Showing 9001 words to 12000 words out of 112099 words
Chapter 4 - KASHE FITILA Book Complete by Batul Mamman.txt
tsakiyar katon kafet din falon. Sai da ta gama sannan tazo ta durkusa har kasa tana gaishesu tana satar kallon fuskar Maamu. Wangesi dai yace gidan zafi zaiyi mata da kanta zata nemi a mayar da ita inda ta fito. Wani murmushi tayi sannan ta cigaba da tambayar Rumana yaya mutan gida.
Da yake Maamu banda amsa gaisuwa da kalmomi kadan ita ba Hausa ta iya ba shiyasa bata shiga hirarsu sosai. Baaba ma yau da gobe tasa Hausarta sai a hankali, ta iya amma sai ka zata ba bahaushiya ke magana ba. Haka Rumana da Zakiyya su duk da sun dan iya amma ba kamar Awaisu mai auren bahaushiya da kuma Harisu dan kasuwa ba. Bolanci yafi kama bakinsu. Hirar dai aka ake yinta wani abin sai kaci dariya. Idan kaga Gimbi a tsakiyarsu sai ka rantse ko goyo suka nema zata yi musu. Shiyasa basu taba korafi akan ta ba. A ganinsu yanayin aiki ne yake sawa bata zuwa Fika sosai.
Dakin da aka tanadarwa Maamu nan Baaba tayi masauki tare da Zakiyya. Gado ne kato wanda zai ishi mutum hudu ma. Ba karamin kashe kudi Awaisu yayi ba. Harda tv ya saka mata da fridge. Baaba da aka soke zuwanta Abujan itama yayi shirin sake gyara mata nata dakin kafin su dawo daga Hajji.
Ranar a wurinsu ya yini shi da Harisu. Da safe zai tafi aiki ya bar sallahu cewa drebansa zai dawo sai ya kai Harisu kasuwa ya ga shagon nasa.
Kwananusu biyu babu wata matsala da ta taso. Ranar laraba Awaisu zai tafi aiki Gimbi take sanar dashi ta dauki hutu na tafiya Hajji. Ya nuna mata jindadinsa tunda ga baki dama a gidan. Bayan fitarsa bai dade ba Anti Bebi tazo. Da yake safiya ce babu wanda yasan tazo ta shige dakin Gimbi. Mayafinta ta cire wanda ya bayyana siraran kitson da akayi mata da karin gashi. Dama ita da wuya tasa dankwali. Dan mayafi ne guntu shara shara kullum take fama dashi.
"Ke kuma sai naji ki shiru babu wani jawabi game da bakinki?"
Gimbi ta tabe baki "hmmm Anti wannan anya ba kudina yaci ba. Kullum naje dakin sai tayi ta murmushi babu alamun ta soma gajiya da gidan. Ita fa fuskarta kullum a sake kamar mara lafiya. Har tunani nake ko aljanun nan ne masu sa dariya basuyi mata kamu sosai ba aka tsaya a murmushi"
Dariya sosai Anti Bebi tayi "Shegiya Gimbi, ashe kema baki da mutumci, yarinya tayi gadon uwa. Kuma ina mai tabbatar miki indai zakiyi yadda nake yi to babu wanda ya isa ya taka ki"
Gimbi shiru tayi. Idan da Mama zata ji abin da take yi yanzu Allah kadai Yasan fadan da zatayi mata. Balle kuma Alhajinsu da ya dauki son duniya ya dorawa Awaisu. Shi a ganinsa ba karamin dace yayi da surukai ba.
Sai bayan azahar Anti Bebi ta dauki mayafinta
"Tashi muje na ga bakin naki sai na wuce daga can. Idan anyi sati babu chanji da kaina zan koma wurin Wangesi"
*****
A falo suka tarar dasu harda su Haris sun dawo sun tsaya basu labarin makarantarsu.
Anti Bebi kallo daya tayi musu taji babu wanda yayi mata a cikinsu. Duk da cewa zata yi sa'ar Ummu kulsum 'yar Baaba Hure ta uku domin ita ce autarsu Mama amma daga tsaye ta dan dago musu hannu
"sannunku"
Zakiyya ta amsa mata tana yi mata wani irin kallo. Wannan mata duk inda ta fito akwai rashin kamun kai a tattare da ita. Labaran da akeyi a tashar NTA Hausa shine ya dauki hankalin Baaba Hure ga Rumana ta biyewa su Amir suna ta hayaniya. Remote din tv ta dauka zata karo sautin yadda zata ji jawabin mai kawo rahoton. Tana cikin dannawa Anti Bebi ta kwashe da dariya
"Mhmmm ashe harda su kaza a cin danko. 'Yata kinyi sa'a su o'o hannu baya gani ya kyale. To gaskiya a dage a sayo musu computer"
Baaba Hure ji tayi kamar an zuba mata ruwan zafi saboda yadda zuciyarta ta harzuka. Bata bukatar wani bayani tasan cewa da ita wannan bakuwar take. Ajiye remote din tayi jikinta babu kwari tana jiran amsar da Gimbi zata bayar sai ji tayi tace
"Waya ga dan wake a hotal"
Zakiyya da Maamu sai dan murmushi sukeyi. Ita Zakiyya duk da tana dan jin Hausa ko kadan bata fahimci inda zancen nasu ya dosa ba balle kuma Maamu.
Baaba Hure ganin haka itama sai ta biye musu tana murmushin. A iya saninta Gimbi bata san cewa ita asalin bahaushiya bace. Kuma yanayin da Hausarta ke fita da wuya ace tana gane karin magana indai ba yarenta bane. Gara ta nuna musu itama bata ji ko don ta ga iya gudun ruwansu. A lokaci daya kuma tausayim Maamu ya cika mata zuciya. Ashe Gimbi ba son Allah da Annabi take yi musu ba. Indai hakane kuwa akwai matsala wannan zaman da zata yi a gidan.
Da yamma da Harisu da Awaiau suka shigo. Baaba taso ta sanar da Harisu abin da taji sai kuma tayi tunanin kada ta zama uwa mai sa ido. Daga faruwar abu daya bai kamata ta yanke hukunci akan cewa Gimbi ba mutuniyar arziki bace. Hakan yasa ta fasa cewa komai.
*****
Bayan kwana hudu aka kirasu sune diba na biyu. Awaisu da drebansa sukayi mota biyu aka kaisu Airport. Basu dawo ba sai da jirginsu ya tashi.
Madina suka fara wucewa. Tun a hanya Gimbi ta soma zazzabi mai zafi da amai. Suna isa aibiti aka kaita likita yace taci wani abu ya bata mata ciki. Duk rashin kirkin da taso gwada musu sai ta koma abar tausayi suna jinyarta. Kwanakin Madina kaf bata ji dadinsu ba. Haka suka je Makkah can ma bata da wani kuzari. Wannan Hajjin dai bata ji dadinsa ba kwata kwata. Daga zazzabi ya warke sai mura mai zafi da ciwon wuya. Haka sukayi kwana talatin suka dawo da ita duk ta fige sai mugun nufi a zuciya.
*****
Sai da sukayi sati da dawowa sannan suka koma Fika aka bar Maamu da Rumana. Gimbi ce ta samar mata makaranta wadda bata da nisa sosai da gidansu. Makaranta ce mai tsada mai kyau don kawai ta burge Awaisu.
Da taga hankalinsa a kwance yake da abubuwan da take yi ta koma gidan Anti Bebi tana korafin rashin aikin maganin Wangesi.
"Kwantar da hankalinki naje na same shi. Yace wannan magani ranar da suka je gidan wani abu ya bata sihirin da yake ciki." Wata leda ta dauko ta mikawa Gimbi.
"Ga wannan yace ki dafawa mijinki abinci dashi. Daga ranar a hankali duk wani so da kulawa da yake yiwa uwar tasa zai fara fita daga zuciyarsa. Sai kiyi amfani da wannan damar ki gasa mata aya a hannu. Da kanta zata kwashi kafarta ta gudu gashi an daure bakin"
Karba tayi jindadi ya bayyana a fuskarta
"Ina fata wannan karon a dace. Idan ba haka ba kuma zanyi maganinta da kaina. Shiru shirunta irin na munafukai shi nafi tsana. Kinsan irinsu abin tsoro ne. Ga wannan yarinyar da suka zo tare mai cin tsiya. Ina tsammanin horon yunwa zan fara yi musu a gidan"
[4:19PM, 2/18/2018] +234 803 369 4017: *KASHE FITILA*💡10
*Batul Mamman*💖
Ranar laraba da daddare Gimbi da kanta tayi girki sabanin yadda ta saba saboda yanayin aikinta Laminde ce take yi. Maganin da aka karbo mata ta juye shi tas a miyar Awaisu ta kara maggi.
Da ya dawo dakin Maamu ya fara zuwa ya gaisheta tare da zama zai fara hira ta dube shi duk da alamun gajiya a tare dashi
"Ka tashi kaje kaci abinci ka huta na yafe hirar nan"
"Maamu ni sai kiyi ta korata. Da Yaya Harisu ne ai sai kin gama sauraronsa"
"Sannu baban kishi. Yanzu dai ka tashi, ka ga matarka itama ba zama take yi ba. Dan lokacin naku kuma bazan so na hanata sakewa ba. Ni ban zo gidan nan don takura muku ba. Abokan hirar nawa ma abinci suka tafi ci. Yanzu zaka ga sun dawo"
Tashi yayi rike da coat dinsa a hannu yace zai dawo bayan yaci abinci yayi wanka. Har ya fita tana cewa ta yafe hirar yau.
Wanka yayi Gimbi ta biyo shi da abincinsa daki wai falon hayaniya tayi yawa. A haka tana yi masa hira ya cinye tuwon da ta zuba masa harda neman kari. Dadi ya kamata kuwa. Yanzu abin da ya rage kawai shine ta fara gwada aikin maganin.
*****
Washegari saboda fitarsu aiki da zuwan yara makaranta tun asuba suke tashi ranakun aiki. Kitchen ta shiga ta aunowa Laminde shinkafa sannan ta fito da kazar da ta tafasa tun dare.
"Kiyi min jallof din shinkafa taji alayyahu da busasshen kifi. Wannan kazar kuma pepper chicken nake so kiyi. Kiyi komai cikin sauri kinsan Abbansu Daula baya son jira."
Laminde ta gyada kai "To Hajiya, amma shinkafar bazata ishemu har su Hajiya Babba ba da 'yan makaranta"
Gimbi ta koma store din da yake cikin kitchen din ta dawo rike da wata karmasasshiyar doya. "Shinkafar ki dafa mana ni da yara da babansu. Wannan doyar kuma fate zaki yi muku ke da sauran mutan gidan"
Laminde ta kalli doyar ta kalli uwargijiyarta. Ita dai tunda take a gidan ba'a taba yi mata wulakanci akan abinci ba. Wani lokacin ma ita Gimbi take barwa zabin abincin da za'a dafa. Kasa shiru tayi ta dan rausayar da kai tana kara kallon doyar da ta bushe
"Wai Hajiya nace ba, uhmm ita Hajiya Babba nake nufi ki karo shinkafar saboda ita"
Daure fuska Gimbi tayi "sunanta Maamu ba Hajiya Babba ba. Wannan so kike yi wani yayi zaton ni da ita uwargida da amarya ne. Anyway, itama faten zaki zuba mata naji ance tana son doya. Ga langa can da na karbo wurin Mama. Kinsan mutanen da suna son komai irin na zamaninsu. Shine na nace har sai da Mama ta bani cikin nata tun na aure. A ciki zaki rinka zuba mata abinci. Kuma kiyi sauri tare zamu fita zan aike ki"
Kasa hadiyar yawu Laminde tayi domin tsananin mamaki. Langa ce da gaske ga kuma doya da akace ta zuba mata. Ko ita da take aiki yau tasan anso wulakanta ta bare uwarmiji. Magana take son yi amma sam bakinta ya kasa hada kalma ko daya. Tana ji Gimbi tace ita zata yi musu nasu girkin wanda suke tafiya dashi wurin aiki yaran kuma suje dashi makaranta. Ita kuma tace tayi sauri tayi faten kada su makara.
*****
Rumana cikin sauri ta gama shirinta tsaf saboda bata so a jirata. Tun fara zuwa makarantarta kwanaki biyu da suka wuce tare suke fita da yaran gidan da Gimbi. Dreba ne yake kaisu makaranta ya wuce da ita wurin aiki. Tunda a banki take shiyasa suke yin sammako sosai.
Ko da ta fito falo Mu'allim ne kawai Gimbi take bashi abinci a baki yana ta rigima shi bacci yake ji. Har kasa ta durkusa ta gaisheta sannan ta nufi dinning table inda kayan tea suke zata hada.
"Dakata Rumana me zakiyi a nan?"
Murmushi tayi ta kirata yadda yaran gidan suke kiranta "Mummy tea zan sha kafin su Haris su fito"
"Kinga daga yau ki rinka zuwa wurin Laminde ki sha tea din a can."
Bata ji komai a ranta ba tayi hanyar kitchen. Sake dakatar da ita Gimbi tayi "Kiyi sauri kisha ki fito kada ki makara"
Dayake bata san sunan dreban ba sai tace "Mai kaimu makarantar har yazo ne? Bari na fadawa su Amir suyi sauri su ma"
"A'a kina jina ko Rumana, makarantarku ba wani nisa gareta ba. Ki rinka shiryawa da wuri kina tafiya. Tafiyar da mukeyi da ke tasa ina makara kwana biyu. Gashi ba'a gama abinci ba. Idan kin dawo sai ki ci. Tea din ma ruwan zafin aka juye a girkin sai an dafa wani"
Sai a lokacin Rumana taji wani iri a ranta.
"To Mummy bari na tafi, sai kun dawo"
Gimbi harda murmushi "yauwa Rumanan Abba. Allah Ya kiyaye kinji."
Rumana ta dan tsaya jim ko zata bata kudi tunda sai hudu da rabi suke tasowa. Gimbi ta fahimci dalilin tsayuwar ta dan sake fuska "ko akwai wani abu ne Rumana?"
"A'a babu komai. Na tafi"
Fita tayi tana tafiya a hankali. Allah Yasa makarantar a bakin titi take kuma babu wuyar ganewa. Tafiyar minti shabiyar zata kaita idan tayi sauri. Iyayenta ne suka fado mata a rai taji kamar ta fashe da kuka. Bata san yadda zata fassara abin da Gimbi tayi mata ba. Tayi kamar minti biyar tana tafiya taji mota ta tsaya a gefenta. Horn da akayi yasa ta kalli motar. Mace ta gani tasha lullubi sai wata yarinya mai uniform irin nata. Da ta sake kallonta ta tuna ajinsu daya duk da bata san sunanta ba. Gaishe da matar tayi cikin hausarta.
"Shigo mu karasa kin fito cikin sanyin nan ko rigar sanyi babu. Kada kiji tsoro ga Yusra ajinku daya tace min"
Bayan motar ta shiga ta sake gaisheta sannan Yusra ta juyo "Sunanki Ummu Ruman Abali ko"
Rumana ta gyada kai tana murmushi. Hira uwa da 'yar suka cigaba da yi har suka iso kofar makarantar.
"Umma baki bani kudin break ba fa"
"Yusra bana son wannan kashe kudin da kike son koya. Ga abinci nan a jakarki"
Yusra ta sake kwantar da kai "Umma ko hamsin ce saboda siyan ruwa"
Dari biyu maman ta mika mata "gashi ku raba da Rumana idan kun fito. Allah Ya bada sa'a"
Rumana tayi mata godiya suka jera cikin makaranta tare da Yusra wadda take yi mata tambayoyi akan makarantar da ta baro. Da haka ta manta da bacin ran da ta fito dashi.
*****
Duk sun gama shiri sun fito Awaisu ya tambayi ina Rumana. Gimbi tace
"Ta tafi, wai makarantar babu nisa zata rinka tafiya da kanta."
Bai ce komai ba suka fice saboda ya leka Maamu tana bacci.
Bata farka ba sai karfe tara da kusan rabi. Sabanin yadda ta saba ganin tray din abincinta na safe yau babu komai a wurin sai wata langa da cokali makale a hannunta. Bata kula ba ta shiga bandaki tayi wanka. Sai da ta gama shirinta ta zauna shiru Laminde bata kawo abinci ba. Fita tayi falon taji gidan tsit alamun ita kadai ce. Komawa dakin tayi tana tunanin ina Laminde taje haka. Dama ita take tayata hira kafin yaran su dawo daga makaranta. Langar ta sake kallo bayan ta koma sai ta bude. Faten doya taci karo dashi yayi wani baki ya cure wuri guda saboda rashin wadatar mai. Haka aka yi shi kandas sai kan sauran kifin da Gimbi tayi musu abinci. Mayarwa tayi ta rufe zuciyarta tana karyata cewa wannan abincin nata ne.
[4:19PM, 2/18/2018] +234 803 369 4017: *KASHE FITILA*💡11
*Batul Mamman*💖
Haka Maamu ta zauna har azahar bata ci komai ba ga yunwa tana ji. Tasan dai wurin biyu da rabi yaran suke tasowa daga makaranta. Kila su dawo tare da Laminde. Da wannan tunanin ta cigaba da zama har uku ta wuce.
Karfe daya da rabi dreba ya kira wayar Gimbi ya sanar da ita zai je dauko su Haris. Ta umarce shi da idan ya daukosu ya taho dasu bankin su jira har ta tashi. Da farko wurin Mama tayi niyar cewa ya kaisu. Sai ta tuna zata iya cewa me ya hana su koma gida saboda Islamiyya. Ita kuma ko tana hauka bata jin zata taba tura yaranta gidan Anti Bebi. Ita din ma da take zuwa yanzu don biyan bukatar kanta ne kawai.
Shi dai dreba sai mamaki yake yi amma haka nan ya dawo cikin banki ya sami inuwa yayi parking. Nan fa daga mai kiran fitsari sai mai jin yunwa ko bacci. Haris da ya fisu hankali korafin rashin zuwa islamiyya yake yi. A haka suka yi ta zama har bacci ya kwashesu.
*****
A makarantarsu Rumana kuwa da break sai ga Yusra tazo ta bata naira dari kamar yadda Ummanta tace su raba. Da kyar ta karba duk da cewa yunwa take ji. Yusra tayi mata tayin abinci taki karba shima. A ganinta basu yi sabon da zata ci mata abinci ba bayan ita bata zo da nata ba. Karfe hudu da rabi suka fito ta nufi titi za ta tsallaka. Yusra ta dakatar da ita
"Rumana ki jira Umma tazo. Yanzu za ta biyo idan ta ajiye kannena a islamiyya"
"Idan na tsaya za'a yi min fada a gida."
Daga haka suka yi sallama ta tsallaka daya gefen ta kama hanyar gida. Tafiya ta rinka yi tana jan kafa saboda tsabar yunwa. Yau da azumi take yi ba karamar wahala zai bata ba. Daren jiya tun takwas da rabi tayi bacci ko abincin dare bata ci ba. Gashi yau bata samu ko ruwa ta sha ba.
Da sallama ta tura kofar falon sai dai babu alamar akwai mutane a gidan. Dakin Maamu ta wuce. Tana taba kofar dakin Maamu tayi saurin tura langar faten karkashin gadonta. Tsoronta kada Rumana ta gani har wani yaji ayi tunanin Awaisu ko matarsa basa sonta ne. Zata yi bakin kokarinta wurin kare mutumcinsu a idon duniya.
Takalmi kawai Rumana ta iya cirewa ta fada kan gado tana rike ciki.
"Maamu yau naji yunwa sosai har jiri ya rinka daukana a hanya"
Tasowa Maamu tayi ta dawo kusa da ita ta zauna tana dora hannu a kan Rumana
"Baki da lafiya ne kika ki cin abinci?"
Bata boye mata komai game da yadda sukayi da Gimbi ba da safe. Hatta kudin da Umman Yusra ta bata sai da ta nuna mata domin ko kwandala bata kashe ba. Hakan ba karamin daga mata hankali yayi ba da kuma neman tabbatar mata da zargin da take gudun dorawa iyalin Awaisu.
"Tashi ki je ki hada shayi ki sha kafin su dawo. Doya aka dafa ke kuma nasan ba kya ci"
Rumana ta yamutsa fuska saboda yadda ta tsani doya. Falo ta koma sai dai babu kayan tea a tsakiyar dinning table kamar yadda ta saba gani tun farkon zuwanta. Ta shiga kitchen nan ma babu wani abin kirki sai ta tafi zata dauko indomie a store. Nan fa taji kofar a rufe. Tunani ne ya isheta game da sauyin da ta gani a gidan yau. Haka ta koma wurin Maamu ta fada mata.
Hankalinta ya sake tashi sosai. Duk da tana jin yunwa itama amma tausayin Rumana ne ya kamata. A ranta tana adduar Allah Yasa ba wani sabon salon zama zasu koma yi da Gimbi ba. Da wane ido zata kalli su Baaba Hure.
"Dauko wayata ki duba nambar Gimbi ki kira"
Rumana ta aiwatar da abin da aka sata. Tana