Showing 15001 words to 18000 words out of 112099 words
Chapter 6 - KASHE FITILA Book Complete by Batul Mamman.txt
ido cikin ido ya daga hannu zai mareta. Sai a lokacin Maamu ta tashi ta rike masa hannu.
"Idan ka taba yarinyar nan zaka hadu da bacin raina Awaisu"
"Maamu kada ki bari Rumana ta tashi a sangarce. Baki ga yadda take yiwa Gimbi rashin kunya bane"
Gimbi dai bata jin me suke fadi da yarensu. Jin an ambaci sunanta ta matso 'yar kwalla
"Abban Haris ka bar maganar nan haka. Bana so Maamu tayi fushi da kai akan wannan 'yar matsalar. Rumana kiyi hakuri kinji"
Tsabar mamaki yasa ta kasa magana ma. Shi kuwa Awaisu ficewa yayi rai a bace a ganinsa sangarta Rumana za'ayi tunda tana yiwa matarsa rashin kunya kuma an hanashi hukunta ta.
Da suka fita Rumana ta fashe da kuka Maamu ta kasa rarrashinta. Ita da idonta har ya kumbura ya kankance cikin dan lokaci amma Awaisu ko kula baiyi ba me zata ce mata a wannan lokacin. A haka Laminde tazo ta kawo musu tuwonsu. Dole suka ci tunda sun wuni da yunwa.
*****
Kallo suke yi a falo tare da yaransu suna taba hira. Hankalin Awaisu ne ya tafi wurin Mu'allim da yake fadawa 'yan uwansa ya iya buga ball da karfi har Maamu ya bugawa a fuska.
Daga kashingidar da yayi ya tashi da sauri "wa ka bugawa ball kace?"
Gimbi tayi saurin tarewa "ku tashi ku tafi ku kwanta dare yayi"
Awaisu ya janyo hannun Mu'allim. Fuskarsa babu alamun wasa ya tambayeshi me ya faru a dakin. Gimbi ya fara kallo sai dai bata da ta cewa a wurin. Dolensa ya fadi abin da yayi da marin da ya sha.
Da sauri Awaisu ya tashi yayi hanyar dakin Maamu. Gimbi ta soma kiransa sai dai ko juyowa baiyi ba.
Yana shiga ya tarar da Maamu a kwance ta rike kankarar pure water a daidai idonta yayin da Rumana har yanzu kuka take yi. Kankarar ya karba ya ga idon ya suntume.
"Subhanallahi Maamu kiyi hakuri. Yanzu nake jin abin da ya faru"
Tashi tayi zaune idonta cike da kwalla tace Rumana ta fita
"dama irin zaman da kake son yi dani kenan ka takura muka taho?"
Kansa ya sunkuyar kasa yana bata hakuri.
"Yaushe rabon da ka shigo dakin nan balle ka duba lafiyarmu? Bance kada kaso iyalinka ba amma ka tuna cewa nima ina da hakki a kanka. Bana neman komai a gareka da ya wuce ka bani girman da Allah Ya bani akanka sannan ka kula da amanar Rumana. Idan ka wulakanta zuri'ar Baaba Hure kafi kowa sanin irin kallon da duniya zata yi maka. Sannan a lahira ka tashi cikin masu tozarta zumunci."
"Kiyi hakuri, nasan nayi kuskure amma zan gyara in sha Allahu. Na rasa abin da yake damuna ni kaina"
Duk da ranta a bace yake amma taji dadi yau ya nuna damuwarsa garesu
"Ka tashi ka tafi ya wuce"
"Asibiti zan kaiki saboda idon. Shi kuma zai gamu dani wallahi."
A fusace ya fita daga dakin. Rumana da take tsaye a gefe yace mata daga yau ta rinka fitowa da Maamu falo suna shan iska baya son suna kulle kansu. Dakin yaran ya wuce Gimbi tana tambayarsa me zaiyi da wayar chaja bai kulata ba sai gani tayi ya fara laftawa Mu'allim dan shekara bakwai a jikinsa. Yana dukansa duk ya cika gidan da ihu Gimbi ta kasa karbar chajar sai ma rabonta data samu a baya.
Maamu tana jinsu ta kwanta abin ta. Bata kin jikokinta amma ta kula da yadda suka bi sahun babarsu wurin banzatar dasu a gidan. Ranar Awaisu da Gimbi barambaram akayi babu mai kula dan uwansa tun bayan da ya gama hukunta Mu'allin tare da ja mata kunne sosai akan Maamu.
Da safe a motarsa suka dauki Rumana zuwa makaranta ya bata dubu biyar yace ta ajiye sauran a gida. Yaso kai Maamu asibiti ma tace ta warke.
*****
Gimbi tana fita da suka kai yara makaranta gidan Anti Bebi ta wuce. Tana kuka ta fada mata irin dukan da Awaisu yayiwa Mu'allim. Gashi tana ganin kamar maganin ya fara sakinsa.
"Ni dai kawai kizo muje gidan Wangesi kada komai ya lalace min"
"Gimbi kenan wato mugu baya so a dandana masa zumarsa sai ya birkice. Don yau daya anyi miki meye na fushi. Can wurin aikin naki fa?"
"Ni dai kawai kizo muje zan san karyar da zanyi musu"
Ko mijinta bata sake lekawa ba ta dauko dan gyalenta suka fice. Gimbi ta sallami nata dreban suka wuce da dan koran Anti Bebi. Wangesi ya bata wasu kwayaye guda hudu duk anyi musu zane da jar tawwada da wasu layu da kulle kullen magani. Komai yayi mata bayanin yadda zata yi amfani dashi ta kawo kudi ta ajiye masa.
Suna komawa gida ta wuce. Kwai daya a kofar dakin Awaisu ta fasa shi ta rufe da door mat. Sauran biyun kuma daya a bayan dakin Maamu dayan kuma ta dafa shi ta cinye.
Da ta gama ta dauki motarta ta koma gidan Anti Bebi sai lokacin tashin yara ta dawo. Manajan bankin da take ya kira Awaisu kan cewa yayi mata magana akan fashi da rashin zuwa da wuri ko kuma fita kafin a tashi. Don ma yana ganin kimarsa ne da tuni ya bata takardar jan kunne.
Hakuri ya bashi tare da godiya. Yana dawowa ya hauta da fadan sai ta gaya masa inda take zuwa. Ta rasa amsar da zata bashi. Abincin da ta zuba rabin maganin kuma yaki ci. Daren ranar yaransa yasa a gaba suka taya Maamu da Rumana hira a falo.
Gimbi kuwa Anti Bebi ta kira tana kuka Wangesi ya ci kudinta a banza.
"Kin fiye wutar ciki. Haka aka ce miki asirin yana kama mutane kamar a fim? A hankali zai cinye shi ya dawo miki tamkar sakarai shashasha"
Tsaki tayi ta ajiye wayar. Ita Anti Bebi bata da aiki sai fadin bakar magana. Awaisunta ba sakarai bane ta fada a zuci tana huci ita kadai.
Sai bayan sati ta kula ya fara sanyi fiye da yadda yayi a baya ma. Sa idonsa akan lamarin su Maamu da suka fara shanawa yanzu babu.
Gidan jiya aka koma inda take horasu da yunwa wai don kada suji dadin gidan su cigaba da zama.
[4:30PM, 2/18/2018] +234 803 369 4017: *KASHE FITILA*💡14
*Batul Mamman*💖
*Bayan Sati Uku*
Zaune take gaban madubi tana kwalliya taji kamar ana kiranta. Jagirar hannunta ta ajiye ta fito daga dakin tare da leka falon ta saman bene. Mijinta ne ya shigo rai a bace sai huci yake.
"Shuhada kina ina ne?"
Saurin saukowa tayi har tana hada bene biyu a lokaci daya
"Me ya faru T?"
Mugun kallo ya bita dashi kafin yayi magana "kizo ki fice daga gidan nan na sakeki"
Ji tayi kamar an sakar mata guduma a tsakiyar kanta
"Ka sakeni? T kalmar saki fa ba kalmar wasa bace"
Idanunsa kara rinewa sukeyi suna yin ja saboda bacin ran da ya rasa dalilinsa.
"Ni zaki rainawa hankali, to zamana dake ya kare. Ki tattara ki fita kafin kiji hannuna a jikinki"
Shuhada rasa bakin magana tayi. Anya mijin nata hankalinsa daya kuwa. Ya fita suna farinciki da juna. Me ya kawo wannan chanji haka. Dan matsawa tayi kusa dashi
"T ka zauna don Allah muyi magana. Na rasa gane abin da yake faruwa. Abokanka sun baka wani abu ne kasha da baka sani ba?"
Saukar mari taji har biyu "kina nufin ina shaye shaye ne."
Dafe kuncinta tayi tana kuka "Tajuddeen kana cikin hankalinka kuwa. Nice fa, me nayi maka haka"
Girgiza kai yayi yana yamutsa fuska "tsanarki kawai nayi S. And I want you to get out now kafin raina ya kara baci"
Kuka ne sosai yaci karfinta. Gabadaya kwakwalwarta ta toshe. Mutum ya fita lafiya ya dawo a birkice. Ba karamin so yake nuna mata ba tun kafin aurensu har zuwa yanzu da suka sami shekara daya tare. Gani tayi ya hau sama ya fara cillo mata kayanta ta saman bene. Lallai da gaske yake. Tana kallo ya gama ya sauko ya bude wallet dinsa. Kudi ya debo ya watsa mata a fuska.
"Now get out"
Itama nata ran ya gama baci "babu inda zani Tajuddeen, a musulunce ma dai mace a dakinta take yin idar saki daya ko biyu. Sannan a daren nan ina kake so naje? Ba fa Nigeria muke ba inda zaka sakeni na tafi gida."
Cikin halin ko in kula yace "tafi wurin kaninki"
Bude baki tayi "yaron da yake hostel din maza"
"Indai don ki kwana ne to na sakeki saki uku. Ai dai babu sauran igiya tsakaninmu."
Karo na biyu kenan da Shuhada ta shiga tashin hankali dalilin saki. Na farko a gabanta ita da kaninta mahaifinsu yayiwa babarsu saki uku. Yau gashi anyi mata batare da wani kwakkwaran laifi ba.
Jiri ne yake dibarta amma a haka ta fara hawa benen zata koma sama. Tajuddeen yayi saurin tareta yana cewa bazata kara shigar masa daki ba.
Bata da kuzarin fada saboda duk abin da ya faru tamkar mafarki haka take jinsa. A sanyaye tace "wayata zan dauko da mayafi. Sannan ka bani passport dina"
Saman ya hau ya dauko mata wayar da passport. Mayafi kuwa kayanta da ya watsar ya nuna mata. A nan ta durkusa ta dauka ta fita. Wani sanyi ne ya ratsa ta ga dare karfe goma da rabi.
Da kyar ta sami taxi wadda ta kaita jami'ar da Suhail kaninta yake karatu a nan Singapore. Da ta sauka ta kira wayarsa tayi sa'a ya dauka a kiran farko. Tana jin muryarsa ta saka kuka mai cin rai. Nan hankalinsa ya tashi da kyar ya samu ta fadi inda take a wajen makarantar ya fito.
"Sis me kike yi a nan a daren nan ke kadai?"
"Ya sakeni Suhail, har saki uku." Wani kukan ta soma sai gashi ya koma babban yana ta rarrashinta. Bayan ta dan nutsu ta labarta masa abin da ya faru.
"Hotel zanje na kama sannan na kira Daddy ya turo min kudi. Kaga last week ka ranci kudi a hannuna yanzu bani da enough da zan sayi ticket na koma Nigeria."
Suhail ya sunkuyar da kai yana ajiyar zuciya "Sis ko kin kira bazai aiko miki da komai ba. Kudin da na ranta wurinki ciko nayi na biya kudin registration."
Shuhada ta zaro ido "me kake nufi?"
"Na fi wata ina cewa ya turo min kudin registration yana cewa babu. Dana matsa masa rannan sai yace wai dama ai saboda mijinki yana aiki a nan ya turoni karatu. Tunda bashi da kudi meye amfaninku. Ganin kada su dakatar min da karatu yasa na ranta kafin ya turo min sai na baki"
Dafe kai tayi tana mamakin wannan abu. Tasan waye mahaifinsu a Nigeria. Babu yadda za'ayi yace kudin makarantar dansa ya gagare shi. A yadda yake ko da da gaske babu bazai taba bari su sani ba zai nemo ko bashi ne. Hankalinta ne ya kara tashi ta ce masa zata nemi wurin kwana washegari yazo ya sameta.
A dakin hotel din baban nata ta kira kamar yadda ya fadawa Suhail itama cewa yayi ta nema ko ta bawa mijinta hakuri ya biya mata. Tayi kuka a daren har asuba bata runtsa ba. Da sassafe ta koma gidanta da sunan kwashe kayan sawarta. Tajuddeen ta roka ko zai biya mata kudin jirgi ta koma gida. Nan yayi mata rashin mutunci ya koreta. Dole ta kira mahaifiyarta mai fama da hawan jini ta sanar da ita. Da dan kudin hannunta take biyan hotel din. Kullum suna tare da Suhail suna shawarwari. Bayan kwana takwas mamanta tasa aka turo kudin jirgin. Filinta ta sayar domin duk wani abu na kadara da ta samu wurin babansu sai da ya karbe bayan sakin.
Ana gobe zata tafi Suhail yana tayata hada kaya harda kukansa. Shekararsa ashirin da biyu ita kuma da hudu. Text ne ya shigo wayarta daga numbar da batayi tsammani ba.
_Kada ki kuskura kizo min gida da sunan zawarci. Kamar yadda kika kirga min aure da na auri ubanku kema yanzu kika fara. Ke da duk wani naki baku isa ku ja dani ba_
Sai yanzu ta gane dalilin sakin da Tajuddeen yayi mata. Yadda aka raba iyayenta itama haka akayi mata. Gashi an rabasu da mahaifinsu. Bata nunawa Suhail komai ba. Sai dai ta kuduri niyar canjawa daga Shuhadar da mai shiru shiru da hakuri.
Washegari da daddare jirginsu ya tashi. Uku na yamma suka sauka a Nnamdi Azikiwe Airport Abuja. Tana saukowa daga jirgin tana saka yadda zatayi maganin Anti Bebi matar babanta.
*****
Gimbi na kwance a daki yau asabar tana hutawa taji waya daga Mama. Bayan sun gaisa take sanar da ita cewa ta fita unguwa ne kuma suna hanya zata biyo su gaisa da Maamu. Zumbur Gimbi ta mike daga kan gadon. Karfe biyu da rabi ko abincin da za'a dafa bata aunowa Laminde ba. Da sauri ta shiga kitchen din tana kwala mata kira. Dama tasa tayi miya tun dare. Shinkafa tace ta dafa ita kuma ta hau aikin salad. Bayan ta gama ta dauko dabinonta wanda ya kwana biyu a jike cikin fridge tare da kanunfari da dakakkiyar danyar citta ta hada da kwakwar da tasa Rumana tayi mata grating ta zuba a blender. Nan da nan ta gama markadesu ta tace ta kara madara. Kankara ta fasa ta hada a jug ta jera a tray. Bayan an gama shinkafar ta cika mata cooler madaidaiciya ga miya taji nama. Cikin awa daya sun gama komai sai jiran Mama.
Abincin Maamu a langar nan ta zuba ko salad bata samu arzikin a zuba mata ba. Laminde a ranta tace lallai uwa tafi uwa. Suna kitchen din suka ji sallamar Mama. Gimbi ta kalli Laminde tana ta murna
"kinsan Mama bata son zuwa gida 'ya'ya ba kamar wasu tsofaffin ba. Shiyasa kika ga na hada mata wannan. Ki biyoni da abincin nata. Maamu ki kai mata nata daki ba sai tazo falo ba"
Da murna ta taro Mama suka gaisa sannan ta tashi tana rike da hannun Amir
"Kinsan ba wurinku nazo ba. Kaini dakin Maamu"
Yayi mata jagora har dakin. Gimbi ta koma dakinta da sauri ta sake gyarawa ta fesa air freshner sannan ta shimfida katuwar dadduma a kasa. Fitowa tayi zata je kitchen ta hango Laminde a kofar dakin Maamu da katon tray din kayan abincin Mama. Da sauri tace
"Ke, ke, ke Laminde dawo"
Laminde tana ji tayi biris da ita ta shige dakin.
Maamu ta samu da Mama suna taba 'yar hira da kalmomin da Maamun take fahimta. Har Mama tana cewa ta rame ko kewar babban danta take yi. Laminde ta ajiye musu abincin a tsakiyarsu. Mama tayi ta korafin meyasa basa gama abinci da wuri.
Maamu ta bude ido tana kallon wannan gara wadda ta manta rabon da ta ga abincin arziki irinsa. Ita kuwa Mama plate din da ta gani guda daya ta zuba musu abincin tare. Tuni idanun Maamu suka fara cika da kwalla da Mama tace mata su ci. Ita da gidan danta ta koma tamkar almajira. Mama ta rinka kara musu suna cinyewa tare. Maamu ta saki ciki taci ta koshi tasha lemon kwakwa. Rumana da take dakin ma sai da Maamu ta cika kofi taf ta mika mata.
Gimbi kuwa daki ta koma tana ta kai kawo. Ta rasa wane hukunci ya dace da Laminde.
Sai daga baya ta fito ta koma dakin Maamu. Laminde tana hango shigarta ta bawa Mu'allim langar abincin Maamu tace ya kai mata. Haka ya karba yana turo baki yaje ya dangwarar mata a gabanta.
Mama ta daka masa tsawa "nifa shiyasa bana son wasan jika da kaka, wani lokacin sai raini yayi yawa. Abincin waye wannan duk kanzo"
Maamu tayi murmushi ta mika hannu "nawa ne"
Gumi ya karyowa Gimbi saboda kallon da Mama ta jefa mata. Baki na rawa tace "Mu'allim dauki ka cewa Laminde wai wa ta zubawa wannan abincin"
Da yake gwanin tsiwa ne yace "Mummy langar abincin Maamu ce fa." Sannan ya fice abinsa.
Maamu da yarensu ta fadawa Rumana ta ajiye a gefe zuwa anjima idan ba'a gama na dare da wuri ba sai suci.
Mama ta ritsa Gimbi da idanu, ita kuwa taki yarda su hada ido saboda tasan yau me rabasu sai Allah.
*KASHE FITILA*💡15
*Batul Mamman*💖
Laminde tana daga kitchen ta hango Mama a gaba rai a bace Gimbi na bin bayanta suka shiga hanyar dakinta. Rufe kofar kitchen din tayi ta kwashe da dariya.
"Haka kawai kin mayar da mata almajira a gidan danta. Allah Ya budi idon Alhaji dai ya gane irin matar da yake aure"
*****
Mama ko zama bata yi ba ta juyo tana hararar Gimbi. Kana ganinta ta gama tsorata sai dai kuma a yanzu jan ido bazai hanata kudirinta na ganin Maamu ta bar musu gida ba.
"Gimbi me yaron nan yake nufi da cewa abincin kakarsa ne a wannan kodaddiyar langar?"
"Haba Mama yanzu shine duk kika bata ranki? Har kin tsorata ni. Dambun nama ne na zuba mata a ciki kwanaki to shine suke ganinsa a dakin"
Mama ta danyi jim kamar bata yarda ba
"Yanzu surukar taki kika zubawa dambun nama a ciki don wulakanci. Idan nice kinsan jifanki zanyi dashi. Ko da wasa wallahi kada ki kara"
Gimbi tayi mamakin saurin saukowar Mama ta bata hakuri da alkawarin bazata kara ba.
Mama tace "na kula dai ba karamin ci tayiwa abincin nan dazu ba. Ki dena barinta da yunwa. Abincin rana ace sai hudu saura babu dadi"
Tabe baki tayi saboda samun wuri
"mhmm Mama don ba a gidan nan kike ba. Haka take wannan cin abincin. Kuma Abban Haris na dawowa sai kiji tana cewa bata ci abinci ba "
"Ni dai na fada miki gara uwarmiji ta cuceki akan ki cutar da ita. Mijin da kike takama dashi aljannarsa tana tare da farincikinta dashi"
Zama Gimbi tayi tana ta fadin karairayi duk tace Maamu ce take yi mata. Sai dai tana kula tamkar zancen bai shigar Mama. Suna nan ta jiyo muryar Awaisu ta tashi. Bata jima da fita ba wayarta da ta bari akan gado ta hau kara. Mama ta mika hannu ta dauko
*Anti BB* ta ga an rubuta. Zata amsa kenan Gimbi ta shigo, kusan fizgar wayar tayi daga hannun Mama har ta bata tsoro.
"Wata mata ce da nake bi bashi take kin daukar wayata shine ta kira yanzu."
Dauka tayi tace zata kira tana tare da mamanta. Anti Bebi tana jin haka tayi dariya kawai a ranta tana mamakin Gimbi. Ita kaifi daya ce babu kumbiya-kumbiya. Gimbi kuwa fuska biyu gareta. Wato sai tana da bukata take nemanta. Zasu gamu ne. Mama abin ya kara daure mata kai yadda Gimbi ta canja.
Awaisu yazo