Showing 96001 words to 99000 words out of 112099 words
Chapter 33 - KASHE FITILA Book Complete by Batul Mamman.txt
dakinsa. Kafin ta iya amsawa yayi gaba. Wani guntun zazzabo ne taji yana barazanar kamata. Ina ita ina zuwa dakinsa a daren nan. Ita fa tunda gari ya fara duhu tsoro ya sami gurbin zama a zuciyarta.
Kamar dazu da rana abinci ya mikawa Gimbi saboda baya son ko kadan ya shiga sahun masu tauye hakki sannan ya wuce yayi wanka. Ya kusa rabin awa babu Rumana babu dalilinta. Katan din su viju da juice da ya siyo mata ya dauko daga mota ya shiga dakin dasu. Tana takure akan gado jin ya taba kofar ta tashi a guje zata shige toilet harda bigewa da gefen gado ta saki kara amma duk da haka bata tsaya ba. Kansa kawai ya girgiza ya bude karamin fridge din ya fara jera mata lemukan. Dama saboda zuwa makaranta ne ya siyo mata. Karamar jarka ya gani da wani abu kamar zuma ya dauko ya kare masa kallo sannan ya fice ya tafi nasa dakin dashi. Ita kuwa wanka tayi saboda zaman bandakin ya isheta. A hankali ta leko ganin baya nan ta fito ta shirya cikin kayan baccinta ta haye gado ta kwanta tana fargaba kada ya dawo. Da Awaisu ya gaji da jiranta ya dawo dakin sai ya ganta tana bacci. TV din da ta bari a kunne ya kashe ya koma dakinsa yaci abinci yana tunanin Rumana da ta kwanta bata ci komai ba. Shima da kyar ya iya bacci yana ta tunanin maganganun da sukayi da ita a kitchen yana murmushi. Maganar Malamin da yaje ya gani ne ta fado masa tunaninsa ya karkata kan Gimbi har bacci ya dauke shi.*KASHE FITILA*💡49
*Batul Mamman*💖
Ana kiran assalatu ya farka yayi alwala sannan yaje dakin Rumana ya tasheta. A firgice ta tashi duk a tunaninta bata dade da kwanciya ba
"Uncle yanzu zan taho"
Gefen fuskarta ya shafa yana kallonta cike da so "kin yiwa kanki, kwana bakwai din da aka baki kin cinye uku a gudun miji. Ki tashi kiyi alwala asuba tayi"
Maganarsa ta farko tasa ta jin kunya amma jin yace asuba tayi ya sanya jikinta yin sanyi. Tsoro take kada ya fara ganin kamar tana masa gardama ne. Fita yayi gidan da yake jikin nasa akwai masallaci nan suke sallah dayawa mazan unguwar.
Da ya dawo dakinta ya sake komawa ya sameta akan abin sallah. Tana ganinsa ta gaisheshi ya mika mata hannu ta tashi tsaye. Gani tayi kawai ya rungumeta yana shafa kanta dake kwance a kirjinsa
"Jiya kin barni ina ta tunaninki da kyar nayi bacci. Naso in fada miki yau zaki fara zuwa sch na tarar kinyi bacci"
Kanta ta kara turawa jikinsa a hankali tace "kayi hakuri"
"Its ok gobe sai kije. Ni zani office muje ki tayani shiryawa"
Hannunta yaja ta bishi cikinta har wani kadawa yake yi. Ta tayashi shiryawa fa yace. Ita kam yau taga boni ta fada a zuciyarta.
Suna shiga yace ta dauko masa tawul a toilet ta wuce ta dauko yana binta da kallo. Da zata bashi hannunta har rawa yake yi ta rufe idonta ta mika masa saboda tana fitowa ta ga yana cire jallabiyar. Hannunta ya riko da tawul din "muje ki tayani kada na makara"
Ai tuni da bude idanun a rikice "Wa? Ni din?? Don Allah Kayi hakuri"
Wuceta yayi yana cewa "lokaci ne dai nima zanyi miki yangar nan" ya shige bayan ya fada mata ta ciro masa kayan da zai saka.
A iya saninta suit yake sawa idan zaije aiki. Bude wardrobe dinsa tayi ta gansu kala kala an jeresu makale a hanger. Guda daya ta dauko dark green tayi sa'a kowanne akwai matching shirt da tie shiyasa bata bata lokacin nema ba. Turaruka ta samu a kan dressing mirror ta fesa wannan ta fesa wancan a jiki. Jin motsin kofa yasa ta koma bakin gado ta zauna tare da rufe ido harda janyo hular kanta ta sake rufewa.
"Allah idan baki bude idonki ba zamuyi fada. Don ma kinyi sa'a ina sauri bance muyi wankan tare ba"
Wani yawu ta hadiya ta bude idon amma ta kasa daga kai. Da sauri sauri taga yana shiri kanta a kasa ita dai har ya gama. Kayan da ta dauko ya saka ta dan dago kai tana juya hannuwa
"Uncle...uhmm Son So me zan dafa maka kaci kafin ka fita?"
"Kada ki damu ina da uzuri ne da sassafen nan zan sha tea a office idan na nutsu. Ke dai ki tabbatar kin sami abinci kinci zan turo miki na rana sai na taho da dinner idan na taso. I may be late amma kiyi hakuri zan kira ki. "
Kai ta gyada ya nuna mata kumatunsa ta dan daga gira alamar rashin ganewa yace "goodbye kiss"
Gani yayi zata kuma sunkuyar da kanta yayi saurin dago habarta "please Son So i need it, kuma kinsan sauri nake yi dai"
Rufe ido tayi yace yaga alama makauniyar Awaisu zai koma kiranta. A hankali ta matso harda dagenta sai dai lips dinta na karasowa ya juyo da fuskarsa sosai tayi masa a baki maimakon kumatu. Kunya sosai taji shi kuwa ya rinka dariya ya rike kugunta suka fita tana dauke da briefcase dinsa. Daga falo yace ta koma baya so ta fito a haka. Daga masa hannu ta tsaya yi har ya fice sannan ta koma dakinsa ta hau gyara.
*****
Yana shiga mota yace da Gambo drebansa su wuce police station na zone 4. Da zuwa ba bata lokaci bayan ya gabatar da kansa aka kaishi wurin D.P.O. Bayan sun gaisa yace da Awaisu dalilin wayar da yayi masa jiya sun ga mota wadda ta dace da kwatancen motar matarsa da yace an dauke.
Waje suka fita kafin ma a bude motar ya tabbatar ta Gimbi ce. Ciki suka koma a gabansa aka kira mutumin da ya saya shi kuma ya sake jaddada musu ba sata yayi ba da kudinsa ya saya. Nan dai aka nemi ya fadi a inda ya saya ya basu kwatancen gidan Ovi.
DPO ya tabbatarwa Awaisu zasu je kamasu idan sun kawosu station za'a neme shi. Jikinsa a sabule ya fita yana fatan Allah Yasa Gimbi ba da kanta ta bada motar ba saboda ta sami kudin zuwa wurin boka. Haka ya wuni ranar baya jindadin aikin ga tunanin Rumana da ya addabe shi. Wuraren la'asar bayan Gambo ya dawo daga kaiwa Rumana abinci mutumin da Awaisu ya tura neman Anti Bebi ya kira yace bai sameta ba a Niger din da akace musu ta tafi. Inda aka kwatanta masa yaje wurin wani tsohon malamin tsibbu ne amma ance ta dawo Nigeria kwana biyu da suka wuce. Godiya yayiwa mutumin ya aje wayar.
Nemanta yake yi dama saboda ya hadata da Gimbi ya kaisu gaban malamin da Nuru ya rakashi wurinsa. Mutumin babban limami ne a garin Abuja wanda ya tabatarwa da Awaisu idan suna son rayuwarsu ta tafi cikin kwanciyar hankali batare da fargabar wani sihiri ko cutarwa daga Gimbi ba sai ya kaita anyi mata nasiha da wa'azi da dukkan wani abu da za'a iya yi domin tsoratar da ita laifinta da azaba da kuma kwadayin rahamar Allah. Sosai ya gamsu da bayanin malamin saboda ko ba komai Gimbi uwar 'ya'yansa ce. Baya fata wannan halin nata yayi naso ya taba masa zuri'a.
Shida da rabi ya isa gida ana gab da kiran magariba. Alwala kawai yayi ya fita.
Kafin ya dawo Rumana tayi sallah ta fito falo jiransa. Kwalliya tayi kamar yadda Fattu ta koya mata tana sanye da riga da skirt na material ta rike dankwalin a hannu saboda yaki daurowa.
Gimbi ce ta fito ta watsa mata mugun kallo Rumana ta dauke kai.
"Wato kinyi aure kin girma shiyasa bazaki iya gaisheni ba ko"
Kamar tayi shiru sai dai tace mata ina wuni.
Kwalliyar da tayi da komai nata suka tsayawa Gimbi a rai. Duk wannan wai mijinta Awaisu Rumana tayiwa ya gani yaji dadi.
"Rumana ki taimaki kanki ki bar gidan nan tun ban lahanta ki ba. Ki bar ganin na kyaleki har kinkai wannan lokacin. Duk ranar da na waiwayeki banajin za'a sake samun mamora a tare dake. Banza 'yar gidan masu zuciyar kare makwadaita"
Rumana taji zafin maganar sosai ta tashi ta kalli Gimbi "karo na karshe da zaki sake zagar min iyaye kenan na kyaleki."
Gimbi ta hayyako mata a fusace "nice kike kyalewa? Lallai Rumana bakya kaunar kanki shiyasa bakinki ya bude saboda kina ganin mun zama sa'anni mijinmu daya amma zanyi maganinki ina zuwa...."
Ciki ta koma ashe kitchen ta shiga. Rumana tana tsaye zuciyarta na radadin zagin da akayiwa iyayenta sai ji tayi an kwara mata wani abu da bata gane ko meye ba da farko. Jikinta ne ya hau bari ganin danyen manja yana binta tun daga kanta har kafa. A daidai lokacin Awaisu ya shigo idanunsa suka gane masa Gimbi da galan din manja ga Rumana a tsaye ta gama baci.
Ya harzuka karshe ya karaso gabansu sai dai ko kala bai cewa Gimbi ba zuciyarsa kawai ke masa zafi.
"Son So tsaya a nan ina zuwa"
Dakinsa ya tafi sai gashi ya dawo da roll din tissue har uku. Ya wuce kitchen ya dauko leda sannan ya tattare hannun rigarsa ya fara goge mata jiki yana rage manjan. Kuka take son yi amma ya makale jikinta ne kawai yake rawa. A zuciyarta tace dama me take tsammani daga Gimbi. Sai da ya karar da tissue biyu da kusan rabi yana goge mata jiki da wurin da take tsaye sannan ya dauketa har lokacin tamkar babu Gimbi a wurin suka shige dakinsa. Bai sauketa a ko'ina ba sai cikin baho ya tara ruwan zafi a bokita yace mata yana zuwa.
Kofar dakin ya sakawa mukulli ya rufe sannan ya cire rigarsa daga shi sai dogon wando da ya nade zuwa gwiwa ya koma bandakin.
******
Wata irin kururuwa Gimbi tayi ta saka kuka mai cin rai. Ji take kamar son Awaisu zai kasheta. Wannan wulakancin da tayiwa Rumana tayi ne kawai don ya kulata ko fada ne yayi mata taji dadin muryarsa. Wannan wace irin masifa ce take masa so fiye da wanda take yi masa a da. Kuka take sosai tana rike kirjinta da yake zafi sosai.
Daki ta koma ta shiga laluben numbar Ovi. Tayi sa'a 'yan sandan da suka je kamasu basu samesu a gida ba suna kasuwa taje sayar da sarkar gwal din da Gimbi ta kaiwa boka. Suna gudun tusar nan ta dafeta ko bokan bai sani ba. Kuka Gimbi takeyi kamar ranta zai fita.
"Ovi kece gatana ki taimaka ki fada min yaya zanyi da rayuwata. Kullum son Awaisu tamkar ana hura wuta nake jinsa ga wannan tsinanniyar yarinyar ya fifita ta akan komai"
Ovi taja gajeren tsaki ita fa Gimbi ta isheta ta hanata sukuni. Karya kawai ta sharowa Gimbi da sawa ranta zata jefar da sim card dinta ta sake wani. Idan sun sayar da sarkar gida zasu sake gabadaya ta nemesu ta rasa
"Boka yace matar nan da akayiwa aiki na karshe itace nata aljanun suka hana komai yiwuwa. Yana tsammani itama boka gareta mai karfin gaske"
Gimbi tayi shiru tana tunani. Tabbas biri yayi kama da mutum. Lokaci lokaci sai taji ana ja mata gashi ko ta kwanta a makureta akan gado. Abubuwan dake faruwa da ita sun wuce hankali ashe itama likitan 'yar hannu ce shine ta tona mata asiri a asibiti? Murmushi tayi ta ajiye wayar. Abinda tasan inda zata sami Dr. Yana. Komai zaizo mata da sauki. Iyaka dai ta bata hakuri akan ramuwar da tayi na bata mata aiki da Yana tayi duk da bata san me aka raba Yana din dashi ba.
*****
Inda ya barta a tsaye haka ya dawo ya sameta. Tausayinta fal a zuciyarsa ya fara kokarin cire mata kayan da suka gama baci da manja ta rike masa hannu. Fuskarta ya kalla idanunta suna kyallin hawayen da yake barazanar sauka a kowane lokaci.
Kai ta ga ya girgiza mata "Umm Ruman kada kiyi min gardama kuma kada kiyi kuka kinji ko. Raina a bace yake fiye da yadda kike zato. Kokari nake na danne fushina saboda bayyana shi bashi da wani alkhairi. Biyayya da hakurinki shine zai bani strength din cigaba da daurewa"
Jikinta ne yayi sanyi sai ta koma tausayinsa ba ita da Gimbi tayiwa aika-aika ba. Duk da yanayi da suka tsinci kansu na tsantsar bacin ran da Gimbi ta kunsa musu bai hanata jin matsananciyar kunya ba. Tun daga kanta Awaisu ya soma wankewa sai da ya kusan karar da sabulu guda saboda yadda manjan nan ya sami wurin zama a cikin gashinta. Yafi rabin awa yana wanke mata jiki bandakin kansa ya fita hayyacinsa da mai sannan da ya gama yace tayi alwala ta jirashi a dakin.
Kafin tayi alwalar ya fita tana gamawa ya dawo ya rufa mata tawul ya kaita daki sannan ya rufe kansa a toilet din. Sai a lokacin yaji wani hawaye mai dumi ya sauko masa. Zuciyarsa ta karye sosai daurewa yayi a gaban Rumana. Tuhumar kansa yake yi ta yaya akayi ya kwashi shekaru tare da Gimbi bai san haka zuciyarta take ba. Dubban mata sunyi abinda yafi watsawa kishiya manja saboda kishi, ya tabbatar ita ba kishin bane kawai a ranta. Son zuciyar da tayi ne yake bata masa rai ace maimakon nadama sai kara botsarewa take yi. Ashe kaddara bata fi karfin kowa ba. Duk inda kaji aure ya lalace sau tari ma'auratan suma sunyi zama na soyayya da yarda da juna. Sai wani tsatsayi ya gifta kaddarar rayuwarsu ta bayyana komai ya lalace. Har zuciyarsa yake jin wani irin tsoron Allah Yana kara shigarsa. Babu wayo fa babu dabara, kowanne bawa zai taka yaje inda Allah Ya rubuta masa. Yanzu da shi Allah Ya jarabta da son wani abin duniya har ta kaishi ga shirka don neman biyan bukata shikenan ya bata. Kenan idan kaga bawa a yanayi na sabon Allah ba tozarci bane ya kamata ya shiga tsakaninku. Addu'ar neman shiriya gareshi da nemarwa kanka kariya daga tarkon shaidan ya kamata kayi. Lallai Allah Ya soshi da Maamu bata mutu tana fushi dashi ba. ya tabbata da tuni sunansa ya dade da shiga cikin littafin tababbu wadanda sukayi asarar lokacinsu a duniya.
Abinda ya jima baiyi da kansa ba yayi wato wanke bandakin sannan yayi wanka da alwala ya fito. A zaune ya tarar da Rumana ta takure jikinta wuri daya. Tana ganinsa ta sake matse jikinta yayi mata murmushi
"Son So kwaila"
Baki ta soma turowa "wallahi ni ba.....uhmmm... sai na fadawa Maamu" ta kare tana shura kafa.
Murmushinsa ya fadada "ni kuma zan fada mata yau wanka ma don shagwaba ni kika sa nayi miki"
Ai kuwa taji kunya don rufe kanta tayi da bargo ya rinka dariya. Ganinta kawai ya sassauta masa bacin ransa. Tana ta turjewa a haka ya shafa mata mai ya saka mata wata t-shirt dinsa mai girma tazo mata har kusan gwiwa.
Duk tabi ta tsargu da yadda yake kallonta ta koma ta zauna har ya gama shiryawa ya sake fita. Ba jimawa ya dawo da hijab dinta da zani yace tasa suyi sallah yasan an idar a masallaci. Bayan sun idar abincin da ya siyo ya bata suka ci sannan ya koma gaban kujerar dake kallon tv a dakin ya zaune a kasa yace tazo. Da rarrafe ta iso don bata so ya ganta a tsaye. Fuskarsa ce ta dan sauya babu wannan fara'ar sosai sai alamun tausayi ya kama mata hannuwa ya rike.
"Son So don Allah kiyi hakuri da abinda Gimbi tayi miki. Na rasa kalmar da zanyi amfani da ita na kawar miki bacin ran da kika ji dazu."
Ko ba'a fada mata ba tasan yaji babu dadi saboda duka yanayinsa ya canja. Ji tayi itama ya kamata ta faranta masa kamar yadda yayi mata. Sai ta mayar da abin wasa. Matsowa tayi gabansa a kunyace "idan ka sake cewa nayi hakuri kukan da na boye zai fito na kwana ina yi"
"To me kike so nayi miki kiji dadi ?"
"Ka goyani"
Gabanta yazo ya durkusa yaji shiru "hau mana"
Baya ta matsa "wasa fa nake yi"
"In durkusa din kice wasa kike yi, bazan yarda ba"
Gani tayi da gaske yake ta dauki zaninta tace masa zata je ta kwanta. Yace daga ranar duk girkinta a dakinsa zata kwana. Da gaske tsoro ne ya kamata ta kama kofar zata fita ya soma magana
"Yanzu har kin fara kin yin abinda nace? To jeki dakin sai da safe."
Kawar da kansa yayi yana murmushi saboda yadda yaga jikinta yayi sanyi tsoron nata ya koma na gudun bacin ransa. A sanyaye ta dawo ta tsaya daga gefe
"Kayi hakuri bazan kara ba"
Zaune dama yake akan gadon ya nuna mata cinyarsa "zo ki kwanta muyi magana"
Ba musu ta kwanta ta dora kanta a cinyarsa gabanta na faduwa.
"Umm Rumana!"
"Naam"
"Ina so ki saurareni ba a matsayin mijinki ba. Ki dauki maganata daga bakin Uncle Awaisu. Gidan nan ba bakonki bane sannan Gimbi a gabanta kika karasa girma. Kinga yadda lamura suka koma tsakanina da ita duk da irin son da muke yiwa juna. Rayuwar aure is more than mata da miji suna kwana a daki daya ko gado daya. Rayuwa ce ta taimakon juna da rufawa juna asiri komai wuya komai dadi. Ko da wasa ban taba tunanin abubuwan da suke faruwa yanzu zasu ziyarci rayuwarmu ba sai gashi mun wayi gari a wannan yanayin. Shawarata gareki don Allah kada ki taba bari son zuciya ya kaiki ga aikata dana sani. Kina da hankalin sanin mene ne aure saboda haka idan kinga abu ya faru ba yadda kike so ba ni mijinki ne kiyi min magana ta fuskar da ya dace mu fahimci juna. Kada ki kuskura tsoron wani abu da bashi da tabbas ya kaiki ga afkawa haram "
Maganganunsa sun tsaya mata a rai tunda ya fara take kuka. Nasiha sosai ya rinka yi mata saboda ya tsorata da yadda Gimbi ta rufe ido daga gaskiya lokaci guda. Yasan yanzu duk wani wa'azin da zaiyi mata bazata taba sauraronso ba ko don kishin Rumana. Shiyasa ya sami wannan limamin wanda yayi masa alkawarin yana dawowa daga tafiyar da'awa da ta kaishi Lokoja zai fada masa yazo da Gimbin gidansa.
Kukan da Rumana take yi ne yasa ya fara shafa mata kanta wanda yake a jike har lokacin. A hankali rarrashin da yake mata ya juye zuwa soyayya mai wuyar fassara inda