Showing 48001 words to 51000 words out of 112099 words
Chapter 17 - KASHE FITILA Book Complete by Batul Mamman.txt
yake ba domin ita ce tushen zaman lafiyar gidan.
*****
Kafin tara na safe Gimbi ta gama hada kayanta da na yara duka. Makaramtarsu tayi niyar fara zuwa sanarwa zasuyi tafiya.
Suna zaman jiran dreban ya iso Ovi ta kirata bayan sun sake shawara da Rita.
"Munyi magana da Boka yace kada ki kuskura kije garin nan sai yayi kwana biyar da rabi bai dawo ba. To daga daidai wannan lokacin sai ki hau hanya ki bi bayansa saboda sharrin makiya daga can garin nasu"
Gimbi ta danyi jim tana tunani. Gashi ance kada ta kira yanzu kuma kada taje. Anya bazata janyowa kanta matsala ba kuwa? Shirunta yasa Ovi gane me take tunani tayi saurin cewa
"Kada ki damu yace aiki zaiyi akan mijin naki da babat tasa yadda zasu tsani juna. Zuwanki yanzu zai bata masa aikin ne"
Sai a lokacin hankalinta ya kwanta tayiwa Ovi godiya sukayi sallama. Ovi ta kira Rita tace tayi maza taje ta fadawa bokan yadda sukayi da Gimbi koda zata zo kada ya karyatasu.
******
A rana ta biyar da tafiyar Awaisu Gimbi ta shirya tahowa Fika.
A can kuma Maamu tana ta samun sauki don har an mayar da ita amenity. Yanzu har hira anayi da ita kuma ta soma cikowa. Awaisu shanu biyu ya saya yasa aka yanka kullum ana sarrafawa a kawo mata. Suma jamaar gidan sun sami nasu rabon. Kaji da kayan lambu da na marmari kuwa wani na tarar da wani. Barin kudi yake yi kamar bai san ciwonsu ba. Burinsa kawai Maamu ta warke ya cigaba da kyatata mata.
Yau bayan ya dawo daga sallar azahar ya tarar da Dr.Yana a dakin. Wajen dakin ya biyota bayan ta gama duba Maamu da barkwancinta yace yana son fitar da ita waje yana bukatar takardun gwaje gwajensu domin tafiya dasu.
Dan daure fuska tayi "a haka kuke sawa muji babu dadi. Yanzu duk kokarin da muke yi kuma ciwon bai gagaremu ba shine zaka ce zaka fitar da ita?"
"Baki fahimceni bane, ina so ta sami kulaw ne sosai saboda wasu dalilai nawa"
Dariya tayi ganin yadda yayi da fuska da gaske yake.
"To don Allah ka bari ta kara samun sauki sannan ko fitar zakayi da ita sai kayi."
Godiya yayi mata ya koma cikin dakin. Rumana wadda har yanzu bata kula shi tayi saurin mikewa zata fita.
Girgiza kai yayi ganin da gaske yarinyar nan fushi take yi dashi "Rumana ina zuwa?"
Kamar yayi magana da dutse ko girmansa bata gani ba tayi hanyar kofa. Ai kuwa manyan dake dakin suka hauta da fada ta fita a fisace tana hawaye. Tasan har abada bazata taba manta rayuwar gidan Awaisu ba. Idan ta kalli Maamu haushin kanta na barin gidan ita kadai take yi da kuma na Awaisu da ya gagara kula da ita.
Maamu na kallonta ta kalli yadda ya bita da kallo wai itama ta zama 'yan mata ta iya fushi. Daga inda take zaune ana bata abinci tace ya bi bayanta ya rarrasheta.
Anti Suwaiba tace ya rarrasheta ko ya zane ta dai "yarinya taki sakawa ranta salama kullum fushi"
Maamu ta sake kallonsa "idan ka taba min ita zamu sa kafar wando daya da kai da yayar taka mai bada shawarar"
Anti Suwaiba na dariya ya fita yana cewa yanzu duk duniya ai babu da mai ladabinsa.
Ya dan wahala wurin nemanta kafin ya hangota can wurin ajiye motoci a durkushe tana share hawaye. Wurin ya karasa tana ganinsa ta kuma tashi sai dai kafin ta fita ya rufe hanyar. Dama tsakanin wasu motoci biyu ta zauna a wani dan tudu wanda bayansa fence ce babu hanyar fita. A tsiwace tace "zan wuce"
Yana kada kai yace "Rumana..."
Bai kare magana ba ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya. Idan da zata tona abubuwan da Maamu ta rinka dannewa a zuciyarta a zamansu a gidansa bata jin ko ruwa zai kara sha da dadin rai. Gabadaya komai ya sire mata har tsoro take ji kada itama ta girma duk yadda tasan Awaisu yana son Maamu ya koma haka itama ta zama hakan.
Tausayi ta bashi sosai ya mika hannu zai rungumeta sai kuma ya fasa. Wannan ba 'yar karamar Rumanan nan bace. Shi bai san ma yana ina yarinya yar shekara goma sha shida ta zama 'yan mata haka ba.
Da hannunsa ya nuna kansa ya dan rage murya "nine ko? Kiyi hakuri Umm Ruman Uncle Awaisunki bazai kara bari abin da ya wuce ya kuma faruwa ba"
Baki ta dan tsuke "ni ba Uncle Awaisuna bane"
"Har kin manta haka kike fada a gida kice naki ne ke kadai? Muje a tambayi su Baaba idan mun koma gida "
"To na fasa ba nawa bane"
Kwaikwayonta ya sami kansa da yi yace harda yin alamun kuka yace "don Allah kice naki ne ko na fadawa Maamu"
Dariya yaso bata sai ta wani gimtse fuska wanda ya lura da hakan. Inda ta baro yace tazo su zauna ta fada masa duk abin da ke ranta ko zata sami sauki.
Dr. Yana da take tsaye a jikin motar Mujahid tun dazu ta sauke ajiyar zuciya ta shiga. Kallonta yayi yace sannu da shanya ta dan kwanto a jikinsa tana fada masa wani kyakkyawan gamo tayi wanda dole ma ta ga faruwarsa.
[15/08, 17:45] +234 803 272 5896: *KASHE FITILA*💡31
*Batul Mamman*💖
A hankali take taku kamar ba ita bace mai aiki da kuzari a asibiti. Tana taka kafarta a kofar falo taji ana kokarin kinkimarta. Dariya ce ta subuce mata domin da kyar ya iya rabata da kasa kafin ya ajiyeta yana maida numfashi da kyar bayan ya sanya hannuwansa duka biyu ya rike gwiwoyinsa a duke.
"Wai fa irin dan surprise dinnan zanyi miki na dagaki sama na juya ina miki wakar i love you. Gaskiya nauyi ne dake matar nan..."
Tana dariya tace "kamar shari'a ko"
Sai kuma ta dan bata rai "yanzu ni irin daukan da maza ke yiwa matansu sai dai na gani a tv" zama tayi harda tagumi ita a dole bata ji dadi ba.
Kusa da ita ya zauna tare da sakala hannu a kafadarta "banda abinki wannan daukan da kike gani duk buge ne fa. Indai matar ba bugun fulawa bace katuwa a ido shafal a hannu to sai dai idan mijin kakkarfa ne jikan Antaru"
Dariya sosai Yana da Mujahid suke yi ta mike "bari naje na gaishe da Hajiya sai na dawo ka fada min nice bugun fulawar ko kuma kaine rago baka cikin jikokin Antaru"
Kamar yace ta dawo yadda suke nishadin nan haka yaji yana kallo ta fita ta zagaya bayan gidan bangaren mahaifiyarsa. Ajiyar zuciya yayi ya gyara kwanciya akan doguwar kujerar falon yana jiranta.
Da sallama ta shiga wata mata da zata girmeta sosai tana durkushe gaban Hajiya tana kwaba lalle a wata roba ta amsa. Hajiya kuwa dauke kai tayi ta cigaba da sakace hakorinta.
Yana ta durkusa ta gaisheta ta kara kawar da kanta gefe. Mai kwabin lallen wadda musamman yayar Mujahid ta daukota tana biyanta ta rinka taya Hajiya zama idan Yana ta tafi aiki tace Hajiya ana gaisheki .
Da ido daya ta kalli Yana ta tabe baki "anje an gama gantali da sunan aikin an dawo? To sannu da zuwa sarauniyar masu gida"
Murmushi tayi domin ta saba da halin surikar tata wadda ta kasance yaya ta uwa daya uba daya ga mahaifiyarta.
"Hajiya yaya gida da sanyi sanyin nan?"
Kin amsawa tayi sai ta janyo kafarta daga bangaren Laraba mai aikin nata ta dorawa Yana akan cinya saboda a kusa da ita ta durkusa.
"Kinga cire mayafin nan zakiyi ki saka min lalle."
Laraba tayi saurin janyo robar daga hannun Hajiya mai shirin turawa Yana
"Haba Hajiya da ganinta yanzu ta dawo ki bari nayi miki ita taje ta dan huta"
Wata uwar harara Hajiyan ta doka mata sannan ta fizge robar lallen "aikinta ne dama ba don ta sawa zuciya kwadayi ta gagara zama tayi bautar aure ba me zaisa ma a daukoki. Ga gida har gida ana neman shekara biyu taje tana bankar tarkacensu na asibiti nasara ya hore musu kunne anki haifa min jikoki."
Yana kanta a kasa ta soma shafa mata lallen a kafa idanunta fal hawaye taji Hajiyan ta cigaba da fada
"Ke nifa da ace ba Mujahid bane kadai namiji babu abin da zai kawoni gidansa. Yo gidane banda yahudanci da nasaranci babu abin da ake yi. Ni dai hadin zumunci baiyi min rana ba. Da bare ya aura mai halin nan da tuni tasan inda dare yayi mata. Yanzu kuwa ko me nayi sai ace babu kara babu zumunci. Ko ita uwar taki Yakaka ai tasan ina kokari"
Cikin siririyar murya tace "Hajiya kiyi hakuri"
Tsaki tayi tace ita dai a saka mata lalle kuma ta rinka yi daki daki kada wani wurin yafi wani kamawa.
Mujahid da yake daga wajen dakin yana jinsu ya koma bangarensu zuciya babu dadi. Samun mace irin Yana sai an tona. Matar da bata da burin da ya wuce ta kyautatawa mutane. Idan ya nuna rashin jindadinsa game da yadda Hajiya take yi mata ranar kwana take yi tana fushi dashi. A cewarta bazata taba jindadin rayuwa ba idan ta zama silar da mijinta yayi wasa da aljannarsa dalilin kin kyautatawa mahaifiya.
Zaman jiranta yayi sai bayan awa biyu ta dawo. Tana shigowa dundu tayi masa a baya tana fara'a kamar ba ita ba. Wanka suka yi sannan suka ci abincin da tayi musu kafin ta fita aiki. Suna gamawa aka kira magariba ya fita sallah ita kuma bayan ta idar ta gaggauta dora tuwo wanda ta gama kafin isha. Da ya dawo ne suna hira take bashi labarin Maamu da taji a wurin Rumana
"Yaya ba don cin fuska ba nake baka labarin nan amma gaskiya wasu matan basu iya samun wuri ba. Yanzu ita Allah Ya bata wadda zasuyi zaman fahimta ga zuria amma ta daukowa kanta balai da hannunta"
Hannuwanta ya rike tare da kokarin hada ido da ita "Kanwata don Allah kada naji kin shiga wannan case din. Nasan halinki na tarar aradu da ka. Amma har yau ban manta mutumin da kika taimaki matarsa akaje alkali ya kashe auren saboda dukan da yake mata. Kinfi sati ba kya fita daga gidan nan saboda fakonki da ya rinka yi. Ni kaina a tsorace na rinka fita kada a sabauta ni" ya kare da dariya
Jinsa kawai take yi amma ko kadan bata tsammanin yadda labarin nan ya shigeta zata dauke kai. Ita fa salihancinta daya ne a rayuwa gaban uwar miji. Daga nan kuwa bata ki a hau sama a rikito ba indai zata kwatarwa mutun yanci.
Yadda ya kula tana juya kai yasan maganar bata shigarta. Girgiza kai yayi don yasan aiki ya same shi.
*****
A gaggauce Awaisu yake ta shiri ya watso kaya daga wardrobe yana cusawa a karamin akwati. Takun Gimbi yaji gabansa ya fadi sai dai ya dake ya cigaba da zubawa amma a hankali. Kallonsa tayi tare da akwatin
"Indai kayan tafiyarka Lagos ne na hada maka tun jiya"
In'ina ya soma sannan da kyar ya iya saita kansa yace "nasan wancan kayan duka suits kika zuba. Ni kuma yanzu Fika zan tafi na fasa zuwa Lagos din."
Duk da ta razana ta daure tace "bangane ba"
"Ashe tun daren jiya Yaya Harisu ke kirana Maamu tana kwance a asibiti. Bansan yadda akayi wayar ta koma silent ba sai da safe naga text dinsa"
Gimbi ta hade girar sama da ta kasa. Dama ita tayi silencing wayar da ta ga Harisu yana kira "yanzu don sun rainaka shine tun tafiyarsu baa nemeka ba sai yau zasu ce Maamu babu lafiya. Anya ba wani abu suke kullawa ba? Kayi tafiyarka Lagos din kawai Abban Haris ina zaton maganar da Amir ya fada min bayan dawowarsu daga Fika kwanakin baya gaskiya ne"
"Me ya fada miki?" Ya tambaya yana kokarin zuge karamin akwatin.
Shiru Gimbi tayi taki magana. Awaisu ya sake tambayarta sai kawai ta fashe masa da kuka. Hankalinsa ba karamin tashi yayi ba domin kuka take mai cin rai. Duk yadda zatayi kada ya tafi sai tayi domin gudun bacin aikin boka. Zama yayi yana ta rarrashinta har zuwa lokacin da idea tazo mata sannan ta fara magana murya a dashe.
"Kasan tun bayan dawowar Maamu garin nan ka rage zuwa Fika."
Kansa ya gyada yana cigaba da kallonta.
"Dasu Amir suka dawo shine yace min wai yaji Kawu Harisu da Baaba suna cewa yanzu ka rage basu kudi tunda Maamu tana nan. Wai zasu san yadda zasuyi ta koma Fika dole ka rinka zuwa"
Jin haka ya mike da sauri rai a bace "bari naje na sami Amir din naji gaskiyar zancen nan"
Kafin ya kai kofa Gimbi ta riko shi tana wasu hawayen "kada ka tambaye shi saboda ranar da ya fada min baka ga irin dukan da nayi masa ba nace bana son gulma. Nace masa kuma yayi min alkawarin bazai sake zancen ba"
Hannunwanta ya zame daga jikinsa ya sake nufar kofa "ai ba wani zai fadawa ba sai ni."
Har ta fara tsorata tace "amma Abban Haris baka ganin bata tarbiya ne hakan. Ni nace yayi alkawarin barin zancen kai kuma zaka sa ya fada. Kaga zai tashi da rashin sanin girman alkawari"
Har zuciyarsa yasan ko kadan bai gamsu ba amma kuma zuciyarsa tana ingiza shi akan ya hakura. Wani irin bacin rai ya rinka ji ya juya a fusace ya dauko jakar da ta zuba masa kayan zuwa Lagos ya fita. Wani asirtaccen murmushi tayi a fuskarta kuwa tsantsar damuwa ce kawai take nunawa. Har waje ta biyo shi tana bashi hakuri akan kada ya dauki zafi da su Harisu 'yan uwansa ne. Shi dai bai tanka mata ba ya shige bayan mota dreba ya ja.
Dakinsa ta koma ta daka tsalle tana murna. Su Harisu basu isa su dagula mata lissafi ba. Tasan duk ranar da hankalin Awaisu ya dawo jikinsa akwai rikici tsakanisu. To amma ko kadan bazata lamunce uwar miji ta rinka juya mata miji ta zama borar karfi da yaji ba. Aure tayi don taji dadi bata fatan irin zaman da wasu suke yi iyayen miji su mayar dasu tsumman goge goge. Mace ta kasa sakewa a gidanta saboda suruka me kenan akayi. Gara da tayiwa tufkar hanci taci karenta babu babbaka.
Awaisu kuwa tunda suka fita zuciyarsa take masa wasu sake saken banza. Har ayyana masa takeyi Harisu ya killace Maamu ne kawai don yaci kudinsa. Abin haushin shine duk nemansa saboda su da iyalinsa ne. Me ya ragesu dashi da zasuyi masa haka? Numbar Maamu yayi niyyar kira sai wata zuciyar ta hana shi. Tsaki kawai yaja ya lumshe idanunsa har suka isa bankinsu. Aiki zai dan rage kafin lokacin tafiyarsu airport yayi.
*****
Kwanaki biyu a tsakani Harisu ya cika fam da bacin rai. Ya sake kiran Awaisu wai shi yake fadawa ayyuka sunyi masa yawa yanzu ma yana Lagos. Harda cewa ya duba accout dinsa yayi masa transfer na dubu dari biyu su kara a kudin asibiti. Da wannan takaicin ya tafi asibiti yana zuwa Baaba take tambayarsa yaya sukayi da kaninsa ya daure fuska kuwa. Ganin haka Maamu ta soma hawaye. Bacin ranta ba na komai bane sai yadda danta ya juya mata baya. Harisu ya kula da haka ya dawo kusa da ita ya zauna yana murmushi.
"Maamu ki dena saka damuwa a ranki. Kina warkewa da kaina zanje Abuja na sami Awaisu. Yanzu kinga likitoci sunce baa son komai ya bata miki rai. "
Baaba ta kara da cewa kada ta damu tare zasu je sai wannan Gimbin ta gane bata da wayo. Ita dai jinsu kawai take yi tana yake don nuna musu bata damu ba.
Suna haka Dr. Yana ta leko dakin da fara'arta suka gaisa ta tambayi jikin Maamu. Bayan ta dubata ta ne ta dan kalli Harisu wanda a cewarta bata ga mutum mai karamcinsa ba.
"Uhmmm dama nace an kirawo mata Awaisun da take kira kuwa? "
Baaba Hure tace "amma wannan yarinya da fitina kike. Yanzun nan mun samu hankalinta ya dan kwanta zaki zo ki tada zance."
Langabe kai Dr. Yana tayi tana kallon Maamu "ni wallahi tausayi take bani. Idan yaki zuwa ne wani ya bishi mana a fada masa bata da lafiya yazo kada Allah Ya raba ganawar"
Harisu ya dafe kai yana kallon yadda yanayin Maamu ya sauya tana neman kara rikicewa. Tsawa ya dakawa Dr. Yana yace ta biyo shi waje. A zuciyarta tayi dan murmushi bukatarta ta biya. Sumsum tabi bayansa suka koma can reception suka tsaya daga gefe.
Hannuwansa biyu ya hada a gabanta yana roko "don Allah likita ki tsaya a iya duba jikinta ki dena tado mana zantukan da zasu hanata warkewa da wuri. Idan da kinsan irin wahalar da tasha za ki tausaya mata ne"
Dr. Yana ta dago kanta ta gyara fuskarta alamun ba da wasa tazo ba.
"Tunanin hakan ne yasa nake ganin ya kamata duk yadda zakuyi ku taimaketa kuyi. Bazan boye maka ba gaskiyar magana wannan baiwar Allah da wuya ta tashi. Ka dubi yadda jikinta gabadaya ya bushe ga cututtuka sun hadu da tsohon kashi. Idan kuka tsaya dogon tunani rai yayi halinsa baku hadata da Awaisun nan ba ku kanku bazaku ji dadi ba"
So take ta sanar dashi tasan komai amma tana gudun yadda zai dauki abun. Tana kallo ya zurfafa a tunani tace "ko kasan ganinsa yana daga cikin abubuwan da zasuyi saurin kwantar mata da hankali ta sami sauki da wuri? Kuyi tunani akan shawarata. Indai yana da rai duk yadda zakuyi ku kawo mata shi ku kawo shi ko yaya ta saka shi a ido"
Tana kaiwa nan tayi gaba. Rumana dake tsaye a bayansu dauke da kwanakan abinci ta goge kwallarta. Ita da kannenta ne Abba ya kawo su. Ji tayi ta sake tsanar Uncle Awaisu sosai. A iya sani da fahimtarta kawai yayi kudi ne yake wulakanta mahaifiyarsa da danginsa.
Karasowa sukayi suka gaishe da Harisu sannan suka wuce. Maamu tana nan jiya iyau sai damuwa da ta karu. A cikin halin ciwo take sanar da Baaba Hure tana zargin akwai hannun Gimbi a wannan halayyar ta Awaisu. Abubuwa da dama da suka wakana a Abuja ta bata labari wanda itama Baaban ya kara tabbatar mata da zarginta na asiri ake yi masa. Hakuri ta kara bawa maamu da alkawarin Harisu zaije da zarar Awaisu ya dawo daga Lagos din da yace ya tafi. Da yake su kadai ne a dakin Maamu tana hawaye ta soma yiwa