Showing 51001 words to 54000 words out of 112099 words

Chapter 18 - KASHE FITILA Book Complete by Batul Mamman.txt

23 Jun 2024

14012

Baaba magana


"Baaba kada kiga ina nuna damuwa kamar babu kara. Idan kika zauna a gidan nan yanzu ko yini daya ne zaki gane danki baya cikin hayyacinsa. Ina tsoron in mutu duk wani sauran zumunci namu ya yanke. Abubuwan da kuka yi mana bani da bakin saka muku ko godiya. Nayi tunanin Awaisu zai fitar dani kunya ya kyautata muku da zuciya daya. Sai gashi ni da na haife shi ma...." kuka ne ya kwace mata sosai sai tari ya sarke ta.


Rumana tana daga waje duk ta gama jin abinda suke fada domin ta wuce sauran yan uwanta. Dama da kuka ta karaso na maganganun babanta da Dr. Barrister. Zantukan Maamu sun kara karya mata zuciya. Tana jin ta soma tari ta tura kofar ta shiga. Baaba ta gani rike da Maamu jikinta babu kwari tana ta tari. Dago kan da Maamu tayi daga cinyar Baaba sai jini suka gani yana fita ta bakinta. A razane suke duka su biyun Rumana ta soma kuka don tsoro ta kasa komai.


Baaba Hure itama a tsoracen take tace "ki ruga ki kirawo min babanku da likita"


Ta juya a guje zata fita taji muryar Maamu tana cewa "ki fadawa Awaisu na yafe masa"


Bata jira jin karshen maganar ba ta fita. A hanya suka hadu da Harisu tana kuka ta fada masa Maamu na aman jini. Nan suka tafi shi da Abba kiran likita.


Dr. Yana tare da wasu likitoci biyu suka taho dakin cikin sauri. Suna isowa suka sallamesu daga dakin suka rufo kofar. Jikin kowa a sanyaye suka tsaya jiran tsammani.[15/08, 17:45] ‪+234 803 272 5896‬: *KASHE FITILA*💡34


*Batul Mamman*💖




Cikin kuka Rumana ta rinka zayyanawa Awaisu wasu abubuwan da suka faru dasu a gidan. Ciki wasu ya sani har yana mamakin sai yanzu da take fada yake jin haushinsu. Me yasa a lokacin baiyi yunkurin daukar mataki ba. Ita ce tambayar da yayi ta maimaitawa kansa. Zuciyarsa ba karamin nauyi ta kara yi masa ba. Ba don a gaban Rumanan bane babu abin da zai hana shi kukan bakinciki.


A raunane yace "Abin da yasa kika dawo gida kenan? Me yasa baki taba fada min ba?"


Tambayar tasa ta biyu ce taji a kamar wani rainin wayo. Ita fa yanzu daga shi har matarsa tayi alkawarin dena ragawa kowa sai dai idan tayi a daketa ace mata mara kunya.


Wani kallo ta bishi dashi kafin tace "Uncle a gabanka fa yawanci ake yi"


Ajiyar zuciya yayi "haka ne....hmmmm...tashi ki koma ciki. Komai zai daidaita in sha Allah"


Mikewa tayi tana tafiya yabi bayanta da kallo. Hakuri yaso bata na kasa rikonta da yayi sai kuma ya fasa kada sauran girmansa ya zube don ya tabbatar yanzu ba wata kima gareshi ba.


Ita kuwa tana tafiya tana tuno wasu abubuwan da kunya tasa ta kasa sanar dashi. Yaushe zata manta cewa a iya zamanta na gidan kafin tayi rabin shekara ta koma yin gunzugu na mutan da da dankwalayenta saboda rashin kudin siyan pad. Daga baya ne da suka shaku sosai da Yusra ta fada mata shine take bata a makaranta. Tsigar jikinta ce ta tashi da ta tuna yadda take kasancewa duk wata.


Awaisu bai bar wurin ba ya zurfafa a tunanin wannan rikirkitacciyar rayuwar tasa da ya kasa fahimtarta yaji wayarsa tana ringing. Kyalewa yayi sai da yaji mai kiran ya nace ya dauka.


Muryar mace yaji tayi masa sallama a hankali ya amsa yana tunanin inda yasan wannan murya.


"Shuhada ce, ka gane ni ko?"


Ji yayi hankalinsa ya kuma tashi. Yaushe zai manta da ita, matar da Maamu ta dage sai ya aureta lokaci guda.


Jin yayi shiru yasa ta kalli Daddynta da yake zaune kusa da Mamansu wadda ta dawo sati biyu da suka wuce.


Alh Maitama ya mika hannu ya karbi wayar yayi masa sallama.


"Suna na Alh Maitama mahaifin Shuhada"


A mutumce Awaisu ya gaishe shi. A garin Abuja waye bai san wannan sunan ba. Tsoronsa daya ba dai maganar auren bace zasu sake tayarwa.


Daga daya bangaren yaji Alhajin ya soma yi masa magana.


"Malam Awaisu ina son haduwa da kai ne domin wasu maganganu masu mahimmanci "


"Shikenan" ya fada a ransa yana tunanin tabbas zancen auren ne. A zahiri kuwa ya sanar dashi baya gari kuma bai saka ranar dawowa ba yanzu saboda rashin lafiyar mahaifiyarsa.


Fatan samun lafiya yayi masa sannan yace "don Allah ka nemi ne idan ka dawo yanzu Shuhada zata turo maka nambar da zaka sameni. Ina kuma yi maka adduar yadda Allah Ya fitar dani kaima Ya fitar da kai lafiya. Sai naji daga gareka"


Yafi minti biyu yana kallon wayarsa yana kokarin gano me Alh Maitama yake nufi da maganarsa ta karshe. Daga karshe ciki ya koma ya sami wuri ya zauna kusa da gadon Maamu. Idan ta dago kai sai ta ga yana yi mata kallo mai cike da tausayi. Murmushi kawai take yi tana ayyanawa a ranta ko yanzu ta bar duniya Alhamdulillah.
*****


Bayan sun gama wayar Alh Maitama ya mikawa Shuhada wayarta.


Mamanta Haj. Rahama ta ce "Daddy yanzu kana ganin zai yarda idan ka fada masa abubuwan da matarsa da Bebi suke yi?"


"Ni da na yarda a yanzu nasan ba komai bane illa karfin addua da ikon Allah. Gabadaya jina nake kamar rayuwar da nayi da ita a mafarki ta faru. Lokaci yayi da matan nan zasu fuskanci hukuncin laifukansu. Dubi Shuhada duk irin son da mijinta yake mata Bebi ta shata musu layi bazasu kara zama tare ba idan har ba wani auren ta kuma ta fito ba. Kina ganin akwai iyayen da zasu so a rinka kirgawa 'ya'yansu aure ne?"


Haj Rahama ta girgiza kai. Ita kanta Allah ne Yayi da sauran zama tsakaninta da masoyinta uban 'ya'yanta. Saki uku Anti Bebi tasa yayi mata daga shigowarta gidan. Fushin da tayi akan wannan sakin yasa tana gama idda tayi aure don ta nuna masa tana da sauran daraja. To da yake bata son mutumin zaman nasu yaki dadi ga kishiya can ma ta matsa mata. Auren bai jima ba ta fito.


"Waccan ledar yaya za'ayi da ita ne" ta nuna ledar da aka kulle da tarkacen layoyi, guraye, ruwa kala kala a robobi da kananun tukwanen kasa duka dauke da sunayen Alh Maitama da iyalinsa.


"Munyi magana da wani malami a islamiyar da su Shuhada sukayi. Yace zai zo karshen sati ayi addu'o'i sosai a gidan sannan a konasu."


'Yarsa ya kalla tana gefe tayi shiru sai ta kara bashi tausayi.
"Ki kara hakuri kinji 'yar Daddy. In sha Allah da sannu Allah zai baki miji nagari. Jiya shima Tajuddeen nayi ta masa nasiha akan yayi hakuri ya fawwalawa Allah komai. Ni da kuka ganni duka abubuwan da suka faru kara min imani sukayi da sanin cewa lallai Allah Shi kadai Ya cancanci a bauta maSa."


Sun jima suna hira wadda kusan dukkanta akan yanayin da suka tsinci kansu ne bayan zuwan Anti Bebi. Basu tashi ba sai da yayi musu alkawarin tafiya wurin Suhail cikin wata mai kamawa sai su jira ya kammala jarabawa su taho gida tare. Kudi kuwa ba kadan ya tura masa ba yace ya biya duk abubuwan da ake binsa na makaranta da bashin abokai idan yaci.


*****


Yau Harisu ya tsaya a daya daga cikin shagunansa sunyi lissafi da yaron wurin. Yana dawowa Baaba Hure dama a shirye take ta fito su tafi asibiti cikin Damaturu. Sun kusa fita daga layin gidan nasu ta hango ta yi saurin cewa Awaisu ya tsaya. Juyowa yayi yana kallonta ta waiga baya


"Wata na gani a motar can da ta wuce kamar Gimbiya"


Ransa har ya baci jin sunanta yace "Gimbiya kuma Baaba me zai kawota yanzu?"


"Juya mu koma gidan dai. Na tabbatar ita na gani"


Ba musu suka koma. Ai kuwa suka hadu da Gimbi da yaranta a waje suna fitowa daga mota.


Harisu da Baaba suka kalli juna ganin yadda ake ta fito da kaya daga boot. Kwalayen juice ne kala-kala da kayan abinci irin su shinkafa, maggi, taliya, mai da sauransu. Motar wata hadaddiya ce amma mai mazauni uku.


Tana ganinsu Baaba ta dena yamutsa fuska musamman ganin yaranta sunyi wurinsu da gudu suna murna. Harisu yaji dadin ganinsu domin jinin Awaisu ne don yana kin babarsu baya jin akwai dalilin da zai sashi kin yaran.


Gimbin ma da sauri ta karaso wurin Baaba ta fada jikinta tana ta murna.


"Baaba mun sameku lafiya? Yaya gida ?"


"Da kin bari mun shiga ciki sai gaisa sosai" Baaba tayi gaba yaran na biye da ita.


Suna shiga ciki Gimbi ta nufi dakin Maamu tun a tsakar gidan take kwala mata kira kai kace 'ya tazo ganin babarta ne bayan sun jima basu hadu ba.


A bude kofar take saboda an ajiye kayan wankinta da safe baa rufe ba. Ganin babu kowa kuma dama tasan babu din ta fito tana gaisawa da matan gidan. Su mamakin kayan da ake shigowa dasu sukeyi. Harisu ta kalla tana murmushi


"Yaya Harisu shine daga zuwa ka dauke mana Maamunmu ko? To kafata kafarta tare zamu koma kuma mu hada da Baaba Hure kaga mun koma 'yan gata ko ta ina. Tana ina ne? Maamu???" Ta kare da daga murya tana kiranta.


Murmushi Baaba Hure tayi wanda Gimbi tayi zaton na murnar tace zasu tafi da ita Abuja ne. A zuci tace kwadayayyu. Ita kuwa Baaba Hure tsabar mamakin rashin kunyar Gimbi take da gogewa a kissa. Tana kallonta tace


"Su Makiru manya"


Gimbi a razane ta kalli Baaba ba dai da ita take ba ta dan hade rai da tsoron kada a dagota.


Baaba ta fahimce yadda fuskarta ta sauya ta daga kai tana kallon sama tana magana cikin kulawa da sassauta murya


"Makiru shegen tsuntsu, idan baka iya takunka ba da ranka da lafiyarka sai ya sunkuce maka da ya barka da ciwon zuciya. Tsuntsaye da dama tsoronsa suke yi. Gimbi kuna dashi a Abuja? "


Harisu ne yayi saurin magana saboda tsoron kada daga nan Baaba ta fadi maganar da zata janyo rikicia take a wurin don bata da hakuri indai an taba nata bisa rashin gaskiya. Yafi so cikin ruwan sanyi su shayar da Gimbi mamaki akan abin da tayi.


"Babana ina Abbanku ne" ya dafa kan Mu'allim yana tambayarsa. Yayi sa'a babu kowa a wurin sai shi da Baaba kada wani yayi saurin cewa Awaisun yana nan.


Gimbi tayi saurin cewa yaran "kai ku shige ciki"


Bayan taga shigarsu dakin Maman Rumana ta dan tabe baki "Yaya Harisu lamarin kaninka sai addua kasan yadda ayyuka suke masa yawa. Tare muka so zuwa tun farkon tahowarku da Maamu sai aka tura shi Lagos. Na kasa hakurin jiransa ne nace bari na taho kawai kewar Maamu ta dameni. Shi kuma kwana biyar ban sami wayarsa ba ma, ina zaton aikin can din ne yayi masa yawa ko an sace wayar."


Ikon Allah, wato da haka ta taho zata nuna bata san me yake faruwa ba kenan ta mayar da laifin kan mijinta. Girgiza kai yayi kawai yace "Allah Ya kyauta. Kuci abinci ku dan huta sai mu tafi Damaturu. Dama asibiti zamu je wurin Maamu muka ga shigowarku shine muka dawo"


Jakar hannunta mai mugun tsada ta saki a kasa ta dafe kirji "asibiti kuma? Me ya sameta?"


Bai kai ga bata amsa ba ta soma kuka harda daga murya. Nan da nan kuwa aka fara fitowa daga dakuna kallonta. Su Haris ta kira tace su zo su tafi asibiti Maamu babu lafiya.


Wadanda ke wurin manya mamakin diramar Gimbi suke yi yayin da ta zamewa yara abin kallo. Tare da Baaba suka sake fita ta shige tasu motar da 'ya'yanta wsu Harisu na gaba suka dauki hanya.


*****
Kana shiga dakin Maamu zaka san cewa akwai soyayya da shakuwa tsakanin ma'abota cikinsa. Maamu zuciyarta ta sanyaya har tana ganin ya kamata a sallameta ta karasa jinyar a gida. Ga su Anti Baraka da 'yan uwanta ana ta wasa da zolayar juna. Lokaci lokaci sai ta kalli Awaisu wanda ya kasa dena yawan kallon Rumana.


Murmushi tayi domin bai dade da fada mata cewa yana tsoron dasa kiyayyarsa a zuciyarta ba duba da cewa yarinya ce kada abubuwan da suka faru su kasa gogewa a ranta. A lokacin Maamu cewa tayi kada ya damu indai Rumana ce zata hakura. Yanzu ma ganin yadda ciwo yaci karfinta ne yasa ta zama haka har take ganin tamkar laifinta ne na dawowa ita kadai. Da ta fada masa haka cewa yayi yadda ta bashi labarin abubuwan da suka faru a gidansa yasa jikinsa yayi sanyi. Yasan Girmansa ya fadi tana masa kallon wanda ya kasa rike mahaifiyarsa bai cancanci a ga girmansa ba.


Maamu gani tayi abin ba komai bane Rumana yarinya ce mai ladabi da hakuri komai zai wuce nan gaba. Amma yadda Awaisu yake ta jan maganar da nuna damuwa yasa tace masa to yasan yadda zaiyi ya dawo da kimarsa a idon Rumana tunda abin ya dame shi haka.


Jin ta fadi haka yasa shi saurin mikewa "Maamu ba fa wani abu nake nufi ba abar zancen nan dai".


"Dawo dai mu karasa sai ka fada min me kake nufi"


Matsar da kujerarsa yayi can gefe cikin 'yan uwansa shi kadai namiji a cikinsu yana dariya. Sai dai duk motsinsa a idon Maamu tana kallon inda idanuwansa suke yawan sauka.


Wasu ne suka zo dubiya daga Fika dangin Baban Awaisu maza da mata dakin ya dada kaurewa da hayaniya da gaishe gaishe. Rumana da ta kasance karama duka dakin sai ta matsa can gefe bayan ta gaishesu. Sallamar Babanta taji ta tashi karbar kayan da yake hannunsa idanunta suka sauka akan Gimbi. Nan take jikinta ya hau bari tsoro ya kamata ta kasa motsin kirki a wurin. Awaisu na ganin yadda ta tsorata don bai ma ga Gimbi ba ya taso yazo gabanta ya tsaya tare da rage tsaho ya hura mata iska a fuska.


"Umm Ruman are you okay?"


Hawaye ne taf ya cika idonta duk yadda ta rinka tsara rashin kunyar da zata yiwa Gimbi ranar da duk suka sake haduwa ji tayi abubuwa da dama sun dawo mata a lokaci guda sai matsanancin tsoro da fargaba.


Ledar da ta fara karba a hannun Harisu ya karbe ya ajiye a kasa yace mata ta wuce su fita daga dakin. Daga kan da zaiyi ya mikawa Harisu hannu su gaisa ya hada ido da Gimbi wadda tayi mutuwar tsaye.


A zuciye take da yadda ta ga yayiwa Rumana. Harda wani sabon salo wai Umm Ruman. Sunan da rabon da taji ya ambata tum farkon zuwansu Abuja kafin Wangesi ya fara aiki a kansa ita da Maamu ya manta da lamarinsu ballantana sunayensu. Kishi ne ba bala'i a cikin idanuwanta da suka kada sukayi jazur. Me yasa boka yace kada ta biyo mijinta washegari? Me ya faru a kwanaki biyar dinnan da ya dawo Fika?


Daga kan gadonta Maamu ta gama kallon komai tsaf ta kuma gano ta inda in sha Allahu zata nunawa Gimbi nata ikon na mahaifiyar Awaisu. Tun da ta fara samun lafiya ita da Baaba Hure suka saka shi a gaba da fada akan sakaci da azkar. Sun karfafa ko ma meye ya same shi da yadda ya damu da neman kudi kawai batare da yawaita yiwa kansa addu'ar neman tsari ba.


Yaransa ne suka rungume shi suna murnar ganinsa shima yayi murna domin yayi kewarsu. Gimbi da duk abubuwan da take yi tun zuwanta shawarwarin Ovi ne ta rasa me yake mata dadi saboda ganin da tayiwa Awaisu da Rumana yana nuna damuwarsa a kanta. Kenan asirinta ya soma karyewa tunda har ya damu da wata karan kada miya Rumana. Kula da tayi dakin ita suke kallo yasa ta mayar da idanunta ga Maamu wadda kallo daya yasa ta gane ba karamin ciwo tayi ba. Kanta tayi da gudu har tana takawa Hindu matar Bomai hannu ta fada jikin Maamu tana kuka.


"Maamu me ya sameki haka? Ina can ni ban sani ba"


Tsigar jikin Maamu har tashi tayi jin rungumar da Gimbi tayi mata. Tsana da kyankyaminta take yi sosai saboda tasan ita ce silar wargajewar farincikinsu.


Ba Awaisu da yake da tabbacin ya sanar da ita rashin lafiyar Maamu har tace karya ne ta kara da yiwa su Baaba sharri kowa na dakin da yasan me yake faruwa mamaki ne ya kamashi na wannan karfin hali irin na Gimbi.


Da fuska cike da hawaye ta dubi Awaisu ta soma korafin me yasa bai fada mata ba shine ya taho shi kadai don ya sa tayi bakin jini. Wannan abu da take yi duk tuggun Ovi ne da tace mata a haka zata wanke kanta. Ita kuma sukuwa bata san bakin jini Ovi take son kara mata ba yadda asirinta zaiyi saurin tonuwa ta bar gidan Awaisu.


Baaba ce tayiwa Rumana alama da hannu akan su fita ita da yaran. Sauran bakin ma duka suka fice don abin ya zama matsalar family.


Jikin Awaisu har wani tsuma yake yi saboda bacin rai wai shi Gimbi zata yiwa wannan rainin hankalin a bainar jama'a. Yunkurin karasawa gabanta yayi mata magana yayi Harisu ya girgiza masa kai. Cikin bacin rai ya kaiwa bango naushi zuciyarsa na kuna. Da wace irin mace yake zaune tsahon shekaru sai yanzu halayenta ke bayyana kansu gare shi.


Maamu tana kallonsa ga tausayi ya bata taji kwalla ta cika mata ido. Sanin cewa Gimbi bata jin yarensu kuma ita idan ta fada mata da hausa sakon bazai isa yadda take so ba yasa ta yafito Baaba da hannu. Magana tayi mata kasa-kasa yadda sauran bazasu ji ba. Baaba ko dogon nazari batayi ba akan maganar duk da tayi matukar mamaki ta dago ita da Maamu duk suna murmushi


"Awaisu jeka wurin Rumananka ka rarrasheta naga ta fita kamar zatayi kuka. Kaima a yadda ranka ya baci dinnan ganinta nasan zai sanyaya maka rai."


Anti Baraka da kanenta duka suka bi Baaba da ido cikin rashin fahimtar inda zancen ya dosa. Shi kuwa Awaisu kamar jira yake yi ya fice daga dakin don yasan idan zai cigaba da zama yana kallon Gimbi tana wannan karyar kulawar zai iya kai mata hannu a yadda zuciya ke dibarsa.


Fitarsa tayi daidai da zare dukkan wani farinciki da yayi saura a zuciyar Gimbi sai nauyin da taji kirjinta yayi mata. Tsabar takaici ma kasa magana tayi ta rinka kallonsu daya bayan daya. Wai yaje wurin Rumanansa??? Kai kila kunnena baiji daidai ba ta fada a fili ba tare da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login