Showing 57001 words to 60000 words out of 112099 words
Chapter 20 - KASHE FITILA Book Complete by Batul Mamman.txt
son gano ainihin me yake faruwa dasu biyun. Harisu da kansa yaja hannun Suwaiba tana ta fada yayi waje da ita sauran yan uwansu suka biyo bayansu. Baaba takaici ya isheta ta cewa Maamu bari taje ta tabbatar duka sun tafi yau ita zata kwana.
Tana fita Gimbi tabi bayanta sai ta tuna da maganin da aka bata. Lekawa tayi ta kallo hagu da dama ta tabbatar babu idon sani sannan ta dawo ta rufe kofar. Fitowar Baaba da leken da Gimbi tayi akan idon Dr. Yana wanda fuskar Gimbi ta kasance bakuwa a gareta. Saurin barin matar da take yiwa kwatancen dakin hoton kashi tayi ta taho dakin Maamu da sauri saboda alamun rashin gaskiya da ta gani a jikin mai leken. Tana bude kofar ta ga Maamu a tsaye tana matsawa baya ga Gimbi rike da wani abu kamar izgar doki tayi kanta tana kokarin shafa mata. Cikin zafin nama Dr. Yana tayi kantza.....[15/08, 17:45] +234 803 272 5896: *KASHE FITILA*💡36
*Batul Mamman*💖
Gimbi bata ankara ba taji an damki hannunta ana kokarin kwace abin da take niyar shafawa Maamu. Damkewa tayi iya karfinta ta dage ta ture Dr. Yana sannan ta boye abin da sauri. Mikewa Dr. Yana tayi ta tafi ta riko Maamu wadda ta gama tsorata jikinta sai rawa yake yi. Kirikiri Gimbi ta nufota da abin har tana fadin wasu kalmomi da bata gane ba. A tsorace tace da Dr. Yana ta fitar da ita daga dakin gida zata tafi. Duk yadda Dr. taso kwantar mata da hankali tace ita dai fita zatayi kawai. Saboda jikinta bai gama kwari ba dafata tayi suka fito waje tana cewa su Harisu suna nan wajen suyi sauri kafin su tafi.
A bakin mota suke tsaye Baaba sai fada take yiwa Anti Suwaiba. Awaisu da ya rasa inda Rumana tayi ya hango Maamu da Dr. Yana ya nufo su yana tunanin me ya fito dasu. Kafin ya karaso sun kusa zuwa wurin motar Harisu. Gimbi suka gani ta taho cikin mugun sauri har tana haki kafin duka suyi magana ta iso tare da yiwa Dr. Yana kallon banza.
"Ke wace irin likita ce zaki shigo daki haka kawai ki fitar da mara lafiya batare da wani bayani ba?"
Su Harisu sanin halin Dr. Yana sai suka fara tunanin ko wani salon shiga rigimar nata ne. Gimbi ta cigaba da magana tana kallon Maamu da tausayawa
"Maamu kinji tsoro ko? Ai in fada muku kuna fita wani abu ne ya shigo mana a guje na kasa ganewa ma bera ne ko mage. Shine na samo abu zan kore shi ganin Maamu ta tsorata kawai sai wannan matar ta shigo ta fito da ita. "
"La ilaha illallah muhammadur rasulullah sallallahu alaihi wa sallam" Dr. Yana ta fada tana tafa hannuwa saboda tsabar mamakin wannan matar.
Kallonsu tayi duk sun zuba mata ido ta fada musu abin da ta ga Gimbi tana shirin yi a dakin.
Gimbi ta dafe kirji rai a bace "anya kina da hankali kuwa, uwarmijina ce fa kike cewa zan shafa mata wani abu. To a chajeni idan kun yarda da abin da take fada. Maamu fada musu gaskiya"
Wani irin kallo Maamu ta yiwa Gimbi wanda ya tsorata ta sannan ta kada kai ta bude mota ta shige ta zauna. Gimbi ba karamar makira bace. Gara su tafi gida kawai ayi wadda za'ayi gudun kada suyi abin fadi a asibitin.
Baaba tace "likita mungode miki bari mu tafi da ita kawai tunda dama gobe ne sallama."
Dr. Yana tace "ku tsaya kawai Baaba bari na kira security yaje ofishin 'yab sanda mafi kusa yayi report. Ni nafi so ayi komai a gama yanzu. In ga abu da idona mata ta nemi raina min hankali"
Tsoro karara ne ya bayyana a fuskar Gimbi kada ayi binciken da gaske yasa ta fara masifa baji ba gani tana cewa itama gida zata tafi ta fuskanci basuyi maraba da zuwanta ba shiyasa suke yi mata haka gashi abin ya hada da zargi kuma. Dreban da ya kawota ta kira yazo ta shige mota ko waige babu don tsoron kada a nemi ta fito ma suka tafi rai a bace wannan shegiyar likita ta cuceta domin damarta ta karshe kenan wurin amfani da wannan maganin kuma ta rasa.
Tana tafiya Dr. Yana tace ya kamata wani cikinsu ya tsaya karbar magungunan Maamu da takardar sallama sannan ta kara jaddada musu lallai a binciki Gimbi ba karya take ba. Awaisu yace to su tafi zaije yayi settling komai.
Su Baaba duka motar Harisu suka shiga suna al'ajabin halin Gimbi. Anti Baraka ce ta leko ta taga tace ko dai ta fito ne ta taya shi hada kayan da suka baro a dakin.
"Ki barshi kawai Rumana sai ta hada kafin na gama da wurin karbar maganin"
Dariya matan suka soma yi masa harda zolaya sannan suka tafi. Dr. Yana ya tsayar yanayin fuskarsa babu alamun wasa yace ta fada masa abin da ta gani.
Tana fada masa yanayin fuskarsa ya sauya zuwa bacin rai sosai yace idan babu damuwa yana bukatar numbarta saboda zai yiwu ya nemeta shaida. Kafin ya gama magana ma ta fada masa numbar. Katinsa ya zaro ya mika mata sannan yace zai fara zuwa dakin ya duba ko Rumana ta koma don bai ganta a waje ba.
Yana zuwa kofar dakin suka kusa karo da ita ta fito da gudu. Ganin Awaisu yasa ta dan dakata amma hankalinta a tashe yake
"Uncle ban ga su Maamu ba kowa ya tafi"
Dan sakin fuska yayi saboda ganinta kawai yaji ransa ya soma sanyi.
"An sallameta ne yanzu suka tafi."
"Sallama kuma Uncle ba ance sai gobe ba. Ko wani abu ya sameta ne?" Ta fada ido yana kawo ruwa gabanta na tsananta bugu.
Rage tsaho yayi ya kura mata ido ba shiri taja baya ganin ya matso da fuskarsa kusa da tata.
"Maamu lafiyarta kalau. Ki hada kayan kafin naje nayi settling bills sai mu tafi"
Bata san lokacin da tace "mu kadai?"
"Eh mana, Uncle da Umm Rumanansa"
Baki ta bude jin me yace shi kuwa ya juya ya fita. Ita fa ta kasa gane meyasa yake yi mata magana yanzu a wani irin yanayi daban ba yadda ta saba ba. Duk da ita take ce masa Uncle Awaisun Rumana a da yanzu idan ya fada kunya ma take ji.
Kusan minti talatin yayi kafin ya dawo suka kwashe kayan suka kai mota. Dr Yana har bakin motar ta rakasu sukayi sallama da Rumana.
Sun fara tafiya shiru sai lokaci lokaci da ta kula yana yawan kallonta. Ta rasa me yake damun Uncle Awaisu yan kwanakin nan.
Katse shirun yayi ta hanyar yi mata tambaya.
"Saura sati nawa ku koma school?"
"Bai kai sati biyu ba"
"Yayi kyau ana komawa sai SSCE ko"
Ta gyada kai fuskarta na nuni da farincikinta.
"Idan kika gama zaki yarda ki dawo Abuja?"
Da saurinta tace "Allah Ya kiyaye"
Awaisu yayi murmushi. Ai dole ta tsani Abuja to kuma gashi a nan yake aiki
"Ba kya son zama dani ne?"
Ta hau girgiza hannu "A'a ina so mana, amma dai ...."
"na gane kada ki damu aure zan kara sai ki zauna da amarya"
Murna yaga tayi sosai harda juyawa ta fuskance shi da kyau "Allah Uncle, ashe zamu sha biki"
"Sai na fadawa Gimbi kina murna zaayi mata kishiya"
Gimtse dariyarta tayi ta sunkuyar da kai tana yi kasa kasa. Allah Ya kara tace a zuci har taji tana kwadayin zama a gidan ko na kwana daya ne ta ga Gimbi da kishiya.
"kema ance tunda kika dawo kike ta tara samari. Kuma wanda ya fada min bazai miki karya ba"
A raunane tace "ayya Uncle dan abokin Baba ne na bayan gida kuma nace bana so. Sai wani malamin English a makaranta sannan yayan wata yar ajinmu. Duka fa nace bana sonsu"
Hannu daya ta ga ya saka ya danne kirjinsa bangaren hagu yace "wayyo zuciyata"
A rikice tace "yi parking a gefe Uncle me ya sameka? Ina wayarka na kira Baba"
Kashe mata ido yayi yana dariya "kishi ne dama kuma ya koma tunda naga an damu dani"
Matsawa tayi kunya ta rufeta bata san lokacin da tace "wai Uncle sai ya rinka yi min abu kamar budurwa da saurayi"
Dariyarsa ce ta tabbatar mata da cewa yaji me tace ba shiri ta rufe fuskarta da mayafinta ta shiga kogin tunanin chanjawar Uncle Awaisu. A hankali yaji numfashinta ya sauya jikinta ya dan saki. Mayafin ya ja a hankali ya bude mata fuska ya ga ashe bacci ne ya dauketa.
A daidai wannan lokacin yaji wata irin soyayyar Rumana ta shiga ransa. Tabbas da farko yaji ransa ya kwadaita masa amsarta a matsayin mata kuma komai tayi yanzu yana burge shi. Amma a yanzun nan da ya kalleta soyayya ce ta kamshi wadda ta bashi mamaki shi kansa. Rumana bata cikin jerin matan da ko a mafarki ya taba tunanin wani abu makamancin wannan zai shiga tsakaninsu.
Allah mai iko. Mutane biyun da Gimbi ta sanya masa fita harkarsu ya manta da lamuransu sune a yanzu cikin dan kankanin lokaci yake jin zai iya komai indai bai sabawa shariah ba domin ya faranta musu.
Har gama parking bata farka ba kuma dole ya tasheta don har kannenta sun fito daukar kaya daga motar. Rasa yadda zaiyi ya tasheta yayi sai yayu saa Daula ta fito yace ta tasheta su shiga ciki.
Ranar har dare yayunsu mata suna gidan ana shawara game da matakin da zasu dauka akan Gimbi. Maamu ta tabbatar musu da zancen Dr. Yana gaskiya ne tace tana rokon alfarmar su gaggauta hukunta Gimbi kafin ta bar Fika. A lokacin Awaisu ya kira Alh Maitama ya roke shi akan ya fada masa idan abin da yake son fada ya dangan ci asiri da Gimbi da Anti Bebi sukayi. Alh Maitama bai boye masa komai ba har yadda aurensa da na 'yarsa ya mutu. Ya tausaya musu sosai kuma ya sanar da su Baaba yadda suka yi.
******
Kamar sun san haka zata faru dama tun jiya Harisu da Awaisu sun sanar da kawun nansu na kusa batun hada aure da Rumana. Duk da sunyi mamaki amma kowa ya basu hadin kai a ganinsu hadi ne na kara dankon zumunci a tsakaninsu. Shiyasa tun wurin karfe tara na safe Harisu ya tura Abba ya sanar dasu dalili yasa dole a daura auren nan a yau bayan sallar Juma'a. Shi kanshi Abba da aka aika yayi mamaki matuka.
A cikin gidan kuma tun daren Harisu ya sanar da matansa. Mama da Anti Amarya murna sukayi sosai. Maman Rumana kuwa ta kasa magana har suka fita daga dakin da yake girkinta ne. Kuka ta sawa Harisu tace tana tsoron kada Gimbi ta sabauta mata 'ya. Kusan kwana yayi yana rarrashinta da ban baki. Shima akwai wannan tsoron a ransa amma shawara ce da iyaye kuma yasan ko da aure ko babu Awaisu mai rike masa iyali ne bisa amana ba don ya hadu da hatsabibiya Gimbi ba wadda bata san wainar da ake toyawa ba. Tun da ta dawo daki ta shige ta hada kayanta da zummar zata bar garin da safe.
Ganin basuyi mata maganar abin da tayiwa Maamu ba yasa tayi tunanin wayar da tayiwa Ovi daga can bangaren boka ya rufe musu baki kamar yadda ta bukata
Ita kuwa Rumana bata san me akeyi ba don kitso ma tayi tafiyarta makota.
*****
Duka iyalin gidan tun daga kan su Baaba, Harisu da matansa, su Anti Baraka, Awaisu da Gimbi ne zaune a falon Harisu na karbar baki. Da Awaisu ya hana Gimbi tafiya yace ta jira zasuyi magana bayan masallaci bata yi tsammanin haka zata shigo ta tarar da wurin a cike ba. Gabanta ne ya fadi sosai ta sami wuri ta zauna a can gefe.
Kawun nansu da suka shaidi daurin auren Rumana da Awaisu a masallacin Juma'a duka Harisu ya sallamesu akan cewa sai washegari zai sanar da jama'a ayi walima a kofar gida. Yau suna da abu mai mahimmanci da zasuyi shi da Awaisun.
To gasu duka a falon Baaba ce ta soma magana tana kallon Gimbi ido cikin ido..
"Ba tare da dogon zance ba Gimbiya wannan zaman naki ne. Bisa amana mijinki ya dauki mahaifiyarsa da 'yar dan uwansa ya kai gidanki kin nemi halaka su. Bansan me zuciyarki ta ayyana miki ba a lokacin da kike azabtar da surukarki da yunwa. Babu ci babu sha sannan kin hana dan cikinta shiga lamarinta "
Mikewa Gimbi tayi a fusace saboda indai ba borin kunya ba zatayi asirinta ya riga ya gama tonuwa.
"Awaisu kana ji kana gani yadda 'yan uwanka suka saka ni a gaba da sharri tun da na sa kafa a garin nan. To wallahi ni bazan yarda ba ai nima ina da gata ba daga sama na fado ba."
Da yake yana kusa da ita wani wawan duka ya kaiwa bakin a take ya fashe sai ga jini. Baaba kuwa ta hau shi da fada tace ya tashi daga inda yake.
Bayan ya matsa ya kalleta cikin bacin rai "Gimbi kin cutar dani kin sanya mahaifiyata zubar da hawaye a dalilin juya mata baya da nayi"
Idonta da hawaye tace "kada ka yarda sharri suke son yi min"
"Nafi kowa sanin halinki Gimbi. A lokuta da dama sai kiyi abu raina ya baci sosai amma na rasa dalilin da yasa ko kallon banza bana iya yi miki. Allah sai Ya saka min gwargwadon hawayen da mahaifiyata ta zubar saboda bakinciki. Kuma ki sani yadda kika yi abin da kike so a lokacin da kike so nima yanzu lokacina ne. Gimbi sai na soya miki gyada a hannu kinyi nadamar aurena"
A gabansu ta dauko waya zata kira Ovi saboda tashin hankalin da ta shiga na maganganun Awaisu. Haka 'yan uwansa kaf suka ci mata mutumci tasha Allah Ya isa babu iyaka akan halin da tasa Maamu.
Tunawa tayi da inda take ta fasa kiran wayar amma ranta ya kololuwar baci. Idanunta jazur tana kumfar baka tace
"Awaisu idan ka cika dan halak ka sakeni. Meye a cikin auren naka wanda bazan iya samu ba idan na auri wani?"
Murmushinsa da take masifar so a da yayi mata "aure ni dake yanzu muka fara. Yanzu dai ki tsaya a kawo miki amarya ki karbi amana. Idan kuma kinfi so ku hadu a Abuja babu damuwa"
Komai na jikinta ne ya tsaya a lokacin da ya ambaci amarya. Jikinta na rawa tace "aure kayi Awaisu? Ni zaka wulakanta kayiwa kishiya. Wace shegiyar ce take jin zata iya zaman kishi dani?"
Magana take kamar zata zare ransu fes duka da ganin ko babu komai sun soma ramawa. Maamu ce tace "kada ki sake zagar mana 'ya"
"Auuuu wani munafukin ne yazo ya bashi 'ya ya aura? To mu zuba ni daku wallahi baa isa a daura auren ba idan har ina numfashi"
Su Anti Baraka sai dariya Gimbi ji take kamar tayi hauka don takaici. Ledar goro Anti Suwaiba ta jefa mata
"Yau dai bokanki yayi karya domin an riga an shafa Fatiha tun dazu. Awaisu ya zama angon Rumana"
"Jakar uba, Rumana??? Rumana fa kika ce?" Kafin su ankara tayi kan Awaisu a gigice zata kaiwa wuyansa shaka.
[15/08, 17:45] +234 803 272 5896: *KASHE FITILA*💡37
*Batul Mamman*💖
Fincikota taji anyi ta juya a fusace ta ga waye ya rikota taji saukar mari. Anti Baraka ce da wannan aikin halin Gimbi ya kaita makura duk da kasancewarta mafi hakuri a cikin 'yan uwanta.
Kumatunta ta rike don ba karamin shigarta yayi ba kalli Awaisu dake tsaye ya rasa yadda zaiyi. Kunyar ace matarsa ke wannan aika-aikar da bacin ne suka cika zuciyarsa.
Idanunta babu hawaye ko kadan tunda shima kuka wuri yake samu
"Abban Haris yanzu ka yarda da abin da nake fada maka ko? Mutanen nan sam basa kaunarka shine saboda sun rasa yadda zasuyi su rinka tatsarka suka hadaka da Rumana....wai Rumana yarinyar da ba haihuwarta ba uwarta ma a kan idonka aka aurota."
"Gimbi kada ki kure hakurina wallahi. Ban taba sanin cewa akwai ranar da zanyi nadamar watsawa Yaya Harisu kasa a ido a lokacin da ya nema min matar aure na bijire ba sai yanzu." Cewar Awaisu yana daga murya.
"Dama har wata matar ya taba sama maka? Hasashena bai zama kuskure ba da nace kudinka suke nema. Wato yaso baka wadda zata rinka sata ta kawo maka"
Hannu ya kai zai daki ko ma ina ya samu a jikinta Harisu ya rike "Awaisu kada kayi abin da nan gaba zakayi dana sani. Ka tuna akwai rabo a tsakaninku bai dace ka daketa ba"
Har wani huci yake yi ya dubeta tana kallon kowa daidai
"ki tashi ki kama hanya ki koma Abuja ki jira sauran abin da zai biyo bayan cin amanar da kika yi min na hadani da 'yan tsibbu"
Ga mamakin kowa durkusawa tayi a gaban Maamu zata dafata tayi saurin janye jikinta sai ga wasu zafafan hawaye suna ambaliya kamar famfo a idanun Gimbi
"Maamu don Allah na tuba ki yafe min duk abubuwan da ake zargin nayi miki. Naji na karba amma ki yafe min. Indai don wannan ne aka sa ya auri Rumana ni ko me kike so daga yau na dauki alkawarin yi miki indai zai saketa"
"Mutuwa ce kadai zata rabani da Rumana kisa wannan a ranki Gimbi" Awaisu ya bata amsa
Tashi tayi tana share hawaye "wannan cin mutumcin da kayi min na rantse maka sai na rama. Yau ba don Rumana ka aura ba da ko kaki ko kaso sai ka sakeni. To amma abin kunya ne a gareni aurena ya mutu akan wannan yarinyar da bata gama zama mace ba. Banda son zuciya irin naka da na iyayenta ina zaka kai ta"
Baaba Hure ce wannan karon ta daka mata tsawa wanda yasa ta fita daga falon ranta yana kuna. Dakin da ta sauka ta shiga ta harhada kayanta cikin sauri ta janyo akwatin tsakar gida.
Budar bakinta ta soma kiran yaranta "Har....bari mu koma gida ko me zan yanka domin canja maka suna sai na canja don bazaka taba tashi da sunan makiyana ba"
Daga falon suka ji tana kiran 'ya'yanta Awaisu ya taso da sauri. Tare suka taho da sa'aninsu na gidan saboda dama wasa sukeyi a can baya.
"ku wuce ku dauko kayanku tafiya zamuyi." Ta fada fuskarta babu alamun wasa.
Amir ne yace shi dai a nan zaiyi hutunsa. Ai kuwa Gimbi ta surfa masa na maguzawa zata huce haushi a kansa. Awaisu ta gani yace yaran su koma ciki.
"Ni