Showing 60001 words to 63000 words out of 112099 words

Chapter 21 - KASHE FITILA Book Complete by Batul Mamman.txt

23 Jun 2024

15960

da 'ya'yana ta yaya kake so na barsu a gidan nan?"


Ganin suna kallonsu da fargaba a idanunsu yasa Awaisu cewa "Haris ku tafi tafi ciki kunji. Mummy is very sick. Irin zazzabin da Mu'allim ya taba yi yana ta surutu ne ya kamata. Yanzu zamu je asibiti daga nan a mayar da ita Abuja. Mu kuma ranar sunday sai mu tafi tare ko "


Da tausayin mahaifiyar tasu Haris da kannensa suka koma har suna yi mata sannu.


Bude baki tayi zata fara masifa Awaisu yayi mata wani irin kallo duk rashin kunyarta sai ga bakin hangame a iska ta kasa furta koda kalma daya. Matsowa yayi kusa da ita harda daukan akwatin saboda yaransa da basuyi nisa ba sannan ya rage murya yadda zata ji


"Kada kiyi yunkurin daga murya a gidan nan wallahi zan baki mamaki. Ki duba ciki da waje baki da mai kwatarki idan kika shigo hannuna domin kin gama bata rawarki da tsalle a idanunsu"


Bata iya sake tanka masa ba ta bi bayansa har mota. Dreban ya kira gefe ya ja masa kunne sosai akan cewa kada ya kuskura ya tsaya ko ina sai Abuja. Sannan ya kara da cewa idan sun isa ya karbi mukullin motar Gimbi yace zai sha mata mai. Idan ta bayar ya hada da na motar da suka zo ya tafi kada ya dawo gidan sai ya neme shi da kansa. Dreba mamaki ya ishe shi amma baice komai ba. Dama ba dadewa yayi a gidan ba bai san meye tsakanin ma'auratan ba.


Baya Awaisu ya zauna kusa da Gimbi ya zaro kudi ya damka mata.
"Ga wannan ki rike ko bukata zata taso miki kafin na dawo. Sannan naji labarin za'a fara wahalar mai nace Gambo ya tafi da motarki ya sha miki mai idan kun isa. Sannan bana so kina tada hankalinki don kinsan bana jindadin ganinki a haka. Ki tafi kafin nasan yadda nayi na kawar da matsalolin dake son rabamu"


Bacin ranta taji ya fara sauka kadan saboda a tunaninta ko akwai sauran asirin da yake aiki a kansa. Ba dai tace komai ba don burinta kawai ya fita daga motar ta kira Ovi. Sallama yayi mata harda sakin fuska ya koma cikin gidan.


Yana fita ta kira Ovi ta juya harshe da turanci tana kuka tana fada mata me ya faru. Ovi dama a speaker tasa wayar ita da Rita sukayi dariya mai isarsu sannan tace zata jirata idan ta dawo su koma wurin Boka. Har tuna mata takeyi tasan dai aikinsa babu wasa kaifi daya ne. Gimbi taci kukanta dai kafin su isa. Kamar yadda aka umarci dreba ya karbe mukullin motarta da na wadda suka zo yayi tafiyarsa.
*****


Da Awaisu ya koma ciki sun cigaba da tattaunawa inda 'yan uwansa mata suka nuna tsoron kada Gimbi ta koma wurin da take karbo kayan asirinta. Nan ya fada musu umarnin da ya bawa Gambo dreba da kuma kashedin da yayiwa maigadin gidansa a waya kan cewa kada ya bar kowa ya shiga ko fita daga gidansa har sai ya dawo.


Baaba tace duk da haka sai ya tashi tsaye sosai da ibada saboda ta nan bangaren yayi raunin da aka sami galaba akansa duk da tasan cewa asiri gaskiya ne. Bayan nan suka ce ya kamata aje har gidansu Gimbi a fadawa iyayenta abubuwan da suka faru.


Awaisu yace dama yayi niyar idan ya koma yaje


"Ba'ayi haka ba. Wannan ba maganar mutum daya bace. Idan ka tashi tafiya sai mu tafi tare har da Harisu ko wani cikin kawunnai domin su dauki zancen da mahimmanci" inji Anti Baraka.


Maamu da Baaba ne sukayi ta saka musu albarka sannan suka tashi domin yin sallar laasar. Kafin su fita Mama uwargidan Harisu tana dariya tace "akwai fa amaryar da bata san an aurar da ita ba."..


Tsokanar Awaisu suka fara har suna cewa ya tsaya su gaisa da surikinsa suna dariya. ita dai maman Rumana ficewa tayi. Ko ita bazata iya kishi da Gimbi ba bare Rumana. Auren nan don dai kawai anfi karfinta ne. Amma tana jin tsoron yadda zaa zauna gashi bai saki Gimbin ba kamar yadda yace zamansu tare ya rama abubuwan da tayi masa shine kawai zaisa ya huce.


Kowa ya fita daga dakin ya rage Awaisu da Harisu. Wani nauyin yayan nasa yake yi. Harisu ya kula dashi ya dawo kujerar kusa da tasa


"Menene yake faruwa Awaisu?"


Iska ya dan furzar "Yaya don Allah hankakinka ya kwanta da auren nan? Wallahi bana son abin da zai zo ya taba zumuncinmu ko kadan"


Zulumi da fargaba ya gani a cikin idanun kanin nasa. Da farko shima auren nan bai wani kwanta masa ba amma yanzu yaji dadin wannan hadin.


"Awaisu abu daya kawai nake so ka fada min shine dalilinka na saurin amincewa da auren"


Abin mamaki ga Harisu gani yayi kanin nasa ya dan dukar da kai kafin ya bashi amsa "Abin da ban taba tunani bane ko a mafarki Yaya shine jin soy....uhmmm...soyy"


Shiru yayi ya dafe goshi ya dago kamar zaiyi kuka
"kunyarka nake ji"


Harisu ya kwashe da dariya irin wadda Awaisu ya dade bai ga yayi ba
" kaima yadda akace shiru ko kunya a wurin budurwa amincewa ne to kaima kunyarka ta cire min duk wata damuwar da tayi min saura. Nasan Awaisu a matsayin kani kuma dan uwa nagari. Fatana ka zamewa Rumana abokin rayuwa nagari. Na sani ko babu ni iyalina bazasy taba tagayyara ba idan kana raye. To menene abin fargaba idan kana auren 'yata."


Shi dai Awaisu godiya yayiwa yayan nasa sosai suka tafi masallaci.
*****


Wurin biyar da rabi na yamma Rumana ta dawo daga gidan kitso. Ana mata fadan dadewa tace kawayenta na primary ta hadu dasu a gidan suka tsaya hira. Sai da taci abinci aka kirata dakin Maamu. Bata kawo komai ba ta tafi. Da shigarta ta fada jikin Maamun tana murnar ganin kara samun lafiyarta. Baaba tace to ta tashi dai kada ta karyata.


Baaba tace "Rumana kin tuna duk wahalhalun da kuka sha da Maamu a Abuja ko"


Tace eh yaushe zata manta.


"A dalilin haka kawunki ya kara aure yau dinnan kuma muna fatan wannan karon in sha Allah an dace da matar kwarai" Baaba tana magana tana kallon yanayin fuskar Rumana.


Murmushi tayi mai nuni da farinciki "dama jiya ya fada min zai kara aure ashe abin ya matso haka. Yeeyyy zamu sha biki...." tashi tayi zata fita tayiwa 'yan uwanta shela Baaba tace ta dawo ta zauna.


A dofane take don sauri take ta samu ta fita ta kai musu labari. Dole suyi shagali wallahi ko don ta konawa Gimbi rai saboda bata san Gimbin ta tafi ba.


"Nasan bazaki so Maamu ta sake zama irin na da ba a gidansa ita kadai da Gimbi.."


Rumana ta firfito da idanu tana kallon Baaba kafin ta dafe kirji a dan tsorace "Ba dai Abujan kuke so na kara zuwa ba. Ni wallahi bazan koma ba"


"Wane irin zance ne haka ina magana kina cewa bazaki koma ba?" Baaba ta fada cikin fada. Kafin ta kara cewa komai Rumana ta tashi tana bubbuga kafa ta fita daga dakin. Ko dukanta Baba zaiyi bazata yarda ta koma Abuja ba. Wa yasani ma ko matar tafi Gimbi iya mugunta.


Maamu ta kalli Baaba tace "gashi nan kince na bari ki fada mata har ta fita baki fada ba sai kara hargitsa mana ita da kika yi"


Rike baki Baaba tayi "to ni dai babu ruwana kuma iyayenta su karata. Wannan yarinya da gani zaayi daru da ita"


*****
Tun da ta shiga daki take ta kumburi taki fita falo. Bayan isha kanwarta Hafiza ta sanar da ita babansu yana kiranta a dakinsa. Tashi tayi da kudurin ko me zaice zata dage bata koma Abuja ba.


Mamanta ta gani a gefensa fuskarta babu wata walwala. Zama tayi ta gaishe shi.


"Rumanan Baba kuna magana ashe dazu dasu Baaba baki gama ji ba kika tashi"


Kuka ta soma yi masa. Dama plan din da tayi kenan tayi ta kuka tana rokonsa ya barta a nan.


"Baba bana son sake zuwa Abujan ne"


"Naji Rumana amma ai baki tsaya sunyi miki cikakken bayani ba. Dazu auren dake aka hada"


Zama tayi dabas daga dan durkusun da tayi "Baba ni me nayi kuma zaka min aure? Shi wannan dan Baban bayan gidan Allah bana sonsa. Kuma ko makaranta ni ban gama ba"


Kuka ne ya kwace mata ta tashi ta fita muryarta har ta soma karade gidan ta shige dakinsu ta kuka.


Harisu ya kalli mamanta "ko sunan mijin ban fada ba kinga ta tashi"


Da alamun rashin damuwa don ita fa auren nan baiyi mata ba ta tabe baki "ni meye nawa a ciki?"


Kusa da ita ya koma ya rungumota "kinsan ina alfahari dake saboda saukin kai "


"Shiyasa zaka cutar min da 'ya" ta amsa mai da hawaye


"Kiyi hakuri. Nasan ko ba Gimbi yake aure ba dole abin nan yazo mana wani iri. Amma ki kyautata zato ga Allah in sha Allah auren nan alkhairi ne"


Wayarsa ya dauka ya kira Awaisu ya fada masa yadda sukayi
"Ka tura a kira maka ita kayi mata bayani da kanka"


Awaisu ya kalli su Baaba da suka gama fada masa ya suka kare da Rumana dazu. Allah gani gareKa yace sannan ya fita ya ce a fada mata ta same shi a falon Harisu.


Kukanta ne ya fara sanar masa da isowarta ta shiga ko sallama babu.


Wuri ya nuna mata a kujerar kusa da wadda ya zauna. Ta zauna idanunta a kumbure ta sake fashe masa da wani kukan


"Uncle aure akayi min" ta fada murya na rawa.


Tausayi yaji ta bashi "kiyi hakuri, kinsan komai nisan lokaci dama wata rana zakiyi aure"


Bakinta ta turo tana wani hawayen "to kuma ni sai ayi min auren dole ko karatu ban gama ba. Kuma ko sonsa banayi"


Awaisu yayi murmushi "indai karatu ne zan barki kiyi ta yi har sai kin gaji don kanki"


Dagowa tayi suka hada ido yaji wani sonta ya kara shigarsa. Ita kuwa murmushi ta danyi "Allah da gaske zaka yiwa ko waye mijin magana ya barni nayi karatu? Daga nan ma ka roke shi ya sakeni kawai." Ta dan cije lebe cikin takaici "nasan ba kowa bane mai nacin nan sai wannan dan abokin Baba da na fada maka"


Dariya Awaisu yaso yi jin tace mai naci.
"Bana fatan ki fito daga gidan mijinki indai ba da sunan zuwa unguwa ba. Ko kin yarda zaki bini Abujan?"


Duka biyun babu wanda yayi mata. Amma idan ta tuna yadda ta tsani yaron nan mai naci sai taji gara Abujan
"To amma don Allah uncle idan anje Abujan ka damka ni a wurin Anti Amarya"


"Umm Ruman kenan, wato Anti Amarya ko don iya dadin baki" yayi dariya yana kallon yadda ta hade fuska ita da gaske take.


Goge hawayenta tayi ta tashi "to yaya sunanta?"


"Umm Ruman Harisu Sa'ad"


Idanunsa ya kafeta dasu yana kallonta babu alamun wasa. Jikinta tuni ya fara wani irin rawa "Ni Rumanan?"


Sai da ya tashi tsaye ya rungume hannuwansa a kirjinsa sannan ya gyada kai "ke Rumanan"


Wai me yake fada ne. Kanta ta nuna da hannu tana masa kallon rashin fahimta "Uncle ni ka aura? Innalillahi"


Kafin ya ankara tayi hanyar fita daga falon. Da saurinsa ya isa bakin kofar ya rufeta da kafarsa tare da riko Rumanan. Kuka ta fashe masa dashi tana kokarin kwacewa. Rungumeta yayi yadda bazata iya kwacewa ba tana kuka tana maganganun da baya fahimta sosai "Uncle bazan iya ba. Ka rufa min asiri. Wayyo Allahna. Kalli ka gani fa nice 'yar karama dani..."


Hannu yasa akan bakinta yace "shhhh Umm Ruman everything will be okay I promise."


Tun tana kokawa dashi na son kwacewa daga jikinsa har ta gaji ta dena. Ji yayi ta dena kokarin kwacewa sai ajiyar zuciya da take yi lokaci-lokaci.
[15/08, 17:46] ‪+234 803 272 5896‬: *KASHE FITILA* 💡38


*Batul Mamman*💖






Tausayi Rumana ta bashi sosai sai dai kuma baya jin zai iya rabuwa da ita a yadda yake jin soyayyarta a ransa. Cikin 'yan kwanakin nan komai nata burge shi yake yi.


Hannunta ya kama suka koma wurin kujera amma da kyar ya samu ta zauna kanta a kasa taki dagowa.


"Dago ki kalleni" yace yana leken fuskarta.


Maimakon ta dago sai ta cusa kanta a tsakanin cinyoyinta gabanta yana tsananta bugu. Abu ne kamar a mafarki wai Uncle Awaisu ya zama mijinta.


Kyaleta yayi don baya son takura mata.


"Ki dena kukan nan kada ki fita ido a kumbure. Just calm down idan kin sami natsuwa ki shiga ciki"


Zumbur ta mike suka hada ido tayi saurin kawar da fuskarta. Idanunta banda kumburi sunyi ja sosai. Kafin ya sake mata magana ta fice da gudunta don ma kada ya sake tsareta. Komawa yayi ya zauna yasa hannu yana matsa gefen kansa da yake masa ciwo. Abubuwan da suka faru dashi a tsukin kwanakin nan sun daure mishi kai haka kuma dasu yake kwana yake tashi.


Rumana na fita dakin Maamu ta tafi suna tare da Baaba. Tana shiga ta fada jikin Baaban ta fashe da wani irin kuka. Bayanta Baaba tayi ta shafawa tana rarrashinta. Maamu itama rarrashin take yi. Ta dauki lokaci a haka kafin ta dago kanta


"Baaba don Allah kuce ya sakeni. Ta yaya zan auri Uncle don Allah" wani hawayen ke bin kumatunta ta rinka bin kakaninta da ido.


"Kul Rumana kada na sake jin zancen saki a bakinki" cewar Baaba


"Ni wallahi bana son aure yanzu. Yanzu sai ayi ta cewa na auri kanin Babana. Kuma ma ko sonsa banayi"


"A'uzubillahi" Baaba ta fada tana doke bakin Rumana. Bare baki ta sake yi Maamu ta janyota jikinta.


Maamu tace "Rumana ba kya sonsa? To babu maiyi miki dole "


Dan kunya taji "ina sonsa mana Maamu amma ba son so ba"


Dariya suka so yi su biyun sannan Maamu tace "to wanne kike masa.? Bansan meye son so ba"


"Ina nufin ina son shi amma ba na soyayya ba" ta kare a hankali muryar ma bata fita sosai saboda yadda taji kunyar abin da take fada.


Baaba ta rike haba, gaskiya akwai rigima don tayi zaton Rumana tafi haka wayo sai gashi ta gane har yanzu tana da sauran wauta. Wai son so, saura son ki.


Rarrashinta suka rinka yi da ban baki don ranar a dakin ta kwana.


Washegari ko alamun Awaisu bata gani ba ashe ya tafi gaishe da dangin Maman Rumana tunda basu san da auren ba shi kuma lahadi yake son komawa. Da kanin Malam Saad babansu Harisu da kuma kanin Maamu suka je sanar da kakan Rumana na wurin uwa domin fita hakkinsu tunda abin yazo babu shiri basu sani ba. 'Yan uwanta sunyi mamaki sosai amma sunsa albarka tunda an riga an daura sai fatan zaman lafiya.
*****


Gimbi ta gama shirinta da sassafe ko ruwa bata iya sha ba ta fito tana neman keys din mota sai dai babu ko daya. Tunawa tayi ta bawa Gambo dreba ta fita ta tambayi maigadi ko ya bashi da ya dawo da motar don ta ganta a cikin gidan.


Maigadi yace ai bai ma fita da ita ba tun a jiyan. Abin ya bata haushi ta kira wayarsa yafi a kirga amma yaki dauka. Matarsa har cewa tayi ya dauka mana matar oga ce yace umarnin ogan yake ba.


Iyakar kulewa Gimbi tayi gashi tun a hanya take kiran Ovi da Rita bata samu. Data dawo gidan bata ga Rita ba duk ta damu. Shiyasa duk irin gajiyar da ta kwaso ko runtsawa bata sami yi ba saboda tunani.


Tsaki taja ta nufi gate tana ta masifa. Isarta ke da wuya tace maigadin ya fita ya nema mata taxi ya dan sunkuyar da kai


"Oga yace kada a bari ki fita har sai ya dawo"


Kallon rainin hankali tayi masa sannan ta daka masa tsawa
"Zaka bude min ko sai nasa an koreka a yau dinnan?"


Matsawa yayi ya bata wuri taje taji kofar garkame da kwado. A fusace ta koma ciki tana ta kai kawo. Da ta gaji ta sake dawowa ya kuma tabbatar mata bazai bude ba. Suna haka tana ta sauke masa kwandon zagi suka ji bugu. Tambayar ko waye yayi Rita ta amsa.


Gimbi har ta soma jindadi zai bude ta samu ta fita sai ta ga ya koma kan kujerarsa ya zauna.


"Kai malam baka ji ana buga kofa ne?"


"Oga cewa yayi babu shiga babu fita" ya amsa mata.


Kallon mamaki tayi masa "ina jin baka ganeta ba. Rita ce mai aikina"


"Hajiya kiyi hakuri ko ki kira shi a waya. Ni dai abin da ya fada min kenan"


Jikinta har tsuma yake yi don bacin rai ta kira Awaisu. Lokacin tasowarsu kenan daga wurin kakan Rumana zasu tafi wurin da ya ajiye mota. Sai da ya bari ta kira sau biyar a jere sannan a na shidan ya dauka.


"Ina jinki" ya fada muryarsa na nuni da baya maraba da wayar.


"Abin da zaka ce min kenan bayan jiya ka yaudareni kasa na bada mukullin mota ko. Wallahi baka isa kaci mutumcina ba kaima ka sani"


"Meye dalilin kiran naki yanzu I am busy?"


"Sannu agogo sarkin aiki. Ba wani abu bane kasa maigadinka ya bude min kofa na fita "


"Babu mai fita ko shigar min gida sai na dawo"


Bacin ranta ne ya karu "to kace ya budewa Rita ta shigo"


Dadi yaji ashe matar da baisan daga ina ta samota ba bata gidan. Murmushi yayi kafin yace "wani abu ne haka Rita din?"


Wulakanci! Lallai Awaisu bai santa ba har yau. Danne bacin ranta tayi domin burinta ta fita da kanta taje wurin Boka. Daga shi har dangin nasa sai ta mayar dasu waina don juyasu zata rinka yi.


"Awaisu kaga na shanye duk wani abin da 'yan uwanka suka yi min. Ka barni naje gidan iyayena mana..."


Shiru taji na dan lokaci bai amsa ba sai kuma taji yayi yar siririyar dariyar da take matukar so a wurinshi. Kashe murya taji yayi yana magana kasa-kasa "ashe haka kike da rigima my little princess, don kina son tausa sai kin haye min cinya"


Hannun da Gimbi ta rike wayar dashi ne taji ya fara karkarwa kafin duka jikinta ya dauka. Wayar da kanta ta subuce ta fadi a kasa ta tarwatse. Kunnenta ta kaiwa duka tana son tabbatar da abin da Awaisu yace....runtse idanu tayi tana hango Rumana akan cinyar Awaisu. Wani irin ihu ta saka na tsananin bacin rai "Awaisuuuu, karyarka ka hadani da wannan afiruwar. Rumana tayi min kadan sai dai nayi da uwarta. Dani kuke zancen duka, sai na baku mamaki."


Da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login