Showing 102001 words to 105000 words out of 112099 words
Chapter 35 - KASHE FITILA Book Complete by Batul Mamman.txt
tun wuri ka fada mata ta fara hada kaya watan zawarcinta ya kama" kit ta kashe wayar ko *a* bai sami damar fada ba. Ajiyar zuciya yayi tunda lafiya take bari ta dawo gidansu zata koma ya gaji haka. Rumana ce ta fado masa ya tashi yayi ciki da sauri.
Fitowarta kenan daga bandakin daure da tawul idanunta sun kumbura sunyi ja. Bata san yadda akayi ba sai gashi a gabanta ya rungumeta.
"Kiyi hakuri Son So nayi miki fada akan abinda bai shafeki ba"
Dan ture shi tayi ta dago kanta. Sai lokacin ya kula da idanun
"Subhanallah kuka kika yi? I am realy sorry bana son bacin ranki. Dazu na rasa tunanin da zanyi ne kawai nace ki tafi kada nayi abinda bazai miki dadi ba. Ashe ma na riga nayi"
Ita dai bata ce komai ba har ya zaunar da ita ya tallafi fuskarta da hannunsa daya, dayan kuma yana wasa da yatsunta ya zauna daga gabanta.
"I love you so much Umm Ruman. Kinga sakona da safe?"
Kai ta gyada wata bakuwar kunya na shigarta.
"Ina so ki zama mai hakuri da juriya akan rayuwa. Yadda na daga miki murya dazu bai kamata ba...."
Girgiza kanta take yi saboda a ganinta bai dace mutum kamar Awaisu yana ta bata hakuri irin haka ba.
"Ka dena cewa nayi hakuru ba fushi nayi ba fa ni bani da lafiya ne."
"Bayar da hakuri yana da mahimmanci a zaman tare."
Saitin zuciyarta ya dafa itama ya dora hannunta a nasa kirjin.
"Yanzu kece nan dina nine nan dinki. Mun zama daya saboda haka kada ki rinka boye min duk abinda yake ranki. Ina reply din sakona na safe ko babu?" Ya tayar da ita zuwa gaban mudubi zai shafa mata mai.
Murmushi tayi kanta a kasa "yana dakinka"
"To muje ki bani"
Turjewa tayi zata masa kuka "ni dai tsoro nake ji Son So ka barni a nan bani da lafiya fa nace"
"Naji ai muje magani zan baki"
Wani irin tausayinta yaji. Yasan yarinya ce dole sai yayi da gaske wurin lallabata. Sonta yake har kasan zuciyarsa baya son yana ganin hawayenta.
"Bacci zamuyi idan kin nuna min reply din naga kin fara tsorata....I promise" ya kare da dariya
Sai lokacin da saki jikinta ya taimaka mata ta shirya suka koma dakinsa. Haka suka kwanta yana rungume da ita a kunne ta rada masa
"I love you Uncle Awaisu Son So"
Nan ya manta da komai ya shiga karanta mata wasu darussan da bata san da irinsu ba a zamantakewar aure.
******
Kiran sallar farko ya tayar da Gimbi ta tashi ta ga Haj Fanta tana sallah. Alwala tayi da sallah amma a ranta tana mamakin ashe dai masu zuwa gun bokaye suna ibada sosai.
Da sukayi wanka suka shirya Haj Fanta taci abinci amma ta fadawa Gimbi tun jiya sako yazo daga Gogojiya kada tasha ko da ruwa ne. Gimbi babu musu tace to tun yanzu ta fara jiyo kamshin sa'a a tafiyar.
Da Mujahid da Yana suka tafi da yake sun fita da wuri goma a cikin Maiduguri tayi musu. Haj Fanta tasa ya kaita unguwarsu Yakura mahaifiyar Yana tace su tafi gidan daya daga cikin yayyensa mata su jirata. Duk su biyun suna son mata tambayar me zata yiwa Gimbi amma babu fuska.
Kafin su sauka tasa Mujahid ya kira kanin Yana mai suna Bukarti ta karbi wayar cikin yaren kanuri ta kwatanta masa Gimbi da inda zai ganta sannan tace yasan yadda zaiyi ya sace mata jakar hannunta batare da ta kula ba. Gaban su Yana har faduwa yayi jin me tace ita kuwa ta matse abinta. Shiyasa suna ajiyeta suka wuce wurin Malam wanda yayi nasarar rabata da aljanunta.
Da yake safiya ce unguwar babu mutane sosai Haj Fanta ta nunawa Gimbi wata hanya wanda idan aka mike zata kai mutum filaye da gonaki ne.
"Gogojiya tace ki dora jakarki a ka sannan kiyi ta tafiyar minti ashirin babu waige a kan hanyar nan. Idan minti ashirin ya cika ki dawo nan inda kika fara sannan ki sake maimaitawa har sai inuwarki ta karkace tana kallon Yamma maso gabashin arewa"
"Me kika ce?" Gimbi ta fada a rude.
Sake maimaitawa tayi sannan tayi dan murmushi "aikinmu tamkar yankan wuka yake"
Jikinta ya fara sanyi tace "to yanzu batun biyan fa"
"Haba Gombo aljanun gaske ko kwandala bai kamata su karba ba. Su da suke bawa mutane sun fi karfin abin. Idan kin gama zaki ga wani yaro matashi zai kwatanta miki gidan da zaki sameni. Na barki lafiya "
Gimbi na gani ta juya tayi gaba ta saita agogon wayarta ta fara tafiya. Ga rana ta take cikin dan lokaci ta fara gumi ga yunwa. Duk wanda yazo wucewa sai ta tambaye shi ko inuwarta ta karkata yamma maso gabashin arewa sai ayi mata dariya. Wurin shadaya da rabi ta tambayi wani mutum shi kuwa gani yayi kamar bata da hankali yace eh. Murna ta kamata ta sami wani tudu ta zauna kenan taga zugar samari suka rufo kamar zasu daketa kawai Bukarti ya sunkuce mata jakar da ta sako takardun filinta. Ihu ta rinka kurmawa ba jimawa sai ga wani yaro yazo bisa umarnin Haj Fanta ko magana baiyi mata ba ya kama hannunta suka tafi gidan Yakura.
Ta gaji sosai kafafunta sunyi futu-futu suka shiga gidan. Haj Fanta ta gani da kanwarta wadda take ta yi mata fadan abinda tayi.
Haj Fanta ta dago ta kalleta cikin bacin rai "Gombo kinyi babban kuskure da kika kawo kanki gidana. Nice mahaifiyar Mujahid mijin Yana wadda kika zubarwa ciki. "
Yakura tace "haba Ya Fanta me zai sa ki biyewa jahila wadda bata san me takeyi ba har ki daukarwa kanki hakkin cutar da ita? Ke Gombo kike ko me fita ki koma inda kika fito"
Gimbi ta tsaya turus tana kallosu. Me suke nufi? Duk wahalar da tasha dama karya ne. Ranta yayi masifar baci ga tsoro sai ga hawaye babu shiri.
Haj Fanta ta harareta "au kuka kike yi tun yanzu? Baki ga komai ba a abinda nayi miki tanadi. Gogojiya kuma yanzu ta fara min wasan kura dake"
"A gaskiya Fanta kin bani mamaki"
Dukkansu ukun suka dago kai suna kallon Dr. Yana da Mujahid sai kuma wani farin dattijo mai shekaru. Fuskarsa ma'abociyar kwarjini da haiba ya hade yace a nuna masa inda zasu zauna magana ce yake so suyi.
[28/08, 19:16] +234 813 154 5123: *KASHE FITILA*💡51
*Batul Mamman*💖
Yakura wani karamin falo ta bude musu daga waje kofarsa take duka suka shiga suka zazzauna. Malam ne kadai akan kujera sauran kowa na kasa. Gimbi ya kalla a nutse ya soma magana bayan basmallah da korar shaidan.
"Baiwar Allah Yaya sunanki?"
Ba karamin kwarjini gareshi a idonta ba tace Gimbiya.
"Na gaskiyar dai. Gimbiya ai ba suna bane"
A hankali ta fadi sunanta yadda ko Haj Fanta da tafi kusa da ita bata ji me tace ba.
"Sunanki mai daraja kuwa...ko zaki iya duba girman Allah ki fada min matsalarki batare da kinyiwa kowa karya ko sharri a cikin labarin ba?"
Dan tunani ta tsaya kamar bazata yi magana ba sai kuma ta fada masa abubuwan da suka faro tun daga lokacin da Awaisu yace zai dauko Maamu da komawarta gida kafin su tare a sabon gidansu, zaman da tayi da Maamu, dinkewa da Anti Bebi da sakin da yayi mata har dai zuwa matsayin da suke a yanzu. Wasu abubuwan ta fada wasu ta sakaya.
Malam yayi ajiyar zuciya yana gajeren murmushi
"wato idan na fahimceki tsoron kada uwarmiji ta kashe miki aure yasa ki yiwa kanki rigakafi kika hau farautar farinciki da kwanciyar hankalinta a gidan danta."
"Malam mata irin wannan Gombon wallahi annoba ne a cikin al'umma. Da Mujahid take aure da ta dade da komawa gidan ubanta..itama surukar taki ina tsamman asirin da kika yi mata bai gama sakinta ba" cewar Haj Fanta tana jin kamar ta hau Gimbi da duka don takaici.
Yakura ce ta dan tabata alamar tayi shiru. Malam yace "barta tayi idan zamana ne bata so a nan din sai na tafi"
Wannan karon Mujahid ne yayi magana "kayi hakuri don Allah"
"To ku bani hankulanku nan muyi magana ta fahimta" duka kuwa suka koma fuskantarsa.
"Tun duniya na kwance lokacin da abubuwa basuyi tsanani kamar zamanin yanzu ba kusan kowa a kowane bangaren duniya yasan da matsalar dake tsakanin uwarmiji da matar danta. Lokuta da dama mata sukan fasa aure idan suka tabbatar gida daya zasu zauna da surukai. Abin mamaki shine wannan rigima kusan iri daya ce a ko ina. *Kishi* ne mara tushe. Ita uwar miji tana ganin ta haifa wata bazata fita morar wahalhalun da tayi da danta ba musamman da tasan kaf duniya tafi kowa iko dashi. Mata kuma tana ganin mijinta ne dole ya sauke hakkinta dake kansa. Kowacce cikinsu tana da gaskiya sai dai duka suna mantawa da cewa matsayi daban garesu a rayuwar namiji idan kowacce ta tsaya a iyakar da Allah Yayi mata dangane da alakarta da mutumin to zata fi kowa samun nutsuwa a rayuwa"
Gimbi ta dakatar dashi tace "Malam ba fa da ka nayi abuna ba. Labarai da yawa naji wasu kuma na gani da idona. Kusa da gidanmu kafin nayi aure uwarmijin a kofar dakin dan take zama har ya dawo komai dare idan da leda ta karba ta raba ko ma menene a ciki nata yafi yawa ta bashi sauran ya kaiwa matar da yaransu. Nawa mijin babana ne ya sama masa aiki kaga kuwa ni nafi dacewa da kyautatawarsa fiye da Maamu."
Harara su Haj Fanta suka rinka maka mata Malam ya jinjina kai "idan da mata goma masu surukai zasu tsaya a wurin nan to ina da yakinan takwas cikinsu zasu miki korafi da uwarmijinsu. Baiwar Allah duk abubuwan da kika sani game da su bazan boye miki ba yawanci duka gaskiya ne to amma fa akwai abin da baku zurfafa tunani akai. Kowacce halitta a duniya baka rabata da kishi. Kuma yawa yawan kishin yana faruwa ne idan kika ga wani ko wata yana samun fiye da abinda kike tunanin hakkinki ne daga wurin wanda ake kishin dominsa. Uwa da kuke ji da gani daraja da kimarta tafi karfin wasa. Baku san ayoyin da Allah Yake cewa ayi da'a gareshi Yake bin wannan umarnin da cewa a kyautatawa iyaye ba. Shi kuma Annabi SAW ya tabbatar mana da cewa a iyayen ma uwa tafi uba cancanta da kyautatawa har sau uku? Cikinku wace bata san wahalar ciki, haihuwa da raino ba? Banda ke Yana muna da miki fata samu amma ana haifa a gabanki ko. Kina mace ki kare wannan wahalar ki dawo gidan danki sai ya baki daki kamar akurki a bayan gida yana ganin alfarma yayi mata. Ita da ta haifa ya tare jikin mata idan taci sa'a ya leko suka gaisa kamar yana kan kaya zai tashi yayi gaba. Ya koma rayuwa daga shi sai iyalinsa ita uwa ko iyayen duka biyu kuji ana cewa haka zamuyi ta hakuri dasu har a rabu lafiya. Allah sarki iyaye mutuwarsu kawai 'ya'yan ke jira su cigaba da fantamawa babu damuwar komai a ransu. Ana haka ko ba'a yi? "
Jikinsu ya fara sanyi harda Gimbi kuwa suka ce anayi. Malam yace "to wannan dalilin ga kuma rikici na girma suna taimakawa wurin sanya uwarmiji takurawa surukai. Itama taji labari ko ta gani ya faru da wata sai tayiwa kanta rigakafi irin yadda kika yi" ya yi maganar yana kallon Gimbi.
Shiru tayi tana tunanin rayuwarta. A iya saninta zata iya rantsuwa ko sau daya Maamu bata taba yi mata kallon banza ba tun kafin zuwanta Abuja. Kafin abubuwa su lalace ba ita kadai ba hatta Baaba Hure da 'ya'yanta basu taba saka mata ido ba. Wata zuciyar tace mata amma duk don suna son turo miki Maamu ne da 'yarsu ya aura. Kwanciyar maciji suka yi miki sai kin sakankance kiji harbi irin yadda suka so yi ba don kin taimaki kanki ba. Kallonta su Malam sukeyi ta zurfafa a tunani. Ta dago kai
"yanzu kana nufin dai komai laifina ne, nayi ba daidai ba saboda na nemawa kaina da yarana 'yanci?"
Wannan karon yaji ta soma bashi haushi ana ga yaki tana ga kura.
"Baiwar Allah da kinsan girman zunubin da kika aikata bana jin zakiyi magana irin wannan. Duk duniya babu zunubin da ya kai shirka kuma kinyi. Manzon Allah SAW ya fada mana mu al'ummarsa cewa mu dage duk runtse mu mutu muna musulmai, saboda Allah mai rahama ne da jinkai yasan cewa indai laifi ba hakkin wani muka tauye kamar yadda kika yi ba to idan Allah Yaso duk tulin zunubanmu sai Ya yafe mana Yace mu shiga aljanna cikin rahamarSa. Duk wanda ya mutu yana mai imani da bokaye da malaman tsibbu mushirikine ko yaki ko yaso."
Gimbi ta dafe kirji "A'a fa Malam ni ba imani nayi dasu ba tunda ina sallah ina azumi "
Murmushi yayi mai ciwo da nuna bacin rai saboda masu bin bokaye da dama haka suke cewa su musulmai ne alhalin daga lokacin da ka yarda wanin Allah zai iya biya maka bukata to ka tabe kai da rahama sai ranar da kayi tuba irin wanda sharia ta aminta dashi.
"Gimbiya! In tambayeki mana shin tunda kika shiga matsalolin nan kin taba daga hannu kin roki Allah Ya yaye miki a matsayin Ubangijinki majibincin lamuranki?"
Nan ake yinta, tabbas bazata iya tuna yaushe ta kai kukanta ga Allah ba. Hasali ma sai yanzu ta farga cewa kullum fa burinta a sami bokan da yafi kowanne kwarewa a aiki. Jikinta a take ya fara rawa kamar mazari da ta tuna duk wata kadararta ta kare a gidan boka.
Basmallah yayi yace " *WA IZA SA'ALAKA IBADI ANNI FA INNI QAREEB. UJIBU DA'AWATAD DAA'I IZA DA'AN. FALYASTAJIBULI WAL YU'MINU BI LA'ALLAHUM YARSHIDUN* " Ayar da duka suka ji Malam ya karanto kenan yana karewa sai hawaye ya ziraro daga idonsa daya.
Daga nan fa kwakkwaran motsi duka sun kasa saboda firgici da tuna ayar Allah musamman wadanda suka fahimci me ya fada da larabci.
Malam yace cikin murya da yanzu take nuni da bacin rai da son firgita mai sabo
"Kina ina Allah SWT girma, da isa da buwaya sun tabbata a gareshi baShi da matamaki azza wa jalla sarki zuljalali wal ikram Yake cewa Annabi Muhammad SAW idan bayiNa suka tambayeka game daNi ka fada musu cewa Ina kusa...wannan kusancin ina mai tabbatar muku cewa Allah Yafi jijiyoyin dake cikin jikinmu suna gudanar da jini kusanci damu. Sannan yace Shi Ubangijinmu mai jin addu'ar mai roko ne idan ya roke shi. Saboda haka mu roke Shi kuma muyi imani daShi ko zamu samu shiriya. Na rantse da Sarkin da Ya busa min numfashi wannan ayar tana kwantar da hankalina da sanya nutsuwa a lokacin damuwa. Idan har bawa ya tuna wannan zance na Mahaliccinsa kuma yana ikirarin imani da musulunci to babu abinda zai dame shi ya kasa daga hannu ya kai kukansa inda za'a share masa hawaye."
Idanun Gimbi a take suka shiga kwararar da hawaye masu zafin gaske.
Malam kuwa cikin daga murya domin ya kara tada mata da hankali ya kori duk wani sauran shaidanci da yake yawo a zuciyarta ya cigaba da magana.
"Kina da Ubangijin Annabi Muhammadu me ya kaiki wurin boka? Kina da Sarkin da gyangyadi bai taba daukarSa ba me ya kaiki wurin wanda ko yau ko gobe rana zata zo da za'a turmutsa shi a kabari? Kina da Mamallakin sammai da kassai wanda Yace da zai biyawa dukkanin bayinSa na farko zuwa na karshensu dukkan bukatunsu to babu abinda zai ragu daga taskarSa. Har Annabi SAW ya bamu misali da cewa kamar fa a tsoma allura ne a cikin makeken teku a tsamota. Kai mata! Kuna da Sarki mai _kun fa yakun_ me yake kaiku wurin kazaman bokaye a dazuka suna shiga tsakaninku da ganin hasken rayuwa? Bokayen da suke nema daga aljanu su kuma aljanun suke sata su basu ko kuma suje su yi ta sanya wasi wasi a zukatan bayi su farraka masoya su bata alkhairi su maye gurbinsa da sharri. Idan kura tana maganin zawo ya kamata bokaye sufi kowa kudi da samun manyan mukamai a duniya amma sai kiga mutum a jeji yace zai biya miki bukata amma sai kin biya wasu makudan kudade kin kuma bar ibada. Bayan kuma wanda Ya halicceki domin ki bauta Masa baYa gajiya da jin rokon bayinSa. Koda yake rashin hakuri shine babbar matsalarmu munfi son mu roka mu ajiye hannu tare da biyan bukata. Sai dai Allah Yafimu sanin me ya dace damu a kowane mataki na rayuwa. Shine mai biyan bukata take yanke sai dai Yakan jinkirta mana zuwa lokacin da amsawar adduar yafi dacewa."
Zuwa yanzu ba Gimbi ba hatta Haj Fanta kuka suke yi sosai. Gimbi ta dafe kirjinta tana kiran ta shiga uku ta cuci kanta.
"Muddin kina numfashi baki shiga uku ba domin kuwa addua bata barin komai" cewar Dr. Yana.
"Ina so ku sani cewa rayuwa da mutuwa gaskiya ne kuma zaman kabari da busa kaho abu ne tabbacce da zai faru komai nisan lokaci. Gimbiya ki kiyaye ranar da zaa tona rami a kasa a sanyaki daga ke sai halinki Mala'iku su zo gareki domin amsa tambaya. Shirka bala'i ce, bokaye da yan tsibbu da matsafa duka masifa ne, sannan duk wata halayya da mutum zai tsira domin haddasa husuma tsakanin mutane ko da ba masoya bane halaka ce gareshi. Allah mai rahama ne da jinkai...ni da ku duka muna kyautata Masa zato da kwadayin ranar da Zai umarcemu da shiga aljanna mu rayu cikin ni'ima. Jahannama da Qur'ani da Annabi SAW suka bamu labarinta wuta ce da ko tururinta bazamu jura ba balle ita kanta. Kuma kada kuji da wai, ana gama hisabi zaa kawar da mutuwa babu wanda zai kara mutuwa. Rayuwa ce ta dindindin har abada. Ko ba'a tambaya ba nasan babu wanda zaiso yin yini daya cikin wuta balle rayuwa mara yankewa. Mijinki yana da rai sannan surukarki tana da rai saboda haka zabi ya rage naki"
Kuka mai tsuma zuciya Gimbi take yi saboda tausayinta su Dr. Yana ma kukan suke yi.
"Allah na tuba! Allah na tuba!! Malam yaya zanyi na kankare wannan masifar da na janyowa kaina da hannuna daga littafina? Malam yaya zanyi idan aka bani littafina ranar lahira a hannun hagu? Shikenan ni bani da