Showing 72001 words to 75000 words out of 112099 words
Chapter 25 - KASHE FITILA Book Complete by Batul Mamman.txt
Allah"
"Haka nake son ji. Allah Yayi albarka Ya tsare hanya Ya kaika lafiya. A kiyaye haram komai kyau da dadinta halaka ce"
Yaji dadin adduar sosai yayi sallama da kowa ya fita sannan Rumana ta fito don kunyar biyo bayansa take ji gaban mutane. Gaishe shi tayi sanna ta shiga ta zauna. Kallonta ya rinka yi tayi kyau duk da hijab ne ma a jikinta.
Sun fara tafiya taji hannunsa akan cinyarta.
"Kin hanani jinya bayan ni na jawo ciwon. How do you feel yau?"
Kunyarsa ta yau har tafi jiya saboda hasken gari yana ganinta sosai. Da kyar ta amsa masa. Bakin ATM machine ya tsaya ya ciro kudi suka tafi gidan Anti Ummukulsum.
Da sauri sauri suka gaisa don yace baya son tafiyar dare. Dubu dari ya bata yace tayi masa magana idan bai isa ba. Rumana ya nema har ta tafi wurin Iman aka kira masa ita.
Su biyu ne a falon da suka zauna jiya. Idonsa a kanta yace "kin tuna me ya faru a falon nan jiya?"
Wayyo tace a fili tana rufe ido. Haka zata zauna dashi yana sata jin kunya haka. Yaushe zata manta ita kuwa.
Tashi yayi tsaye "ban manta assignment din da kika bani ba. Ki shirya ina dawowa zaki cika alkawarinki kema"
"Bafa alkawari nayi ba Uncle"
"Har kin karaya kenan. To ki kwana da saninki ina dawowa zaki biya da abin da na fada miki jiya" ya dan daga kai ita kuwa sai ta juya gefe.
"Zan tafi Umm Ruman babu ko sallamar miji da zan samu? "
"Uncle Allah Ya kiyaye hanya Ya kaika lafiya"
"Amin amma sauran wannan"
Hannuwansa taga ya ware alamun tazo ya rungumeta. Sakin baki tayi tana mamaki. Ko da wasa bazata iya ba.
Hannunsa ya kuma nuna mata da kansa yana jiranta.
"Zaki sa nayi dare fa. Ni fa babu inda zani sai kinyi min irin sallamar da nake so"
Tsaye take tana ta shawarar me zatayi. Uncle Awaisu ya sakata a tsaka babu mafita. Tana dago kanta suka sake hada ido ya kyabe mata fuska shi ya gaji. A hankali ta rinka takowa gabansa. Har ta kusa karasawa cikin hannuwansa yana murmushi sai kawai yaga ta zagaye ta bayansa ta rungume shi a hakan ta hanyar zuro hannuwanta ta karkashin nasa ta kwantar da kanta a bayansa. Motsin kirki Awaisu ya kasa saboda yadda yaji. Yatsunsa ya zura cikin nata masu dauke da jan lalle mai kyau yana ta murmushi ya kasa ce mata komai. Rumana ta gama masa komai ta shige ko'ina a cikin zuciyarsa. Tsoron abinda zai iya biyo idan ya kalleta yasa bai juyo ba sai hannunta da ya dan matse sannan yace
"Kamar kullum ki kular min da kanki. Ina yi miki son so Umm Ruman. Wannan new way of saying I love you ne"
Daga bayan nasa tayi wani kyakkyawan murmushi cike da kunya ta sake shi. Wai Uncle Awaisu yana sonta. Shima bai juya ba ya yi gaba yana kara jin sonta ya wuce.
******
Bayan tafiyarsa Anti Ummukulsum ta kirata daki. Plate ta miko mata ta kalli abin ciki ta kasa tantance ko menene.
"Daga yau kada na sake ganin kina cin komai sai abin da na baki kina jina. Wannan kasusuwan nake son rufewa kafin ki tare. Kuma kina bukatar kayan gina jiki don haka kada na kuskura wallahi na kamaki da kayan kwalamar da kuke ci da Iman."
Rumana tayi murmushi "To Aunty meye wannan din?"
"Zogale ne na dafa na soya soya da albasa mai yawa da tumatir da kwai. Kici kisha wancan youghurt din" ta amsa mata.
Rumana ta ja plate tana kwasar dadi. Daga ranar Anti Ummukulsum ta dauki damarar gyaran 'yarta. Kullum sai tayi mata farfesun kaji, kifi, kayan ciki ko nama. Ganye kuwa wasu ko sunansu bata sani ba haka take yi mata miyar tuwo ko farar shinkafa. Ga maltina sai tasha gwangwani hudu a rana. cikin dan kankanin lokaci ta soma canjawa ita kanta tana ji a jikinta.
******
Washegarin komawar Awaisu yaje gidansu Gimbi ya sanar da iyayenta zai kawo su Daula na dan lokaci. Mama tace dama taso tayi masa magana tun ranar da yazo ma. Sun sanar dashi lokacin da ya tashi komawa Fika ya fada musu tare zasu je. Gidan nasa kuma a lokacin suka bi bayansa zasu taho da yaran su ga Gimbi.
Suna ta sallama ba'a amsa ba yana daga bayan Alh Mudi yace su shiga kawai yaran suna islamiyya ne. Mama kai tsaye dakin Gimbi ta wuce. Waya take yi ma bata ji shigowarta ba tana ta fada sai sakin kudi take yiwa su Ovi a kaiwa boka amma babu wani chanji. Ganin Mama yasa ta tashi da sauri ta katse wayar.
"Mama yaushe kika shigo?"
"Fito falo babanki yana jira"
Gabanta ne ya fadi. Rabonta da shi tun lokacin da Awaisu ya saketa taje gida. Dankwalinta ta janyo ta daura ta fito. Ganin Awaisu a wurin yasa tayi wani dan murmushi, wato ta nan ya bullo kuma.
"Alhaji sannu da zuwa, Abban Haris yaushe ka shigo?" Ta fada fuska a sake.
Alh Mudi ne ya soma magana "kinga bana son gulma ki zauna kawai muyi abin da ya kawo mu. Duk abubuwan da kikayi Gimbiya mun sami labari. Wallahi kin bamu kunya amma ki sani ba kowa kika cuta ba sai kanki."
Kuka ta soma yi "Alhaji sharri yan uwansa suka kulla min don kawai basa sona. Zancen da nake muku fa 'yar yarinyar nan da na rike suka aura masa"
Mama tace "Allah Yayi musu albarka da wannan hadin. Gimbi kada ki manta Bebi kanwata ce saboda haka idan ma kina shirin wani rainin hankalin ne ki nemi wanda zakiyiwa ba mu ba. Awaisu da danginsa bazasu miki sharri ba domin idanuna sun gani tun kafin ma Maamu ta dade a gidan nan kika ce min ba haka ba."
Alh Mudi ya karba "Jiya muka dawo daga wurin Inna (babarsu Mama da Anti Bebi). Rokon su Amina gafara take akan yadda ta juya musu baya komai sai Bebi. Tayi rantsuwa bata san lokacin da take wasu abubuwan ba musamman danne musu hakki da Baba ya rasu da ta hada kadarorinsa da dama ta bawa Bebi a boye. Abin da ya rage aka raba daidai kuma da ita. Ke bari na takaice miki a yanzu Bebi da mahaukaciya fa bambancinsu bashi da yawa. Idan bazaki tub.... "
Murmushi yaga Gimbi tana yi wanda ya bayyana tsantsar farincikinta jin ance Anti Bebi ta zama kamar mahaukaciya. Abin ya konawa Mama rai ta kai mata duka. Haka suka zauna suna ta nasiha da fada yana bi ta bayan kunne. Da suka tafi ta tashi harda kade riga tabi bayan Awaisu.
"To me zuciyar yara a karo na karshe ina fada maka ka barni na fita daga gidannan kafin ka ga ba daidai ba"
Yana zare necktie dinsa yace "na nawa kuma. Kada ki damu kwana nawa ne zaki kara gaba"
Tsoro ne ya kamata don har mamaki takeyi wani azababben so da take masa yanzu. Duk wannan ruguntsimin da suke fama dashi son Awaisu karuwa yake a ranta kamar ana hura wuta 'yan kwanakin nan. Da farko neman mafita take ko dai zamansu ya gyaru ko kuma ya saketa. Yanzu kuwa ido rufe gyaran take nema. Haka ta fita ba don taso ba. Har juma'a ta zagayo suna faman rigima tana son fita ga yaranta an kwashe sun koma gidan iyayenta. Wannan abu ma yayi mata ciwo. A cikin kwanakin bashi da nutsuwa sai idan yana waya da mutanen Fika musamman amarya Rumana. Daga banki sai gida yake zuwa. Bincike yake yi akan wadanda Gimbi ke muamalar zuwa wurin yan tsibbu tare dasu.
Abin da Gimbi bata sani ba shine kwanaki uku da suka wuce Anti Bebi da kyar da sidin goshi Wangesi ya yarda ya ganta. A nan ne take fada masa cewa tana zargin Gimbi domin aljanu har magana suke mata a kunne suce Gimbi tafi karfinta gashi sun jawo ana ganin kamar bata da hankali. Bayan dogon bincikensa na tsafi ya gano gaskiya ta fada. Fushi yayi mai tsanani har yaushe Gimbi ta isa tayi masa wasa da hankali. A dalilin haka yayi alkawarin ko me Anti Bebi take so ayi mata zaiyi. Shine ta rokeshi ya cusawa Gimbiya soyayya da kishin Awaisu na fitar hankali. Irin son da ko macen kuda bataso ta rabe shi. Ita kuma zata je ta tona mata asiri ya saketa. Tasan wannan son shine zai zamewa Gimbi masifa a duniya. Ko babu asiri mahaukacin son da take masa ne yasa bata son kowa ya rabesu musamman uwarmiji kada asa shi ya saketa.
*****
Dan sakin fuska yau ta shiga dakinsa tana tsaye daga gefen mudubi shi kuma yana ta aiki "kasan dai ina da hakki a kanka ko Abban Haris. Yaushe rabonka da zuwa inda nake?"
Tafi ya rinka yi har ya isa gabanta "amma dai baki da kunya Gimbi. Wai hakkinki. To na karfine sai ki kwata ko kisa bokanki ya baki tunda dashi kika dogara."
Ranta a dagule ta soma fada "nifa bazaka dokeni ka hanani kuka ba. Ka rufe ni a gida babu fita sannan ka tauye min hakki. Ga waccan shshh....."
Babu yadda za'ayi ta karasa zagin don wani mugun kallo yake watsa mata.
"Kina iya fita gobe duk inda zaki kada ki wuce karfe hudu ki dawo gida." Taji yace
Anya kunnenta ya jiye mata daidai kuwa? Bata son jan zancen kada yace ya fasa tace to kawai ta fita. A baya ya bita yana jikin kofa yaji tana waya tana cewa zata zo gobe. Dariya yayi ya koma daki. Ya rasa yadda zaiyi ya dauki wayarta saboda balain yadda take kaffa kaffa da ita ko bandaki ta shiga idan ya duba dakin baya gani.
Ba dai haka yaso ba amma dole ya kira Rumana ya bata hakuri na rashin zuwansa a satin. Dama ita da take jin kunyarsa sai ta nuna bata damu ba har yana ta mita wai taki fara yi masa son so har yanzu yana so ta fara shiri tarbarsa sati mai zuwa.
Washegari kafin tara na safe Gimbi ta fita don ko ganinta baiyi ba. Yana fitowa daga daki da yaga bata nan ya koma yayi alwala tare da nafila raka'a biyu don neman kariya. Dakin Gimbi ya fara shiga ya fiddo kayanta daga wardrobe ya bincikesu. A ciki ya tsinci layu da guraye sunfi goma. Karkashin gado, kasan kafet har su toilet babu inda bai duba ba. Abubuwa ya rinka gani harda wasu irin ruwa masu kala a robobi. Jikinsa sosai yayi sanyi karshenta babu wanda baa zuba masa ba.
Yana gamawa da dakinta nasa ya koma shi kam har cikin pillow da kasan katifa akwai ajiyar layu. Haka ya wuni yana wannan aikin harda su kitchen, dakin Maamu da duka dakunan baki da na yaransa. Bayan ya gama hadasu ya fita duk inda babu interlock a gidan yace maigadi ya tayashi tonawa. Yawanci duk wuraren shuka ne amma sunyi sa'a babu komai a wurin.
Ciki ya koma duk yayi gumi ya watsa ruwa ya gyara dakinsa sannan ya kira cikin yaran shagonsa yace yazo yana nemansa.
Kayan gidan kaf banda na dakin Gimbi amma komai harda kayan kitchen yace a samo dillalai masu saya saboda da yawa basu tsufa ba. Kafin ya tafi suka shawarta ina zaije wurin kayan furniture masu kyau. Sunan wani shago ya bashi a wata babbar plaza. Zama yayi yayi dogon list na abubuwan da zai saya nasa da Rumana da yaransa. Kayan kitchen da su labulaye da komai ya gama tsarinsa. Kudi dai zasuyi ciwo amma yadda ya tsorata da kayan tsafin nan ko bai kara aure ba ya zama dole ya rabu da komai na gidan domin samun kwanciyar hankali.
Yaron shagon sai da yayi kusan awa daya ya dawo gidan tare da masu ganin kaya. Babu bata lokaci sukayi ciniki suka turo motocin dibar kaya.
Gimbi na dawowa wurin karfe shida ta ga gate a bude motoci biyu manya cike da kaya suna fita. A gigice ta shiga gidan ta sami Awaisu a falo ya zuba hannuwa a aljihu yana magana da wani cikin mutanen inda yace duk da yasan zasu chanja kujerun amma suyi hakuri ya farke dukkansu ta kasa. Kasa magana tayi jikinta na bari tana tunanin ba dai ya ga ajiyar da tayi masa a daki ba. Ko da ta shiga nata dakin haka ta sami kayanta watse ko ta ina. Zama tayi jiki babu kwari ta dago jakarta tana tunanin ta ina zata zuba masa wannan maganin da akayi mata alkawarin karshen duk wata damurta yazo indai yasa shi a bakinsa.*KASHE FITILA*💡42
*Batul Mamman*💖
_Allah Ya tabbatar da alkhairi Ya baku hakurin zama da juna da zuri'a dayyiba. Alhamdulillah_
💝 *U & H* 💝
*Its your dayyyyy*
Aiki su Awaisu sukayi tukura ranar sai bayan isha suka tafi zasu dawo dibar sauran waahegari sannan shima zaije duba kayan da zai siyo.
Dakinsa ya wuce babu komai sai barguna da ya shimfida a kasa don hatta pillowas yayi waje dasu. Kayansa kuwa da takardu wasu suna cikin akwatuna wasu ya turasu gefe a dakin. Wanka yayi ya kwanta bayansa har ciwo yake masa saboda tsabar gajiya. Yana jin yunwa amma baya tunanin zai iya fita daga gidan saboda ciwon jiki. Wayarsa ya dauko yana ta binciken aikin da Rumana ta bashi har yau ya kasa gane me take nufi. Zuwa yanzu ma dai gani yake ko kawai tsokanarsa tayi. Murmushi yake yi shi kadai idan ya tuna rabuwarsu. Bugu yaji a kofar dakin kamar daga sama ana yi da karfi. Sai lokacin ya tuna ya rufe dakin da mukulli da zai shiga wanka kada tazo ta saka masa wani abin a cikin kaya don ya tabbatar tunda ta fita babu abin da zai hanata dawowa da wani maganin. Tashi yayi ya bude mata ta kura masa ido. Yanzu komai nasa kyau yake mata fiye da yadda ta saba gani. Haushin kanta take ji sosai na wannan makauniyar soyayya da bata yi ba ko da can da kuruciya da ta tabbatar ta so shi sosai.
"Naga an fitar da kusan komai na gidan nan banda dakunan baki da nawa"
"Sababbi zan siyo ai kinsan nayi aure ko? To amaryar ce zata tare nan ba da dadewa ba" yana magana yana kallon hannuwanta da take kokarin taba shi dasu. Ja da baya yayi ya hade fuska ta sauke hannun ba shiri.
"Ba zuwa nayi ka fada min bakar magana ba mijin Rumana mai budurwar zuciya. Nazo yi maka tuni ne akan kayan fadar kishiya da ban ga kana da niyar yi min ba tunda kayan dakina banda hargitsawa ko tsinke baa dauka an fitar ba"
Yatsansa ta ga yana kadawa a gefen kansa "Gimbi kin fara shaye shaye ne? Ni kike tambaya kayan fadar kishiya? Idan har sai na baki zaki saka kaya to ki fara shirin yawo tsirara. Ke bari na fada miki wannan hannun da kika shafowa kayan tsibbunki idan kikayi gigin tabani dashi sai na karya shi. Sauran tarkacen da kika ajiye a lunguna da sakon gidan nan ma na konasu gabadaya kuma in sha Allah kin gama samun nasara a kaina da 'yan uwana na."
Borin kunya ne ya kamata amma dayake ta kware ta daga kai tana hura hanci "ni ba damuwa zanyi da sharrin da aka cusa maka yarda dashi daga gidanku ba. Idan ma ka tsinci wani abu baya wuce wanda aka bawa Rumana ta binne a gidan nan don ka aureta. Kuma gashi bukatarsu ta biya sai su zuba ruwa a kasa su sha"
"Kinga na gaji idan kin gama abin da ya kawoki sai anjima" kofar ya janyo ya rufe ya barta a tsaye daga waje.
Shu'umin murmushin da yanzu take yi idan ta sami nasarar aiki tayi ta juya ta tafi. Indai itace sai ya dawo bata hakuri don tun kafin ya bude kofar ta shafa maganin a jikin hannun kofar dakin. Fatanta idan ya taba yaje ya dauki wani abu yaci da hannun ta samu maganin ya shiga cikinsa.
Sai bayan wurin rabin awa da tafiyarta ya bude kofar ya fito rike da karamin towel jike da ruwa. Bismillah yayi ya goge kofar tun daga sama har kasanta. Duk da bai ganta ba amma yaji a jikinsa yanzu ko ta wane hali Gimbi zata yi kokarin hadashi da magungunanta. Ji yayi kamar ya saketa tun yanzu sai ya fasa. A kalla ta zauna ko na wata daya ne da Rumana ta kwashi guzurin bacin rai ta tafi dashi.
Rumana ya kira Iman ta dauka tace masa tayi bacci. Ya kula tana kwanciya da wuri shiyasa yake kiranta da farkon dare. Yau da bai kira ba ta sami kanta da jiran wayar tasa har bacci ya dauketa. Gashi ita kuma tana kunyar kiransa da kanta.
*****
Washegari Rumana da wuri tayi wanka saboda Mama tayi mata waya tace taje gidansu Hajiya Umma tana kiranta. Tana shiryawa Iman tazo ta zauna a kan gado
"Rumana kina kiran Uncle Awaisu kuwa?"
Ta madubi ta kalli Iman din "bangane ba?"
"Naga kullum sai dai yayi ta kiranki a waya. Jiya ma ya kira kina bacci. Ke ko dan text dinnan bana jin kina masa bare su chatting a whatsapp."
Juyowa tayi da kyau ta kalleta "Iman, Uncle ne fa. Sai in yi masa text don rashin kunya."
Dariya Iman din ta yi taje ta kamo hannunta suka zauna "Jiya Ummanmu ta tambayeni ko kina masa waya nace kuna waya dai don ban san dalilin tambayar ba. Shine tace in fada miki ki rinka sakin jiki dashi gidansa zaki koma. Kuma dai Rumana baki gani mu masu samari ma ko babu kudin kira mukanyi text balle ke da mijinki. Mijin ma kamar Uncle dan gayu dan boko"
Rumana tayi shiru jikinta ya danyi sanyi "tsakani da Allah ina son yi amma tsoro nake ji kada ya fassarani yace sonsa nake yi"
Wani mugun duka Iman ta sakar mata a baya saki kara tare da mika hannu tana shafa wurin. Iman tace "Wai kada yace kina sonsa. To da bazaki so shi ba bayan ya zama mijinki? Ko don kinga babba ne" ta kare da sanyin jiki.
Kuka Rumana ta soma yi mata ta girgiza kanta "kunyarsa kawai nake ji har cewa yake yana sona Iman. Idan ya fada sai naji har tsigar jikina na tashi. Wai ni yake so. Ta yaya zamu zauna idan aka kaini