Showing 111001 words to 112099 words out of 112099 words
Chapter 38 - KASHE FITILA Book Complete by Batul Mamman.txt
abinda kika yi bansan da me zan gode miki ko saka miki ba. I simply love you"
Gimbi tana jinsu hawaye ya zubo mata ta share tana murmushi "ehemm ehemm da mutum dai a kusa"
Awaisu yayi dariya "kinsan uwargida a ko ina ita ce gaba sai na sallameta zan zo wurinki"
Rumana taji gabanta yayi mugun faduwa ta matse hannun Awaisu. Kallon cikin ido yayi mata
"Kada ki karaya kinsan bazan taba wulakanta ki ba" hannunsa ya hade yayi mata alamar yana sonta yadda suke yawan yiwa juna sannan ya juya ya fuskanci Gimbi. Da sauri Rumana ta fice daga dakin tayi sa'a iyayenta da Maamu da Baaba ashe basu tafi ba. Jikin Maamu ta fada tana kuka duk suna bata hakuri Harisu ya sanar da su abinda tayi.
A cikin dakin kuma Awaisu bakin gadon Gimbi yaje duk da yaji kamar ya bi bayan Rumana.
"Amaryar Abban Haris yaya naki jikin?"
"Me kace?"
"Ina nufin dazun nan aka mayar da aurenmu da Gimbiyata"
Wani kuka ne ya taso mata ta rungume shi tana yi yana bata hakuri
"Rumana ce ko? Ashe zan sake amsa sunan matar aure kafin..."
Bakinsa ya hada da nata ya shiga kissing taji kamar yau ta fara ganin Awaisu yau ta fara sonsa.
"Abinda kuka yi min Allah Ya saka muku da alkhairi nagode. Allah Ya baku zaman lafiya da Rumana. Da zan sake haihuwa sai nayi mata takwara saboda tayi min halacci. Ta bani abinda ban taba zaton sake samu ba. Rumana ta hadani da farinciki mara misaltuwa. I love you so much"
Rumana dagewa tayi a sallameta a ranar dole suka bari ta tafi. Ita kuwa tayi haka ne saboda ta bar Awaisu da Gimbi su kadai.
Da suka koma gida su Baaba sai tarairayarta suke yi. Awaisu kansa sai waya yake yawan yi mata a karo na hudu da ya kira ta kashe wayar.
Washegari su Dr. Yana suka zo sai ga su Anti Baraka. Gida ya cika da mutane haka asibitin.
Anyi nasarar kamo Ovi Awaisu yaje police station din ba don an rike shi ba yadda ya fara kwallo da ita da itama a asibitin zata kare. Yana dawowa ya samesu a waje aka ce masa jikin Gimbi yayi tsanani. A firgice ya shiga dakin doctor zai salleme shi Gimbi a wahale ta hana. Gaban gadon yaje ya durkusa ya rike hannunta. Nan likitan yace zuciyarta a kumbure take za'ayi mata gwaje gwaje yace ya amince ko me zasuyi ayi mata. Fita yayi kiran masu daukarta a kaita dakin gwajin.
Awaisu ya shafi fuskarta "Me yasa kika boye mana rashin lafiyarki?"
Murmushi tayi cikin jin ciwo "gashi yanzu ya fito har ka kawo mij sauki"
"Nagode da dukkan soyayyarki gareni Gimbiya. I love you so much"
Kai ta kada a hankali "Abban Haris ka dade baka kirani da sunana ba"
Kanta ya dora a kafadarsa suna zaune kusa da juna hannunsu sarke " _Nana Fadima_my best friend"
Ajiyar zuciya tayi sai yaji muryarta ta kara yin kasa tana ambaton Allah a hankali. Bayan kamar minti biyu yaji shiru sai sassautawa rikon da tayi kasa. A razane ya dagata " *Gimbi!!!!*"
Kan kace me dakin ya cika Baaba Hure ta janyeta daga jikin Awaisu ta kwantar tare da rufe mata ido. Hakan yayi daidai da bugawar zuciyarsa ya sulale a kasa shima.
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun...Allah Ya jikanki Gimbiya" cewar Alh Mudi
Kuka ne ya kaure a dakin doctor na dawowa ya tabbatar musu ta rasu sannan aka bawa Awaisu taimakon da ya dace.
Sun ga tashin hankali Rumana ta rinka kuka ta tsorata da mutuwa. Ga su Daula da Awaisu abin tausayi. Kafin azahar an kaita makwancinta suna ta yabon yadda karshenta yayi kyau ana dada yafe mata.
Kamar daga sama Anti Bebi ta shigo gidan ta fada jikin Mama.
"Yaya Amina ki yafe min ni na sawa Gimbiya ciwon zuciya saboda muguwar soyayyar da aka dasa mata na Awaisu. Gimbiya ta tafi ta barni a wannan duniyar abar banza ko gafararta ban roka ba na cutar muku da 'ya saboda keta"
Mama ta dago jajayen idanu "wadda kika yiwa ma ta tafi me zai hana na yafe miki Bebi? Duniya ce dai ki kiyayeta don bata da alkawari"
Zaman makokin kwana uku akayi sannan suka watse sai adduar Allah Ya jikan mamatanmu Ya bamu cikawa da kyau da imani.
****
*Bayan Wata Shida*
Rumana an gama SSCE ta dawo gida Awaisu ya shirya mata walima ta iya su mutan gidan. Taji dadi sosai suka wuni suna hayaniya da yara yadda suka saba.
Da daddare sun kwanta yake fada mata an kawo kudin Shuhada bikinta saura wata biyu.
"Ashe zamu girgiza jiki a wurin biki"
Baki ya rike yana kallonta "ke! Wa zaki je ki girgizawa jikina?"
Ta hau dariya dama tsokanarsa take yi tasan shi da kishi. To ma me zai kaita rawa gaban wasu da aurenta, yan mata ma ana musu nasihar su bari.
"Dariya kike yi ko. Kin fasa zuwa bikin"
Kafa ta soma bugawa "haba Son So nice fa"
Ya kalleta a karkace "ban sanki ba"
"Shuuuuhhhhh ...wayyo bakina naga boni"
Daukota yayi ya dorata kan cinyarsa shima yana dariya "za dai ki ganshi yanzu, me ya sami bakin"
"Ka bani magani indomie mai romo naci"
"Ai ba sai kin roka ba"
Sun dade yana kissing dinta sannan suka kwanta ta kamo hannunsa tana wasa dashi
"Son So"
"Yes kwailar Awaisu"
"Na fasa yi maka albishir din ma"
"Yi hakuri ni da na shaida mata ta tafi kwaila"
Zumboro baki tayi ta tashi zaune tana shafa cikinta "little Gimbi kinji Abbanki yace min kwaila ko"
Zama yayi sosai yana kallon cikin "are you serious?"
Kunya taji ta kwantar da kanta a kirjinsa "jiya da nace maka zamu je asibiti da Amir yana mura harda kaina na kai. Kuma in sha Allah Nana Fadima Gimbiyar Uncle Awaisu da Umm Rumana zan haifa"
"Amin Son So Amin"
Bargo ya ja ya rufe su aka bude sabon shafin soyayya.
*Alhamdulillah*
Dukkan yabo da godiya ya tabbata ga Allah Madaukakin Sarki da Ya bani ikon farawa da gamawa lafiya. Abinda na rubuta daidai daga Allah ne ina rokonSa Ya bamu ikon aiki dashi. Wanda nayi kuskure daga gareni Allah Ya yafe min daku baki daya.
*Sadaukarwa*
Ga dukkan uwarmiji da suruka ta hanata zaman lafiya da danta. Allah Ya ganar da masu wannan hali su san cewa uwa ba abar wasa bace kuma soyayyarki ga miji shine kiso iyayensa.
*Tukwici*
Gareki Aisha Maman Abida. Nagode Allah Ya bar zumunci.
*Gaisuwa da fatan alkhairi*
Taurarin Fikra Writers Association
Dukkunan matan BMN Batul Mamman grp ban dauke kowa ba. Allah Ya saka da alkhairi. Abin da yawa wallahi bazan iya jero sunaye ba amma kunsan kanku. Nagode da soyayyarku gareni.
Zauren zumunci online
Taskira
Zauren Biebee Isa
Maman Haneep novel
Feenat Ja'afar novella
ROF 1 and 2
Hausa Nvls only
Futuhatul khair novels
Aysha Garkuwa nvls
RAZ novella
Umm Subay'a fans
*Bazan manta daku ba*
Riri Turaki
Zee Bells
Murjanatu Alkali
Meela Adeel
Rally Garba
Wasila (mmn haneep nvl)
Mum Little
Umm Nass
Pherty Zahra