Showing 30001 words to 33000 words out of 112099 words
Chapter 11 - KASHE FITILA Book Complete by Batul Mamman.txt
danyar kubewa a bakin kofa tayi zumulmula."
Dariya ce ta kwacewa Rumana harda kyakyatawa. Amma har suka koma aji zuciyarta tana mai kara samun karfin gwiwar aiwatar da shawarar kawarta.
*****
Maamu ke zaune a daki ita kadai. Irin yadda take ji a zuciyarta ko kuka tayi bata tsammanin samun sassauci. Ta rasa me ta tsarewa Gimbi har take yi mata irin wannan cin kashin a cikin gidan dan da ta tsugunna ta haifa. Kwanakin baya da tayi rashin lafiya Awaisu ya dawo mata yadda yake a da. Tattali da mutuntawa da ya dace da mahaifiya babu inda ya rage ta. Lokaci guda kuma kamar anyi ruwa an dauke. Shigowa dakinta ya gaisheta dama har ta hakura. Abin da yafi damunta bai wuce yadda Gimbi take mata wulakanci a kan idonsa ba amma kallon wayarsa ko tv yafi masa mahimmanci. Tunawa tayi da yadda suka rabu da safe taji wani siririn hawaye yana bin idonta.
Rumana Gimbi ta sa firar dankali mai yawa irin kananun nan masu cin rai tun dare. Bata kwanta bacci ba sai daya saura. Karfe biyar ta tashi yaranta ta aiko Daula ta tashi Rumana. Cike da fitsara tasa kafa ta hauri Rumanan da take bacci a kan abin sallah a ciki, caraf a idon Maamu. Ta kuwa kai mata duka tana mata fadan abin da tayi. Daula ta bude baki ta saki wata irin kara kamar wadda aka sokawa wuka.
Da sauri Gimbi ta shigo tana tambayarta me aka yi mata.
Maamu bata ma san da yarensu take magana ba don haushi ta nuna mata Rumana rike da ciki tana sanar da ita me ya faru.
Gimbi ta wani kankance ido "ke dallah ba ke na tambaya ba sai son zance ke da ba'a gane yarenki"
Maamu har dan firgita tayi da tsawar, ita kuwa Rumana jikinta yayi sanyi don abu ne da bata taba gani ba yiwa babba tsawa. Kafin ta gama tunani taji Gimbi ta rike mata kunne ta murdeshi sosai. Rumana sai kuka tana kokarin kwacewa.
"Mummy kiyi hakuri" ta fada da kyar
"Ke kuma idan kika sake taba min yara sai jikinki ya gaya miki. Kuma daga yau sai yau kada ki kuma kirana Mummy. Uwarki na kyauye kwadayayyu masu kama da may..."
Kasa karasawa tayi saboda shigowar Awaisu. Maamu tayi saurin fada masa yadda akayi
"Kace matarka ta sakar min jika haka. Ba Rumana bace ta daki Amina nice na dake ta"
Ya juya ya tambayi Daula ta gyada kai tana cigaba da kuka. Gimbi ta saki Rumana kunnenta yana radadi kamar ya tsinke. Awaisu ta kalla fuskarta babu alamun wasa.
"To ka yiwa Maamu magana wallahi babu ruwanta da yarana. Duk ta bi ta tsanesu kamar ba ita ta haifeka ba"
Daga shi har Rumana shiru sukayi na dan lokaci. Sai daga baya kamar an tsikare shi ya hau Maamu da fada yana jaddada mata bai ga wanda ya isa ya taba masa yara ya kyale ba. Yana gama fadan ya fita daga dakin. Gimbi ta galla musu harara ta bi bayansa.
Da suka gama shiri Rumana ta fito ta kwashe kayan da sukayi amfani dasu ta wanke kamar yadda Gimbi ta shardanta mata kullum kafin ta tafi makaranta. Tana cikin wankewa Amir ya shiga kitchen din da nasa kofin tea din ko rabi bai sha ba. Jin muryar Gimbi kuma yasan zata masa fadan kin shanyewa yasa shi saurin jefa kofin cikin sink tea din ya watsowa Rumana a gaban hijab da rigar makaranta. Ta bude baki zata yi magana sai ta tuna yadda akayiwa Maamu shiyasa ta fasa. Wannan dalilin yasa ta dauko dayan uniform din a kayan wanki ta saka saboda yadda wancan ya baci.
*****
Ana tashi daga aiki Gimbi ta wuce gidan Anti Bebi. Yanzu sun kara dinkewa sosai. Gimbi ta ma dena tsoron me su Mama zasu fada. Harkar gabanta kawai take yi. Yau ma labarin yadda tayiwa Maamu da Awaisu da safe taje bata. Anti Bebi tayi dariya sosai da taji labarin.
"Me akayi akayi maza dama...dadin aure fa a zamanin nan bai wuce ki wawuri duk abin da zaki iya a hannun dan iska ba. Mazan yanzu kina tarairayarsu da ladabi da biyayya suna kunsa miki bakinciki da ciwon zuciya. Mace na shekara a gidan miji sai ki ganta a layin karbar maganin hawan jini"
Dariya Gimbi tayi suka tafa da Anti Bebi
"Kuma fa hakane, kawayena biyu duk kafin haihuwar fari sun kamu da hawan jini. Nagode da kika bude min ido wallahi. Mijin da nake aure ma yayi kadan ya daga min hankali bare wata tsohuwa"
Faffadan murmushi ne ya bayyana a fuskar Anti Bebi
"Da kyau Gimbiya. Da ace mata sun fahimci meye aure da bakincikin da namiji bai kashesu ba"
Hira suka sha sannan Gimbi ta tashi ta tafi gida ana kiraye kirayen sallar Isha. Lokacin Rumana ta dawo ta gyara gidan tsaf sai dai baa bata izinin shiga store ba bare girki.
Da abinci a leda Gimbi ta dawo ta bawa yaranta. Bayan sun gama da kanta ta tukawa Awaisu tuwo ta dibarwa Maamu da Rumana dan kadan a kwano daya wuraren goman dare. Suna ci Maamu dan kadan take tsakura saboda Rumana ta koshi. Haka suka gama cikinsu babu nauyi sai ruwa da suka sha sosai domin kada yunwa ta hanasu bacci.
Shadayan dare Awaisu ya dawo a gajiye. Ko hanyar dakin Maamu bai kalla ba ya wuce nasa. Gimbi don zolaya harda cewa ko zaije taya Maamu hira yau. Rai a bace yace bata ganin yadda ya gaji. Murmushi tayi tana bashi hakuri shi kuma yana wani hade rai.
*****
Haka rayuwa ta juyawa su Rumana. Kullum da fargaba suke tashi domin yanzu Gimbi bata boye musu mugun nufinta. Burinta kawai su bar gidan taci karenta babu babbaka.
****
Kwanan Shuhada biyar da gama iddah. Anti Bebi harda dauko wasu mutane wai malamai ne zasuyi mata adduar neman tsari. Alh Maitama kamar kullum bashi da bakin magana sai ma godiya gareta saboda kula da yarsa da taje yi. Suhail ya gama jarabawa amma rashin kudi a hannunsu yasa Shuhada tace ya zauna kawai har a koma hutu ya cigaba da karatunsa .
Daga dakinta ta fito zata kwaso kayan shanyarta don mai wankin gidan daga na Alhaji sai Anti Bebi yake wankewa.
Daya daga cikin malaman karyar ne ta gani da Anti Bebi a wani karamin falo suna magana a hankali ta lallaba ta tsaya a gefe babu mai ganinta. Daga ciki take jiyo muryarsa a hankali
"Wannan maganin Wangesi yace ki zubawa ita babar taki a abin sha. Yadda zata shanye haka duk wani fushi ko bacin ran da zaki haddasa mata zata shanyeshi tas"
Juya maganin tayi tana dan murmushi.
"Shi Alhajin yace na barshi haka ko"
"Yaji tsoron kada yawan asirin ya haukata shi shine yace a saka masa ido na dan lokaci"
Dafe kirji Shuhada tayi don tasan da babanta ake. Barin wurin tayi niyar yi taji mutumin ya ambaci sunanta.
"Ita yarinyar nan Shahada take ko me ga nata maganin. A abinci zaki zuba taci. Da zarar taci yace ko sunan mutumin kika kira sai taji gabanta ya fadi sonsa ya karu a ranta. Ki kwantar da hankali bazata yi musu ba har ayi auren"
Karbar wannan magani yasa Anti Bebi nishadi da murna sosai.
"Sai na koya musu hankali su duka. Awaisu dama nasa matarsa ta gama juya masa tunani. Abin da ya rage bai wuce na aura masa Shuhada ba kuma na tsaya mata har sai ya saki Gimbi. Ni da ka ganni nan bana yafe rashin mutumci ko kadan"
"Kiyi yadda yace zaki ga biyan bukata"
Daga haka ta karbi maganin kafin su fito Shuhada ta bar wurin da sauri.
Dakinta ta koma ta hau kuka. Ta rasa wace irin mutum ce Anti Bebi. Share hawayenta tayi ta shiga tunanin neman mafita. Wurin rabin awa ta kwasa a dakin kafin ta fita.
Kitchen ta dosa dauko abinci ta tarar da Anti Bebi a falo.
"Ke ina zuwa?"
"Abincina zan dauko ko shima an hana ne?"
"Aa Shuhada, ni bana jindadin yawan rigimarmu kamar ba mata ba. Ga abinci can akan dinning table kije kici."
Ba musu Shuhada ta wuce ta diba ta cika plate har yayi tsororo. Hanyar dakinta ta nufa Anti Bebi tayi dariya
"Shegiya mai cikin zani. Baki iya komai ba sai ci da kashi. Ji wannan tulin abinci kamar mai aikin karfi"
Shuhada tayi kamar bata ji ba ta wuce. Leda ta samu a gabanta tana juye abincin cokali cokali kamar ci take. Ba zato taji an turo kofar dakinta. Anti Bebi ke son tabbatarwa ko taci.
Ita kuwa Shuhada sai ta wayance tana kokarin kai cokalin baki. Anti Bebi bata ce komai ba ta juya ta fita. Shuhada ta juye fiye da rabin abincin a leda sannan ta mayar da sauran kitchen.
Anti Bebi ce ta biyota har kitchen ta dafa mata kafada. Shuhada don tsoro kamar ta saki fitsari. Bata kaunar hada inuwa da ita. Ji tayi Anti Bebin tace
"Kina son Awaisu mijin yar nan tawa Gimbi?"
Da kyar ta iya hadiyar yawu kafin ta tattaro hankalinta ta nutsu. Kai ta sunkuyar ita a dole kunya take ji tayi murmushi
"Kai Anti har kin gane"
Anti Bebi tayi wani juyin farinciki sannan ta sake maimaita tambayar. Wannan karon Shuhada hannu tasa ta rufe idanunta tana wani fari
"Ni dai Anti kunyarki nake ji"
Daga haka ta kwasa da gudu ta bar kitchen din.
Anti Bebi taji dadi mara misaltuwa ta kama dariyar mugunta. Da Shuhada zata wargaza rayuwar Gimbi.
Shuhada na shiga daki rufe kofar tayi tana numfashi da kyar. Tunda ta tari Anti Bebi da wannan karyar ya zama dole tayi amfani da wannan damar wurin sanin sirrinsu da kwatarwa kanta da duk wanda suka kafawa takunkumi 'yanci.
[15/08, 17:45] +234 803 272 5896: *KASHE FITILA* 23
*Batul Mamman*💖
_*Waiwaye*_
_Shuhada ta nunawa Anti Bebi asirin da akayi mata domin ta kamu da son Awaisu ya kamata. A bangaren Gimbi kuma tana nan tana cigaba da wulakanta Maamu._
Ladabin karya da biyayya Shuhada ta cigaba da nunawa Anti Bebi. Ita kuma dadi ya isheta ta sami hanyar ganin hawayen Gimbi cikin ruwan sanyi.
Bayan kusan sati biyu tana sanya ido akan Shuhada wadda ta dage sosai wurin nuna ita idan ba Awaisu ba yanzu sai rijiya. Hakan yasa Anti Bebi fara tunanin hanyar da zata bi domin ganin sun hadu ta fara aiwatar da kudirinta.
******
Kiran sallar magriba akeyi Rumana ta shigo gida da sauri rike da ledar kosai. Kitchen ta wuce inda take jin muryar Gimbi tana tashi taje ta mika mata ledar.
Gimbi ta karba ta bude hade da zaro idanu ita ta ga abin mamaki.
"Yanzu wannan kosan dari ne? Lallai wake ya soma arha. Wannan kosan ya yiwa Maamu yawa ai. Cikin tsofaffi sai ana sa ido sosai"
Plate din roba ta dauko ta debi kosai guda bakwai 'yan miri-miri ta mikawa Rumana.
"Maza ga kunu ki dauka ki kai mata an sha ruwa tun kina hanya."
Rumana ta kalli dan siririn kofin da ko cika baiyi ba da plate din kosan sai ji tayi hawaye na barazanar kwace mata. Wai yanzu wannan ne abincin shan ruwan Maamu a gidan danta.
Gimbi na kallon yadda yanayinta ya chanja a ranta tace mayu masu zuciyar kare. Zaman gidan sai kace dole sunki tafiya.
Haka Rumana ta tafi dakinsu ta ajiyewa Maamu abincin shan ruwanta wanda yasa idanunta kawo ruwa itama. Kunun kansa bai wuce kurba hudu zuwa biyar ba kwarara bare kuma kosan. Rashin wadatuwa da abinci ya sanya Maamu azumin dole kusan kullum yanzu shi take yi. Abincin da aka basu rana da dare sai su hada su ci lokacin shan ruwan don su fi koshi. Wani lokacin Rumana tana yi itama. Yau kamar gaske ganin idon Awaisu da safe Gimbi tace zata yi mata kayan buda baki. A yadda ta nuna kamar ranar Maamu ta fara azumin shi kuwa ya fita yana kara jin babu macen kirki sama da matarsa.
Maamu na kallo Rumana ta shige bandaki taci kukanta na tsantsan bakinciki da nadamar zuwa Abuja. Da ta fito wayar Maamun ta dauka tana shashshekar kuka ta kirawo babanta. Da yake wayar ba'a ji sai an sakata a speaker Maamu tana jin muryarsa ta karbe wayar daga hannun Rumana kafin ta tona asiri.
"Harisu"
Dadi yaji na samun kira daga garesu saboda kwana biyu idan ya kira ta wayar Awaisu baya rasa uzurin da zai fake dashi a matsayin dalilin rashin bata waya su gaisa. Ita kanta muryarta raunana tayi da taji yace
"Maamuna"
"Harisu yaushe zaka zo ka kaini Fika? Kewar mutanen gida nake yi sosai. Ina Baaba da sauran mutan gidan?"
Dadi yaji domin suma suna kewarta yace "Zanyi magana da Awaisu sai ku taho idan anyiwa su Rumana hutu. Ko nazo da kaina mu taho tare"
Za tayi magana ya katseta ta hanyar yi mata tambayoyi akan lafiyarta da kuma kula da cin abinci akan lokaci.
"Bana so ki sake kwanciya kamar wancan karon"
A ranta tunani take yi idan ba a yi saurin mayar da ita cikin dangi ba kila gawarta za a kai Fika. Bayan duk sun gaisa da 'yan uwa domin Harisun kashewa yayi ya sake kiransu Maamu rokon Rumana tayi akan ta rufawa kawunta asiri har Allah Ya kawo karshen zamansu a gidan. Ita dai Rumana ko magana ta kasa yi saboda bacin rai. Maamu na gama magana ta fice daga dakin ta nufi kitchen. A yau dole ta dauki shawarar Yusra ko don ta huce takaici.
Inda ake ajiye kayan kadi na miya ta bude ta debo karkashi ta zuba a kofi wanda rabinsa ruwa ne. Tana juyawa da yatsanta bata sani ba ashe Daula ta ganta. Dakin Awaisu ta nufa inda suke hira da Gimbi ta fada musu ga Rumana tana kwaba milo da ruwa zata sha.
Da sauri Gimbi ta tashi tana kallon Awaisu.
"Kana ji dai da kunnenka yarinyar nan ta fara sata duk irin kokarin da nake yi akansu ita da Maamu"
"Ki kyaleni da ita zanyi mata magana" shi tashin hankali ne baya so musamman da yake ya kwaso gajiya.
Bata saurare shi ba ta bi bayan Daula. Yau sai ta koyawa Rumana hankali kila da safe ta bar mata gidanta.
A bakin kofa suka hadu Rumana zata je dakin Gimbi ta juye kwabin karkashin a bakin kofarta. Ba karamin tsorata tayi ba da suka hada ido da Gimbi. Kofin ta fizge tayi wurgi dashi abin ciki ya watse don ma na roba ne. Sannan ta kwashe Rumana da mari.
"Barauniya kawai kwadayayyiya. Wato dama kece kike karar min da madara da milo ban sani ba"
Rike kumatu tayi tana kukan sharrin da akayi mata sai ga Daula ta yo kan Gimbi santsin karkashin da ta taka ya kwasheta tana neman faduwa. Garin haka bata kula ba tana kokarin rike 'yarta itama ta taka suka yi sulu a kan tiles duk su biyun suna ihu. Daula tsoron faduwa yasa ta damki kan Gimbi wanda aka yiwa kananun kitson barebari. Jela ukun da ta damko tana ja yasa Gimbi sanya wata muguwar kara, hakan yayi daidai da cizgewar kitson sai gasu a hannun Daula. Su duka biyun suka fadi a kasa jikinsu dame da karkashi.
Rumana kuwa me zatayi banda dariya. Kana kallon kan Gimbi sai kayi dariyar yadda ya kwashe. Sai fada take yiwa Daula. Da kyar suka iya tashi santsi na kara dibarsu. Sai da Rumana ta ji tahowar Awaisu yana tambayar ihun me akeyi ne ta durkusa ta rike ciki. Duk da bukata ta biya amma tsoron hukuncin da zaiyi mata take yi.
"Me ya sameku haka, ku duk kun zube a kasa ke kuma kina rike ciki"
"Abba faduwa mukayi da wannan abin da Rumana ta hada" cewar Daula
Taimakawa Gimbi yayi ta tashi amma kafarta kamar bazata iya daukanta ba don buguwa. Runtse ido kawai take yi ta kalli Rumana
"Uban mene kika hada a kofin nan"
Fuska Rumana ta kwabe ita abar tausayi
"Cikina ne yake ciwo tun a makaranta shine wata tace min ana jika karkashi da kanwa"
"Karkashi da kanwa kuma Rumana? Baki da lafiyar bazaki fada min ba sai ki hada wani karkashi"
Awaisu yana magana yana kallon Daula mai kawo rahoto.
"Na zata fa milo ne" ta fada kai a kasa. Dama ita ce mai zuwa hada milo da madara ta sha duk dare. Lokacin da ta ga Rumana ma abin da ya kawota kenan.
Baice komai ba ya tallabo Gimbi suka tafi daki ciwo a kafarta ta hagu ya isheta. Daula sai harara take dokawa Rumana ta tafi dakinta. Ita kuwa da murna ta tafi harda danewa jikin Maamu. Bacin ranta duk ya kau saboda dadin da take ji a lokacin. Maamu bata san me yake faruwa ba amma canjin yanayin da ta gani wurin Rumana ya dan kwantar mata da hankali.
*****
Daren nan Gimbi batayi baccin kirki ba saboda ciwon kafa ga kanta yana zugi. Gari na wayewa kafar ta kumbura suntum daga wurin gwiwa. Awaisu da kansa ya tashi Rumana tayi abincin safe zai kai Gimbi asibiti.
Ta dan ji faduwar gaba ko a dalilinta wani abu ya sami Gimbin. Amma da ta tuna gasuwarsu a gidan sai ta share. Da kyar ya taimaka mata suka fita waje tana jan kafar. Kwakkwaran motsi idan tayi sai taji kamar ana soka mata wuka.
Bayan fitarsu Rumana ta shiga fadar Gimbiya matar Awaisu inda ake horasu ta dafa shayi ta soya kwai ta zubawa su Daula nasu ta hada mai yawa a flask ta kaiwa Maamu. Ga kwai ga bread.
"Rumana wannan daga ina?"
"Allah ne Ya bamu Maamu. Kiyi sauri ki ci kafin su dawo daga asibitin"
Dan fito da ido tayi "waye babu lafiya?"
Rumana tana dariya ta labarta mata yadda sukayi jiya. Maamu ta soma yi mata fada akan kada ta kara. Amma Rumana ta kula fadan bai kai zuci ba don har dan murmushi tayi.
Ranar sun ci sun koshi suna gamawa taje ta dora na rana da wuri kafin goma ta gama ta sake zuba musu mai yawa. Sai da ta koma gyara kitchen Awaisu ya dawo ya sanar dasu an kwantar da Gimbi a asibiti kashinta ne ya goce ga buguwa kafar tayi tsami.
Haka nan yaji yana son ganin Maamu bayan kusan sati ko hanyar dakin baije ba. Yana shiga ta fito daga wanka. Ji yayi jikinsa duk yayi sanyi saboda wata muguwar rama da Maamu tayi. Hankalinsa yayi mugun tashi yace
"Maamu baki da lafiya ne?"
So take tayi kuka sai ta dake "Ka kaini Fika"
Muryarta ma ta kankance kamar yadda ta rame. Duk yaji ya tsani kansa da rashin kulawa da ita.
"Kiyi hakuri a dan