Showing 36001 words to 39000 words out of 112099 words
Chapter 13 - KASHE FITILA Book Complete by Batul Mamman.txt
rufe gate.
[15/08, 17:45] +234 803 272 5896: *KASHE FITILA* 💡27
*Batul Mamman*💖
_Taqabbalallahu Minna Wa Minkum_👏🏽
Wani irin numfashi Anti Bebi ta rinka saukarwa mai kama da gurnani. Bata san tsahon lokacin da dauka a haka ba sai ji tayi ana kwankwasa glass din motar ta saitin inda take. A firgice ta bude ido ta saukesu kan wasu jajayen idanu manya. Tafiya tayi luuuu zata sake suma taji ance
"baiwar Allah lafiya kike?"
Mace ta gani a kusa da mai jajayen idanun taji hankalinta ya kwanta. Da sauri ta bude ta fito. Sai a lokacin ta kula mutane sun kai biyar da suka zagaye motar ana tunanin ko wani abu ne ya sameta. Karyar ciwo tayi musu ta kulle motar ta nemi tasi ta shiga. A cikin motar ma duk da shata tayi ta zauna a baya amma haka taji duk an matseta. A takure ta isa gida babu damar magana don shi kanshi dreban motar tsoronsa take yi.
******
Da shigar Anti Bebi gida ta soma kiran Wangesi baya dauka. A yadda take jin jikinta kamar ana daureta dole ta tafi wurinsa neman taimako. Drebanta ta kira bata la'akari da yamma ta kawo kai tace su tafi kan tudu wurin Wangesi.
Sun isa farko-farkon magriba. Jikinta duk ciwo yake mata saboda wata irin matsuwa da tayi a bayan motar. Gashi dai ita kadaice amma kamar su biyar ko shida take jin sun zauna a takure. Tsabar sauri kafarta daya babu takalmi haka ta fada cikin gidan Wangesi. Dakin da yake ganin bakinsa irinta ta shiga ko iso bata tsaya yaransa da suke masa aiki sunyi mata ba.
Mata uku ta samu a wurin suna gabatar masa da matsalolinsu. Yana ganin Anti Bebi kamar an jehota daga sama ya mike tsaye
"Hajiya Bebi lafiya?"
Haki take yi tana maida numfashi da kyar murya a sarke tace "ina fa lafiya Wangesi yau nayi gamo"
Matan da suke dakin suka fara kallon-kallo. Wangesi ya samu ta dan nutsu ta labarta masa abubuwan da suka faru da ita tun daga farko.
Wani tsalle ta ga ya daka ya daga hannuwa sama
"Ehooooooo, Ehooo. Waye yace dani bani ba? Sai ni nan uban kan tudu mai aiki da hatsabiban aljanu"
Juyi yake yi yana furzar da yawu ransa yayi matukar baci. Can ya fita ya dawo da wata tukunyar kasa sai wari take yi.
"Bebi tun farkon zuwanki wurina sama da shekara goma me na fada miki?"
A daburce ta tambayeshi "meye hadin farkon zuwana da wannan masifar da na tashi da ita?"
"Bari na tuna miki idan kin manta. Aljanin da yake miki aiki baya son kishiya kuma na sanar dake duk ranar da kika je wurin wani bokan yace a bata duk wani sihiri da aka taba yi miki. Sannan ki jira abin da zai biyo baya. Na tabbata wurin wani kika je shiyasa haka ta faru"
Idanu ta zaro kamar su zube a kasa "ni kuwa me zai kaini wurin wani ina da kai....na rantse maka da....."
Tusssss taji kafin ta gama rantsuwar ya saki tukunyar da take kunshe da dukkan wani asiri da ya taba yi mata.
"Aljanin bashi da hakuri ko kadan Bebi. Ki fita daga gidan nan kafin yazo mu duka mu fuskanci bacin ransa."
Matan nan uku na jin haka suka runtuma a guje. Anti Bebi kuwa a gaban tukunyar ta durkusa tana wanj gunjin kuka
"Wangesi ka tona min asiri. Cikin kasa da awa biyar duniya tayi min juyi irin wannan? Na shiga uku...."
Kara murtuke fuska yayi "ke kika janyowa kanki ko ma menene. Ki fice min daga gida kafin ya iso gareki"
Jikinta sam babu kwari ta mike tsaye da kyar. Zuciyarta ke fada mata ko dai mafarki take yi duk wannan bala'in ba gaske bane. Da jan kafa ta fita waje. Tana sa kafa a wajen taji an rungumeta tsam ana yi mata magana a kunne har tsigar jikinta na tashi
"Oyoyo Bebi, kika barni ina ta jiranki a nan. Zo mu tafi na fara jin yunwa"
Drebanta yana cikin mota ya hangota ta fadi a sume ya fito a guje ya fara neman yadda zai sakata a mota.
*****
Maamu ta gama cin tuwo kenan Baabu Hure ta shigo dakin suka fara hira. Cikin hirar Baaba ta sako zancen auren Awaisu da yake ta matsowa
"Yanzu Maamu kina ganin babu matsala wannan auren na yaron nan? Kin dage sai anyi auren nan ba kya tunanin kada matsala ta taso ganin akwai alaka tsakaninta da Gimbiya"
Hannun Baaba ta kama ta rike tana magana a hankali "Baaba Hure ina ganin a bar maganar auren nan kawai. Ni bansan me ya kaini tunanin hadasu ba "
Baki Baaba ta saki tsabar mamaki ya cikata. Maamu da har kusan kuka take yi akan anki gaggauta auren shine zata ce ta fasa. Anya mutanen nan haka suka barta kuwa?
Katse mata tunani tayi da muemushin da yafi kuka ciwo
"yarinyar nan Gimbi nake so ayi masa bikonta. Ita kuma waccan sai a basu hakuri. Ba kiji yadda raina ke suya ba idan na tuna uwardakinta Bebi dinnan. Matar tsoro take bani."
Baaba kasa magana tayi don abin yafi karfin mamaki. Maamu sai magana take yi mara kan gado. Karshe ta kwanta ta juyawa Baaba baya. Tashi Baaban tayi zata fita taji sheshshkar kukan Maamu. Fita tayi tana share kwalla. Ta rasa mene ne yake damun Maamu da har take kuka amma ta kasa fadawa kowa damuwarta.
*****
Daren ranar Anti Bebi tamkar tayu hauka. Dadinta ma Alh Maitama yayi tafiya. Shuhada kuma ganin yadda ta shigo musu a birkice ko ta kanta bata bi ba.
A bangaren Gimbi tun da ta koma gida ta kasa nutsuwa. Zuwa yanzu yaci ace aikin bokan Ovi ya fara kamawa. Idan taji shiru har safiya tasan akwai matsala dole ta canja salo. Wurin shadayan dare wayarta tayi kara alamun text ya shigo. Tayi zaton kamfanin layin wayarta ne ta share. Sai dayan dare ta dauki wayar zata duba lokaci ta ga sakonni sumfi hamsin daga Awaisu wanda mugun son Gimbi yayi masa kawanya a zuciya.
Murmushi tayi ta duba na farkon
(Na mayar dake Gimbiyata ki dawo gareni
Na biyun kuma
(Ki bani izinin kiranki a waya)
Haka tayi ta bin sakonnin tana karantawa a tsaye don zama ya gagareta. Murna take yi mara misaltuwa. A daren ta hada kayayakinta ko runtsawa ta kasa yi. Kafin takwas na safe ta turo akwatunanta falo tana kiran maigadi yazo ya kai mata mota.
Hayaniyarta ce tasa Mama fitowa ta ganta a shirye zata fita.
"Ina zuwa da sanyin safiyar nan?"
Fuskarta na nuni da tsananin farinciki ko gaishe da Maman bata yi ba ta mika mata wayarta
"Gida zan tafi Abban Haris ya mayar dani"
Marinta Mama tayi niyar yi sai ta fasa ta samu wuri ta zauna a sanyaye
"Gimbi a tunaninki abubuwan nan da kike yi kin dauko hanya mai billewa kenan? Da ban fito ba sai dai mu nemeki mu rasa kenan ko. Hmm bazanyi miki baki ba amma ina mai baki shawara ki kiyayi duniya. Komai nisan jifa kasa zai fado, komai nisan dare gari zai waye...karshe kuma ki sani abin da ka shuka shi zaka girbe."
Kallon Mama tayi na dan lokaci sai kuma ta figi karamin akwatinta tayi gaba tana cewa ta gaishe da Babanta idan ya tashi. Tana fita Mama ta fashe da kuka tana yiwa Anti Bebi Allah Ya isa.
******
Cikin bacci yake ta buge buge batare da ya sani ba. Kana ganinsa kasan duk yadda akayi mugun mafarki yake yi. Mutanen kusa dashi suka fara juyowa ana kallonsa. Hakan yasa abokinsa da suke tare Kamilu ya soma girgiza shi.
"Kai T a train muke fa. Meye haka?"
Tajuddeen ya bude idanunsa da suka masa nauyi a hankali. Hannun Kamilu ya damko tamkar wanda zai gudu ya barshi.
"Kamilu meyasa na saki S?"
Harara Kamilu ya jefa masa sannan ya fizge hannunsa
"Dalla malam cikani"
Tajuddeen ya sake rike masa hannu
"wallahi Kamilu da gaske nake. Haka kawai fa ranar na shiga gida na hauta da fada mara dalili sannan na saketa"
Kamilu sake hararsa yayi sai ya kula hawaye Tajuddeen yake yi. Zuciyarsa ce ta dan karye ya dafa kafadarsa.
"Wannan ba magana bace ta nan T. Ka bari mu karasa gida sai muyi a nutse. Kaga sai kallonmu ake yi"
Ba don yaso ba ya hakura amma da shigarsu gidan Kamilu ko zama basu yi ba Tajuddeen ya sake tado maganar.
"Wai T kayi gamo ne a train dazu? Dama wani shure shure naga kanayi cikin bacci har kasa ana kallonmu. Anyways me kake son ji game da rashin mutumcin da ka aikata"
Sunkuyar da kai yayi yana tuna ranar da ya saki Shuhada da irin wulakancin da yayi mata.
"Bani da wani dalili na abin da na aikata Kamilu. Haka kawai kamar wanda akayiwa asiri. Saki har uku" ya karashe hawaye na bin kuncinsa.
Duk irin haushinsa da Kamilu yake ji dole ya tausaya masa.
"Al'amarin nan naku da daure kai. Kasan da ka dena kiran mutanen gida akan fadan da suke maka na sakin da kayi Umma ni take nema. Kuma abin mamaki ana nake jin ashe itama Mummynsu Shuhada itama nata auren ya mutu"
Tajuddeen ya dan kada kai "kasan labari mara dadi babu amfanin bayar dashi. Shiyasa ban taba fada maka ba. Baffanmu ya bani labari ba karamar soyayya bace tsakanin iyayen S. Kasan duk garinsu daya. Shiyasa muka yi mamaki sosai da yayi sakin. Tunda ya auro wata mata Bebi shikenan gidan ya rikice."
"Bebi fa kace" Kamilu ya maimaita da sauri.
Kai Tajuddeen ya gyada masa kawai.
"Bebi dai wata doguwa siririya ko, idan tana tafiya duk jikinta sai ya motsa"
Murmushin dole T yayi saboda yadda Kamilu yake kwatanta Anti Bebi
"Ita ce, ka santa ne?"
"Allah Masani amma ina kyautata zaton ita ce sanadiyar wannan sakin naka da na baban Shuhada. Ta taba auren wan mamanmu, cikin wata biyu sai da ya saki matansa uku da suke gidan. Dama cikon ta hudun ya saka ya aurota. A shekara dayan da sukayi tare sai da ya zare hannunsa kan duka yaransa daga shi sai Bebi poison yadda yaran suke kiranta"
Lallai biri yayi kama da mutum. Dama irin labaranta da yaji daga wurin S da kuma wanda ido ya gane masa yasan zata aikata. Muguwar tsanarta ce ta kara shigarsa ya fara tunanin irin hukuncin da zaiyi mata.
Kafadarsa yaji an dafa ya kalli abokinsa Kamilu
"Wallahi bata ci bulus ba. Gida zan koma a cikin watan nan. Kafin nan za ka rakani wurin Suhail a makaranta"
*****
Awaisu tun jiya ya kasa zaune ya kasa tsaye saboda tunanin Gimbi. Kafin gari ya waye sau uku yana kukan da ya rasa dalilinsa. Shi dai a iya saninsa da kansa ya saketa saboda baya son halayenta. Yanzu kuma ya rasa wace jarabarce tasa duk da baya son halayen nata yake jin idan bai dawo da ita ba komai zai iya faruwa dashi. Haka nan a daddafe ya jira gari ya waye ko wanka baiyi ba ya fita zuwa gidan Alh Mudi bikon matarsa.
Mama da Alhajin ya tarar suka gaisa a mutumce sannan suka sanar dashi ta tafi gida. Ko sallamar kirki bai iya yi musu ba ya fice.
"Amina kada fa Allah Ya kamamu da hakkin Awaisu. Kinga babban mutum ya zama wani lusari akan mace."
"Alhaji na fika damuwa domin ta bangarena Gimbi ta samo wannan mugun halin. Na rasa yadda zanyi da ita" kuka ne ya kwace mata na takaicin halin 'yarta Alhaji yayi ta rarrashi da bata baki akan su dage da addua.
Gida Awaisu ya wuce ya fara karo da wani mugun hayaki da Gimbi ta soma yiwa gidan. Suna hada ido ta fito rike da kasko a hannunta yaji jikinsa ya mace bashi da wani kuzari. Da fara'a ta tarbe shi suka shige daki yana binta kamar rakumi da akala.
Ko awa biyu batayi da dawowa ba tace ya tura dreba a dawo mata da yaranta. Haka kuwa akayi babu musu ya tura dreban yace a dauko harda Maamu da Rumana da sassafe washegari su taho.
Rumana tayu kuka har hawaye suka nemi kafe mata saboda bakincikin komawa Abuja. Maamu kuwa bata iya cewa komai ba. Haka suka shirya da safe Harisu yana ta mita suka tafi. Bayan fitarsu ya kira Awaisu ya nuna rashin jindadinsa game da hakan amma yayi masa uzuri tunda babu mata a gidan. Awaisu bai nuna masa Gimbi ta dawo ba sai da yace zasu taho biko sannan ya fada masa. Har ya ajiye wayar yana ta mamakin sauyi irin wannan daga kaninsa.
*****
Anti Bebi na kwance a daki tayi zuru zuru saboda yadda aljanu suke wasan 'yartsana da ita a daki. Tana zaune zata ji ana fadan waye zaiyi mata wanka da mai taje mata kai. Gashi Alhaji ranar zai dawo. Shuhada ta leka dakin sau biyu tana ganinta a zaune ko gaban mudubi ko a kan gado shiyasa bata kawo komai a ranta.
Kofa taji ana tabawa ta zabura ta tashi tana jan bargo zata rufe kanta. Alh Maitama ne ya shigo a fusace Shuhada tana biye dashi tana tambayar me ya same shi. Wurgi yayi da jakarsa da babbar riga da ya dawo dasu a hannu ya haye gadon ya finciko Anti Bebi.
"Munafuka algunguma zo ki fita daga gidan nan"
Tunda Wangesi ya juya mata baya dama tasan tata ta kare sai dai batayi tunanin abin zai kai haka ba. Tattaro dan karfin hali tayi harare shi
"Alhaji ni kake yiwa tsawa haka"
Mari ya rinka zabga mata Shuhada da take gefe ta tsorata sosai. Tana kallo babanta yayiwa Anti Bebi duka kamar bazai barta da rai ba sai da ya gama ya koma wurin 'yarsa ya rungumeta yana kuka
"Shuhada kuyi hakuri na dauko muku jaraba ta wargaza mana gida. Ni yanzu Kaduna zani wurin Mummynku."
Kukan farinciki take itama tace zata bishi. Cewa yayi ta shirya tana fita ya rufe kofar dakin da mukulli
"Hajiya Bebi so nake duk inda takardun kadarorina suke ki dauko ki bani tun muna shaida juna. Na rantse miki ko tsinkina bazaki tsira dashi ba."
Dan abin da take sa ran tsira dashi taga Alhaji zai shiga tsakani ta fara tsiwa baki bai mutu ba. Ai kuwa ta jawowa kanta sabon duka. Sai da taji kamar bazatayi rai ba ta tashi da kyar ta dauko masa wasu da suke dakin. Sauran kuwa a wani store taje ta dauko. Security yasa suka tafi da ita police station yace zaiyi waya da komishina. Burinsa a tsareta har ya dawo daga wurin uwar 'ya'yansa.
Sai bayan sati uku aka maida auren iyayen Shuhada. A lokacin Anti Bebi duka accounts dinta Alh Maitama yasa an rufe ya bita da saki uku kwarara.
A bangaren su Gimbi wannan dawowar su Maamu suna gasuwa sosai. Kanwar Ovi mai suna Rita ta dauko matsayin mai'aiki. Itace kuma yar aike zuwa gurin boka. A haka ne wahala tayi wahala Rumana tayi suman karya ta samu ta koma Fika gaban iyayenta.
*Wasa farin girki*
_ayi hkr da rashin editing_
[15/08, 17:45] +234 803 272 5896: *KASHE FITILA*💡 28
*Batul Mamman*💖
Maman Rumana ta daga labule ta shigo daki da sallama ta tarar da Rumana tana zazzaga madarar cowbell a hannunta tana lasa. Har wani lumshe ido take yi tana kada kai duniya ta samu. Ran Mama ya baci ta kai mata duka a gadon baya.
"Tun dazu nake kiranki kunnenki kamar an toshe da auduga kin kasa ji bare ki amsa"
Watsi tayi da madarar ta hau sosa wurin da hannuwanta duka biyu ta soma bata hakuri. Mama ta cigaba da mita
"Tun da kika dawo gidannan sai cin tsiya da kwadayi kamar 'yar yaye. Da girmanki kike wani lasar madara"
Rumana ta dan murmusa "wallahi Mama protein ne yayi karanci a jikina."
"Ke kika sanshi ni ban sanshi ba"
"Mama wai baza'a dauko Maamu bane? Ta fini shan wahala sosai" sai kuma ga hawaye ta fara kukan rayuwar da ta baro Maamu a ciki. Sau biyu tana mafarkinta kwana biyun nan duk ta damu. Jin Maman bata ce komai ba ta dan matsa kusa da ita.
"Mama don Allah ki yiwa Baba magana kada ta mutu da yunwa.."
"Kada na sake jin wannan maganar a bakinki. Yanzu haka babanku zaiyi bincike kuma wallahi idan karya kika shara mana don kawai ki dawo nan kema kinsan bazata kare miki da kyau ba. Kuma zamu tattaraki ne a mayar"
Zumbur ta tashi tsaye jin hakan "Mama ni da gidan Uncle Awaisu fa har abada. Kai ni ko Abuja bana fatan Allah Ya sake kaini. Mama! Mama!! idan kuka mayar dani Abuja wallahi guduwa zanyi na shiga duniy... "
Bakin nata Mama tayi saurin dokewa kafin ta kai karshe. "Bana son sakarci kinji ko, wace irin magana ce wannan fita ki bani wuri"
Rumana ta juya ta fita baki na radadi suka hada ido da Baaba Hure wadda ta gama jin hirarta da mahaifiyarta. A guje ta bar wurin tana tsoron ko kakarta taji abubuwan da ta fada.
Sai dare Harisu ya dawo Baaba Hure ta zaunar dashi ta fada masa abin da Rumana ta gayawa Mamanta.
"Tun da Rumana ta iya bushe ido da zuciyarta ina kara tabbatar maka da cewa da wuya idan karya take yi musu. Kafin abubuwa su kara lalacewa gara ka shirya kaje Abujan kamar yadda ka fadawa Maamun a waya kuyi magana da ita. Idan akwai cutarwa ta dawo nan muyi zamanmu. Ana uwar miji na gasa suruka ita kuma matar dan ce mara kirki "
Harisu da baya son rigima yace "haba Baaba ai baki tabbatar ba. Ba don al'amura sun taso min ba ai da tun shekaranjiya zan tafi Abujan ma"
Haka suka yi ta shawarar yadda tafiyarsa zata kasance jibi sannan ya tashi ya tafi nasa dakin. Rumana duk abin duniya ya isheta saboda kewar Maamu da halin da ta barota.
*****
Kwance Gimbi take tana karkada kafa daya tana tunanin yadda take cin karenta babu babbaka. Yanzu jin kanta take yi daidai da kowa. Miji yana da kudi kuma yana tafin hannunta.
"Uwarsa kuma ta zama hoto abin kallo." ta fada a fili tana murmushi. Kafin ta hanata zaman gidan mijinta ita tayi saurin maganin abin. Anti Bebi ce ta fado mata ta kwashe da dariya har da kyakyatawa. Ko ina take yanzu oho. Cikin dan lokacin da bai wuce wata guda ba ta gina fadarta yadda take so. Agogon wayarta ta kalla biyar da rabi ta dan wuce ta fito zuwa dakin Maamu.
Tana zaune akan abin sallah ta kara ramewa duk ta dashe ta jingina bayanta da bango tana kallon fanka tana tunani. Jin muryar Gimbi a kanta ba karamin tsoro ya bata ba ta dawo