Showing 81001 words to 84000 words out of 112099 words

Chapter 28 - KASHE FITILA Book Complete by Batul Mamman.txt

23 Jun 2024

14026

ne. Ya zama dole ginin da ya soma ya banzatar ya cigaba da yinsa saboda babu yadda za'ayi idan ta tare duk lokacin da zasu zo garin ya tare musu a gida shi ba yaro ba yana rabe-rabe idan zai ga matarsa.


Idan ya shiga tabbas akwai yiwuwar haduwa da Mama sannan idan bai je ba sai su iya tunanin bai damu da ita ba. Uwa uba yadda ya matsu ya sanyata a idonsa bazai barshi ba. Shiga cikin gidan kawai yayi ya gaisa da sauran matan gidan da ya gani suna fitowa daga kofar dakinsu Rumana.


Har yaje bakin kofar sai kuwa ya jiyo muryar su Baaba da mama. Maamu wadda bai san itama tana ciki ba yaji tana cewa dasu Baaba


"Yarinyar nan duk wata haka muke fargaba idan ta kusa a gidan Kawunta. Saboda ciwo dama indai a gida ta fara ranar bata zuwa makaranta. Da yake babu wanda ya damu da lamarinmu lokacin haka zata ci ciwonta na kwana biyu sannan ta ware. Idan munyi sa'a kuma kwana daya take ta tashi "


Mama yaji tace "sai dawowarta muka san tana yi amma idan anyi mata allura tana dan samun sauki"


"Mata sai hakuri wai kafin ayi maganar ciki da haihuwa ma fa kenan. An fadawa mijinta?" Cewar Baaba.


"Ai kuwa a tura yazo maza-maza ya kaita asibiti idan tayi wanka. Sannu kinji Rumanan Maamu" Maamu ta fada tana tashi ita da Baaba.


Awaisu na jinsu ya dan ja baya don bazai shiga Mama tana ciki ba. Da suka fito gaishe su yayi ya tambayi mai jikin a ransa yana cewa mai yasa ta zauna a dakin da bazai sake ba. Baaba tace ya shiga tana ciki yayi saurin sake yin baya yana cewa zai dawo ya dubata. Murmushi tayi tace masa yaje dakinta ya jirata tana zuwa zasuyi magana ita kuma ta koma dakin.


"Rumana zaki iya tashi?"


Mama tace "tun dazu nima nace ta tashi ta kasa kafar taki daukarta"


Baaba ta fita ta kira Anti Amarya da kanta tace ta kama Rumana ta mayar da ita dakin ita Baaban saboda a nan hayaniya bazata bari ta huta ba. Suna fita ta mayar da hankalinta ga Mama wadda ta kasa fahimtar dalilin Baaba.


"Awaisu na gani a kofar dakin amma nauyi ya hana shi shigowa" tayi murmushi ganin Mama ta dan sunkuyar da kai itama sannan ta cigaba da magana


"Dama ina so nayi miki godiya da baki tayarwa mijinki hankali akan auren nan ba. Nasan dole zaki ji babu dadi kiga an hadata da mutum kamar Awaisu mai shekaru kusan arba'in. Amma kamar yadda na riga nasan kin sani kowane bawa yana da kaddarar da Allah Ya rubuta masa"


Mama tace haka ne. Baaba ta cigaba da cewa "addua'armu bata wuce Allah Ya basu zaman lafiya da juna. Mu namu auren ma ko shekarunta bamu kai ba. Nasan wacece Rumana a tarbiya shiyasa banji komai ba na bada goyon baya ga bukatar Maamu. Abu na gaba da nake son jan hankalinki shine ko da nan gaba Awaisu ya nemi karin aure saboda yayi alkawarin rabuwa da Gimbi don Allah kada ki tada hankali ganin tana da kuruciya. Bai zo min da zancen ba amma kinsan yau da gobe sai Allah. Ko ba komai ina ganin tayi kankanta da daukar dawainiyar miji da yaransa wanda suka tashi kamar kannenta ita kadai."


Mama da taji yar kwalla ta tarar mata saboda tausayin Rumana tace "Baaba kada ki damu in sha Allahu tsakanina da ita sai karfafa gwiwa da fatan alkhairi. Kuma ni a nawa ganin gara yayi aure idan yana da ra'ayi saboda nasan a yanzu kam wani lokacin sai yaji kamar ya zaneta" tayi dariya.


Baaba ma dariyar tayi "Yo wannan shirmen nata ai shi ne zai kara sawa ya sota. Ku yaran yanzu baku san komai game da soyayya ba. Misali yanzu da bance ta tafi dakina ba haka zaki barta a nan shi da yazo saboda ita haka zai juya gobe ya tafi. Dan irin wannan lokutan kamata yayi a barsu tare tunda matarsa ce. A haka zasu saba tunda ba wani lokaci sosai tarewa zatayi. Idan akayi tariya tana tsoronsa ko ta kasa masa kallon miji kinga babu kanta."


Mama dai kunya taji sosai amma tasan halin Baaba. Ko a gaban waye duk mai girki cikinsu idan Harisu ya dawo ta rinka cewa bata son gulma a tashi a bi miji. Tun suna jin kunya har ya zama indai ya dawo ko tana wurin sai su tashi.
******


Awaisu yana zaune jiran Baaba amma hankalinsa gabadaya yana wurin Rumana da tunanin wane irin ciwo ne yake damunta haka.


Muryar Rumana yaji tana cewa bazata iya cigaba da tafiya ba Anti Amarya na cewa tayi hakuri saura kadan. Tasowa yayi ya fito Antin na ganinsa tayi murmushi "wato Baaba turo maka matarka tayi kayi jinya. To ni nayi nan ku karasa"


Hannun Rumana ta mika masa ya riketa ita kuwa ta juya tana tsokanarsa. Ko gama tafiya batayi ba Awaisu ya dauki Rumana tana ta mutsu-mutsu ya shige dakin da ita. Kan gado ya kwantar da ita fuskarta da sauran hawayen da take ta yi saboda ciwo.


Tausayinta yakeji sosai ya zauna a gefen gadon ya rike hannunta na dama.
"Me ya sami Son So dina?"


Ga ciwo kafafunta kamar ana sarawa ga kunyar an kawota dakin wurinsa ta rufe ido kawai. Matsawa ya sake yi kusa da ita kamar zai rungumeta kamshin turarensa ya mamaye wurin shi kadai take shaka.
"Naji Maamu tace duk wata kike yi. Period pain ne yake kama miki kafa?"


Wata irin kunya taji duk da ciwon da take ji ta soma sunne kai. Shi kuwa murmushi yayi yana tsareta da ido gashi yayi kusa da ita sosai
"Ashe dai ba kwaila na aura ba. Nana da shekara zaki shaifa mana babyn So"


Kunya ta kamata amma dayake ba wuya tayi dariya saboda kalmar kwaila da yace sai gashi tana yi a hankali amma taki kallonsa. Yaji dadi ganin ta dan sake dama tsokanarta yakeyi don ta saki ranta ta dena hawayen.
"Kada ki damu kin kusa denawa in sha Allah."


Dan ware ido tayi "da gaske Uncle?"


Shan kunu yayi "nima sunana Son So kema kuma sunanki kenan"


A hankali ta dago ta kalle shi amma bata yarda sun hada ido ba. Wani iri take ji a ranta game da Uncle Awaisu musamman idan yana mata irin wannan abin kamar yaro daidai da ita.


"Mace da namiji duk suna daya?"


"Mata da miji dai zaki ce"


Fuskarta ya gani ta chanja alamun tana jin jiki ya gyara zamansa sannan ya dago kafafunta ya dora a cinyarsa. Janyewa take son yi ya rikesu
"Ki bari idan ba kina so muyi rigima ba. Matsa miki zanyi ko zaki ji saukin ciwon."


Dogon wandon bacci ne a jikinta rigar kuwa baya iya gani saboda hijab da tasa wanda ya sauko har kusan cinyarta. Tausa ya soma yi mata a hankali yana matsa kafafun tana lumshe idanu.


"Tun yaushe kika fara ciwon nan?"


Bude ido tayi jin tambayar tasa sai kuma ta sake rufewa. Kamar bata son magana saboda kunyar magana irin wannan dashi tace da ta koma Abuja.


"Kenan duk zamanku a can kina wannan ciwon kafar kowane wata?"


Kanta ta daga tace eh. Yanayinsa gabadaya ya sauya zuwa takaicin irin zaman da yayi dasu a gidansa. Gimbi ya tuna a matsayin wadda ta zame masa shamaki ga sauke hakkokin da suke kansa yaji ya kara tsanar wannan mummunar dabi'a da ta fadawa a dalilin son zuciya.


Muryarsa a hankali cikin nutsuwa take fita yace "Son So bani labarin yadda kike managing a irin wannan lokacin"


Ya tabo abin da bata son tunawa ko kadan saboda yana cikin abubuwan da suka saka mata jin haushinsa a lokacin. Ta kwashi kusan minti uku yana kallonta kafin ta fara fada masa yadda suke kwana kuka ita da Maamu domin idan ta gaji da rarrashinta itama kukan take yi. Babu zancen magani sai dai ta gasa mata kafar tunda Allah Yasa kowane daki na gidan akwai heater ta bandaki.


Zuciyarsa ta karye sosai da tausayinsu. Da ace zai iya maida hannun agogo baya da ya mayar ya gyara abubuwan da suka gabata. Godiyarsa daya ga Allah daga ita har Maamu duk suna raye da baisan yadda zaiyi ba. A lokacin kuka take yi sosai da ta tuna yadda lokutan al'adarta suka zama lokutan ciwo da kazanta a gareta.


"Uncle Awaisu yana so kiyi hakuri da dukkan abubuwan da suka wuce kinji. Sannan mijinki yayi miki alkawarin sauke duk wani hakkinki harda kari. Nasan kinsan komai game da abin da Gimbi tayi min amma duk da haka ba uzuri bane a ganina"


Hawayen da yake bin kumatunta yasa yatsansa yana gogewa a hankali. Akan abu da bai kai ya kawo ba Gimbi ta tarwatsa musu farincikin rayuwa. Tsoron kada uwarmiji ta koreta ya kaita ga aikata manya manyan laifuka da sunan soyayya.


Cigaba yayi ta matsa mata yana ja mata yatsun karfar daga ita har shi suna jin wani yanayi. Suna haka Hafiza tayi sallama ta shigo da kayan Rumana a hannu. Wai itama 'yan mata harda rufe ido ganin Awaisu yana yiwa Rumanan tausa a kafa. Itama kunyar ce ta kamata tana ta kokarin dauke kafarta sai dai ya rike sosai gashi wani sabon ciwo da yafi na dazu take ji.


Dariya kunyar tasu ta bashi yace da Hafiza kayan waye ta kawo


"Maamu tace tayi wanka ka kaita asibiti ayi mata allura"


Rumana ta kwabe fuska "ni wallahi bana son allurar"


Hafiza dai ficewa tayi duk kunya ta isheta tana dariya. Ba jimawa ta dawo da ruwan zafi a bokiti ta shigar dashi bandakin Baaba ta sake fita.


Awaisu ya tashi ya miko mata hannu "taso kiyi wanka"


"Ni bazani asibitin ba. Allurar kara rike min kafa take yi"


Yayi murmushi "naji amma dai ya kamata kiyi wanka kafin na fara toshe hanci matata bata wanka"


Daga hijab din tayi batare da ta sani ba ta fara sansana jikinta. Shi kuwa sai dariya. Da taimakonsa ta tashi ta shiga toilet din. Sai da ta rufe kofar yaji tace


"Uncle amma zaka fita kafin na gama ko"


"Sai kin kirani Son So" ya bata amsa yana daga kayan da Hafiza ta ajiye. Riga da wrapper skirt ne na atamfa sai underwears da bodyspray. Wata leda ya gani ta pad ya tuna labarin da ta bashi dazu. In sha Allah kwalaye zai rinka ajiye mata a gida don kada ta taba nema babu.


"Uncle pleaseeeee"


"Son So pleaseeee" ya kaikwayeta.


Gaskiya bata so ta fito yana nan da ta sani ta kwashe kayanta ta shiga dasu.


Kamar mai rada yaji tace "Son So"


Shiru yayi ta sake fada yana jindadi sai a na ukun yace mata ya tafi.


Ta dade tana gasa kafafunta sannan tayi wanka ta fito kai tsaye daure da tawul.


Ganinsa tayi a zaune yana juya bra dinta a hannu yana dagowa suka hada ido yace "wannan ma acuci ce ko size din kenan idan na koma zan hada lefe. Nasan yanzu ance mata komai kari kuke yi"


Mantawa tayi da ciwon kafar ta nufeshi gadan-gadan ta mika hannu zata karba saboda kunyar da taji da sauri shi kuma ya daga hannun sama yana kare mata kallo. Kula tayi da abin da yake yi ta kwasa a guje ta koma bandakin tana cewa
"Yau naga boni"


"Za dai ki ganshi yarinya har me akayi kike gudu tun yanzu"


Yadda ya saba jin farinciki idan tana wasu abubuwan haka yaji yanzu musamman idan ya tuna dan jikinta da ya gani. Tashi yayi don kada ta kasa fitowa ya dan jingina da kofar ta waje


"Fito ki shirya kinji zan jiraki a dakin Maamu"


Sai da ta dan kara lokaci ta leko don ta tabbatar ya tafi. A gaggauce ta shirya saboda kada ya dawo ta koma gadon ta kwanta tana zumbura baki yau gabadaya Uncle ya gama da ita.
*****


Hawayen da Dr. Yana take yi sune suka tabbatarwa da Hajiya cewa ta farka. Matsowa tayi kusa da ita ta dafa kanta.


"Sannun kinji Yana. Allah zai baki wani. Mutanen Maiduguri na hanya kada su iso kina wannan kukan ki karyawa kanwata zuciya"


Yana ta daga hannunta mara kwari ta share ido. Mafarkin da tayi da Gimbi tar take tuna shi kamar yanzu yake faruwa.


Mujahid na shigowa ta sake saka wani sabon kukan mai cin rai. Hajiya fita tayi ta barsu yana ta rarrashinta. Bayan kusan rabin awa Hajiya ta koma dauko purse dinta da ta saka goro a ciki taji suna magana. Kara kunne tayi sosai yadda zata ji da kyau.


"Shiyasa nace ki dena shiga sabgar mutane a asibitin nan"


"Yanzu sai na ga abu da idanu na na dauke kai don bai shafeni ko wani nawa ba?" Ta fada tana kuka


Rarrashinta ya koma yi "ba haka nake nufi ba amma kuma ba kowa ne zaki shiga lamarinsa ba haka kawai ya rabu dake. Wannan Gombo din din take ko Gimbo da bakinki kika ce an fada miki tana asiri. Infact da idonki kika ganta..."


"Da ban taimaka ba Allah kadai Yasan me tayi niyar yiwa tsohuwar nan. Ban taba nadamar taimakawa mutane ba domin kawar da kai da mukeyi idan abu bai shafemu ba shine babban rashin hadin kan da mukeyi a matsayin musulmi. Ya Mujahid idan har Allah Ya bani iko to duk inda naga rashin gaskiya zanyi kokarin taimakawa."


Girgiza kai yayi "ban hanaki ba Yana amma ba kowane abu bane zaki shiga. Wanda yafi karfinki sai ki nemi mutanen da ya dace. Yanzu dubi yadda matar nan tayi mana sanadin zubewar cikin nan. Wallahi bazan yafe mata ba "


Yana ta dafa hannunsa "kayi hakuri in sha Allah zamu sami wani amma nima wallahi wannan matar sai na nuna mata kurenta"


Hajiya ce ta bude kofar dakin ta shigo tana kallonsu zuciyarta a hasale.
"Cikinku waye zaiyi min bayanin Gombo dinnan yadda zan fahimta"


Mujahid ya matso kusa da ita ta daga masa hannu.
"Wallahi kada ma ka soma cewa nayi hakuri don bazanyi ba. Yana ke nake saurare don wannan mijin naki babu abin da zai iya"


Ba don taso ba Yana ta bata labarin da ta samu a wurin Rumana da wanda idonta ya gani. Hajiya ta dan cije lebenta na kasa


"Sai tasan ta taba gudan jinin Hajiya Fanta. Hatsabibanci gidansa tazo da kafarta"


Yana da Mujahid duka a tsorace suka fara rokonta tayi hakuri kada tayi abinda tayi niyya. Bata sauraresu ba ta dauki jakarta ta fita.


Hajiya Fanta mutuniyar Damboa ce a jihar Borno. Tun tana karama take fama da lalurar aljanu wanda da kyar aka rabata dasu. Su suka saka mata fitina, rashin hakuri da zafin nama wurin aiwatar da kowane irin aiki. Bayan tashon lokaci da aka diba ana nema mata magani an samu sun fita sai wata guda daya da ta nace wai bada magani take so Fanta tayi. A hankali ta zama wata karamar yar bori inda daga kallo daya zata iya fadin ciwon dake jikin mutum kuma ta fadi magunguna na gargajiya da zaayi amfani dasu a dace. Har tayi aure ta gama haihuwarta kowa yasanta da sana'arta. Wani babban malami ne su Mujahid da yan uwansa mata suka nema da kyar ya samu Fanta ta amince ta dena bada magani domin lokuta da dama abin yafi kama da wani nau'i na sihiri. Magani da wasu lakani babu wanda bata bayarwa. An rabata da aljanar da kyar amma kafin ta tafi ta nanata cewa duk sanda take neman taimakonta sunanta kawai zata kira tayi alkawarin share mata hawaye. Malamin nan ya nuna mata hanya ce kawai take nema ta dawo saboda haka duk runtsi duk wuya ta kai kukanta ga Allah shi kadai. Labarin Gimbi da abin da tayiwa jikanta da ko numfashi bai fara ba tayi sanadin zubar dashi ya tuna mata da cewa shekarun baya karyar mutum ya kara da ita. Aljanun ma bata shakkarsu balle wata Gimbi.
*****


Baaba da kanta taje ta koro Rumana tace suje asibiti. Ba yanzu ake ji ba sai dare yayi ne abin ke tsananta ta kwana tana kuka mai jinyarta ko rintsawa bazai sami yi ba.


Mayafi ta yafa fuskarta duk tayi fayau dama haka take yi tana dafa bango ta fito ta shiga motar. Baya ya bude mata yace ta kwanta sosai tace gaba zata zauna amma ya kunna mata AC zafi take ji.


Kujerar gaban ya kwantar mata yadda zata fi jindadin zaman ya kaita wani health centre dake kusa dasu. Sunyi sa'a da likita ya rubuta mata allura irin wadda ake yi mata tun dawowarta fika. Jikinta a sanyaye suka bi bayan nurse din da zatayi mata. Allurar ba karamin zafi gareta ba har wani dan tsayawa akeyi ruwanta ya shiga a hankali.


Nurse din tana tsartar da ruwan allurar daga sirinji tana dan kada shi Rumana ta zuba mata ido wanda yake cike da kwalla . Awaisu ya kalleta duk ta bashi tausayi yace "kina so na rikeki?"


"A'a ka fita" sai ga hawayen ya sauko.
Nurse din tayi dariya "bazanyi miki da zafi ba. Hannuna kamar auduga yake wurin allura"


Tashi yayi zai fitan don yasan kila kunya take ji ayi mata a gabansa. Allurar ta sake kallo yana daf da fita yaji ta cakumo shi a gigici.


"Don Allah Uncle ka rikeni wallahi da zafi allurar"


Murmushi yayi "Suna na Uncle?"


Ta girgiza kai da sauri "Son So"


Nurse din ya kalla shima ba karamin tsanar allura yayi ba don ko ciwo yake aka rubuta allura baya zuwa idan ba yaji jiki ba.


"Yanzu dole sai anyi mata?"


Wani dadi ya kama Rumana tace "ina fa ba dole bane. Lokacin da ba'ayi min kwana daya nake warkewa"


Ya kama hannunta har lokacin nurse din yake kallo "to kinji ki bata magani kawai mu tafi"


Rumana sai gyada kai take yi har wani kuzari yana kara shigarta "bari na jira a mota ko Uncle idan ta baka sai mu tafi. Ni kaga bani da lafiya bazanyi ta tsayawa ba"


Shi kuwa yace ta tafi nurse din ta kwashe da dariyar yadda suke yi duk su biyun sannan tace idan har Rumana tana son lafiya ta bari ayi mata allurar saboda kada nan gaba kafarta ta sami matsala. Awaisu na jin haka ya janyota yace ta tsaya zai riketa.
Haba tuni hankalinta ya tashi ta soma kuka. Rungumeta yayi a hankali ya daga hijab dinta ya kuma janye rigarta kadan. Nurse din na dukawa da allurar zata dan janye zanin kasa ya runtse nasa idon kamar shi za'ayiwa. Kankame shi da Rumana ta sake sosai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login