Showing 84001 words to 87000 words out of 112099 words
Chapter 29 - KASHE FITILA Book Complete by Batul Mamman.txt
tana kuka a hankali ya gane an tsira allurar shima ya kuma riketa sosai yana cewa tayi hakuri.
Nurse ta gama ta dago kai tana kallonsu. Shi da Rumana sai ka rasa wa akayiwa allurar idan ka kalli fuskokinsu. Kasa hakuri tayi ta tambayeshi yaya suke da Rumana.
Bai saketa ba har lokacin tana kuka yace "matata ce Son So dina"
"Kun burgeni wallahi. Rumana zaki zama kawata daga yau ko?"
Zumbura baki tayi "bayan allurarki da zafi sosai"
"Tuba nake amarya bari na danna miki wurin kada ya tashi"
Kafin ta kai hannu Awaisu yasa hannunsa a wurin yana dannawa a hankali yana hura daidai kunnenta. Daga shi har Rumana babu mai magana Nurse din ta rike baki kafin ta fita ta rufe kofar tana cewa wannan sai ku makanta mutane ai. Kira taji daga bayanta
"Sister A'i maman hudu dagq ina haka?"
Daga hannu tayi ta rage murya sosai "hmmm soyayya na gani zata tayar min da tsohon tsumi"
Tafawa sukayi suna dariya ganin Awaisu ya fito rike da Rumana tana dingisa kafa.
[15/08, 17:46] +234 803 272 5896: *KASHE FITILA*💡45
*Batul Mamman*💖
Karkashin wata katuwar bishiyar umbrella fruit dake gaban gidan nasu Awaisu yayi parking din motarsa. Da yake babba ce sai ta yiwa wurin inuwa sosai don suna yawan zaman hira a wurin. Kuma yayi sa'a babu hayaniya sosai saboda yawancin mutane sun tafi cin kasuwar dake kusa dasu mai ci duk asabar. Kallon Rumana yayi tayi bacci sai layin hawaye da yake kwance a kyakkyawar fuskarta. Tunawa yayi da irin kukan da ta rinka yi masa a hanya wai ya bari anyi mata allura. Bata san ko a jikinsa akayi iyakar abinda zaiyi kenan ba saboda yadda shima yaki jinin allurar. Tana kukan yana rarrashi yaji shiru ashe bacci ne ya dauketa.
Yanzu da suka dawo yayi parking kallonta kawai yake yi yana kara jin sonta har cikin ransa. Bayan kamar minti goma aka soma kiran sallar azahar. Tunani yake me ya kamata yayi. Da gani tana jindadin baccin musamman da akace jiya kwana tayi tana fama da ciwo. Fita yayi ya zagaya bayan motar tasa hadaddiyar jeep navy blue ya dauko abin sallah. Tagar bangaren da take ya sauke kadan ya zira abin sallar ta ciki sannan ya mayar ya rufe. Sai yayi mata kamar labule babu yadda za'ayi rana ta dameta ko wani ya ganta idan ba gaban motar ya zagayo ba wanda kuma babu hanya don ta kusa taba bango. Sai da ya daidaita mata AC din ya kuma kwantar mata da kujera sannan ya fito yayi sa'ar ganin Sajid zai shiga gida. Kiransa yayi yace ya zauna a bayan motar ya jira shi ya dawo.
"Idan na dawo na samu ka tashi yayarka ni da kai ne. Kaga bata da lafiya ka barta tayi bacci"
Sajid ya dago kai a dan rikice jin yace zai gamu dashi "Uncle idan ta farka da kanta fa"
Hannu Awaisu ya dora a lebensa "shhhh da wannan surutun zaka tasar min ita."
"Ita kadai ce taka Uncle mu kuma fa?" Sajid ya fada fuskarsa na nuna rashin jindadi.
Murmushi Awaisu yayi yasan halin Sajid da tambaya idan ya biye masa zai iya makara sallah. Robar ribena daya ya dauko cikin wanda ya siyowa Rumana ya bashi ya fita daga motar yana nanata masa ya kula da mukullin da ya bari a jiki saboda AC da bai kashe ba.
Har ya dawo daga masallacin bata farka ba sai ma gyara kwanciya da ta kara yi. Gaba ya koma ya zauna ya cewa Sajid ya fita ya tafi gida. Yaro yayi kwal da idanu zaiyi kuka.
"Don Allah nima ka barni in sha AC bazanyi surutu ba"
Girgiza kai Awaisu yayi yana dariya ya daukowa kansa karfen kafa. Yadda yake da surutu yasan ko hannun Rumana ya taba sai ya kai rahoto cikin gidan. Wayarsa ya dauko kawai yana karanta labarai ba jimawa shima Sajid din ya bingere a bayan motar yana bacci. Sai bayan fiye da rabin awa ya farka ya fita wai zaiyi fitsari. Buga kofar da yayi da karfi ne ya tashi Rumana ta farka ta mike hannu tana mika ta kusa hadawa da fuskar Awaisu.
*****
Sajid na shiga tsakar gida ya hau bada labarin Uncle Awaisu yasa shi gadin Rumana yanzu ma tana motarsa tana bacci. Mama kunya ta rufeta ita kuwa Anti Amarya kan Sajid din ta make tana cewa bata son gulma.
"Uban surutu idan na kuma ji kana fadin abun da ba'a tambayeka ba sai na dirje maka baki"
Dakinsu ya tafi yana hawaye rai a bace an doke.
*****
Da sauri Rumana ta tashi tana waige gabadaya kanta ya juye ta kasa gane ina take. Awaisu kuwa hannun da ta miko gaban fuskarsa da tana mika ya damke.
"Kwashe min fuska zakiyi Son So?"
Rufe ido tayi a kunyace tana cigaba da waige ta gano ina suke "yi hakuri kaina ne ya juye"
"Har kinsa na fara jin tausayin kaina" yayi maganar yana son hada ido da ita. Kallonsa tayi ta tambayeshi meyasa yake tausayin kan nasa suka hada ido bata ankara ba. Sassauta murya yayi yana mata murmushi "saboda haka zaki rinka bugeni akan gado idan kina bacci"
Zaro idanu tayi "La ilaha illallahu...."
"Muhammadur rasulullah SAW" ya karashe mata.
"Ni dai babu ruwana wallahi" ta turo baki a rude
"Ni kuma da nawa saboda haka kema da naki. Wai me kike zaton ina nufi har kin wani tsorata?"
Baki na rawa tace babu komai. Dariya yayi yana cewa tayi ta gama tsoron da firgicewar zata dena ne.
Wata irin yunwa taji ta kamata don tun jiya rabonta da abinci. Cikin ta dafe ta kama kofar zata bude taji ta a rufe .
"Uncle don Allah zan shiga gida yunwa nake ji"
Wani irin kallon yayi mata ta kuma gane dalilinsa taki yin abin da yake so saboda kunya ta sake cewa tana jin yunwa.
"Babu inda zaki idan baki gyara sunan da kika kirani ba"
A hankali tace "ssssooonnn" don shi dai banda harafin *s* bai iya gane komai ba sai sautin da bakinta ya fitar. Matso da kunnensa yayi daidai bakinta kamshin turarensa ya kara shiga hancinta.
"Banji me kika ce ba fa"
Dagewa tayi ta saita bakinta a kunnensa da karfi tace " *SON SO* "
Da sauri ya daga ya hau dukan kunnen don ji yake kamar ya zama kurma. Rumana ta rinka kyalkyala dariya allurar da aka mata tasa ta manta da ciwon kafa saboda saukin da ta samu.
Harara ya sakar mata amma fuskarsa ta fallasa murmushin da yake yi "so kike yi na kurmance zaki kashe min dodon kunne. Zo ki fita kafin ki sa na rasa na ji"
Dadi taji yadda yake yi kuma yace ta fita. Bude kofar tayi ta sauka sannan ta juyo tana kallonsa
"Uncle na iya maganar kurame fa sai na koya maka"
Hannu ya miko kamar zai kamata yace "ki kiyayi zuwa hannuna?"
Tayi saurin rufewa ta fara tafiya. Bata yi nisa ba ta sake juyawa
"Uncle ka gani" ta fada da dan karfi.
Lokacin abin sallar yake cirewa daga window din. Yana dago kansa yaga tayi masa wannan alamar da hannunta na dama fuskarta dauke da murmushi. Bata san yadda yaji dadin hakan ba har kasan zuciyarsa. A hankali yace "Allah Yasa kiyi min Son So tsakani da Allah ba don babu yadda zakiyi da aurena ba Umm Ruman"
Yadda tayi da hannun shima yayi mata ta sake jin kunya ta shige gidan a guje.
A ransa yace lallai lafiya ta samu. Kafin ya shiga shima drebansa yazo yana bashi hakuri wai ya zagaya ganin gari ne ya manta bai tambayeshi ko zasu fita ba.
"Kada ka damu sai anjima zan sake fita amma ni zan tuka kaina. Kai dai ka shiryawa naka tukin na gobe"
*****
Wanka ta fara yi sannan ta zauna taci abinci. Tana gamawa kamar jira wani baccin ya sake dauketa. Dama haka take idan anyi allura ta wuni bacci washegari ta tashi garau.
Awaisu tare da Harisu suka ci nasu abincin sai ya shiga babban falon gidan ya tura aka kira masa uwargidan Harisu. Tsokakanarsa ta gama sannan ta zauna ya dauko kudade masu yawa ya bata yace gashi nan na hidimar biki. Godiya sosai tayi masa da addu'a ta tashi tace zata kaiwa Harisu.
Sai da suka dawo daga sallar la'asar Harisu ya nuna masa ko kadan baiji dadin wannan kudi da ya bayar ba.
"Awaisu sai kace wanda ya auri wata bare zaka bada kudin hidimar biki" ya fada rai a bace yana mika masa kudin.
"Yanzu Yaya menene a ciki don na bayar. Bani da abin da zan iya biyanka ko na saka maka yawan alkhairan da kayi min"
"Ni dai bana so. Addu'ata kawai ku zauna lafiya shikenan"
Awaisu yaji dadi kuma yana yiwa kansa kallon wanda yafi kowa sa'ar 'yan uwa.
"To don Allah ka bar mata kudin sai su kara a na lefe da zan bawa Anti Baraka"
Harisu ya rasa me zaice karshe dai yace "hmmm wannan shine ba mage ba miyau din. Nace bana son na biki kana zancen lefe. To wallahi kada ma ka fara. Idan tazo gidanka ku kare kalau. Amma yanzu kam ko sisinka bana so kuma bazan karba ba"
Awaisu ya dage shima "Yaya lefen nan dangi zasuyi ta zuba ido kuma kaga ga dangin uwa"
"Shine zaka biye musu ka dorawa kanka nauyi? Kayi gyaran gida ga kayan daki ga wannan zirga-zirga. Babu wani lefe da zaka yi na soke"
"Kada muyi haka da kai Yaya" ya dan rage murya.
"Mun riga munyi ma. Bari kaji tunda haka kake so a matsayina na mahaifin Rumana nace bazan karbi lefen ba"
Dariya maganar ta bawa Awaisu "Yaya harda fidda kokon usuli. To naji amma a matsayina na kaninka dolene na taka rawar gani a bikin Rumana"
Wannan karon Harisun ne yake dariya "akwai wata rawar ganin ne bayan sadakinta da ka bayar. Idan ma akwai rawar sai kayi mata idan ta tare"
Zuwa yanzu duka su biyun dariya suke yi sosai amma haka suka tashi Harisu ya kafe akan baya bukatar komai.
*****
Da sallama Haj Fanta ta shiga zauren Malamin suka gaisa a mutumce.
Tarin littattafai ne a gabansa ya sallami yaron da yake wurin suka sake gaisawa da ita.
"Ashe Damaturu kika koma wurin Mujahidu, rannan muke maganar da kaninki Maina. Ina fata kowa dai lafiya"
Haj Fanta ta dago kai idanunta suna nuni da tsantsar bacin rai "Ina fa lafiya Malam, wata shaidaniyar yarinya ta sako min iyali a gaba. In takaice maka dai haihuwar da nake ta jira daga matar Mujahid ta samu ta zubar da cikin. Ba yadda zanyi ba shiyasa ma ka ganni a garin nan babu shiri"
Mal Ridwan ya murmusa sanin hali da rigimar da suka sha da Haj Fanta a baya ya nemi tayi masa bayanin komai a nutse. Duk abin da Yana ta fada mata game da Gimbi ta sanar dashi tare da dan karin gishiri duk don ya amince Gimbi bata kyauta mata ba.
"Shine nace wai ko yau daya dai ya halatta na kira Gogojiya ta daukar min fansa." Tana maganar tana kwantar murya saboda bata so yaki yarda.
Wani murmushin ya sake yi "Haj Fanta kada fushi ya saka ki yin shirka mana. Har kin manta gwagwarmayar da aka sha shekarun baya? Ko kinsan ba karamin lada kike samu ba da kika hakura da ayyukan da zasu nesanta ki da Allah duk yadda kike jindadinsu. Me akayi akai aljani ke da kika yi imani da Ubangijin aljanun da mutane"
Fuskarta tuni ta nuna rashin jindadin kalamansa na farko sai dai maganarsa ta karshe ta daki zuciyarta.
"Haka ne Malam ni kaina babu aljanin da zai ban tsoro balle wata karamar alhaki nan. Yanzu meye abin yi. Kada kace na hakura na riga nayi rantsuwa sai na rama. Idan ban dauki mataki ba zuciyata tana iya bugawa cikin dare a rasa me ya kashe tsohuwa"
Wannan karon murmushin da yayi sai da hakoransa suka fito. Haj Fanta rigimammiya ce ajin karshe. Ba don karfin addu'a daga iyalinta da imanin da take dashi ba yana kyautata zaton itama da bokar zata zama irin hatsabiban nan.
"Babu abin da yake faruwa da bawa batare da sanin Allah ba. Ki tafi gida kiyi kwanciyarki nayi miki alkawari duk wani sihiri da surkullen da matar nan ta taba yi sai ya karye. Addu'a zamuyi babu dare babu rana gani ga almajirai na. Kuma daga naku bangaren kada kuyi sake. Allah Ya azurtasu da samun rabo mai amfani duniya da lahira"
Sai yanzu tayi murmushi "Amin, Amin Malam nagode sosai. So nake ayi kaikayi koma kan mashekiya" ta saka dariya.
"Ki barwa Allah Shi Yasan ta inda zai kamata. Mu namu addu'a ne kawai."
*****
Karo na shida kenan Gimbi tana son kiran Mama taji muryar 'ya'yanta amma ta kasa. Tasan dayan biyu ne zai faru idan ta kira. Ko dai Maman tayi mata fada ko kuma ta rinka mata kallon ta ciki na ciki. Rasa mafita tayi ta jefar da wayar tana jin wani daci a wuyanta. Ta yaya ma za'ayi Awaisu ya kwashe mata yara. Duk da gidan iyayenta ne amma dai yaro sai uwarsa. Ranta har wani suya yake yi bata ga dalilin da zai sa idan kowa ya juya mata baya ba a hada har da yaran da babu wanda yasan wahalar zuwansu duniya da rainonsu sama da ita. Hawaye taji ya sauko mata tasa hannu ta share a fusace. Awaisu da duka danginsa basu isa ta sake musu kuka ba. Sai dai kuma tana gogewa wani na sauka. Haka ta kifa kai akan gadon tana kuka kamar ranta zai fita.
Gajiya tayi da kukan ta sake dauko wayar ta kira Ovi. Kamar jira take tace ta samar mata hanyar fita daga gidan zasu jirata a gidan Ovi din tazo suje wurin Boka. Sosai taji dadin shawarar Ovi ta tashi ta dauko mukullin motarta. Dubawa tayi bata da isassun kudi ta bude kit dinta ta dauko daya daga cikin sarkokin da Awaisu ya saya mata tun kafin zuwan Maamu. Sarka ce hai hade da zobe da dankunne da awarwaro biyu. Seti ne mai masifar tsada don a lokacin da ya bata bayan tasha matukar wahalar haihuwar autanta Mu'allim ne har an fidda rai zata tashi. Jefashi tayi a jaka ta shiga kitchen dinta da yake fayau babu kayan arziki sannan ta fita waje tana yiwa maigadi kallon daidai.
*****
Rumana ta tashi daga bacci ta sake yin wanka saboda yadda jikinta ke baci sosai a irin wannan yanayin. Gyara jikinta tayi sosai sannan ta amsa kiran Harisu da ya tura a kirawo masa ita.
Tana daga labulen kofar falon nasa idanunta suka sauka akan Awaisu. Wata irin faduwar gaba taji da bata taba ji ba game dashi saboda kwarjinin da yayi mata. Zaune yake a kasa ya jingina bayansa da kujera kafarsa daya ya mike dayar kuma ya dan lankwasa ta yana shan fruit salad wanda ya dauko daga dakin Maamu.
Harisu ke zaune a kujerar dake kusa da tashi ta shiga ta sami gefen kujerar dake bakin kofa ta zauna a kasa tana gaishesu.
Bayan sun gama gaisawa Harisu yace ta dawo kusa da Awaisu ta zauna. Kamar kwai ya fashe mata a ciki haka ta tafi gefensa ta zauna a kunyace.
Harisu yayi gyaran murya sannan ya dubeta "Umm Rumana meye matsayina a wurinki?"
Kanta a sunkuye tace "mahaifi"
"Madalla, shi kuma Awaisu fa?"
Tun da ta shigo ta kula ya dauke idonsa daga kanta har taji babu dadi ko tayi masa laifine. Shi kuwa basarwa yake yi kada ya kunyata kansa a gaban suruki.
A dan karkace ta kallo Awaisu tayi sa'a suka hada ido sai cewa tayi "Son So..."
Allah Yasa irin maganar nan ta ciki tayi ko kadan Harisu bai ji ba shi kuwa Awaisu bowl din fruit salad din ya kusa saki don rudewa zata kunyata shi.
Harisu ya sake maimaita tambayarsa ta kuma bude baki har lokacin tana satar kallon Awaisu da dan karfi tace "Son...."
Bai san lokacin da ya kai hannu bayanta yana bubbugawa ba da sauri "Ruwa kike *so*, sannu kwarewa kika yi"
Dariyar da ya bata ce ta saka ta soma tarin dole harda hawaye. Ga Harisu da baisan me suke yi ba yayi zaton kwarewar gaske ya tashi yana cewa akwai ruwa a cikin dakinsa bari ya dauko mata.
Yana shiga Awaisu ya kura mata ido dariyarta tana bashi sha'awa kamar ya dauketa a lokacin "kinci bashi yarinya ki kuka da kanki ranar da zance ki biya"
Ita kuwa yadda taga ya rude baya son Babanta yaji wannan sunan ne yake kara bata dariya.
Kallon mamaki sosai tayi masa kafin ta fara magana kamar zatayi kuka
"yanzu Uncle sai kace sai na biya idan naci bashinka? Kuma ni yaushe na karbi bashi a wurinka"
[15/08, 17:46] +234 803 272 5896: *KASHE FITILA*💡 46
*Batul Mamman*💖
Bai sami damar bata amsa ba Harisu ya dawo. Cigaba da buga mata bayan yayi ai kuwa ta sake kwashewa da dariya. Da aka bata ruwan kurba daya tayi ta ajiye amma bata yarda ta sake kallon Awaisu ba.
Harisu ya sake maimaita tambayar a karo na uku ta sadda kai kasa tace "Uncle ne"
"Ya wuce Uncle dinki Rumana. Mijinki ne kuma nasan cewa bakiyi kankantar da zaki kasa fahimtar me ake nufi da wannan kalmar ba"
Idonta taji ya ciko da hawaye ta kasa dago kanta don kada su gani. Tana ji ya cigaba da magana tun tana daurewa sai ta soma kuka.
"A da kinsan Awaisu a matsayin kawunki ne kawai. Amma yanzu igiyar aure ta shiga tsakaninku saboda haka ina ja miki kunne wallahi Rumana kada ki kuskura raini ya shiga tsakaninku wai don kina matarsa. Aure girma ne dashi da daraja. A yanzu duk duniya babu mai iko dake sama da Awaisu. Kamar yadda na sanar da yayunki biyu da suke gidan aure kema ina horonki da ki rike Allah da ManzonSa iya tsahon rayuwarki. Ke ganau ce ba jiyau ba akan abubuwan da suka faru a gidansa a baya. Da wannan nake baki shawara ki zama zama tauraruwa mai *kunna fitila* a gidan da aka dade da *kashe fitila*. Ki kiyaye dukkan gabobinki daga sabon Allah musamman shirka ita kam kinsan Allah baya yafewa mai yinta idan ya mutu bai tuba ba. Ana ta cewa ke yarinya ce an aurar dake amma ni nasan kuruciya daban zaman gidan miji daban. Kada ki bani kunya kuma kada ki bawa mijinki kunya. Soyayyar da yake yi miki kada ki bari ta zama makaminki na musguna masa. Abu na karshe da zan fada miki kuma gashi a gabana shaida shine ki sawa ranki kinyi aure na