Showing 12001 words to 15000 words out of 112099 words

Chapter 5 - KASHE FITILA Book Complete by Batul Mamman.txt

23 Jun 2024

13998

zaune Maamu tana fada mata abin da zata ce a wayar.
*****


Zaune take tana cike wasu takardu taji waya. Tana dubawa ta gane numbar Maamu ce. Tsorata tayi ta kasa dauka sai a karo na biyar ta dake zuciyarta. Muryar Rumana taji ta gaisheta sannan tace


"Maamu ce tace na kira wai yau lafiya kuwa. Ko wani abin ya faru?"


"Kice mata babu komai nima na kusa tasowa"


"Su Haris basu dawo ba har yanzu sannan ni da Maamu bamu sami abinci ba. Shine tace ko zaki fadi inda key din store yake"


Maamu daga gefe tana 'yar dariya tace "yau zanyi musu girkinmu don dadi duk wanda yaci sai ya manta hula da takalmi"


Itama Rumana duk da yunwar da take ji jiki babu karfi dariyar tayi tana fassarawa Gimbi abin da Maamu ta fada.


Shiru tayi ta kasa bata amsa daga baya ta fara cewa "hello, Rumana bana jinki."


Daga haka ta kashe wayar ta cigaba da harhada kayanta a jaka. Tunaninta daya kada aikin ya baci ta sami matsala da Awaisu. Ta san yadda yake son Maamu da su Baaba. Tsoro ne sosai ya kama ta.


Lokacin da ta fito shida saura ta fake da cewa dreban ya sha fama da rigimar yara ta sallame shi. Duk sun bata motar da abincin da ta bayar da kudi aka siyo musu a wani gidan abinci mai tsada na kusa da bankin.


Gidan Anti Bebi ta wuce ta bar yaran a mota da gargadin kada wanda ya fito. Tare da maigidanta ta sameta ta gaisheshi yana ta bin ta da ido har suka shige daki ita da Anti Bebin.


"Me ya faru na ganki da yamman nan ko waya babu?"


Muryarta har rawa take yi tace "tsoro nake ji kada Awaisu ya sakeni wallahi. Yau baki ga abincin da na bar musu ba. Ina tsamani bata ci ba"


Yadda tayi a gidan tun safe zuwa wayarsu da Rumana ta sanar da Anti Bebi.


"Mtswww, ni kin bani haushi ma. Matsoraci baya zama gwani Gimbiya. Idan baki shafawa idonki toka ba a yadda nake ganin take takenta tunda har ta fara tambayar mukullin store saura tasa yayi miki kishiya ko ta rabaku gabadaya"


Gimbi ta kara shiga tashin hankali "wallahi bazata yiwu ba. Awaisu da taimakon Alhajinmu ya zama mutum. Duk wannan aikin da nake yi da wahalar da nake sha dominsa ne. Babu wadda ta isa tazo mu zauna taci arzikin da bata san samuwarsa ba"


Anti Bebi tayi dariya "yanzu kike magana, to kada ki damu idan kinje gida ta fadawa Awaisu kinga alamun zaiyi fada. Meye amfanin Laminde? Kafin ya fara fadan kiyi kanta da duka idan ya kama kina kuka kina cewa tana son kashe miki aure zata wulakanta miki uwarmiji. Daga nan ki dauki laifin duka ki nana mata ki sabule kanki ki koreta. Idan kin tashi neman wata mai aikim kizo zan hadaki da mai kawosu daga kauye"


Sai yanzu Gimbi ta sami nutsuwa da kwanciyar hankali. Harda murmushinta ta fita suka koma gida.
*****


Maamu ta kai wuya wurin bacin rai jira take yi su dawo. Bazata bari wannan abin yayi nisa ba gara Awaisu ya taka burki idan ma bisa kuskure ne a tunaninta ya kamata da wayar ta katse lokacin da suke magana da Rumana ta sake kira. Shirun da suka ji har Rumana ta sake kira wayar a kashe shine ya bata mata rai.


Gimbi na shiga gida ta tarar da Awaisu shima shigarsa kenan. Yana son tambayarta inda ta tsaya kuma ga yara da kayansu tun na boko ya ga Maamu ta fito. Kana ganinta yau babu wannan fara'ar wadda da wuya ka ga fuskarta a hade. Jikinta gabadaya babu kwari saboda yini da yunwa. Ruwa kawai suke sha ita da Rumana.


"Yanzu nake shirin shigowa dakin naki" cewar Awaisu yana matsawa kusa da ita.


"Na hutar da kai. Dama nace ko kun manta damu a gidan ne yau baku ajiye mana abinci ba"


Dayake da yarensu take magana Gimbi duk ta tsargu.


Kallon Gimbi yayi "garin yaya kika fita ba'a ajiyewa Maamu abinci ba? Ina Laminde?"


Hantar cikin Gimbi ta kada ta fara in'inar da bata san tana da ita ba "uhmm-dama-da-fate-eh faten doya aka yi mata kafin-kafin mu fita"


Maamu sarai ta fahimceta sai kawai ta koma dakin ta dauko langar faten doya. A harzuke take sosai ta bude a gaban Awaisu, har wani ruwa ruwa ta fara ga baki da tayi sosai
"Wannan abincin zamu ci Awaisu?"


Yadda tayi maganar muryarta ta karaya domin kuka ne yake barazanar kwace mata saboda takaici. Ko aiki take yi a gidan aka bata wannan abincin tabbas anso cin mutumcinta ne.


Dagowa yayi da zafinsa zaiyiwa Gimbi fada. A lokacin ba karamin tsoro ne fal a zuciyarta ba sai ta tuna hudubar Anti Bebi ta daure fuska. Kamar anyi ruwa an dauke haka ya hadiye fushinsa ya koma yana kallon Maamu.


"Ai kuwa da gani faten nan zaiyi dadi. Gimbi ko zaki dumama mata a microwave yadda zata ji dadin ci"


Duk da tayi mamakin saurin sauyawarsa amma saboda tana son tabbatar da aikin Wangesi tace "to my dear, dan tambayar min idan tana son manshanu sai na saka mata ma. Kasan Laminde gwanar girki ce"


Haka kuwa ya tambayi Maamu hankali kwance. Kasa bashi amsa tayi saboda a take a lokacin wani irin abu taji ya soki zuciyarta. Tana kallo Gimbi ta wuce kitchen da langar wai zata dumama ta dawo mata dashi. Awaisu kuwa yana murmushi yace mata zaije ya watsa ruwa yazo suyi hira.


Bayan tafiyarsa Maamu ji tayi jiri zai kwasheta ba don yunwa ba sai don yadda zuciyarta ta karaya da halin da ta tsinci kanta daga zuwa gidan tilon danta abin alfaharinta.
[4:24PM, 2/18/2018] ‪+234 803 369 4017‬: *KASHE FITILA*💡12


*Batul Mamman*💖






Da kyar Maamu ta kai kanta daki inda Rumana take kwance duk sauran kuzarinta ya kare. Tana turo kofar Laminde wadda babu wanda ya lura tana tsaye a bakin kofar shigowa gidan ta dafe kirji. Duk abin da akayi a kan idonta ne. Wannan abu ya kara daure mata kai har ta rasa da me za ta kwatanta shi. Ko ma menene akwai wani abu da uwar dakinta take yi game da surukarta.


Tun safe da suka fita Gimbi ta aiketa kasuwa. Daga can ta ce ta wuce wurin kanwarta da aka kawosu aiki Abuja tare. Haka ta tafi cike da mamaki musamman da ta fada mata kada ta koma sai ta kirata a waya. Wayar da ba'ayi mata ba sai da ta baro gidan Anti Bebi.


Gimbi ta gani ta dawo da langa tana tiriri ta dorata akan wani tray na silver kasanta kuwa duk yayi baki.


"Yaushe kika dawo ban sani ba?"


"Shigowata kenan"


"To aje ayi min wanke wanke"


Laminde tace to ta juya kitchen.
*****


Bayan fitar Gimbi Maamu ko bude abincin bata yi ba ta dauka ta kai kitchen. Lokacin Rumana bata farka daga baccin yunwar da take yi ba. Tana shiga ta ga Laminde ta bude wani flask da shinkafa a ciki tana shirin zubarwa. Abincin Awaisu ne na office ko rabi bai ci ba. Maamu ta rasa yadda zata kwatantawa Laminde ta bata abincin. Can dai ta nuna abincin tace Rumana.


"Rumana zaki bawa?"


Maamu tace eh. Laminde ta mika mata flask din. Karba tayi ta koma daki ta tashi Rumana. Duk da tana so haka ta bar mata. Ita kuwa tana ganin abincin haka ta soma ci babu wanke hannu bare kuskure baki. Maamu na gefe sai hawaye take sharewa batare da ta bari Rumanan ta gani ba. Yarinyar da gidansu ba'a san yunwa ba itace yau ta bawa ragowa. Da Harisu zai ganta yanzu bata san inda zata saka kanta ba. Rumana ta cinye abincin tas ta sude flask din kamar almajiri yaje bara an bashi lomar tuwo uku.


Tana gamawa sai amai tun a dakin ta fara Maamu ta kama ta zuwa bandaki. Tana yi tana kuka domin tun tana fitar da abinci sai da ya koma yawu kawai take zubarwa idan ya yunkuro. Haka Maamu ta gyara wurin tace Rumana ta kwanta. Babu bata lokaci wani baccin ya dauketa baki a bude. A daren Maamu tayi kuka har kanta ya rinka ciwo. A kusa da Rumana tayi bacci.
*****


Bayan asuba Gimbi ta shiga dakin ta tarar da Maamu akan abin sallah ita kuma Rumana tana shafa mai. A ladabce ta gaishe da Maamu kamar bata yi musu komai ba.


"Rumana jiya kika bar kanwarki ta kwana ita kadai. Ko kinfi son kwana a nan ne?"


Kai kawai ta gyada don ta fara tsoron Gimbi yanzu.


Murmushi tayi a ranta tace tafi nono fari.


"To ai babu komai hakan ma yafi. Zaki rinka debewa Maamu kewa"


Daga haka ta fice zuciyarta cike da nishadi. Yanzu zata gyarawa Daula dakin yadda ta tsara tun farko.


Kitchen ta wuce ta samu Laminde har ta gama farfesun kayan cikin da ta sakata. Ta zubawa mijinta da yaranta sannan ta dauko langar Maamu ta soma zubawa.


Laminde tana goge gefen gas cooker din ta saki tsumman tana kallon ikon Allah. Hanji ne Gimbi take ta za6ewa tana zubawa ya kusa rabin langar. Jikinsa duk kitse yayi wani narai narai babu kyaun gani.


Kasa hakuri Laminde tayi "Hajiya nace ko kin manta wannan langar kince ta Maamu ce"


Fuska a hade saboda bata son bada kofar tsawaita zancen tace ban fahimceki ba.


"Na ga kina ta zuba hanji ne a ciki."


"Hanjin ba nama bane? Kinga ki kiyayeni da shisshigi wallahi. Kin saka min ido ni da gidana sai nayi miki bayanin abin da nake yi. To binciken likitoci ya tabbatar da cewa cin dafaffen hanji yana matukar taimakawa tsofaffi da kara musu lafiya"


Awaisu yana daga falo suna jiran ta kawo breakfast shi da yara ya jiyo muryarta tana fada. Kitchen din ya shiga "Me ya faru kuma kike fada da safen nan?"


Rufe langar tayi tace "kyaleni da ita, ina jin ta fara gajiya ne da aikin"
Laminde sai faman bada hakuri take yi.
Ya so jin abin da ya hadasu sai dai shima bai ga fuskar tambaya ba. Yana kallo ta dauki langar tare da bread wanda ta yanka gida hudu ta dauki bari daya sai tea a kofi ta kaiwa Maamu da kanta.


Bayan fitarta Rumana ta gama shirin makaranta. Duk da bata da kwari sosai amma a ganinta fitar zata fiye mata. Kafin ta fita Maamu ta mika mata dari biyu cikin kudin da Harisu ya bata wanda a lokacin tayi ta cewa ya barshi. Ashe zai musu rana.


"Ki sayi abinci a makaranta kici kinji ko. Zan yiwa baban naku magana sai ya rinka baki kudi da safe ko kuma a baki abinci kema"


Rumana tayi mata godiya ta fito falo. Suna zaune dukkansu suna cin abinci suna wasa da yaransu. Awaisu ta gaisar yaran suna tambayarta ina taje jiya basu ganta ba. Murmushi kawai take yi.


"Zauna ki hada tea kuyi sauri kada ku makara" inji Awaisu.


Gimbi ta dan juya ido "har ka manta na fada maka za ta rinka tafiya da kanta. Rumana shiga wurin Laminde kiyi brealfast kinji."


"Me yasa bazata ci a nan ba?" Awaisu ya tambayeta harda dan daga murya kamar zaiyi fadan gaske.


"Bana so Laminde ta ga kamar muna wareta ne. Shiyasa nace su ci tare. Banyi laifi ba ko?" Ta rausayar da kai tana masa fari.


Shiru yayi yana ta auna maganar. Har ransa baiji dadi ba kuma fada yaso yi sai dai yana bude baki yaji bazai iya ba.


"Bakiyi komai ba. Kuyi sauri bana so kowa ya makara"


Daga haka kowa ya karasa cin abincinsa suka tashi zasu tafi. Rumana itama ta fito bayan ta gama cin nata hanjin da bread. Sai tea wanda tana sane ta tsula masa ruwa don ya kara yawa ko zata dade bata ji yunwa ba.


Suna fita itama ta fito ta tafi. Yau bata hadu da su Yusra ba sai a aji. Da break ta hada da kudin da Maamu ta bata da na wurin Umman Yusra ta sayi fanke na dari da meat pie 'yan hamsin guda hudu.


Yusra ta rinka kallonta, ina zata kai wannan abincin ita kadai. Meatpie daya taci da fanke biyu ta saka sauran a jaka zata kaiwa Maamu.
*****


Da farko Maamu kin cin abincin tayi sai daga baya da yunwa ta cigaba da cinta ta dauki kofin tea din ta shanye. Ta bude langa sai ga hanji da romon ya daskare ya hade jikinsa. Idan jiya tana kokonto yau ta tabbatar Gimbi da gaske wulakanta ta take sonyi. Tasan karshenta gidan ne bata so ta zauna musu. To amma komai wahala zata jure. Ta cinye rayuwarta a alfarmar gidan Harisu da Baaba Hure. Yanzu kuwa da kunya ta koma. Idan ta koma din ma ace nata dan ya kasa riketa. Shawara ta yankewa zuciyarta idan ya dawo zata ji ta bakinsa game da wannan gashin kuman da aka fara yi musu. Ko aikatau tazo yi a gidan a tunaninta bata cancanci a wulakanta ta ba. Sai yanzu take kara godewa Allah da aka ki yarda su zo da Baaba. Da bata san da idon da zata kalleta ba don kunya. Haka nan ta rinka cin hanjin tana hawaye.


*****
Da rana Laminde bata kawo abinci ba zuwa da tayi suyi hira. Duk da ba komai take fahimta a zancen ba amma tana jindadin yadda take mutumtata.


Rumana tana dawowa ta dauko abincin jakarta suka ci ita da Maamu. Wannan abu ya tsayawa Maamu a rai sosai. Bakinciki yasa ko fanken hannunta bata gama ci ba ta ajiye. Sai karfe shida su Gimbi suka dawo. Yau ma yaran basu je islamiyya ba. A lokacin ta bude store ta mikowa Laminde semovita tace ta dora tuwo.


Cikin sauri tayi ta gama domin itama ta horu da yunwa. Gimbi da kanta ta raba abincin ta zubawa Maamu tuwo da miya a hade. Rumana itama a plate aka hada mata ta ajiye a kitchen.


A haka suka kwashi sati biyu tana musu kisan mummuke sannan tana auna karfin mulkinta akan Awaisu. Da ta tabbatar aiki yayi kyau ne ta kira Anti Bebi akan tana son na mallaka domin tun a haka tana ganin yadda baya iya yi mata musu ko kadan.
[4:28PM, 2/18/2018] ‪+234 803 369 4017‬: *KASHE FITILA*💡13


*Batul Mamman*💖






Anti Bebi ta rinka yiwa Gimbi dariya
" 'yar gari waye ya fada miki haka nan mata suke zaune, duk wadda tace miki bata dan lekawa wurin neman taimako domin samun zaman lafiya a gidan aurenta karya take yi. Abin da naso uwarki ta fahimta kenan sai ta rinka gayamin maganganu"


Gimbi na jin haka ta daure fuska


"nifa kinga abin da yake hadani dake kenan, akan zagin Mama fa sai naci..." shiru tayi sanin cewa yanzu sirrinta a tafin hannun Anti Bebin yake.


"Karasa mana mara mutumci. Ni zaki zaga Gimbiya. Lallai wuyanki yayi kauri. Yadda na kaiki wurin Wangesi akan mijinki kinsan ba karamin aikina bane na koma akanki ko"


Gaban Gimbi ya fadi a tsorace ta soma bata hakuri. Sai dai tana cikin magana taji ta katse kiran. Da ta sake kira kuwa a kashe taji ta. Yanzu ko da wuka a wuyanta bazata iya kwatanta hanyar zuwa wurin Wangesi na tsangaya ba. Kuma ba karamin aikin Anti Bebi bane taje tasa ayi mata wani mugun abun. A da bata gama sanin wacece ita ba sosai sai yanzu da suke tare. Ban da mijinta da ta shanye hatta mahaifiyarsu wato kakarsu Gimbi bata taba yi mata musu. Duk yadda tace haka ake bawa su Mama umarni kuma dole suyi idan ba haka ba ta nuna musu fushinta sosai. Kuma bata taba yi mata fadan abubuwan da take yi da aure aure ba.


A ranar ta bita gida tayi ta bata hakuri daga karshe suka daidaita.
*****


Watanni biyu kenan da shigar su Maamu cikin kunci a gidan Awaisu. 'Yar hirar da yake zuwa suyi ma sai yayi kwana biyu bata sa shi a ido ba. Ranar da ya zo kuma zai sake yayi ta bata labarai batare da kula ko tambayarta idan tana da damuwa ba. Ya riga ya sakarwa Gimbi komai da ya shafi Maamu da Rumana. Hatta kudin makaranta ko abinci da ta nemi a rinka bawa Rumana cewa yayi zai fadawa Gimbi. Sau tari ya kan tsinci kansa da tunani akan rashin dacewar abin da yake yi mata. Amma ko a bayan idon Gimbi bai taba kuskuren canjawa zuwa Awaisun Harisu da aka sani ba a gaban Maamu.


Yau Rumana ta dawo da yunwa saboda dan kudin hannun Maamu tuni ya kare. Abincin rana kuwa dama an soke shi a hankali. Da safe take sawa Laminde tayi musu girki wanda take tafiya wurin aiki dashi a zubawa yaranta. Da rana tace ba zama suke yi ba Laminde ta huta. Sai biyar zuwa shida idan sun dawo a dora na dare. Kana ganinsu har sun fara rama. Idan sunyi waya da Harisu sai tayi ta kokarin danne damuwarta. A matsayinta na uwa ga Awaisu duk yadda suke da su Baaba Hure akwai abin da dole kaji kunyar fadawa duniya. Yau da wata aka yiwa haka da sauki sai ta iya shiga ciki domin tsawatarwa. Amma ita mahaifiyarsa da kanta wurin wa kuma zata kai kara.


Suna zaman jiran abincin dare a dakin Mu'allim ya shigo yana buga ball. Da karfinsa ya mako ta bata fada ko'ina ba sai fuskar Maamu. Rumana ta tashi da sauri ta kwada masa mari. Dama tuni Gimbi tasa yaran suka dena shiga dakin wai bata so suna damun Maamu.


Jin zafin marin yasa ya kwalla kara. Sai ga Gimbi ta shigo a guje ta dauke shi tana tambayar me aka yi masa. Yana rike da kumatu ya fada mata Rumana ce ta mare shi. Batare da neman ba'asi ba ta sauke shi a gaban Maamu tace ya rama.


Rumana ta zaro idanu "Mummy kinga fa wannan katuwar ball din ya bugawa Maamu."


"Shine zaki mare shi saboda mugunta bayan kinsan ba da gangan bane. Ki bari ya rama ko kuma ni na rama masa"


Rumana ta kalli Maamu tana hawaye saboda irin wannan cin zarafi da akeyi musu. Idan da kara ko cin zalinsa akayi tunda Maamu tana wurin bai kamata tayi magana ba.


"Gara ke ki rama masa akan na bari kanin bayana ya mareni" ta fada tana kuka


Motsin tahowar Awaisu Gimbi taji ta rage sautin muryarta
"Bazaki bari ya rama ba?"




"Wallahi bai isa ya mareni ba" fushi da bacin ran da take boyewa ne ya fito yau. Ita bata ki ace ta tattara ta koma gida ba.


Awaisu ya shigo rai a bace ganin yadda take kallon Gimbi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login