Showing 87001 words to 90000 words out of 112099 words
Chapter 30 - KASHE FITILA Book Complete by Batul Mamman.txt
mutu ka raba. Duk ranar da taku ta hadaku saboda rayuwar yau da gobe har shaidan ya baki shawarar kiyi yaji to ki sani kiyi kayanki a cikin gidanki. Baki da masauki a gidan nan indai ba ziyara ce ta kawoki ba. Su Haris kannenki ne kuma 'ya'yanki yanzu. Ki rungumesu fiye da yadda kika saba a baya."
Kuka take yi sosai tana jin kamar yanzu za'a kaita gidan miji. Harisu ya juya ga Awaisu yana murmushi.
"Abu daya zan fada maka dan'uwana. Kai miji ne kuma uba ga Rumana. Ka tafiyar da ita da fuskar da ta dace ku zauna lafiya."
Daga nan yace Rumanan ta fita ta jirasu a bakin kofa. Haka ta fita fuska duk hawaye da majina. Hannun Awaisu Harisu ya rike.
"Sai kayi hakuri yara biyar ne yanzu a gabanka. Mata duk girmansu basa rabo da shirme da shiririta. Nasan ba sai na fada maka ba amma don Allah ka rike min ita amana"
Duka su biyun zukatansu sun karye. Awaisu ya kara karfin rikon da suka yi da hannuwansu na dama.
"In sha Allah nayi maka alkawarin bata dukkan kulawar da ta dace. Allah Ya saka muku da mafificin alkhairi. Zanyi kokari naga cewa kamar yadda kake alfahari dani a matsayin kani zakayi a matsayin suruki"
Harisu ya kai masa duka a kafada "ana maganar arziki ka sako wasa. Tashi kuje Allah Ya bada zaman lafiya. Na manta ban fada maka ba munyi magana da Alh Saminu yace iyalinsa zasu je Abujan idan an gama biki. Abin Maamu dai baiyi masa dadi ba"
"Yaya ya muka iya. Nagode"
Yana fitowa ya ganta a durkushe a wurin har lokacin bata dena kuka ba. Hannunta ya kama jikinta a sanyaye suka tafi dakinsa. Kamar kada ta shiga da ta tuna yadda suka kare daga cin tuwo. Sai ta daure don jin nasihar Harisu take tamkar a lokacin yake yinta.
Bandaki ya nuna mata shi kuma ya zauna "jeki ki wanke fuskarki magana zamuyi"
Allah Yasa ba wani fada shima zaiyi mata ta fada a ranta sannan taje ta wanko ta dawo.
A kan kafet ta zauna nesa dashi sai ya rabu da ita.
"Umm Ruman"
A ladance tace "na'am"
"Duk kinji abubuwan da Yaya ya fada ko?" Ta gyada kai. "Don Allah ki zama irin matar nan da ko miji yana so ko baya so sai ta shiga aljanna saboda kyawawan dabi'u da mu'amala"
Tana goge hawaye tace "to".
"Ranar monday ya kamata ku koma school amma bazaki je ba. Yaya ya nemi Principal dinku za'a karbo miki takardar transfer. Na cike miki form na wata makarantar so nan zaki koma kiyi SSCE dinki"
Kanta har lokacin a kasa tace tafi son komawa makarantar da ta baro.
"Uhmm uhmm Umm Ruman. Bana son surutu ne a school kawayenki su san kina da aure. Yawancin makarantu basa yarda su dauki matar aure. Inda zan kaiki ma ban fada musu ba kema ko yaya kike da kawa ki bar zancen sai kin gama jarabawa."
"To shikenan nagode" ta iya furtawa.
Tasowa yayi yazo kusa da ita ya kama hannunta yana murzawa.
"Duk kin zama wata saliha ko fadan ya shiga ne da kyau. Amma kada ki manta kinci bashin kirana Son So a gaban Yaya"
Dago kai tayi ta soma dariya.
"Lallai yarinyar nan baki da tsoro amma nasan ta inda zan kamaki. Sati biyu ne fa ya rage miki ki biya bashi"
"Wai da gaske sai na biya. Na zata ko bashin naci kaine zaka biya. Nice fa Uncle, Rumana Son So" ta langabe kai
"Abin naki harda blackmail kuma. To Son So na hakura duk abin da ya biyo baya ba biyan bashi bane so ne kawai"
Sonta yake ji ko ina a jikinsa yadda take langabewa tana shagwaba. Hancinta ya ja yana son kissing dinta amma baya jin zai hakura a nan gara ya bari sai lokacin da ta dawo gidansa gabadaya.
*****
Gaban maigadi Gimbi taje ta zaro wuka daga jakarta jikinsa ya hau bari kamar mazari.
"Ko ka bude min ko na yanka kaina kuma nace kaine kayi niyar...."
Bai jira ta gama fadin abin da tayi niyya ba ya tashi ya bude gate din a gaggauce. Dariya tayi ta shiga mota tana takaicin yaya akayi wannan tunanin baizo mata ba tuntuni. Da zata fita ya leko yana sauka lafiya ta sha kunu.
"Idan ubangidanka ya sami labarin na fita zaka iya rasa aikin nan"
"Wa ya aikeni Hajiya. Ke dai Allah Ya kiyaye hanya kawai"
Gidan Ovi ta je kai tsaye. Ko shiga batayi ba suka fito ita da Rita suka wuce gidan Boka. Gimbi tana kuka tana fada masa matsalolinta da rashin biyan bukatarsu.
Fuskarsa a murtuke yace "Gimbiya kiyi hakuri daga yau babu sauran aiki a tsakaninmu"
Yadda gabanta ya yanke ya fadi ko iyayenta ne suka rasu iya tashin hankalin da zata ji kenan. Dan akwatin sarkar ta dauko ta bude ta ajiye a gabansa.
"Ka taimakeni ka rufa min asiri ka magance min matsalolina. An raba ni da yarana da mijina ga kishiya. Iyaye sun juya min baya. Bani da kowa sai kai sai su Ovi"
Wata rawa ya tashi yayi yana juyi a gabansu sai ga tusa ta fito mai uban karfi hade da wari. Suna toshe hanci sai Rita ta saki tata Ovi ma tayi. Gimbi wari kamar ya shaketa ta rasa dame zata rufe hanci Boka yace "kinga dalilin da yasa bazan kara yi miki komai ba. In takaice miki ma dai babu wani abu da zan sake baki yayi tasiri "
Ga wari ga tashin hankali "Boka me nayi haka da zafi?"
"Kinsan Gogojiya?"
"Abinci ne?"
"Aljana ce da ban taba mu'amala da ita ba. Wannan tusar ma ita ta sakani sakamakon aikin karshe da nayi miki. Bansan wa ya turo ta ba amma tayi alkawarin yi min kisan wulakanci idan na sake yi miki aiki kuma tace ki kiyaye haduwarku. Aljanu na kaf sunki zuwa wurin nan saboda ita"
Gimbi ta rasa me zata ce. Boka dai ya dage yace ta fita daga ita har su Ovi. Da suka fito su biyun tusa suke kamar su tada jejin Gimbi da gudu ta arce ta barsu. Ji tayi kamar ana binta a guje duk tsigar jikinta ta tashi....Gogojiya tayi wata dariya. Albarkacin musuluncin da ta karba lokacin da Mal Ridwan ya rabata da Fanta yasa bata sabauta Gimbi ba a wurin. Hajiya Fanta bata nemi taimakonta ba saboda shawarar malam amma taji komai kuma babu wanda ya isa ya dagawa Haj Fanta yatsa tana gani ta kyale.
Duk yadda Gimbi taso zira mukullin motar tamkar an shafe wurin bata ganin wurin zirawar ta saki mukullin tayi gaba. ga tsoro da gudu tayi titi tana tsayar da motoci da kyar wata tasi ta tsaya ta shiga. Tana ji ana ja mata dankwali da zani irin yadda tasa akayiwa Anti Bebi. Da kyar ta iya karasawa gida ta shiga kamar walkiya maigadi dai bakinsa alaikum.
*****
Washegari tun bayan asuba Awaisu ya gama shiri saboda baya son suyi tafiyar dare. Gashi akwai aiki ranar litinin yana bukatar ya dan huta ko yaya kafin wayewar gari.
Ruwan tea kawai ya iya sha ya shiga wurin Maamu. Sun dade suna hira duk da sun raba dare jiya. Nasiha take masa akan rikon addini da dena sakaci da addu'a. Daga wurinta yaje ya jima wurin Baaba ya fada mata karshenta bazai sami dawowa ba har a gama bikin.
"Babu komai ai dani za'a kawo amarya sai ka gyara dakuna biyu. Wai ina ma take ne miji zaiyi tafiya ana ta baccin asara." Ta fada tana tashi.
Awaisu yace "Baaba kyaleta kinsan bata jindadi "
"Bari na tura a kirawo min ita kuma bance ka kulata ba tunda kace a kyale mara lafiya"
Murmushi yayi ta fita ba jimawa sai ga Rumana ta shigo tana murza idanu bacci bai isheta ba.
"Baaba gani" tace tana neman wurin kwanciya akan gadon. Jin ba'a amsa ba tayi kwanciyarta. Sai lokacin ta kula da Awaisu akan kujerar da take gefen kofa. Da sauri ta tashi tana gyara hannun riga. Dogon wando ne da yar riga mai karamin hannu. Kankance ido yayi daga inda yake "Son So haka kike yawo a cikin gida nan da wannan kayan? Bana so please ki rinka saka mayafi ko hijab a kai"
Jikinta ne yayi sanyi tana tunanin ko tayi masa laifi ta soma bashi hakuri. Ganin garin da duhu baifi bakwai da rabi ba gashi tasan dai babu kowa sai iya su na gidan.
Bakin gadon ya dawo ganin ta damu "ba fushi nayi ba amma ina da kishi bana son kina yawo a haka kowa na ganinki." Goshinta yayi kissing ya tashi zata fito yace ta zauna a dakin ta nemi hijab kuma ya yafe rakiyar kada ya wuce da ita. Daga dakin tayi masa adduar sauka lafiya ta koma tana jin ba dadi. Shi kuwa bata san ganin da yayi mata a haka bane ya ruda shi. Yana mata kallon yarinya ashe ta wuce yadda yake tunani. Ko kadan bazai juri cigaba da ganinta a haka ba shiyasa yayi saurin tafiya.
******
Sun isa Abuja da wuri kamar yadda yaso suna shiga gidan yaga babu motar Gimbi. Maigadi ya tambaya yace tana ciki amma bai san inda mota take ba.
Da ya shiga a bakin kofar dakinta ya tsaya tana kwance akan gadonta da kayanta tun na jiya har lokacin batayi wanka ba.
"Gimbi ina motarki?"
A gigice ta tashi sai lokacin ta tuna inda ta baro motar. Jikinta ne ya hau rawa ta rasa amsar bashi. Ya kula da yadda take yasan bata da gaskiya.
"Na baki zuwa gobe ki dawo min da motar nan" kawai yace ya juya ya tafi dakinsa.
Gimbi ta shiga tashin hankali. Ovi ta kira ta nuna mata jiya basu ji dadi ba ta tafi ta barsu amma basu ga mota ba. Bayan kuma ko awa daya basuyi da mai saya ba sunyi sa'a duka takardun suna ciki suka yi cinikin gaggawa shi kuma yaji arha banza ya biya ya dauka.
Ba karamin tashin hankali suka yi tayi da Awaisu akan motar ba taki fada masa inda take. Kyaleta yayi ya cigaba da shirinsa na zuwan Son So Rumana.
A can Fika suma nasu shirin suke yi. Amarya tana ta shan gyara daga wurin iyaye ko ta ina. Ana gobe fara bikin wata 'yar abokin babansu na bayan layi wanda da yayanta yaso Rumanan tazo. Lokacin suna daki da yayyenta mata ana ta chapta da 'ya'yan gwaggwaninta su Baraka sa'aninsu.
Da sallama Zee ta shiga tana ta washe baki "Rumana amarya yaya shirye shirye"
A darare ta amsa mata saboda ko da can ba wani shiri suke da ita ba.
"Dama cewa nayi bari nazo muyi maganar shirin bikin. Naga baki aiko mana da kati ba mu da sauran kawayenmu gashi gobe za'a fara "
Sauran fita sukayi sai Iman da Rumana. Rumana tace mata bikin ne yazo a gaggauce ba wani abu zasuyi ba daban da na iyayen.
Sake washe bakin nan nata tayi "Hakan ma yayi amma kin ware kawaye masu rakaki Abuja? Kinsan dole aje da kawaye saboda komai yafi tafiya daidai. Idan wata bata rigani ba zanyi miki babbar kawa"
Iman ta soma dariya ita kuwa Rumana cewa tayi " Zee baki ji haushi ba ko saboda yayanki?"
Zee ta firfito da idanu "akan me idan ba bakinciki ba haushin me zanji. Abuja fa zaki koma zaman aure. Ni dai don Allah aje dani ko abokin mijinki na samu ya ajiyeni a can. Kodayake ance mai kudin kawun nan naku ne. Ni wallahi ko drebansa ne ina so kiyi min hanya kinji"
Iman kasa boye dariyarta tayi suka ce indai an yarda a gidansu zasu tafi da ita Abuja. Ledar viva ta hannunta ta nuna musu.
"Ai tuni na tambayo a nan ma zan rinka kwana har a gama bikin."
Washegari da safe aka fara biki irin na Bolewan Fika. Sunyi taronsu na kwana uku ana gobe za'a kaita aka yi mata lalle mai kyau ja da baki.
Tsabar gyaran da ake mata ta chanja gabadaya ta cicciko sai shekin amarci take yi.
Ranar asabar da sassafe aka kama hanyar Abuja. Motoci biyar akayi da guda daya ta kaya a haka ma ana ta rage masu zuwa. Tasha kuka dai kamar bazata tafi ba. Maamu tayi ta bata baki tace mata tana nan tafe. Ita da Baaba sunyi rawar gani a wurin bikin nan.
Baya gidan suka iso sai Gimbi a daki ta cika tayi fam saboda bakinciki. Guda su Hindatun Bomai da Tikeke suke yi da gayya don taji haushi. Dakunansu duka wani matashi cikin samarin Fika da yake kaiwa shago shine ya nuna musu. Nan aka shiga sauke kaya suna ta hayaniya a cikin gidan.
Rumana ta idar da sallah Iman ta miko mata wayarta dake ta ringing. Ta dauka da sallama ganin sunan mai kiran harda faduwar gaba.
"Wa alaikum salam wa rahmatullah wa barakatuhu....welcome home Son So. Ina hanya in sha Allah na fita ne saboda bakin su fi saurin sakewa. Ki gaida min su Baaba kafin na iso"
Jikinta ne taji yayi sanyi sai kuma tsoro da fargabar yadda zata zauna da Uncle Awaisu a matsayin mijinta.
[15/08, 17:46] +234 803 272 5896: KASHE FITILA*💡47
*Batul Mamman*💖
*_Jinjinar ban girma ga dan Arewa na usuli_*
*_Dan uwan 'yan Fikra Mudan dan asali_*
*_Godiyarmu ba adadi don tafi cikin cokali_*
Awaisu na ajiye wayar ya mayar da hankalinsa ga abokinsa Nuru wanda yake ta masa dariyar shakiyanci.
"Angon Rumana kana burgeni fa. Wani salon soyayya nake gani da ban sanka dashi ba"
Awaisu ya shafa sajensa da aka gama gyarawa tare da aski.
"Dole ka sami bakin tsokana mana tunda ka baro aikin da ya hanani zaman gida na tarbeta"
"Seriously abar maganar wasa wallahi so nake na taimaka wurin kara kafaka a zuciyar Rumana. Kasan na dade ina ce maka yarinyar tana da nutsuwa tun sanda na ganta a gidanka"
Tunawa yayi da yadda ta rinka tsokanarsa zuwansa na karshe har tana kiransa Son So a gaban Harisu dariya ta kufce masa a zuciyarsa yace idan ma da nutsuwa akwai fitina.
"Yanzu dai a ina zan sami riga irin wadda nake so tunda kaga komai ya kure?"
Nuru matarsa ya kira ta kwatanta masa wani babban shagon sayar da kayan mata da yake tashe a Abuja suka dauki hanya shi da Awaisu yana yi masa bayanin cewa abincin tarbar su Baaba gidan Alh Mudi sun dauke masa. Shi har kunya yake ji ma duk da abubuwan da suka faru yasan suna yi ne domin rage girman laifin Gimbi.
Kimanin kwana biyar baya kenan da ya bawa Nuru labarin abubuwan da suka faru a gidansa da auren Rumana . Sosai Nuru yaji haushi dama amininsa ne tun Jami'a a Bauchi. Sai dai shi a wani kamfani mai zaman kansa yake aiki.
Awaisu bashi da yawan surutu kuma da kunya dai kace uwar 'ya'yanka ke bin bokaye. Shiyasa ya kasa fada da wuri. Nuru ya tausaya masa duk da yace a baya ya dan kula da abokin nasa ya sauya amma baya son zurfafa bincike a rayuwarsa tunda alakarsu bata chanja ba sai in ka cire rashin barinsa ya kawo tasa mahaifiyar su gaisa da Maamu, kullum yayi magana sai ya bashi uzuri har ya hakura.
A gaban matar Nurun ya bada labarin itama ta kadu sosai amma dama can ba wata aminta sukeyi da Gimbi ba. Shi kuma yace ya bayar ne saboda itama da surukarta suke zaune ya kare da yi mata 'yan nasihohi akan son zuciya.
Washegari sai ga Nuru a bankinsu yace Kubra ta dage sai anyi taro a gidan Awaisu na tarbar amarya. Da fari baiyi tunanin hakan ba amma abokin nasa da matarsa suka dage cewa hakan ba karamin farantawa Rumana da iyayenta zaiyi ba. Dadin dadawa 'yan hotuna da amare keyi da mazansu lokacin biki itama zata samu. Wannan zai taimaka masa wurin kara saka mata nutsuwar zama dashi. Da gaske suka yi ta jan ra'ayinsa sai gashi ana ta shirye shirye sun kama wuri inda za'ayi event din. Abokansu da matansu suka gayyata da gidansu Shuhada da suka dawo daga tafiya sai kuma mutan Fika da basu san za'ayi ba ma. Kusan komai sun gama sai kayan da Rumana zata saka ne Awaisu yake ta ruwan ido gashi har sun iso gari kuma washegari bayan magariba suke son ayi.
Kamar yadda Kubra ta kwatanta kofar wani babban shago suka tsaya mai suna *J.J.Maji Palace*.
Wurin yaji kaya na gani na fada masu kyau sai tsada. Nan ma dai ruwan ido Awaisu yake yi kowacce ya taba sai yaga tafi dayar kyau. Burinsa Son So ta fito sosai ta kece raini. Yarinyar shagon ya tambaya ko akwai irin wadda amarya zata saka amma fa ba fara ba ta auren nasara. Cewa tayi tana zuwa ta shiga wata kofa sai gata sun fito da wata kosasshiyar mata. Kiba gareta sosai tana tafiya da kyar ta baza zobba a kusan duka yatsunta da awarwaro. Da fara'a ta tarbe su.
"Suna na Hajiya Fattu. Ku biyoni akwai wasu rigunan a wannan dakin irin wanda kuke bukata"
Suna shiga idon Awaisu ya sauka akan wata doguwar riga golden mai matukar kyau anyi mata ado da yellow din duwatsu marasa turuwa. Doguwa ce da dogon hannu kuma bata cika ado ba amma kana ganinta zaka ji kamar ka dauka. Dariya Fattu tayi don tasan rigar yake so saboda kyaunta. Ganin yadda yake taba jikin rigar a ranta tasan dole ya dauka tuni ta kara dubu goma akan kudinta.
Bai musa ba Nuru yana rike masa hannu ya dauko rigar yace yana bukatar mahadi. Fattu ta dauko masa wani mayafi mai wasu irin dutsu mai kyau shime light yellow ta kawo yace saura takalma da jaka. Komai ta hada masa ya bata kati da kanta ta zura a POS ganin manyan costumers ne gashi harda su sarka da abin hannu duka ya saya.
"Yallabai naji kuna zancen taro gobe hala mai saka kayan gobe zatayi amfani dasu tunda kun ce na amarya ne?"
Nuru yace "ikon Allah ke dai ki cire kudinki mana ki bamu mu tafi"
Ta sake dariya "ai naji dadin ciniki ne shine zan fada muku ina kwalliyar amare idan kuna so. Wallahi ba kowa nake yiwa ba ma saboda yanayin aikina."
Awaisu ya dan sake kallonta. Lebenta wani irin janbaki ne yayi dau shi ba green ba shi ba shudi ba ga su eye shadow komai ya fito rambajau. Baya fata ko kadan Rumanansa tayi ado irin wannan. Kula tayi da yadda yake kallonta tayi yar dariya
"Don't mind me haka nake tawa kwalliyar amma ka bani dama ka ga yadda zan