Showing 24001 words to 27000 words out of 112099 words

Chapter 9 - KASHE FITILA Book Complete by Batul Mamman.txt

23 Jun 2024

14004

kadai a zuci. Wato don rainin wayo irin na Gimbi so tayi ta rinka morarta a bayan fage batare da ansan tana kula ta ba. In dai Anti Bebi ce bata isa ba. A ganinta duk abin da take yi neman 'yanci ne. Saboda haka idan zaka sha giya gara kasha ta dubu.


Alh Mudi ba a son ransa ya gaisa da Alh Maitama ba. Shi fa komai da ya danganci Anti Bebi to baya baya dai. Lokacin da take auren wani dan unguwarsu tamkar zautacce ya koma. Duk inda ya zauna sunanta yake kira kuma ko a baya idonta baya taba saba umarninta.


Mama ta daure ta cigaba da hira da mutanen dakin tana tambayarsu yaya maijiki. Lokaci lokaci take kallon Gimbi wadda har yanzu bata farfado daga mutuwar tsayen da tayi ba.


Harisu da Alh Mudi da sauran mazan suka fita suna hira. Sai dai Alhaji hankalinsa baya wurin sosai. Karshe ma dai yace musu zasu tafi saboda yamma tayi sai gobe zasu dawo. Wayar Mama ya kira ita kuma a lokacin tana ganin Laminde ta hada kwanukan abinci zata kai mota tayi saurin bin bayanta.


"Laminde dan tsaya don Allah"


Laminde ta tsaya har Mama ta karaso ta sake gaisheta tana dan murmushi.


Fuskar Mama ta kalla mai nuni da damuwa. Mama tace "matar nan da ta shigo da mijinta kin taba ganinta a gidanku?"


"Anti Bebi ko? Inace kanwarki ce inji Hajiya"


Mama ta rike baki, lallai akwai abin da Gimbi take yi wanda basu sani ba.
"Tun yaushe kika fara ganinta a gidan?"


Dan tunani tayi sannan tace "gabanin zuwa Maamu ne"


Kuka ne kawai Mama batayi ba don takaici. A take zuciyarta take raya mata Gimbi ta fara bin sahun Anti Bebi. Hannun Laminde ta rike kana ganinta kasan cikin damuwa take sosai "ki taimakeni Laminde duk ranar da ta sake zuwa ki sanar dani. Kuma ni na baki dama kisa ido sosai akan uwar dakinki. Idan kinga wani abu da kike ganin tayi bai dace ba kada ki boyemin"


"To Mama in sha Allahu."


Mama godiya tayi mata sannan ta wuce. Laminde har tausayinta taji. Iyayen Gimbi mutanen kirki amma ta rasa inda ta koyo wannan halin na cutar da uwar mijinta.
*****


A cikin dakin Anti Bebi ta sake tana ta yiwa bakin Gimbi hira tamkar sun dade tare. Alh Maitama yana tsaye shi kadai namiji cikin mata. Murmushi tayi don tasan izininta yake nema tace ya fita gasu nan zuwa. Kamar an tsikare shi ya fice. Shuhada ta sunkuyar da kai don kunya sai ga hawaye. Wannan tozarci har ina. Dole ma ta bar gidan kafin bakinciki ya kasheta. Da tunanin Tajuddeen zata ji wanda yayi mata sakin wulakanci duk kuwa da son da suke yiwa juna ko yadda mahaifinta ya koma.


Baaba Hure ce ta kula da hawayen da Shuhada take gogewa tace " 'yan mata me ya sameki?"


Anti Bebi tayi caraf ta tashi harda rungumota a jikinta.
"Sharrin namiji, cikin dare mijinta ya dawo haka kawai ya dankara mata saki uku ba laifin zaune babu na tsaye. Ko sati uku ba'ayi ba. Idda ma take yi. Shuhadana ki rinka hakuri. Shiyasa fa nace ki fito kisha iska kada tunanin namiji ya sa miki hawan jini"


Tamkar Shuhada ta shige kasa don kunya. Yanzu me ya kawo fadawa mutanen da bata taba gani ba sirrinta. Tunawa tayi babu wanda yasan lokaci da yadda sakin ya faru sai Suhail shiyasa ta kalli Anti Bebi a razane. Wannan shegen murmushin ta sakar mata mai nuni da tasan komai. Tsanarta ta sake samun wurin zama a zuciyarta.


Gimbi ta kasa zaune ta kasa tsaye tun bayan fitar Mama. Ita a tunaninta ma ko kiranta zatayi a waya aci mata mutumci. Shirun da taji yasa hankalinta ya dan kwanta. Fita tayi daga dakin zata leka ko sun tafi Anti Bebi tayi sallama dasu Maamu tabi bayanta. Dan nesa da motar Alh Maitama suka tsaya Gimbi ta juyo a tsiwace


"Anti Bebi ya zaki min haka? Meye na zuwa asibitin gashi yanzu Allah kadai Yasan me su Baba zasuyi min"


Gira ta daga tana yatsina fuska "sannu uwar munafukai, da cewa akayi dake ni bani da hankali. Kin iya kawo mijinki na kaishi a baki akalarsa a tafin hannunki amma bazaki nunawa duniya matsayina na kawar babarki ba. Haba Gimbiya, dube ni da kyau nafi karfin wani shege yabi ta kaina ya gina kansa sannan yasa kafa ya tureni."


Gimbi ta fusata "nice shegiyar?"


"Yo nufinki nice? Kada ki kuskura kice zaki min rashin kunya Gimbiya, sai nasa ki raina kanki. Bar ganin na hadaki da Wangesi ba dashi kadai na dogara ba. Awaisun da kike takama dashi sai nasa a mayar min dashi tamkar wancan Alhajin. Idan naso albashinsa ma ni zai rinka bawa ajiya"


Gimbi taji cikinta na karar tsoro amma tace "mu zuba mu gani, sai na tona miki asiri"


"Bani da sirrin boyewa, ke dai matsoraciyar banza ki jira hukuncin iyayenki a kanki. Kuma kisa a ranki tamkar na rama wannan rashin mutumcin naki na gama. Bebi ce fa, Bebin maza mata su ganni su watse"


Duk da Gimbi tana tsoron Anti Bebi dakewa kawai take taja tsaki ta juya. Ido hudu sukayi da Shuhada wadda ta gama jin duk abubuwan da suka fada. Gimbi kara tsorata tayi sai dai Anti Bebi ko a jikinta. A wulakance ta kalli Shuhada ta nunata da yatsa
"Wannan fitsararriyar ma da taso nuna min ita wata ce kinga aurenta watansa shadaya na kaso mata shi. Kuma bata isa ta kara wani batare da amincewata ba. Saboda haka kema wannan kan naki da yake rawa ki daidaita shi. Idan ba haka ba uwarki Amina ma sai ta dana zawarci"


Ran Gimbi ya kara baci tace "ba dai uwata ba sai dai...."


Maganar bata karasa fitowa ba saboda marin da Anti Bebi ta kwasheta dashi. Dafe kumatun tayi tana zubar hawaye. Tana tsoron daga murya su Awaisu su ji me yake faruwa. Sannan ga tsoron Anti Bebi ya sake tasiri a ranta.


Shuhada bata ce musu komai ba tayi gaba tana mamakin hali irin nasu. Su biyun duka abin tsoro ne gareta. Tana karasawa bakin motarsu nan ta samu su Harisu a jiki suka jingina suna hira. Su Mama kuma lokacin motarsu ta fita.


Awaisu yana gani ta tsaye jikin wata motar yayi mata alama da hannu ta karaso. Bude bayan motar yayi yana mata murmushi


"Kanwata shiga ki zauna kada ki gaji da tsayuwa"


Daga inda take Gimbi ta hangosu taji kamar an soka mata kibiya. Anti Bebi kuwa murmushin mugunta ta bita dashi. Anya bazatayi maganin Gimbi da Shuhada ba ta hanyar sanya Awaisu son Shuhada kuma ta matsawa Alhaji ya yarda da auren. Da wannan tunanin ta shige gaban mota suka tafi saboda idon mutane.
******


Alh Mudi da Mama har suka isa gida babu mai cewa komai. Tana shiga daki ya bi bayanta da hula a hannu.


"Me Bebi take yi a asibitin nan Amina?"


Dama jiransa take yi don tasan sai yayi magana "nima nayi mamaki, yadda ka ganta haka na ganta"


Daga murya yayi yana mata tsawa " 'Yar uwarki ce kiyi mata magana ta nesanta kanta da iyali na."


Wani kallo Mama ta bishi dashi saboda haushin maganarsa da taji.
"Abin da zaka fada min kenan Alhaji? Da bakina fa na fada maka irin abubuwan da Bebi take yi tun kafin ya fito fili duniya ta sani. kuma na nemi shawararka akan yanke hulda da ita saboda kare mutunci da addini."


Kuka ta soma yi sai jikinsa yayi sanyi. Ya manta rabonsu da fadan da zai janyo ya daga mata murya. Amma yau saboda Gimbi da ta janyo Anti Bebi gashi iyayenta sun sami sabani.


Sassauta murya yayi "Kiyi hakuri Amina, kamar yadda kika sani Gimbi tun tana karama bata son komai nata 'yan uwanta su taba. Saboda wannan halin kin sha dukanta ina hanawa. Tsoro nakeji kada dalilin zuwan surukarta ta canja hali"


"Nima abin da ya dameni kenan, zanyi bincike akai amma dole ka kirata ko bayan bakinsu sun koma ne ka nuna mata bacin ranka" daga haka ta tashi zata shige ciki ko kallonsa bata yi.


Alh Mudi yayi murmushi "Haba Aminatu ban sanki da fushi ba, kiyi hakuri tsawar da nayi miki"


Yadda ya langabe kai sai ya tuna mata da lokutan da sanda suke da kuruciya. Dariya tayi a ranta tace Bebi ba kyau. Yanzun nan sai ta kashe aure da kisisinarta.


******
Bayan kwana biyu su Harisu suna tunanin tafiya washegari cikin dare jinin Maamu ya hau sosai likitoci suka taru a kanta. Haka suka hakura da tafiya sai sun ga an sallameta. Tsabar fargabar tafiyar mutanen Fika ne ya dameta. Duk halin Tikeke da Hinde har da Bomoi baisa taji haushinsu ba. Ganin idanunsu ya kawo sauki a zamantakewarsu da Gimbi da Awaisu. Yanzu tattalinta yake sosai yadda yake yi a baya. Ita kuma Gimbi rashin sanin me Anti Bebi ta tanadar mata yasa ta kasa sukuni. Duk irin luguden da akeyi mata a gida hankalinta baya kai. Wulakancin da ta soma na saka turaren wuta ko ta fesa na ruwa idan sun tashi daga wuri duk ta dena. Tunaninta kaf ya koma wurin neman wani bokan wanda yafi Wangesi. Idan ba haka ba kuwa tana ji tana gani Anti Bebi zata kashe mata aure ta tagayyara mata rayuwa.


So take yi ta fita ma amma kullum a asibiti suke yini. Cikin dare ta kasa bacci sai juyi take yi tana neman mafita. Wata shawara ce ta tsaya mata da sassafe kuwa ta aiwatar.


Dreban Anti Bebi ta kira Balele ta kwantar da kai sosai tace tana son yazo batare da saninta ba. Alqawarin dubu dari tayi masa yace gashi nan zuwa. Duk wahalar da yake da Anti Bebi bakar rowa ce da ita. Daga dubu ashirin sai talatin ke rabasu.


Da yake dan hutun da aka bata na jinya ya kare tunda ga su Ummukulsum ta koma aiki yau. Office yaje ya sameta. Babu wata rufa rufa ta fada masa abin da take nema.


"Idan kin shirya ko yau sai na kaiki wani kauye can jihar Neja. Mutumin bala'i ne me zaman kansa. Amma sai kin saki kudi "


Gimbi tayi murmushi "indai kudi ne kada ka damu. Ko yanzu zamu iya zuwa domin a matse nake."


Mukullin motarta ta bashi dama drebansu yanzu daga kai yara makaranta sai asibiti. Wayar ogansu ta kira ta fada masa jikin surukarta ya tashi tana ICU. Sunyi tafiyar awa uku sannan suka isa wani kauye. Gidan duk yara da mata. Dakin Malamin tsibbun Balele ya kaita inda ta fadi bukatunta akan mijinta da babarsa da kuma Anti Bebi. A take yace ta bashi dubu dari uku. Babu musu ta kirga ta bayar. Ya hado mata wani ruwa a jarka yace ta yayyafa duka gidan tana kiran Maamu da Awaisu a duk zubawa. Anti Bebi kuma daren yau zai karya duk wani tsafi da ta taba yi.


Gimbi taji dadi sosai ta karba tana ta godiya ta fita. Balele ya koma dakin ya kalli yayansa
"Kirgo min nawa nayi sauri mu tafi"


Wan nasa yayi murmushi ya dauko dubu dari da hamsin ya bashi suka tafa suna dariya ya fice.


A hanya ta sauke shi ta wuce gida. Ko mayafi bata cire ba ta fara aikin yayyafa ruwan dattin da suka bata.


Laminde tana kitchen ta dawo saboda su Amir zasu dawo daga makaranta taji motsi. Lekawar da zata yi ta hango Gimbi tana zuba ruwan tana cewa
"Safara'u! Awaisu!"


Hantar cikin Laminde ta kada sosai don tsoro. Komawa tayi ta rufe kitchen din yayin da Gimbi ta shiga daki ta ajiye sauran ruwan ta fice daga gidan.


Laminde ta fito ta yafa mayafinta jiki na bari. Ayatul Kursiyyu ta karanta tana ta tofawa a gidan. 'Yar purse dinta ta dauko domin daga nan gidan Mama ta nufa. Kofar gidan taji an taba Gimbi ta sake shigowa. Sako ta barwa maigadi ya fadawa Laminde yace ai tana ciki. Itama a tsorace ta dawo.


Suna hada ido duk suka rude. Gimbi ta dake tace "kinji shigowata?"


Bakin Laminde ya soma rawa. Hakan ya tabbatarwa Gimbi ta ga abin da tayi.
"fada min nawa zan biyaki ki bar maganar nan a gidan nan"


"Shawara kawai zan baki ki dena bin malamai akan Maamu. Duk duniya babu halittar da Allah Yake ambaton bautarSa tare da yi musu da'a bayan ManzonSa kamar iyaye. Me Maamu tayi miki haka kika canja har kike musu asiri"


Gimbi ta kirkiro murmushin dole "kai Laminde ashe baki fahimceni ba maganin tsari ne na yayyafa saboda kariya "


Laminde ta kalleta ta watsar saboda duk ta sire mata girma ya fadi, hanyar waje tayi Gimbi tana binta da sauri hankalinta a tashe.


"Ki tsaya muyi magana ta fahimta. Zan biyaki sosai yadda ko kin dena aiki zaki sami jari"


Sauri Laminde ta kara tana bude gate Gimbi a gigice don bata san ina zata ba ta cewa mai gadi ya kamota. Jin umarnin da aka bashi akanta yasa ta kwasa a guje sai dai bata duba titin nasu ba mota ta taho da gudu tayi gaba da ita sai jini ne ya wanke wurin.
*KASHE FITILA*💡20


*Batul Mamman*💖






Wata muguwar kara Gimbi ta saki tare da dora hannu a ka ganin yadda jini yake bin jikin Laminde. Duk abinta tana tsoron yin kisa. Mai motar ya tsaya ya fito a guje shima yana fatan Allah Yasa baiyi kisan kai ba. Motoci ne suke tsayawa ganin yadda jama'a suka fara taruwa a wurin saboda gidan nasu a bakin titi yake.


Ana kokarin sanya Laminde a motar mutumin da ya bugeta sai ga 'yan sanda biyu daga wurin junction din da ake bayar da hannu. Tambayoyi suka danyi na sanin wacece sannan sukace a wuce asibiti. Sai da suka isa National Hospital sannan Gimbi hankali ya fara tashi da irin tambayar da suke mata. Daya cikin 'yan sandan yace a cikin 'yan kallo wani yace biyota akayi ko me zata ce game da hakan.


Nan fa ta kara rikicewa tana nemarwa kanta mafita kada asirinta ya tonu. Karya ta sharo a take a wurin irin wadda ko Laminde tayi rai baza'a yarda da abin da zata ce ba tunda mai aikice.


"Ai na fada muku mai aikina ce. Sata na kamata zatayi min shine ta gudu"


Dan sandan yace "kina da shaida akan hakan?"


"Tambayi mai gadi shi nace ya tsayar min da ita"


"Zamu jira likitan ya fito domin ji daga bakinta"
*****


Zaune Awaisu yake yana sa hannu a wasu takardu Ummukulsum ta kira shi. Gabansa har dan faduwa yayi kafin ya daga yana tsoron ko jikin Maamu ne. Muryar Baaba yaji da alamun bacin rai


"Anya Awaisu kai da matarka kuna kyautawa kuwa? Ace mara lafiya tun abincin safe har yanzu shiru "


Ajiye biron hannunsa yayi ya mike tsaye "Baaba ina Laminde?"


"Kaniyarka, Laminde kake aure? To tun dazu ta tafi don sauri ko dreba bata jira ba baiwar Allah tace zata jira yara su dawo ta bayar da abincin. Kuma su Tikeke ma gida zasu koma idan an kawo saboda likita yace muna cika dakin"


Hakuri ya bata sannan ya kira Gimbi. A lokacin tana ta tararrabin farkawar Laminde da abinda zata fada sai waya ta shigo mata. Har wani zabura tayi don tsoro. Yana kira yaji wayarta busy.
*****


Sunan Ogansu ta gani. Jiki a mace ta dauka tana tunanin karyar da zata sake yi masa.


"Mrs Awaisu kin tayar mana da hankali. Sama da awa hudu kince mother in-law dinki tana ICU. Ina ta kira tun dazu baki dauka ba"


Yawun bakinta taji ya kafe ta kasa magana. Shi kuwa ya cigaba.


"Da naji shiru na kira maigidan naki"


Bata san lokacin da ta daga murya ba
"Ka kira wa??? Ya dauka???"


"Ban same shi ba shiyasa na sake kiranki. Idan mun tashi zamu biya asbitin mu dubata ni da sauran staff."


Kafin ta tattaro kalmomin da zatayi amfani dasu domin dakatar da zuwan nasu ya kashe wayar. Ji tayi gabadaya duniyar tayi mata zafi. Kiransa take shirin yi sai ga ba Awaisu ya shigo. Dan sauran kuzarinta a take ya kare taji cikinta ya duri ruwa. Tana amsa kiran ta jiyo muryarsa kamar zata fasa mata dodon kunne.


"Wane irin wulakanci kike yi min ne? Kin barmin uwa da baki a asibiti babu ke babu Laminde. Wannan aikin naki wanda na lura duk tsaurin banki kin mayar dashi wurin gantali shi zan hana kowa ya huta"


Ita mamaki take yi yadda ta kashe kudi har dubu dari hudu lokaci guda amma komai ya rikice mata haka. Sauke murya tayi har ta fara saduda


"Muna asibiti da Laminde"


Wani mugun tsaki yaja "to kiyi maza ku karasa dakin a kai musu abinci. Yau ni da ke ne wallahi idan na dawo. Sai kin fada min what you have against my family"


Tuni ta amincewa ranta Anti Bebi tasa Wangesi ya warware sauran aikinsa sannan an kara mata da na bakinjini. Bayani tayi masa na inda suke yayi saurin fitowa babu shiri. Abinci ya tsaya ya sayawa su Maamu sannan ya wuce asibitin. Bayan yaje ya fada musu inda zashi tare da Harisu sannan ya kira dreba akan yazo ya dauki su Maman Rumana zasu je suyi girki bayan sun gama cin abincin.


Asibitin da aka kwantar da Laminde suka wuce. Suna zuwa ya wuce emergency inda Gimbi tace likita na duba ta, ga kuma police a gefe. Da isarsu likitan ya fito ya sanar dasu an samu jinin da take zubarwa sakamakon wani karfe a gefen titi da ya soke mata cinya ya tsaya. Sannan ta sami karaya a hannu ga kuma fuska da ta kumbura saboda buguwa. Bayan ya tafi Awaisu ya kalli Gimbi tana ta rarraba idanu.


"Abin da ban fahimta ba shine me ya kaita fitowa bayan dreba ne yake mayar da ita idan ta gama girki"


Shiru tayi babu amsa.


"Baki ji me nace bane? Wai ke ma din me kike yi a gida a wannan lokacin. Kina maaikaciyar banki amma sai kiyi ta yawonki son rai"


Tsoron kada ya dawo da fadan kanta tace "kamata nayi a dakinka zata yi sata. Shine da ta ganni ta fito da gudu har hakan ta faru"


"Laminden?, shekara biyu da rabi bata taba sata ba sai yau?"


"Karya kake nufin ina yi mata ko me? Ka bari ta farka ka tambayeta mana"


Harararta yayi yana ji a jikinsa karya take yi masa.


"Dazu na tambayeki babu amsa. Nace me ya kaiki gida lokacin aiki?"


Kafin ta samu karyar da zata yi masa Harisu ya janye shi gefe.


"Wani sabon salo ne ka fito dashi na yiwa matarka fada ko bakaken maganganu a gaban mutane? Ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login