Showing 69001 words to 72000 words out of 112099 words
Chapter 24 - KASHE FITILA Book Complete by Batul Mamman.txt
Wani abin idan kaji sai ka rasa ina hankulanmu suke tafiya. Saboda abin duniya da jindadi na takaitaccen lokaci sai mu koma tamkar jahilan farko. Ga addini amma bama aiki dashi"
Kansa ne yaji har ciwo yake masa saboda tunani da damuwa yace "to ni yanzu yaya zanyi da su Haris? Gimbi mahaifiyarsu ce ina tsoron kada abubuwan da take yi suyi tasiri akansu su fara koyi da ita"
Baaba tayi saurin daga hannu "Allah Ya kiyayemu mugun ji da mugun gani. In sha Allah Allah zai tsare musu imaninsu. Amma ina tunanin me zai hana ka kaisu gidan Alh Mudi kafin asan yadda za'ayi da uwar."
Shawarar Baaba tayi masa yace in sha Allah zaiyi magana da iyayen Gimbi. Don har zuciyarsa baya so yana fita yana barita dasu. Su Maman Gimbin ma sun kira Harisu zasu zo ranar laraba.
"Wai bazaka tashi ka tafi wurin matarka bane?" Baaba ta fada masa tana kallonsa da tausayawa. Duk ya zabge ma tun da aka fara case din.
Agogonsa ya kalla ya dan dukar da kai "Baaba dare yayi ne. Kinga har tara saura. Wallahi abin nan ne duk ya tsaya min"
"Allah Sarki idan damuwa tayi yawa ai babu inda ya dace da mutum sai wurin masoyinsa" tana magana tana dariya.
"Da safe zan biya kafin na tafi" ba dai haka yaso ba shi da yazo musamman saboda ita.
Dan daure fuska Baaba tayi "ai ni bansan dalilin da yasa kuka kulla tafiyarta gidan Ummukulsum ba. Banda ragon azanci tunda a nan zaka kwana ai sai ka fi samun lokaci tare da ita. Kira min yayar taka muyi magana. Sauran ma zamu hadu dasu su tsara yadda za'a danyi taron biki cikin wata mai zuwa ta tare"
Wayar ya mika mata bayan yaji ta shiga. Tana dauka ta fara mitar me ya hana shi dawowa. Baaba ce ta soma labarta mata me ya faru sannan tace maza Rumana ta shirya yanzu zaizo ya dauketa. Ummukulsum tace ta yarda amma don Allah da safe a dawo da ita don akwai shirin da zata fara. Dama Awaisun ma ganin mijinta baya gari bai dace yayi musu zuwan dare ba haka shiyasa yaso hakura.
Cikin minti shabiyar yayi saurin watsa ruwa ya shirya cikin kananun kaya ya fita.
A can gidan Anti Ummukulsum kiran Rumana tayi tace maza taje tayi wanka tayi kwalliya amma ba mai yawa ba.
"Anti wanka a daren nan kuma?" An katse mata kallon da suke yi da 'yan uwanta.
"Maza ki shige kuma wallahi banda jika-jika. Kwalliya kuma yar kadan ta isa. Mijinki zai zo mayar dake gida amma gobe zai dawo dake kafin ya wuce."
Ji tayi ana neman kulle mata kai. Ance tazo ta kwana yanzu kuma ta tafi ta dawo. Ba dai tayi musu ba taje cika umarni.
Har Awaisu ya iso Rumana bata gama shiri ba. Shi da Anti Ummukulsum suka zauna yana bata labarin abin da ya faru. Itama ta kara jin tsanar Gimbi tunda bata ji kunyar idanunsu ba tazo raba da da mahaifiya. Dama tana son ganinshi game da Rumana. Dazu da zata ci tuwo ta kamata ta gutsira shi ta soya mai da yaji wai a haka zata ci. Dama gata ba wani jikin arziki ba musamman ga yadda yunwa ta kassarata. 'Yan sinadaran gina jiki duk babu isassu ga aure daga sama. Shawara ta yanke dole ta gyara 'yarta don wanda ya zauna da Gimbi sai mace tayi da gaske zata iya zama da mijinta. Magunguna da ake sha kuma ba wani tasirin arziki zasuyi ba matukar babu cima mai kyau.
"Ango don Allah ina bukatar 'yan kudi na gyara amarya"
"Kuna cewa angon nan kunya nake ji" yayi dariya.
"tunda kunya kake ji to tashi ka tafi na fasa baka ita."
"Tuba nake ranki ya dade. Yanzu dai nawa kike bukata?"
"Duk abin da ya samu...amma fa ka saki bakin aljihu gyaran gaske zamuyi"
Alkawarin taho mata da kudin da safe yayi domin a lokaci bashi da cash da zai isa ya bata.
*****
Da sallama Rumana ta shiga falon. Ganin Anti Ummukulsum yasa tayi saurin juyawa zata gudu.
"Dawo ke muke jira dama. Sai da safenku bari na shiga ciki."
A bakin kofa ta rabe har Antin ta fito a hankali tace ta saki jikinta mijinta ne fa. Murmushi kawai tayi ta kutsa kai cikin falon suka yi karo da Uncle Awaisu yana fitowa.
Janyota yayi da sauri ganin tana neman dafa bango kada ta fadi.
"Gaskiya akwai matsala. Haka kike ba nauyi, yar wannan turewar tana neman kayar min dake"
"Matsawa fa nayi don kada kace na tureka amma baka ji nauyina ba...."
Sama taji yayi da ita maimakon su fito ya koma cikin falon da baya yana dauke da ita.
Salati ta soma yi sai kuma ihu ya biyo baya saboda yadda taji yana neman juyawa da ita ta kankame masa wuya. Yadda take tsoron hajijiya saboda jiri shiyasa bata ko son ta ga anayi.
Ihun nata da bai gama fita daga bakinta bane ya makale sakamakon bakinsa da taji akan nata.
Wani irin yanayi suka shiga bare ma Awaisu wanda yaji gabadaya komai ya tsaya masa. Baya tunanin komai sai Rumana da soyayyar da yake yi mata.
Da kyar ya iya kyaleta ya kalli fuskarta ta rufe idanu kamkam jikinta har wani rawa yake yi saboda tsananin faduwar gaba. A hankali ta bude idonta suka sauka cikin nashi tayi saurin kuma rufe su da taga kansa ya sake dukowa gareta. Wannan karon peck ya mata a goshi.
"Kinji kunya ne Princess? Kada ki damu muna nan dake idan kika fara yi min son so da kanki zaki...."
Duk da bata san me zaice ba amma bata son ji don ko da wannan kunyar ya barta tana ganin zata shekara bata dawo daidai ba a gabansa. Hannu tasa ta rufe masa bakin har lokacin yana dauke da ita. Shi ga tsaho ga jikinsa ba'a kira shi mai kiba ko siriri ba ita kuma ga kankanta ga rashin kiba.
Wannan karon a tafin hannun taji ya sake mata wani kiss din ta cire da sauri tana salati.
Dariya yayi ya sauketa yana rike mata hannun "Allah Ya hadani da ustaziyya"
Hanyar fita yaga tayi yabi bayanta batare da ya saki hannun ba. Suna fitowa Anti Ummukulsum ta leko ta sama don taji shiru kamar basu fita ba ta gansu. Dadi ne ya cika mata zuciya tana addu'ar Allah Ya kara musu so da fahimtar juna. Rumana abar tausayi ce matsawar Gimbi tana gidansa sannan ga kuruciya bata san komai ba. Shiyasa dole ta gyarata don ta kara mata daraja a idon miji.
*****
Da kansa ya bude mata ta shiga sannan ya shiga ya tayar da motar. Dan kallonta yayi duk ta takure kamar mai jin tsoronsa. Ya tallabo kansa yana kare mata kallo
"Yau fa na janyowa kaina dama da kyar ake yi min magana gashi yanzu ko sannu da zuwa ban samu ba" muryarsa a karye irin abin tausayi dinnan.
"To ba kaine ba..."ta turo baki kamar zata masa kuka.
"Allah Sarki Princess nine nayi miki ki......"
Hannuwanta tasa ta toshe kunnuwanta "don Allah kada ka fadi sunan"
Ya daga gira daya "Au ashe ma kinsan ko meye "
Cikin sauri tace "a'a ban sani ba"
Dariya yake mata sosai yadda ta rude
"To ki bari na fada miko ko da next time kina so kinsan me zaki ce min"
Tace "Na sani"
ya sake daga gira
"Ban sani ba" tayi saurin gyarawa shi kuwa sai dariya yake yi mata ya manta fiye da rabin bacin ransa. Kafadunta ya dafa
"I love you so much Umm Ruman. Duk da abu ne da wata uku da suka wuce ban taba tunanin zan wayi gari naga rana irin ta yau ba. Amma nasan cewa Allah ne Ya bani ke domin samun sassaucin laifukan da na aikata muku musamman Maamu da bani da tamkarta. Aurenki shine hanyar da tafi cancanta na faranta muku ke da ita. Please Princess ko yaya kiyi min son so dinnan kinji. Yanzu ni mijinki ne. Miji kuma yana taka rawa daban daban a wurin matarsa. Ni uba ne, aboki sannan masoyi gareki saidai na biyun da na ukun bazan iya nuna miki su sosai ba sai kin karbeni a sabon matsayin da Allah Ya hadamu"
Idanunta cike da hawaye saboda maganganun sun shigeta muryarta can kasa tace
"Uncle me ya sameka?"
Yadda take turo baki haka shima yayi "yanzu na ajiye kunya na gama fada miki ina sonki shine zaki ce me ya sameni?"
"Gani nayi kamar kana cikin damuwa lokacin da da na shigo kuna tare da Anti Ummukulsum"
Mamaki ta bashi sosai. Yana rainata ashe wayonta ya wuce yadda yake gani.
"Kin kawar min da damuwar tun dazu. Saura amsata "
Ta rasa menene yake saka mata faduwar gaba yanzu a tare dashi. Tasan dai bata kinsa ko kadan amma wanna matsayin nasa na da yasa ta kasa sakewa har ta fuskanci me zuciyarta take ji game dashi. Gani take yi kunya da nauyinsa da wuya su barta. Amma bata so yaji kamar bata damu dashi ba. Dubi yadda ya rama mata zagin da Gimbi tayi musu. Wannam kadai ya zama matakin farko na canja yadda take ji game dashi.
Yatsunta biyu babba da manuni ta hade tare da dunkule sauran ukun ta daga hannun a tsakiyarsu tana murmushi "In sha Allah"
Ya kalli hannun ya kalleta "Umm Ruman me kenan?"
Aha yau ta kure masa bai san me take nufi ba tace a ranta. Dariya ta soma yana binta da kallo cike da jindadi. Da kyar ta tattaro karfin hali tace
"Uncle idan ka canki me haka yake nufi ...."
Ya sake kallon hannun ta katseta "me zaki bani?"
Dadi duk ya cikata ta sake sosai yau tayi abin da tasan da matukar wuya ya gano.
"Abinci me dadi"
"Kin ma isa...wannan aikin naki fa ba mai sauki bane da gani."
"To me kake so?"
Bakinsa ya nuna mata yana dariya a hankali.
Shi da ba gwanin kallo ba saboda rashin lokaci tana ganin kamar bazau taba gane wani salo ne na cewa *I love you* ba da take gani a series din Korea da suke gani a dakin Abba.
Karamin yatsanta ta daga shima ya biye mata ya saka nasa yatsan a ciki yace
"Deal! yarinya ki shirya shan mamaki"
Lumshe ido tayi harda dariya tana ganin tayi nasara.*KASHE FITILA*💡41
*Batul Mamman*💖
Kamar kada su tafi gida haka Awaisu ya rinka ji. Hanyar fita gari ya dauka Rumana ta dago kai a firgice.
"Uncle ina zamu?"
"Kin fiye tsoro Princess. Abu zan saya miki"
Daga nan bai kuma magana ba har suka tsaya daidai wurin wani mai nama da yayi suna sosai a wurin. Murmushi tayi tana tuna lokutan baya kafin zuwansu Abuja. Babu zuwan da zaiyi garin bai tafi da ita da sauran 'yan uwanta siyan gasasshiyar kaza a wurin ba. Har kurar Awaisu babanta yake kiranta sai gashi yau sun kuma zuwa amma tana matsayin matar Awaisu. Tunani ne barkatai suke ta zuwar mata akan wannan sabuwar rayuwa sai da yayi kusan rabin awa ya dawo dauke da ledoji. A baya a ajiye sauran sannan ya shiga mazauninsa ya ajiye mata daya akan cinyarta.
Zabura tayi tana kokarin mikewa tsaye ta ma manta a mota suke. Mamakin tashin nata yayi yace ta zauna. Cinyarta ya gani tana shafawa harda 'yar kwalla
"Uncle ka kona min cinya" ta fada a shagwabe
"Subhanallah" yace tare da kai hannunsa inda yaga tana murzawa. Kayan jikinta material ne mai santsi shiyasa taji shiga zafin har kanta. Hannun nata ya dauke kawai sai ta ga ya duka daidai cinyar yana hurawa.
Tsigar jikinta taji ta tashi ta fara jan kafar yayi saurin rikewa.
"Kiyi hakuri don Allah na manta da zafi na baki don kici yanzu"
Ita dai so take ya kyaleta kawai tace "ya dena zafin ma"
AC taga ya kara sannan ya dan hade fuska babu alamun wasa "bari na janye skirt din kisha iska sosai kafin mu isa gida"
"Iyyeeee, a janye me?" Ta fada tana zaro idanu a firgice.
Ya kama skirt din "nace ki bari yasha iska kuma na ga yadda wurin yayi. Kada yaja ruwa ko tabo"
'Yar dariya ta soma yi wadda bata boye tsoron da yake bayyane a fuskarta ba
"Lahhhh ashe ka zata gaske ne naji zafi...to wasa nake yi kawai."
Dariya yayi wai kamar shi zata yiwa wayo. Tsoron da ya gani tattare da ita yasa ya kyaleta. So yake ta soshi ba taji tsoransa ba. Motar ya tayar suka kama hanyar gida yana satar kallonta tana sosa wurin. Da ta ga ya juyo sai ta dauke hannunta da sauri. Wani chemist ya tsaya ya sayi magani suka wuce.
Cikin kannenta ya kira wani mai suna Jamal ya bashi ledoji biyar manya cike da naman kajin nan yace ya kai ciki a raba musu. Shi kuma ya dauko leda uku a hannu ya zagayo bangarenta ya dauki nata.
"Muje na kaiwa su Maamu nasu sai na shafa miki magani"
"A ina? Wanne?? Maganin meye???"
"Bana son musu ki wuce muje kawai" ya fada tare da yin gaba.
Jikinta a sanyaye tabi bayansa. Ta yaya zai shafa mata magani a cinya. Shi ko kunyarta ma baya ji. Ita ce fa Rumana!
Dakin Maamu suka fara zuwa har tayi bacci. Ya bude fridge zai saka Rumana ta karbi ledar tace bari ta cire albasa da kabejin da yake ciki kada ya bata naman idan ya kwana.
Kamar yadda Hajiya Umma yayar Mama ta fada mata komai tayiwa mahaifiyarsa zai kara mata kima a idonsa haka ta kula da yadda yaji dadi sosai. Jiranta yayi ta cire sannan ta saka a fridge din suka tafi wurin Baaba.
Ga dukkan alamu itama baccin take shirin yi. Fuskarta a sake da ta gansu dadi ya mamaye mata zuciya.
"Awaisu kai da kake da tafiya a gabanka gobe shine baka yi shirin kwanciya ba?"
Leda daya ya ajiye mata yana murmushi "nama na tafi nema miki Baaba"
"A'a wannan kurar dai ta kusa da kai ka sayawa na sani." Ta bude ta dauki daya tana dariya saboda Rumana tace ita ba kura bace.
"Yaya ya shigo ne?"
"Bai dade da tashi ba. Dama maganar tarewar Rumana ne. Kana ganin nan da sati hudu masu zuwa yayi maka? kada ta rasa da yawa a karatunta. 'Yan uwanka suna son su kammala shirye shirye don ko tsinke ba'a fara tanadar mata ba"
Zama yayi sosai Rumana zata fita yace ta zauna itama. Baaba Hure ya kalla sai kuma ya dukar da kansa.
"Yanzu Baaba ni Yaya Harisu zai yiwa haka? Ko ban auri Rumana ba waye zaiyi mata kayan daki idan ta tashi aure?"
Baaba ta dan murmusa "kai ne."
"To wallahi bana bukatar komai daga wurinsa. Ban isa na rama muku komai da kuka min ba Baaba. Bani da wannan niyar ma. Amma burina bai wuce na ga na kyautata muku iya yadda Allah Ya bani iko. Banda al'amura sun zo mana a haka Rumana a gida ya kamata ta zauna har aurenta. To kuma yadda nasan da hakan ta faru bazanso kowa yace zai shigar min kan maganar kayan daki da abubuwan da amarya take bukata ba yanzu ma bana so. Kawai ku saka mana albarka shikenan"
Baaba ta share kwalla "Awaisu meye baka yi mana ba? Yayanka da mazan yan uwanka mata babu wanda baka karawa jari ba. Yaransu duka babu wanda baici moriyar samunka ba. Duk wata aike baya yankewa tsakaninmu da kai ko da baka zo garin nan ba. Me zamu ce maka mu kuwa. Allah Ya kara yi muku albarka Ya rabaku da dukkan sharri"
Suka amsa da amin. Satar kallonsa Rumana tayi tana murmushi hannunta na daidai wurin kunar ta ma manta ta dan sosa wurin.
""Ya soma kaikayi ne?"
Baaba tace meye yake kaikayi kuma. Cinyar Rumana ya nuna mata tare da bayanin me ya sameta. Saman wardrobe dinta ta nuna masa.
"Ga zuma can dauko ka shafa mata kada ya tashi. Kasan ba'a raina kuna."
Rumana ta tashi har tana tuntube da kafar Awaisu.
"Bari na dauko naje daki na shafa"
Baaba ta wurga mata wata uwar harara "kin sami wuri kin zauna ko kuwa. Dauko kaji dan albarka" ta yiwa Awaisu murmushi.
Dariya yayi yadda Rumana tayi kicin-kicin da fuska kamar zatayi kuka. Shima kuma da ya dauko sai ya kalli Baaba a dan kunyace ya mikawa Rumana kwalbar zumar. Duk abinsa da kunya ya kwaye mata cinya a gaban kakarta.
Baaba ta kada kai "Ahaf, abin da yanzu aka fara auren. Meye a shafa zuma mu da za'a kawo mana 'yan dugwi-dugwi mu goya. Indai don nice ku kara gaba don ba fita zanyi na bar muku dakin ba."
Kafin ma ta kai karshen maganar Rumana ta fice da sauri Awaisu ya bi bayanta yana dariya. Ita kuwa Baaba suna fita addua take Allah Ya kara hada kansu.
Da kyar ya kamota zata yi hanyar dakin mamanta.
"Wannan sauri kamar zaki tashi...ga wannan maganin shima na shafawa ne. Ki bara shafa zumar yau gobe sai kiyi amfani dashi. Ga naki naman kici kafin ki kwanta. Lastly kuma kada ki kashe wayarki zan kira"
Juyawa yayi ya tafi ya shige dakin Mama. Bata yi mamakin ganinta ba don taji sanda Baaba Hurw ke fadawa Maamu wai yaran yanzu basa lissafi. Ji dai Awaisu da Ummukulsum wai sun kai Rumana can gidan bayan a nan zaifi ganinta son ransa. Ko da suka fara zancen Mama fita tayi don kunya suka sa taji. Nata naman ne a gabanta tana ci tace yanzu aka raba aka kawo mata. Rumana duk kunya ta isheta ta shige uwar dakin ta dauko charger ta tafi nasu dakin bayan tayi mata sai da safe.
Wayar kusan awa daya sukayi kafin sukwanta duk da shine yake kaso casa'in na maganar.
Tun da tayi asuba bata koma bacci ba ta zauna gari ya danyi haske tayi wanka ta shirya. Takwas da mintuna kadan ya kirata yace ya shirya ta fito ya kaita gidan Anti Ummukulsum ya wuce. Sai a lokacin yake danasanin kin tahowa da drebansa.
Harisu ya fito sunyi sallama yaje wurin Maamu suka taba hira tace yaushe zai dawo yace Juma'a. Ai kuwa ta rinka dariya tana cewa ya hakura sai nan da wata biyu ita ta warke. Yadda yayi mata da fuska ya kara bata dariya.
"Wasa nake maka angon Rumana"
Ya dan sosa keya "Maamu harda ke a tsokanar"
"Nice ma kan gaba." Ta gyara zama "Ka kula da amanar Rumana kaji ko. Kada naji ko na gani. Idan wancan karon tsautsayi ya ritsa damu sake faruwarsa sunansa sakaci daga gareka. A wannan lokacin kuma zan nuna maka fushina"
"In sha Allah bazan taba ganin fushin nan ba kuwa Maamu. Zan rike miki ita tsakani da