Showing 33001 words to 36000 words out of 112099 words
Chapter 12 - KASHE FITILA Book Complete by Batul Mamman.txt
kwana biyu ki kara warkewa sai na kaiki. Amma a haka kowa ya ganki yasan baki da lafiya"
Daga murya tayi ta soma fada
"Ubanka ne ya samin ciwon da zaka ce bani da lafiya? Ka mayar dani inda ka dauko ni tunda ka gagara kula dani da yar amana Rumana"
Jin kansa yake kamar wanda ya tashi daga bacci a lokacin. Me ya faru tun tafiyar su Baaba ya dena bibiyar halin da Maamu ke ciki bayan yasan yadda Gimbi take wulakanta masa dangi .
Kamar wani yaro ya soma hawaye a gaban Maamu amma ya rasa me zaice mata. Tausayinsa ya kamata itama sai kukan.
[15/08, 17:45] +234 803 272 5896: *KASHE FITILA*💡 24
*Batul Mamman*💖
Sai da suka yi mai isarsu sannan tace ya tashi ya fita bata son ganinsa. Jiki a sabule ya fita ransa yana kuna. Mamakin kansa yake yi da yadda yake sakaci da mahaifiyarsa. Shi Awaisu manajan banki kuma babban dan kasuwa shine Maamunsa take wadannan kasusuwan kamar wadda ta shekara ciwo.
Tun shigarsa daki tunani kawai yake yi karshe bacci mai nauyi ya dauke shi.
A asibiti sai shabiyu likitan kashi yazo aka gyara kafar Gimbi. Tasha azaba gumi ya rinka bin jikinta saboda ciwo. Ga kanta inda Daula ta tsige mata kitso ya tashi sosai kafar gashin da ya fita ta kumburo shima ciwon yake mata. Duk wannan ya taru da rashin dawowar Awaisu daga cewa zaije gida ya dawo. Tayi ta kiran wayarsa shiru baya dauka. Nan fa ta damu sosai ta fara tsoron ko aikin Wangesi ya soma rabuwa dashi ne yau daya da batayi masa turare ba. Abu kamar wasa har azahar bai dawo ba kuma babu waya. Ganin haka hankalinta duk ya tashi har ta fi damuwa da rashin dawowarsa akan ciwon da jikinta yake yi. Takurawa wata likita tayi akan lallai sai an sallameta suka ki. Da ta rasa abin yi sai ta kira Anti Bebi.
"Gimbiya ta Awaisu yaya akayi ne?" ta fada tana dariya
Gimbi ta amsa mata da kyar ta labarta mata halin da take ciki. Kamar gaske Anti Bebi ta nuna damuwarta ta shirya ta taho asibitin.
Da tambaya ta gane dakin ta shiga. Tana budewa ta ga kan Gimbi sai dariya har ta kusa kaiwa kasa.
"Gimbiya wannan kyan ki hoto wallahi a kafa shi a kofar gidan Awaisu."
Daure fuska Gimbi tayi "wannan ciwon fa ba na wasa bane Anti Bebi"
Da gayya ta kaiwa kafar da aka nade duka cikin wasa ita kuwa Gimbi ta saki kara har tana jin fitsari na barazanar fita saboda azaba.
Anti Bebi ta dauke kai kamar bata kula ba "nima ban ce na wasa bane, wai.... wannan kai naki kamar na budurwar zabuwa a lokacin da ta fara kora. Awaisu ya caba da Gimbiyar mata"
Ran Gimbi in yayi dubu ya baci har ta fara dana sanin kiranta.
"Idan dariya zakiyi min ki tafi kawai na nemi taimakon wani"
"Dadina dake tsiwar tsiya. Me kike so dai yanzu"
Tunanin yadda zatayi maganin Gimbi a nan gaba take yi. Dauriya ce kawai yanzu take kafin lokacin da zatayi dariya.
"Saboda wannan ciwon yau banyiwa Abban Haris turaren nan ba. Kinga tun fitarsa har yanzu shiru. Ina tsoron kada hankalinsa ya fara komawa kan uwarsa"
Anti Bebi ta murmusa "Gimbi Allah dai Ya baki suruka irinki. Nasan ba karamin dadi zaki ji ba ke me 'yan maza har uku su auri mata masu jajircewa akan mazansu kamar ki"
Gimbi ta dafe kirji jin wannan muguwar addua daga bakin Anti Bebi.
"Ba Amin ba wallahi, wai me nayi miki ne haka kike min mugun baki?"
"Auuuuu, ashe babu dadi kike yiwa Maamu baiwar Allah? To maida wukar wasa nake yi. Amma ni kam gaskiya da ina da da namiji wallahi bazan bari ya aureki ba."
Ganin cewa cin fuska Anti Bebin take yi mata tace ta tafi kawai ta fasa. Anti Bebi taji dadi ga dama ta samu na hada Shuhada da Awaisu tace tayi hakuri. Kwantar da kai sosai tayi tana bata baki Gimbi na hura hanci ita a dole ta isa. Bayan sun gama magana akan cewa Anti Bebi za ta je har gidan da sunan dauko mata kaya tayi masa turare ta dauki jakarta.
"Ki jirani da kansa zai zo har nan ya sameki ki sille shi ciki da waje."
******
Gidanta ta wuce kai tsaye tana murmushi. Da yake ita ke tukin motar ko yaya ta tuna irin mugun tanadin da ta yiwa Gimbi sai ta daki sitiyari tana dariya. Da isarta Shuhada ta umarta da ta shirya zasu fita. Ita kanta wanka ta sake yi tamkar kanta zata kaiwa Awaisu ta saka riga da zani na mutumci harda hijabi. Shuhada ma doguwar riga ta saka mai kyau yalwatacciya da hijab wanda ya wuce kirjinta da kadan. Ganin shigar da Anti Bebi tayi abin ya daure mata kai sosai tuni ta sha jinin jikinta. Dole ta san yadda zata gabatar da kanta ko ma ina zasu je don kada asirinta ya tonu. Wayar da tayi da mamanta da safe ta tuna inda ta nuna tafi son 'yarta ta dawo gabanta ita kuma tayi ta lallabata akan ta kara hakuri na dan lokaci. Ajiyar zuciya tayi ta bi bayan Anti Bebi.
Kasuwa ta biya ta sayi kaji manya manya guda shida danyu sai kayan marmari. Daga nan suka wuce gidan Awaisu.
Yana kwance a daki har lokacin sallar azahar da ya makara a gida yayi. Rumana ko tunanin ta zuba masa abinci bata yi ba. Girki dai tayi yau a koshe suke a ranta a shirye take da duk hukuncin da Gimbi zata yi mata idan ta dawo. Har ayyanawa take idan ma dukanta tayi itama ramawa zatayi sai dai yau a korata gida kamar yadda take so. Kamar daga sama taji dirar mota. Haba a take jikin Rumana ya dau mazari tayi zaton Gimbi ce. Yau tasan mai rabasu sai Allah yadda tayi barna a kitchen. Maamu kanta da ta ga naman da ta zuba mata a miya sai da tayi mata fada akan tayi wauta.
Tashi tayi daga falo zata gudu daki neman ceto a wurin Maamu taji muryar Anti Bebi da wata siririyar murya suna sallama.
Su Haris ne suka fito tarbarta. Rumana tana rarraba idanu taso ta ganeta amma da yake ba haduwa suke yi sosai ba ta manta inda suka hadu. Anti Bebi na ganinta ta ware hannu ta tafi da sauri ta rungumeta.
"Rumanan Maamu ina Maamunki?"
Rumana tayi sakato tana duban su daya bayan daya.
Dafa ta Anti Bebi tayi
"Baki ganeni ba ko, Auntyn Mummyn su Haris ce. Ina Maamu kaini na fara gaisheta kafin na nemi 'yata"
Hannun Amir ta ja tana masa hira wai ina mamansu take ne ko don yau lahadi tana can tana bacci.
Har kasa ta kai gwiwarta ta gaishe da Maamu. Itama Shuhada gaisheta tayi tana tausayin rayuwar dattijuwa da aka asircewa da ya kama ta.
Waige Anti Bebi ta soma yi tana neman Gimbi. Daula ta sanar da ita tana asibiti tun safe. Mamaki ta nuna tare da dafe kirji
"Me ya sameta haka?"
Yaran kusan a tare suke bata labarin hatsarin Gimbi da ruwan karkashi. A haka Awaisu yazo ya samesu ya fito sanye da shirt da wando da gani wanka ya sake.
Ganin Anti Bebi ya sanya shi sake hade fuska ita kuwa ta dan taba Shuhada wadda tayi saurin gaishe shi tana binsa da kallo wanda a zahiri mutum kamar Anti Bebi zaiyi zaton na soyayya ne.
Murmushi Anti Bebi tayi tana nuna Shuhada
"Ka ganta nan ita ta hanani sakat wai zata zo gaishe da Maamu. Tun zuwanmu asibiti dubata take sonta."
Kafe Shuhada tayi da ido ita kuma tayi saurin kallonsa tana rausayar da kai tare da murmushi.
"Don fitina kaji tasa muka saya wai a nan zata dafa mata irin yadda take so. Yini taso yi ni kuma bana jindadi gashi yau dreba yana hutu dole na daure muka fito" ta kare zancen da fara'a kamar yau take sallah.
Maamu dai kallonsu take yi bata ce komai ba har Anti Bebi tace da Rumana su tafi kitchen da Shuhada su gyara naman kada ya lalace. Da ido Awaisu ya bi bayan Shuhada da kallo ya kasa gane me zuciyarsa take ji a lokacin. Suna fita Anti Bebi ta zauna a kasa kusa da Maamu.
"Maamu don Allah ki rinka hakuri da 'yar tawa. Nasan zama tare da sukuka sai an daure anyi hakuri. Dan yanzu ka haifeshi ne baka haifi halinsa ba" Tana magana tana rike da hannun Maamu wanda take ta mammatsawa a hankali kamar mai tausa. Maamu ta dago suka hada ido a take taji wani irin firgici ya ziyarceta. A yadda zuciyarta ke rawa bata jin akwai wani abu da Anti Bebi zata nema a gareta ta gagara yi mata. Wani murmushin gefen baki Anti Bebi ta sake yi tana kara murzawa Maamu sauran maikon maganin da Wangesi ya bata na mallake mata zuciya.
Awaisu da ke tsaye yace da Maamu zaije asibiti idan an gama su dawo. Fada ta soma yi masa na rashin komawa bare ayi batun abinci. Rumana ta kwalawa kira taje ta hada abinci ya tafi dashi. Anti Bebi taji suna yaren da bata ganewa ta tashi wai itama asibitin zata je amma zata bar Shuhada idan ta dawo su tafi tare.
"Maamu bari na bishi na gano jikin nata"
Ba don yaso ba suka tafi tare tana ta yi masa hira duk ta ishe shi. Abincin ma ita ta dauka ta shiga dashi dakin.
A kwance Gimbi take suka shigo tayi saurin tashi zaune. A zatonta an gama yi masa turare ne Anti Bebi ta sako shi a gaba suka taho.
"Ni zaka yiwa haka Abban Haris? ka kawoni asibiti don wulakaci tun safe babu ci babu sha sannan ka ki dawowa. Ina ma ka shiga tun dazu ina ta kiran wayarka ka ki dagawa."
Bata jira amsarsa ba ta cigaba da cewa "akan wannan me billen daga goshi har kan hanci zan huce. Bari na koma gida sai sun gane kurensu"
Zuciyar Awaisu ce take masa wani irin tafasa yana tunanin ko dai Gimbi ta sha kwaya ne ko kuma kitson da aka tsige mata ya taba mata kwakwalwa.
Anti Bebi kuwa ta lumshe ido tana jin cewa lallai hakanta zai cimma ruwa indai Gimbi ta cigaba da hawa dokin zuciya tana sakin layi a tunanin asiri ke aiki.
[15/08, 17:45] +234 803 272 5896: *KASHE FITILA*💡 25
*Batul Mamman*💖
Abubuwa da dama ya rinka tunawa a lokacin wandan da suka gabata. Kamar yadda ya dauke kai daga mahaifiyarsa da kuma wasu abubuwan da Gimbi take saka shi yana yi babu ko tambaya. Ba tare da cewa komai ba ya juya ya fita tana ta kwala masa kira.
Tana ganin fitarsa ta fara kokarin tashi a tsorace Anti Bebi ta daga mata hannu alamun ta zauna. Fita tayi ta bi bayansa ita kuma Gimbi duk ta gigice tana neman yadda zatayi ta sauko daga kan gadon ta bi bayansa.
Mugun saurin da yake yi yasa Anti Bebi sai da ta danyi gudu ta iya taddo shi.
"Awaisu dakata don Allah"
A fusace ya waigo Anti Bebi ta fashe da kuka irin mai tsuma zuciyar nan ta dago kai tana kallonsa.
" Ashe haka kake fama dan nan? kayi hakuri ka ji Awaisu."
Wani kallo shekeke ya bita dashi sannan ya juya ya shige motarsa ya buga kofar da karfi ya fita daga harabar asibitin a guje.
Me Gimbi ta dauke shi ne? Har yaushe raini ya shiga tsakaninsu irin haka? Sannan garin yaya ya sakar mata ragamar gidansa har ta kai zata iya kiran mahaifiyarsa mai bille? Yau ba don a gadon asibiti take ba yana jin babu wani abu da zai hanashi yi mata duka a wurin. Kafin ya karasa gida zuciyarsa ta cika da tsanar kansa da dana sanin auren Gimbi.
*****
"Mai babbar kujera Wangesi na kan tudu na yarda na amince idan ina da kai duk wata matsalata ta kau"
Yayi wata dariya mai sautin kukan rikakken alade daga inda yake kwance wata mata wadda akalla zata kai shekaru hamsin da biyar tana yi masa tausa. A kowane hannun matar yatsu uku sanye suke da zobba na gwal manya. Leshin jikinta mai matukar tsada da kyau. Fatar jikinta kadai ta isa ta nuna arzikinta. Hannu ya daga yana yi mata nuni ta dakata haka sannan ya cigaba da waya da Anti Bebi.
"Idan kina shakku a da yanzu nasan kin tabbata aljanu na sun tsaya min. Kamar yadda suka yi alkawarin tayar da rikici tsakanin Gimbiya da mijinta kin gani da idanunki"
Jinta take kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha tayi dariya "na yarda Wangesi na kan tudu. Aikinka yayi kyau sai nazo"
Kusan tare suka ajiye wayar ya dubi matar da take zaune a gefensa.
"Kin gama komai ne?"
Ta dukar da kai a ladabce "na gama Wangesi"
Dakin nasa ya karewa kallo. Ta share ko'ina tas ta goge. Daga gefe inda bandakinsa yake ta wanke shi har ana jin kamshin turaren da ta saka a dakin. Lokacin da ta shiga wani uban zarni da wari yake haka ta rinka amai kamar zata fitar da kayan cikinta. Bayan ta gama ta wanke masa kayansa su ma doyi suke yi babu kyaun gani. Ga kuma girki wanda ita da kanta yasa tayi masa cefane ta dafa masa shinkafa da miyar kaji.
"To Hajiya Dela kinyi duk abin da Aljani Sukku ya bukata. Yace kije sa'a dai a wannan kasuwancin da zaki fara ko tsinke kika daga zaki sami mai saya."
Murmushi tayi tana kada idanu kamar yarinya.
"Nagode Wangesi, yadda kuke bani sa'a akan dukkan abin da nasa a gaba dole nayi biyayya."
Wani dan kulli ya miko mata. "Wannan ki samu ki jika su tsumu na kwana uku sai ki hada lemo dashi ki bawa shi maigidan naki. Ina mai tabbatar miki ko nawa kika bukata jarin zuwa Dubai din zai baki kuma bazai taba saka miki ido wurin shige da ficenki ba"
Kullin ta bude inda ya zuba faratansa na hannu da kafa zako-zako masu matukar dauda wanda ta yanke masa kafin ta fara aikace-aikacen da ya saka ta.
Godiya sosai tayi masa ta tashi ta fita tana tofar da yawu saboda warin da take ji yana fita daga jikinta.
******
Anti Bebi ta koma dakin Gimbi inda ta sameta tana ta kokarin sauko da kafarta wadda aka gyara ta kasa. Saurin zuwa tayi tana gyara mata kafar
"Haba Gimbiya ina zaki je haka da wannan kafar"
"Ki kyaleni naje Anti Bebi, ko dai kinyi kuskure a turaren ne?"
Gwalo tayi daga bayanta sannan ta karya murya kamar gaske " kada ki daga hankali akan wannan. A yau zanje Wurin Wangesi sai na ga abin da Awaisu yake takama dashi. Kada ki bari komai ya daga miki hankali. Gimbiya ko babu mai tsaya miki duk duniyarnan bazan taba bari ki wulakanta ba".
Da kalamai masu dadi da kwantar da hankali Anti Bebi ta cigaba da hillatar Gimbi har ta sami nutsuwa.
Abu na karshe da ta fada mata shine ta dena yarda da zancen Wangesi shi kadai.
"A matsayinki na mace ban da asiri dole ki hada da kissa. Shigowarsa dazu maimakon ki nuna kinyi kewar rashinsa sai kika saki baki kina diga rashin mutumci. Yayi miki da sauki ma. Nice shi sai na daukeki da mari kafin na fita"
Idanu Gimbi ta ware tana kallon Anti Bebi kafin ta girgiza kai tace
"Lokuta da dama sai na rinka jin kamar ba kya kaunata. Yanzu banda kin kware a mugunta da keta meye na cewa da kece sai kin mareni?"
"Fitsarar ce ta tashi daga yi miki gyara?"
"Admit it Anti Bebi my misery gives you pleasure"
Da yake duk gayu da mugun halin Anti Bebi babu boko don ko sakandire bata gama ba kasa amsawa tayi sai tsaki da ta buga tare da surar jakarta. Gimbi tayi dan murmushi
"Uwata ta kaina tuba nake yi. Idan kika barni yanzu karshenta aurena ya mutu"
Ita ta dawo shawo kan Anti Bebin suka cigaba da musayar bakaken kalamai kafin su daidaita.
*****
Kafin Awaisu ya karasa gida yamma tayi sosai. Yana tsayar da mota su Amir suka tarbe shi da cigiyar Mummynsu. Shafa kawunansu kawai yake rai a bace ya kasa basu amsa.
Falo suka shiga yana sauri ya wuce dakinsa ya kwanta ko zaiji saukin radadin maganganun Gimbi yaji wani kamshi ya doki hancinsa. Bai gama tantance ko na meye ba Shuhada da Rumana suka fito kowacce dauke da tray din abinci. Ai yana ganin Shuhada ransa ya kara baki ya daka wata tsawa da ta tsorata duka yaran da Rumana har hannunta na rawa zatayi bari. Da kyar ta saita kanta suka taru suna kallonsa.
Fuskarsa kamar bai taba dariya ba ya harari Shuhada "zo ki fice daga gidan nan yanzun nan"
Duk da ta tsorata sosai dakewa tayi ta tsaya a wurin. Ba wani abu take nema daga Awaisu ba face ya bata lokaci ko yaya ne tayi masa bayanin matarsa da kanwar babarta. Uwa uba idan ya nuna kyamarta da wuri yadda Anti Bebi tayi imani da asiri tana iya ganewa karya tayi mata. Daga nan kuma bata san hukuncin da zata yanke mata ba. Neman abin fada ta fara Maamu da ta shiga falon a lokacin ta katseta.
"Menene hakan da kake shirin yi? Ka gama wulakanta ni son ranka yanzu Allah Ya kawo mai tausayina za ka koreta. Tun da kuka fita take yi min hidima kamar 'yata ba kamar matarka ba"
Kallonsu Shuhada tayi tana mamaki ashe ba Hausawa bane. Shima cikin yarensu ya bata hakuri sannan dubi Shuhada
"Ana yin sallah ki fito ki tafi ita wadda kuka zo taren tana asibiti."
Bata nuna masa bacin rai ba sai ma marairaicewa da tayi a gaban Maamu.
"Gashi ban iya mota ba kuma bata bar min mukulli ba. Maamu bari na ajiye miki wannan sai na tafi tun yanzu kafin magariba ta karasa na rasa abin hawa"
Maamu tayi murmushi "A'a 'yata ki bari ayi sallah zai kaiki har gida. Nagode miki sosai"
Bai iya cewa komai ba ya wuce. Duk mutum mai alaka da Gimbi haushinsa yake ji. Yana idar da sallah ya bukaci tazo su tafi. Maamu tayi ta sa mata albarka suka yi sallama da Rumana.
Motarsa ya nuna mata ta shiga ita kuwa ganin su Rumana sun koma ciki ta dago ido tana masa kallon da yasan ko me zata fada babu wasa a ciki.
"Ina son muyi magana da kai ne."
Ya dan matso inda take domin jin abin da take son fada suka ji alamun an