Showing 108001 words to 111000 words out of 112099 words

Chapter 37 - KASHE FITILA Book Complete by Batul Mamman.txt

23 Jun 2024

15956

ta gaskiya.


A nasa bangaren ya yafe mata dama kullum fatansa ta gane gaskiya sai dai kamar yadda ta fada bazai taba mantawa ba. Maamu ita ce jigon rayuwarsa ta yaya za'ayi ya manta da hawayenta saboda soyayya.


Wata takarda ya dauko daga aljihunsa wadda ya rubuta tun ranar da taje asibiti da wannan izgar dokin ya rubuta. Niyarsa sai ya hadata da limamin nan sannan ya bata.


Hannu na rawa ta karba ta bude. Saki daya ne yayi mata idan aka hada da na baya ya zama biyu. Kuka ta saka duk da a ganinta ma yayi mata adalci da bai kai biyu ba ya raba tsakaninsu gabadaya.


"Abban Haris nagode, lallai yau hannu ya girbe abinda ya shuka."


Hakika Allah Yayi gaskiya da Yace *_la'in shakartum la aziddanahum wala in kafartum inna azabiy la shadid_*. Yau ga Gimbi da Allah SWT Ya ni'imta da abubuwa marasa kirguwa ciki harda miji nagari da suruka abar kwatance sai gashi haka nan babu gaira babu dalili ta janyowa kanta nesanta daga dukkan jindadin rayuwarta.


"Allah mai gafara ne kisa wannan a ranki. All the best....my best friend. Ina miki fatan alkhairi a rayuwarki ta gaba"


"Kaima Allah Ya baku zaman lafiya da Rumana"


Share hawayenta tayi ta fito tsakar gidan tana kwalawa su Haris kira. Dama sun tashi suka fito a guje suna murnar ganinta. Dakin da aka sauki su Mama ta wuce tare da yaran ta basu takardar sakin.


Sun gama hada kayansu tsaf suka fito nan kowa ya san hukuncin da Awaisu ya yanke tsakaninsa da Gimbi. Sai da taje dakin kowa ta musu sallama sannan ta roki a barsu su tafi da yaranta tayi kewarsu sosai. Baaba Hure tace ai babu mai hanawa. A mutumce suka yi sallama Gimbi ta rungume Haj Fanta tana kuka


"Ki bar kuka Gimbiya inda rai da rabo kinji"


Murmushi Gimbi tayi "ina kika baro Gombo kuma Hajiya?"


"Tun jiya na nemeta na rasa sai Gimbiya uwar Harisu nake gani"


Dariya aka rinka yi da alkawarin zumunci sannan Mujahid yaja motarsa shima kanin Gimbi yaja tasu motar suka kama hanyar Abuja.


Rumana da Awaisu sai washegari suka tafi da sassafe don baya son ta sake fashin makaranta.
******


*Bayan Sati Hudu*


Rumana ta gama girkin dare Daula kuma ta wanke duk abinda suka bata wurin girkin Haris ne mai jere kwanukan akan dinning table suna ta surutunsu. Bayan sun gama Rumana ta zubawa kowa sannan ta tafi tayi wanka kafin Awaisu ya shigo.


Shiru bata fato ba suka gama ci suna kallon cartoon har Awaisu ya dawo. Da murna suka tare shi suna bashi labarin zuwansu gidan Mama yau da sakon Gimbi na gaisuwa gareshi.


"To ina amsawa bari naje nayi wanka na fito. Inna Ammin ku?"


Mu'allim yace itama wanka taje tayi.


Dakinta ya fara zuwa bata nan sai ya wuce nasa dakin. A kwance ya ganta ta rufa da bargo tana bacci. Kasa shiga wankan yayi sai da yayi kissing dinta ya wuce yana tunanin neman mai aiki. Ga karatu ga aikin gida yasan abin yana mata yawa.


Har ya fito tana nan kwance ya gama shirinsa ya kula tana yamutsa fuska cikin baccin sai ya zauna a gefen gadon ya dora hannunsa akan goshinta zai shafa yaga tayi mugun zabura amma bata bude idon ba


"Don Allah Anti kiyi hakuri"


Abinda yaji tana fada kenan sai ga hawaye ta soma kamar famfo. Jijjigata ya somayi a rude taki tashi sai kiran Anti da take yi tana kuka. Rasa abinyi yayi kawai ya bude quilt din da ta rufa ya dagota sai kawai jikinta ya saki jini ya balle mata cikin dan kankanin lokaci ya soma bin gadon. Firgici da tsoro kan Awaisu ya gama yi. A guje ya dauko jallabiyarsa ya dora mata akan rigar baccin jikinta ya dauketa yayi falo.


Yaran duka suka taso yace musu bata da lafiya su kula da gidan zai turo azo a daukesu baya son su zauna su kadai. Duka sun tsorata ganin Ammi kamar yadda suke kiranta bata ko motsi.


Gudu sosai yake yi ya karasa national hospital saboda yana tsoron zuwa private ace babu likita. Sake daukarta yayi ya shigarda ita emergency nan suka karbeta aka fara bata taimakon gaggawa.


Awaisu yana reception ya dai kira Nuru ya fada masa yaje ya dauki su Haris. Shiru likitocin basu fito ba daga dakin da take har Nuru ya kaisu gidansa ya taho shima. Ledar jini uku aka karawa Rumana. Tashin hankali karshe Awaisu ya gani a wannan daren. Da suka fito ne suka yi masa bayani cewa bari tayi ya kuma fita duka amma ba shi bane ya daga musu hankali kamar jinin da take zubarwa. Sai dai suna ganin sun shawo kan matsalar yanzu in sha Allah. Yadda baisan da cikin ba ya tabbatar da wuya idan Rumanan ma ta sani. Tausayinta yaji ya kamashi ya tafi gida dauko mata kaya da shirin kwanciya. Amenity ya biya Nuru yace zai turo Kubra ta kwana Awaisu yace ya gode amma shi zai kwana da ita.


Shabiyun dare ya dawo asibitin har lokacin bata farka ba. Likita dai ya tabbatar masa da cewa bata cikin hatsari yanzu bacci ne kawai take yi saboda allurai da akayi mata.


A zaune ya kwana a gefen gadon. Sai wurin takwas na safe ta farka tana rike ciki. Kanta ne ya nemi juyewa bata gane ina suke ba.


"Son So..."


Da sauri ya taso daga kan kujerar yazo ya duka inda take kwance ya rungumeta yana ajiyar zuciya.


"Sannu kinji"


"Me muke yi a nan?"


Gabansa ne ya fadi "baki da lafiya ne na kawoki jiya. Ina zuwa zan fadawa dr kin tashi"


Hannunsa yaji ta rike "me ya sameni?"


Bai iya bata amsa ba ya fita can sai gasu sun dawo da likita. Dubata yayi ya gama rubuce rubucensa ya fita.


Taimaka mata yayi ta zauna ta sake tambayarsa me ya kawota asibiti.


"We lost our baby Umm Ruman"


Zaro ido tayi tare da dora hannu akan cikinta "dama...dama...ina da...?" Sai kuka kuma.


"Shhhh kada ki damu muyi fatan shine alkhairinmu kinji ko. Allah zai kawo mana wasu masu albarka"


A hankali ta gyada kanta ya rungumeta yana rarrashinta. Suna zaune a haka ya kira Harisu ya fada masa. Nan da nan duka gidan suka sani. Maman Rumana ta shiga damuwa sosai har Baaba ta kula da hakan ta fadawa Harisu gobe idan zasu tafi lallai a tafi da ita ta ga 'yarta.


Yinin ranar Awaisu baya fita daga dakin sai sallah. Daga gidan Nuru aka rinka kawo musu abinci. Washegari da yamma su Maamu suka iso. Kafin su wuce asibitin da kanta ta yiwa Rumana girki. Miya ce ta ganyen alayyahu, ugu, shuwaka wadda taji wanki sosai babu daci sai zogale ga hanta, bushasshen kifi da koda anyita da manja. Kana ganin miyar kasan girkin ya sami kulawa daga maiyi. Tuwon semo ta tuka mai kyau da ya dahu taje yin wanka Maman Rumana ce ta kulle a leda suka shirya suka tafi.


Abin nema ya samu tana ganin iyayenta da Maamu sai shagwaba ta karu. Abincin ma cewa tayi bazata iya ci ba Maamu kuwa tace Awaisu ya zauna ya bata. Kunya kamar ya nutse ganin idonsu Harisu. Maamu ta soma fada idan bazai tashi bane ita sai tayi. Yana mikewa kuwa Mama da Harisu suka kusa karo suna neman hanyar ficewa daga dakin suma kunyar suke ji. Rumana da ta janyo abin daskarewa tayi a zaune tana takaicin me ya hanata ci da kanta.


Maamu ta kallesu duka tace "gulmammu". Nuru da Kubra me zasuyi in na dariya ba.


Bayan kwana uku aka sallameta su Harisu suka koma Fika. A satin Awaisu yace a nemo masa 'yar aiki aka samo wata mata zatayi kusan shekara arba'in Hanne. Ita take kula da shara da goge gogen gidan banda dakin Rumana da Awaisu. Sai taimakawa wajen girki da kula da yara. Zamansu suke cikin farinciki da kwanciyar hankali.


Wata biyu a tsakani Rumana ta sake samun ciki. Wannan karon ma basu sani ba saboda baifi sati hudu ba. Tana wanka Awaisu yana aiki a dakin yaji kamar ta fadi. Bai san lokacin da ya ture laptop din ba ya tashi da sauri ya bude kofar. A kwance ya sameta gefen baho ga jini yana bin kafafunta.


Tsoro sosai yaji ya dagota da sauri yana kiranta. Shiru kamar wancan lokacin sai Anti da take kira cikin galabaitacciyar murya. Wannan karon banda fargaba harda mugun bacin rai. Wancan lokacin baya son saka zargi a ransa amma yanzu tabbas abin ya zauna masa a rai.


Maamu ce tayi zaman jinyarta don sai da aka hada da wankin ciki. Tasha wahala sosai akayi sa'a cikin sati daya ta sami sauki.


Haka rayuwa taci gaba Awaisu na kula da iyalinsa sosai sai dai ya kasa cire abubuwan da suka sami Rumana. Ko da ya tambayeta me take gani kafin tayi barin cewa tayi bata iya tuna komai.


Karo na uku da ta sake yin barin kiransa akayi yana wurin aiki yazo makarantarsu. Kafin yaje sun kaita asibiti saboda irin jinin da take zubarwa. Tana zaune a aji kawai ta kwantar da kanta kamar mai bacci wadda ke zaune a bayanta ce ta sanar da malamar dake ajin tana bleeding. Da yake basu san tana da aure ba duk anyi zaton wata matsalar ke damunta.


Awaisu bai bata lokaci ba ya isa asibitin abinda yaji tsoro ne wato ta sake yin bari. Jikinsa har wani tsuma yake yi yana tabbatarwa ta sami kulawa ga Maamu a kusa ya tafi gidan Alh Mudi.
******


Cikin girmamawa ya gaishe da Mama yace yana neman Gimbi. Tana daki da yake yanzu can tafi zama tana karatu saboda masters da ta koma Mama tace Awaisu yana kiranta. Karamin hijabi ta saka ta fito falon.


Ko zama batayi ba Awaisu ya tareta cikin bacin rai
"Gimbi me nayi miki haka da zafi ne?"


Kallon rashin fahimta tayi masa ita kuwa Mama jin ya daga murya ta kasa karasa barin wurin ta tsaya daga bakin kofar falon


"Bangane ba?"


"To bari nayi miki kashedi gwaro gwari. Wannan ya zama karo na karshe da zaki zubarwa da Rumana ciki. Na rantse miki idan irin haka ya sake faruwa zan kawar da duk wani sauran mutumcin da yake tsakaninmu na dauki mataki"


Kirjinta ta dafe da yake neman bugawa saboda ciwon da yake yi mata. Wannan mugun son da take yiwa Awaisu har yanzu da tuni ta gama iddah bai barta ba sai ma abinda ya karu.


Hawaye ta soma yi "Abban Haris wani ne yace maka na zubar mata da ciki?"


Yatsunsa uku ya daga a gabanta "sau uku kenan Rumana tana bari. Ko yaushe idan abin zai faru sai dai ta kwanta kamar mai bacci tayi ta ambaton sunanki daga nan bazata sake farkawa da cikin ba. Na dauke kai iya yadda zan iya amma bazan zuba ido ki nakasa min mata ba"


A fusace ya fita tana kiransa ko waige babu. Ta juya ta koma daki taji saukar maruka masu radadi har uku a kuncinta. Mama ce tsaye tana hawaye tana hucin bakinciki


"Gimbi ashe tuban muzuru kika yi mana dama? Zubar da ciki har sau uku don rashin imani. Irin haka fa kika yiwa Dr. Yana gashi ita har yau shiru kake ji "


Gimbi na kuka take ta rantsuwar ba ita bace amma a banza. Alh Mudi Mama take jira ya dawo ta fada masa.


Da ta koma daki Dr. Yana ta kira ta tambayeta yanayin da ta shiga lokacin da tayi bari. Ta kasa fahimtar dalilin tambayar gashi Gimbin kuka take yi ta fada mata. Tana ji hankali a tashe ta dauki mukullin motar da take amfani da ita a gidan ta tafi gidan su Ovi.


Ita ce kuwa ta bude kofar tana mata murmushi "gaskiya Awaisun nan naki yana da hakuri indai sai yanzu kika sami sakona"


"Me kike nufi Ovi?"


"Ina nufin duka zubewar cikin matarsa bai taba nuna yasan kece ba sai na yau ko." Dariya take yi ta shige ta bawa Gimbi hanya ta shiga cikin gidan.


Ovi da kanta ta fadawa Gimbi ita ke sawa boka ya zubar da cikin Rumana kuma ya tabbatar yayi yadda za'a zargi Gimbi.


"Mijinki ya bata min rayuwa duk iskancina ban taba kwana a cell ba sai dalilinku ke da shi. Ki dauka ramuwa ce kawai nayi amma bana jin zan taba bari ta haihu yadda kanwata bata shiga ba ita bari zata rinka yi mai ciwo ke kuma ayi ta zarginki"


Mari Gimbi ta sharara mata ta dafe kunci tace ta kiyaye abinda zai biyo bayanta. Fada sosai suka yi na cacar baki sannan Gimbi tazo fita tayi saurin jiyawa gefen kujera inda ta hango wata bakar tukunyar kasa. Dama tasan bokan Ovi ayyukansa yawanci da tukunyar tsafi ne tuni zuciyarta ta bata dashi ake tsafin zubar da cikin. A guje ta ruga ta daga tukunyar Ovi tana ihu ta rotsata da kasa. Kanta Ovi tayo ta fita da gudu ko takalmi bata saka ba Ovi na bayanta ta hankadata kasan benen gidansu dama a sama suke.


Duk abinda suke yi Rita tana daki tana jinsu kawai bata son shiga ne. Gudun da taji ne yasa ta fito daidai lokacin da Ovi ta hankada Gimbi. Duka sun rikice Ovi ta gudu daga gidan ita kuma Rita wayarta ta laluba ta kira Awaisu dama tana da numbarsa.


Yana tsaye gaban Rumana yana jin kamar yayi kuka sai ga Mama ta shigo tana share hawaye tana basu hakuri. Ko da Rita ta kira kamar kada ya daga sai kuma ya daure yasa wayar a kunne. Don kada ya ajiye yaki sauraronta fada masa Gimbi na gidansu ta farayi sannan tayi masa bayanin komai. Bai iya magana ba sai salati ya sake kwasa sai gidansu Ovi yana bin kwatancen Rita.


A kasa ya sami Gimbi bata motsi shima da hawaye baya masa wuya sai gashi sun zubo. A bayan mota ya sakata Rita tabi bayansa a taxi. Emergency aka kaita suka duba ta sannan aka bata gado kusa da na Rumana. Rita gwiwa a kasa ta rokesu gafara sannan ta fada musu duk abinda Ovi tayi.


Mama na rungume da Gimbi tana kuka Rumana ta farka. Lokacin Awaisu ya kira abokinsa DPO ya fada masa duk inda Ovi take su kamata.


Sai gashi Rumana ta tashi amma Gimbi sai yamma ta farfado. Likitan da ya dubata yace ta sami sauki buguwa ce dama da karaya a hannu wadda suka gyara.


Waahegari haka su Awaisu suka sake biyo hanya shima Alh Saminun Kano yazo duka suka hado a asibitin ana yiwa juna jaje. Shuhada da iyayenta ma duka sunje.


Rumana bacci take yi lokacin likita yazo dubasu kowa ya fita. Wurin Gimbi doctor din ta tsaya
"Yanzu bazaki yarda na fadawa 'yan uwanki ainihin ciwon da yake damunki ba?"


Gimbi ta girgiza kai tana hawaye "ko kin fada bashi da magani. Na rasa wace irin soyayya ce nake yiwa tsohon mijina"


"Har fa aman jini kike yi, ki bari a taimaka miki" doctor ta fada tana tausasa murya.


"Kada ki dami kanki ina bakin kokarina wurin cire sonshi daga zuciyata. Akwai kunya mai girma idan nace zan zauna dashi. Labarin darasi ne ga mata. Ke dai duk yadda zakiyi a rayuwa ki tabbatar baki cuci kowa ba, mafi alkhairi gareki shine a cuceki Allah sai Ya isar miki"


Hawaye ne ya gangarowa Rumana amma tayi dif kamar bacci take yi. Zantuka masu ban tausayi Gimbi take yi a take taji mugun tausayinta kuma ta kara sonta domin taji komai game da yadda ta fasa abinda akayi mata tsafi dashi.


Da daddare Rumana ta kafe babanta Harisu da ido idan zai juyo sau biyar sai sun hada ido. Hawaye ya gani fal idon sai yaji tace ya kaita waje tasha iska.


Awaisu da bai san ta tashi ba ya taso da sauri sai dai Harisu ya fuskanci bakinta da magana yace masa bari ya fita da ita shima kafarsa tayi tsami. Basu kawo komai ba ya rike hannunta tana tafiya da kyar.


Waje suka fita ya zaunar da ita kan wani benci sannan ya zauna a gefe yana rike da hannunta "Umm Ruman me kike son sanar da mahaifinki?"


Sunanta kawai da ya ambata ya karyar mata zuciya ta soma kuka. A haka ta fada masa abinda taji. Shima maganar ta tsaya masa a rai


Cike da kulawa yake mata magana "yanzu me kike so?"


Kai ta sunkuyar "Baba don Allah a mayar da aurenta da Son Son...auuuu" ta toshe bakinta da sauri tana dariya.


Shima dariyar yayi "kaniyarki wato Awaisu ya sa kinyi fatali da kunya ko" hannunta ya kama ta tashi.
"Allah Yayi miki albarka Rumana Harisu lallai na yarda da yardar Allah ku ma zaku zama mutane masu sadaukarwa domin farantawa 'yan uwa musulmi. Ina alfahari dake domin kin kasance mai hakuri da biyayya. Muje ciki"


Dakin suka koma kowa na ciki suna shirin fita ne ma. Alh Saminu, Alh Mudi, Nuru, Alh Maitama sai Awaisu. Abin mamaki Baaba Hure ke bawa Gimbi abinci a baki saboda karayarta ga Mamanta a gefe baki har kunne yadda take yaba kirkin wadannan mutane. Harisu ya nemi ganin mazan suka fito duka.


Yadda sukayi da Rumana ya fada musu Alh Mudi hankalinsa ya tashi jin cewa Gimbi na da matsalar zuciya. Awaisu ma ba karamin rudewa yayi ba.


Harisu ya dafa kafadarsa "tashin hankali ba namu bane tunda munsan matsalarta. Shawarata kamar yadda mukayi da Rumana shine Alhaji ka wakilta wani cikinmu ya zama waliyyin Gimbi a maida aurenta da Awaisu tunda akwai sauran igiya daya tsakaninsu."


Da sauri Alh Mudi ya girgiza kai "inaaa, bana marmarin a sake komawa gidan jiya. Gimbi bata kyauta muku ba Harisu"


"Ashe bamu yafe mata ba kenan tunda har yanzu muna tsoronta bazamu iya zama da ita da zuciya daya ba." Cewar Harisu


Awaisu bai iya magana ba sai mamakin Rumana da har ta san ta sowa wani abinda take so. Yana ji suna ta maganganu sai daga karshe yace musu shi dai ya amince a mayar da aurensa da Gimbi. Batare da bata lokaci ba Alh Maitama ya yiwa Gimbi waliyyi shi kuma Harisu ya nemi auren Gimbi ga kaninsa a wurinsa. Basu koma ciki ba sai da aka damkawa Alh mudi sadakin yarsa a hannunsa. Har kuka yayi saboda farinciki yana ta yi musu godiya.


Dakin suka koma akace duk su fito su tafi gida. Mama taso sake kwana da Gimbi Alh Mudi yace tazo su tafi yana da magana da ita. Ya rage dakin daga Awaisu sai matansa.


Gadon Rumana ya fara zuwa yana murmushi ya rike hannunta "Sweet Son So naji duk

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login