kokarin tahowa ko zuwa da safe ne don tunda tazo banda kuka babu abinda take yi tace kuma bazata yi maganar abinda ya kawota ba sai Awaisun yazo.
Hankalinsa a take ya tashi yana tsoron ko wani sabon salon makircin ne ta kulla. Alh Mudi ya nema a waya yayi sa'ar samunsa ya sanar dashi halin da ake ciki. Shima nasa hankalin ne ya tashi yana tsoron me Gimbi taje tayi.
"Awaisu ni dai idan babu damuwa zan kira Harisu na fada masa a yau dinnan ba gobe ba zan tafi Fika na daukota. Lokaci yayi da zaka datse duk wata alaka da Gimbi don wallahi a yanzu ba iyayenka ba kai kanka kunyarka nake ji."
"To abinda za'ayi Alhaji ku shirya har Mama idan zata iya zuwa da su Haris sai mu fito mu same ku drebana yaja mota daya nima naja daya. Sai dai kuyi hakuri zamuyi tafiyar dare kam"
Alh Mudi yaji ya kara son Awaisu yace kada ya damu zai nemi kanin Gimbi yaja su shi yaja tasa su hadu a gidan mai na fita gari sai su wuce tare tafiyar bibbiyun zata fi dadi. Sun yanke shawarar haduwa nan da hudu da rabi.
Dakin ya koma har lokacin bacci Rumana take yi. Yasan ta gaji tana bukatar hutu amma bazai iya tafiya ya barta ba gaskiya. A gurguje ya hada musu kaya shi da ita sannan ya tasheta yace ta shirya Fika zasu tafi.
A tsorace take sosai zai dauki jakar kayan nasu ya kai falo ta riko shi
"Don Allah me ya faru?"
"Kin fiye tsoro Rumana babu komai in sha Allah. Ki shirya zan fita nayi sallah ina dawowa horn zanyi miki. Ga keys nan ki kulle ko'ina"
Ai sai kawai ta fashe da kuka, gani take wani abu ne ya faru baya son fada mata. Idan ba haka ba me zaisa da yamman nan haka kawai yace su tafi Fika.
"Uncle ina da imani zan iya daukar kaddara, ko mene ne kada ka boye min" muryarta na rawa tace "tsoro nake ji"
Rungumeta yayi yana shafa mata baya. A nutse ya fada mata yadda sukayi da Harisu tace to Allah Yasa alkhairi a tafiyar.
Kafin biyar sun dauki hanyar Fika a hanya suka dauki Amir da Mu'allim suka dawo motarsu saboda kada su Mama su takura.
*****
Yau matan Harisu da mai girki da mara girki duka suna kitchen suna girki tare saboda bakin da suke kan hanya da su Gimbi. Dakuna aka gyara inda za'a saukesu. Awaisu ma da yake barin key din dakinsa shima an gyara masa nasa dakin.
Sai shabiyu saura suka iso gidan. Lokacin su Daula duka sunyi bacci. A gajiye suke sosai musamman Awaisu da kanin Gimbi da sukayi tuki.
Suna shigowa hayaniya ta kacame ana murnar ganin su Haris da amarya Rumana. Ita kuwa sam hankalinta bai kwanta ba sai da ta ga kowa na gidan lafiya. Daga dakin da su Gimbi suke suna jiyo muryoyin mutanen gidan da su Amir masu cigiyar Mummynsu.
"Gimbi ba ke ake nema ba kuwa" cewar Haj. Fanta tana kallon kofa.
Murmushi mai ciwo tayi "Hajiya bana son yaran nan su ganni sai na tabbatar su Maamu sun yafe min. Wallahi ba don dare ba ni a yau naso a zauna muyi magana na roki gafara. A haka ji n nake kamar akan kaya"
Dr. Yana ta dafa kafadarta tana murmushi "kada ki damu don bana jin a yadda naga mutanen gidan nan zasu watsa miki kasa a ido. Ga dukkan alamu suna da kirki sosai"
"Kirkin nasu shi yasa nake kara tsanar kaina da abubuwan da nayi musu. Gara ka cuci mugu akan mai kirki doctor "
Daga bangaren su Baaba kuwa sun yiwa baki su Alh Mudi da Mama tarba da mutumci aka kaisu masaukin da aka tanadar musu. Yaran kuma tuni suka shige wurin 'yan uwansu bacci ya gudu. Abinci suka ci kawai suka shiga hayaniya a gidan.
Anti Amarya ta kira Rumana ta bata key din dakin Awaisu
"Ga mukullinku nan har abincinku an ajiye a ciki"
Baki ta turo "to bari na kai masa na dauko kayana"
"Kada ma ki bari babanku yaji wallahi ki wuce bakinki alaikum ki tafi dakin mijinki ni babu ruwana"
Tafiyarta tayi ta bar Rumana saroro tana jin kunya ga su Maamu a wurin da mamanta. Antin ma tana sane tayi mata haka don ta kula da take takenta tunda suka shigo wurin 'yan uwanta take neman shigewa ta kwana.
A falo Awaisu ne da Harisu da kuma Mujahid. Sun tambayeshi dalilin zuwan yayi murmushi yace su yi hakuri har zuwa wayewar gari tunda yanzu dare yayi. Ya dai kwantar musu da hankali cewa alkhairi ne ya kawosu.
Ba don Rumana taso ba Baaba da kanta ta korata dakin Awaisu tana cewa bata son sakarci. Bai nemi Gimbi ba dama saboda ganin dare yayi kuma yasan taji zuwansu. Tunda bata fito ba zai hakura zuwa safiyar kamar kowa.
Da ya shiga daki can karshen kujera ya tarar da Rumana a zaune ta takure. Tunda ta shigo tayi wanka take zaune a wuri daya. Yanzu ace duka gidan sun san tana dakin Uncle Awaisu ai da kunya. Murmushi yayi don kuwa yana jinta ita da Baaba Hure lokacin da tace mata dole ta tafi wurin mijinta. Kin kulata yayi ya shige bandaki yayi wanka ya fito. Tana nan zaune ya gama shirinsa duka baice mata komai ba ya kashe fitilar dakin ya kwanta.
Sheshshekar kukanta yaji yayi 'yar dariya. A dan zamansu ya kula babu abinda Rumanansa taki jini kamar a shareta. Yana daga kwance yace
"waye nan"
"Shine ma kaki kulani" ta fashe masa da kuka bilhakki ita bata ji dadi ba.
A duhun ya taso ya ja hannunta "nima fa kin kulani kika yi, ashe babu dadi. Kuma ina ji sai da aka tilasta miki zuwa nan saboda baki damu dani ba"
Cike da shagwaba tace "na damu mana.."
"Ban ga alama ba"
Rungume shi tayi duk da tana jin kunya sosai "gashi kuwa..ni dama kunya nake ji yadda zan fita daga dakin nan gobe"
Matseta yayi a jikinsa sosai "Sarkin rigima nima ai kunyar nake ji, kada ki damu na kusa gama gini a nan mu koma can duk lokacin da muka zo ko"
Dariya yaji tana yi masa saboda yace yana jin kunya ya girgiza kai yana murmushi daga karshe ya sata yi masa tausa a kafa don ba karamar gajiya yayi ba.
*****
Karfe tara na safe duk wanda ya kamata yazo yana cikin falon Harisu. Su Anti Baraka, matan Harisu, Maamu da Baaba, iyayen Gimbi, Dr. Yana, mijinta dasu Haj Fanta sai kuma Rumana wadda Maamu tace ko me za'ayi ayi a gabanta tunda dai matar Awaisu ce.
Duk sun zauna suna sauraron Gimbi ta taso da idanunta kumburarru ta tafi gaban Maamu ta durkusa. Bude baki tayi zata fara magana sai kuka. Da kyar ta iya hada kalmomin Maamu ki yafe min.
Kowa a wurin banda su Haj Fanta yayi mamaki. Maman Gimbi kuwa sai kuka a ranta tana cewa Alhamdulillah yau sun ga sakamakon jajircewa wurin yi mata addua.
Maamu kanta hawaye ta soma yi "Gimbiya me ya sameki haka? Ko wani salon sihirin ne kika zo dashi?"
Girgiza kai ta rinka yi sannan cikin kuka da tun jiya ta kasa dainawa ta labarta musu komai tun tsoron kada Maamu ta rabata da mijinta zuwa Anti Bebi da kuma wannan zuwan nata Damaturu.
"Wallahi nasan bani da wani uzuri akan abubuwan da na aikata amma ina rokonku ku daure ku yafe min kada na mutu da hakkinku. Maamu ke nafi cuta shiyasa na damu nasan idan kika yafe min kowa a nan zaifi saurin hakura"
Haj Fanta ita ta karbe ta basu labarin zuwansu Maiduguri a jiya da yadda suka kare da Malam sannan ita da su Yakura suka cigaba da nemarwa Gimbi afuwar wadanda ta sabawa. Tuni falon ya kaure da kabbara. Awaisu ya kasa cewa komai sai kallonta da yake yi amma baka iya tantance me zuciyarsa take tunani.
Gimbi ta rike kafar Maamu "ki yafe min Maamu, mata irina da yawa suna cikin halaka. Wannan duniyar da bata da tabbas mun dauketa kamar bazata kare ba muna sabon Allah. Ina rokonku duka kuyi hakuri ku yafeni"
A hankali Maamu ta dora hannunta akan Gimbi "Allah Ya yafe mana baki daya na yafe miki"
Jikinta Gimbi ta fada tana kuka sosai. Dama can ita ba jahila bace son zuciya ne kawai ya kaita ya baro. Wurin da iyayenta suke zaune ta rarrafa suma ta basu hakuri. Maamu ma ta yafe bare su da suka haifeta. Haka ta rungume Mama tana kuka Alh Mudi yana mata addua. Daga nan shi da sauran manyan da suke wurin suka shiga yiwa kowa nasiha mai ratsa zuciya akan shirka da mu'amala da sihiri don neman biyan bukata. Allah SWT Shi kadai Ya cancanci a bauta Masa kuma a nemi taimako a gareshi domin Shine Ya haliccemu.
Kusan awa daya ana ta magana daya sannan da daidai kowa ya fita harda Rumana aka bar Awaisu da Gimbi. Kasa kallonsa tayi da dukar da danta yana kallon hawayenta suna diga akan mayafinta. Tashi yayi tsaye a sanyaye yace
"We used to be best friends Gimbi...what happened to us?"
Sai lokacin ta dan dago kanta itama ta mike "son zuciyata ne ya faru Abban Haris, yau Maamu ko cewa tayi ka sakeni tun zuwanta gidanmu bai halatta na kaita wurin boka ba balle bata yi min komai ba. Ka yafe min mijina, ka taimakeni kada na nesanta daga rahamar mai rahama saboda wannan gagarumin sabon da na aikata"
Idanunsa ya rufe sai ga hawaye suna sakko masa baiyi yunkurin tsayar dasu ko sharewa ba. Hannunta tasa a hankali tana share masa itama yana share nata.
"Ban kyauta mana ba"
"Kaddara ce"
"Baka ce ka yafe min ba"
"Addu'ata Allah Yasa muna da rabon sake zama a matsayin ma'aurata a lahira"
Wata nannauyar ajiyar zuciya ta saki ta rungume shi tana kuka sosai.
"I love you Abban Haris"
Bai iya bata amsa ba sai bayanta da yake shafawa. Dago kanta tayi tayi masa murmushi "uwa ba abar wasa bace kuma nayi imani indai muna raye bazaka taba mantawa da yanayin da ka tsinci Maamu ba lokacin da ka dawo daidai duk lokacin da ka ganni. *Awaisu!* nasan duk duniya bani da masoyi kamarka amma da bakina ina rokonka ka sauwake min domin zamanmu bazai taba yiwuwa ba. Daga ranar da na fara kai kafata gidan boka na bata rayuwar aurenmu"
Hannunsa ya dora akan bakinta yana girgiza mata kai ita kuwa ta zame shi tace ya barta ta fadi gaskiya. Ta tabbatar soyayya dai ta gaske yanzu Rumana yake yiwa kuma bata bakinciki. Fatanta ya sami nutsuwar da ta hanashi da soyayya