Showing 21001 words to 24000 words out of 112099 words
Chapter 8 - KASHE FITILA Book Complete by Batul Mamman.txt
akan za'a tafi da Tikeke, Kawu Bashar da matar Hadi. Idan basuyi haka ba tijarar Hajja bata tsallake kowa. Ba karamin aikinta bane ma tasa danta baban Tikeke ya kaisu tunda dreba ne.
****
Kasuwa Harisu ya koma can wurin masu gwanjo ya hadu da Bomai kanin baban Awaisu. Dattijo ne rigimamme na ajin karshe. Yana cikin masu yiwa Harisu habaici wai sun shanye Awaisu baya bi ta kansu. Bayan jarin gwanjon ma shine ya bashi.
"Alh Harisu kenan, yau an leko mu"
"Kawu Bomai yaya kasuwa?"
Kan benci ya zauna yana zukar sigari kafa daya kan daya.
"Gata nan muna fama. Yaya akayi ne?"
Kamar yadda ya sanar da 'yan uwan Maamu haka ya fadawa Bomai. Wani tsalle ya daka ya tashi dama shi ba jiki ba sai tsawo.
"Maamu tamu ce babu lafiya? Kace ban ga ta zama ba. Kayi kyan kai sosai da ka fada min. Asubar fari zanzo nan gidan naka mu tafi"
"Sai wuraren karfe tara zamu tafi. Nace su sauran zaka sanar dasu ko naje na fada musu. Awaisu yace jikin da sauki dai"
Matsowa yayi daf da Harisu "Tunda na sani ka bar maganar kawai ni zan sanar dasu."
Sai kuma ya gyara tsayuwa yana kwantar da kai gaban Harisu "Maamu mutun ce, wato ba don haduwarta da Mal Sa'adu mai rasuwa ba dama ni naso na aureta saboda kula da maraya. Kuma gashi ni ban haihu ba. Shiyasa nake jin yaron nan a raina sosai. Kaga sau biyar fa yana bani jari. Yaro yayi halin iyayensa wurin karamci"
Harisu gyada kai kawai yake yi ya samu ya bar wurin. Baaba Hure ta hadashi da aiki. Me zai sa tace kowa sai yaje. Tausayin Awaisu da Gimbi wadda za'a hada da baki ne ya kama shi.
Yana kallo Bomai ya kulle gwanjonsa ya saba a kafada yayi hanyar titi.
*****
"Hinde maza maza fito ki fara hada kaya"
Hinde na bandaki ta fito da sauri bota a hannu. Ajiye botar tayi ta sa hannu ta toshe gefen hanci ta rangada guda tana tafa hannuwa
"Ayyiriririiiii, sai yau kaga damar sakin nawa, to ka sani kuma ka jira ina gama idda zan sami miji da ya amsa sunansa ba irinka ba kashi da rai. Nawa kayi min ne sakin"
Botar da ta fito da ita ya dauka ya kafa a baki ya sha ruwan sannan ya kuskure baki ya tofar.
"Dadina dake wutar ciki, baki ji bayani ba kin hau suki burutsu. To ai sai ki tafi nima na huta"
"To dai gaya min me ya faru idan ba sakin bane kake min wannan kiran"
Kan kullin gwanjon ya dare ya zauna "Abuja zamu koma gidan dana"
Wata muguwar shaka Hinde tayi masa har yana zaro idanu "munafuki ashe har da gareka ban sani ba. A wace tashar ka hadu da babarsa"
Hannunta yake duka da kyar yana cewa "Awai,aaaaw,awsu"
Sassauta rikon tayi yace "AWAISU ne fa dan marigayi yayana. Kasheni zakiyi ne?"
Hinde ta zauna shirim a gefensa tare da murza masa wuyan.
"Kaine baka iya kawo labari ba. Kace Awaisu na Maamu"
Nan ya labarta mata yadda sukayi da Harisu da kuma kudurinsa
"Yace kwana biyu zamuyi. Amma so nake ki hada kayan kamar na sati. Sai kuma mu saka kamar uku uku a jikinmu kada a ga Ghana mazigo din kayanmu da girma. Idan munje zan sa ya nema min aiki. Kema ki rinka yiwa Gimbiyar nan ladabi. Kinsan durkusawa wada ba gajiyawa bane."
Hinde sai murna zasu Abuja. Ko Bomai bai fada ba bata ga dalilin da zaisa idan sun je ta dawo Fika ba. Kallonta yayi ta shige daki ta fara fiddo kayansu zata wanke yace
"Hinde don Allah idan munje kada ki nuna hali, banda dauke dauke kinji ko"
Harara ta galla masa idonta kamar ya fado. Me zai kaita sata kuma yanzu, ita da tayi a gidan biki 'yan mata sukayi mata duka sai da hakorinta na kasa ya cire.
******
Daren ranar Gimbi kasa bacci tayi. A haka ma don bata san mutum nawa ne masu zuwa ba. Sau biyu Awaisu yana farkawa ya ganta a zaune sai tace masa jikin Maamu ke damunta. Gashi likita yace harda rashin cin abinci sosai. Harda kukanta tace
"My dear ko zaka tambayi Maamu me tafi so sai na rinka dafa mata. Gobe zan dauki hutu ko na sati ne na kula da ita"
"Kema kinsan bazasu baki wannan hutun ba. Ki bari kawai tunda akwai masu zuwa"
Murmushi tayi, don tana tunanin a goben Anti Bebi zata kaiwa Wangesi bukatarta akan ogansu. Sake marairaicewa tayi
"Duk laifina ne da nake zuwa aiki bana iya kulawa da ita yadda ya kamata. Kullum da safe idan naje fada mata zan fita Maamu sai tayi min addua. Yanzu idan suka zo aka ce na barta da yunwa fa."
Kuka ta fashe dashi Awaisu ya rarrasheta. Karshe tace masa zata bar aikin kawai ta kula da gida. Ga mamakinta sai taga ya bata goyon baya. A zuci tace wato shima bakinciki yake da aikin. To yanzu ta fara.
*****
Da safe tunda babu Laminde gashi tana son burge Awaisu haka tayi farfesun kayan ciki da dankali ta hadawa Maamu Awaisu ya kai asibiti. Bayan su Haris sun tafi makaranta ta fadawa Anti Bebi halin da take ciki da bakin da zasu zo.
"Zage damtse zakiyi ki kyautata musu kada wani ya sami bakin magana akanki" inji Anti Bebi.
Ai kuwa ta wuni a kitchen tana girkin tarbar baki mutum hudu ko dubiya bata samu zuwa ba. Sai yamma likis suka iso mota biyu. Awaisu ma shigowarsa kenan kuma Haris yayi masa waya ya sanar dashi karin da aka samu yace ya amince duka su taho tare akwai wurin kwana. Sai dai kuma ya manta bai fadawa Gimbi ba. Jin tsayuwar mota tabi yaranta suka taho da gudu tarbarsu Baaba Hure. Sai ga Gimbi murmushi ya makale a gefen baki. Mutane ta gani wanda ta sani da wanda bata taba gani ba.
Baaba Hure, Anti Ummukulsum, Harisu, Maman Rumana, Kawu Bashar, Ammu matar Hadi, Tikeken Hajja, Bomai da matarsa Hinde. Mutum takwas. Tun a zuci ta fara kuka.
[4:31PM, 2/18/2018] +234 803 369 4017: *KASHE FITILA*💡18
*Batul Mamman*💖
Zuciyar Gimbi harbawa ta rinka yi sosai saboda wani bacin rai da ya danneta. Kasa daurewa tayi duk iya kokarinta ta fashe musu da kukan bakinciki mai sauti. Ai kuwa hankalinsu Baaba Hure ya tashi matuka sun zata ko Maamu rai yayi halinsa ne. Da yake ta fara kwarewa da kissa irin ta Anti Bebi sai tayi saurin goge hawayen harda rungumo Baaba tana kallon Harisu a zatonta shi kadai yake jin Hausa.
"Wallahi tsabar murnar ganinku ne Yaya. Tun jiya da yace zaku zo nake murna. Allah Sarki Maamu yau zan gani ni da ita wa yafi murnar zuwanku"
Daga gefe taji ance "kissa adon mata, Bomoi ka ga wadda ta fini"
Hinde ta fada da sunan rada duk da tasan ana jinta kuma da hausa. Bomoi ya galla mata harara ya kalli Gimbi yana murmushin dole. Daga zuwansu zata nemi janyo musu bakin jini wurin matar gida.
A razane Gimbi ta kalli Hinde har cikinta yana kadawa. Sakin fuska tayi ba arziki kamar bata fahimceta ba tace su shigo ciki. Mukullin wani daki ta waje ta bawa Harisu inda ya taba masauki lokacin zuwansu Hajji. Nan suka shiga shi da Kawu Bashar da Bomoi wanda yake ta zuba surutun haduwar gidan dansa gudan jininsa.
Daula ce tayiwa Baaba Hure jagora zuwa dakin Maamu inda zata zauna. Wani daki a gefensa kuma Gimbi tace Ummukulsum, Maman Rumana, Ammu, Hinde da Tikeke su shiga suyi wanka sannan su fito cin abinci.
Tikeke ta zumburo baki "Haba Hajiya ko ruwa bamu sha ba zaki ce muyi wanka. Allah Ya gani sai naci abinci nake iya komai."
Ammu ta riko hannun Tikeke tana kokarin fita daga dakin zata koma falo inda ta hango kwanukan abinci an jere su. Kokawar fizgewa Tikeke ta somayi Ammu ta canja harshe tace zata fadawa Kawu Bashar. Rai a bace ta kwace hannunta ta shiga bandakin tare ta bugu kofa.
Jiki a sanyaye Gimbi ta fita daga dakin. Yau kuma irin bakin da tayi kenan ta fada a zuci. Falon taji kamar yana warin gumi a cewarta ta dauko air freshner ta shiga fesawa. Juyawar da zatayi ta hada ido da Baaba Hure tayi saurin ja da baya.
Baaba ta saki fuska
"Dama kwan fitilar bandakin ne naga ya mutu. Idan akwai wani ki taimaka a saka min don in yamma tayi ba gani nake sosai ba bare kuma a duhu"
Mamaki ne ya bayyana sosai a fuskar Gimbi jin Baaba tana hausa. Dazu ma taji wata tayi a waje. Yanzu bata isa ta juya harshe tayi gulmarsu a gabansu ba kenan.
"Baaba bari idan Abban Haris ya dawo sai a saka miki ki shiga"
Baaba ta dafata da hannu daya tana dan tafiya
"muje ki kaini naki sai nayi alwala a can. Banyi sallar la'asar ba ga magariba tana gabatowa"
Ba'a son ranta ta kai Baaba bandakinta ba. Maamu kuwa ko hanyar dakin bata taba takawa da kafarta ba. Tana zaune tana ji Baaba Hure tana kaki. Takaici ya isheta ta fita ta koma dakin Awaisu sannan ta kira Anti Bebi.
"Na shiga uku Anti, su takwas kamar ance musu ta mutu. Ina zan kaisu"
"Ba na son shirme kinji ko. Ki tashi ki je duk yadda suke so kiyi musu. Idan kika bari suka gane wani abu to karshenta su ki tafiya da wuri. Kinga garin neman gira kin rasa ido"
Maganar Anti Bebi gaskiya ce. Da saurinta ta shiga kitchen ta dora macaroni tunda dama shinkafa da miya tayi da kuma tuwon dare. Kafin ta gama Awaisu ya shigo ya tafi wurinsu Harisu suna gaisawa.
Sai da sukayi sallar magariba suka ci abinci sannan suka fara shirin tafiya asibiti gabadayansu. Gimbi tana ta raha da rawar kai ita me son surukai. Sun firfito waje Awaisu ya kira drebansa da yake kai yara makaranta ya bashi mukullin mota
"Sunday gashi ka debe su Yaya Ummukulsum ka wuce dasu asibitin da aka kwantar da Maamu. Zan tsaya a atm ne sannan na taho da su Baaba"
Sunday ya dan rissina a ladabce "Oga yaushene Hajiya babu lafiya, wane asibiti ne.?"
Awaisu yaji kamar ya raina masa hankali yace "Inda ka kai musu abincin rana mana"
"Ban fita ba tunda mun dawo da su Haris"
Idanun Awaisu suka kankance yana kallon Gimbi "da kanki kika kai musu abincin rana? Ina na daren ne ma ban ga an dauko ba"
Idanun Gimbi nan da nan suka yo waje ta rasa amsar bayarwa. Baaba Hure tana kallonta tasan bata da gaskiya
"Gimbiya kada kice min ba'a kaiwa Maamu abincin rana ba bare na dare"
"Uhmmm, uhmmm" nan fa jikinta ya soma rawa ganin idanu a kanta ga Awaisu yana wani huci kamar mayunwacin zaki. Irin wannan fushin nasa ba kasafai yake ba. Kuma a tunaninta yanzu da Wangesi ya gama masa aiki bai isa yayi mata ko da mugun kallo ba.
Tsawa ya daka mata kamar ya kai mata duka "ki bani amsa mana"
Harisu ne yayi magana ganin ransa da na Baaba Hure a bace yake. Yaran ya fara cewa su shiga motar Sunday sannan yace "Awaisu meye haka ne kake yi mata tsawa gaban yara. Gimbiya an kai abincin?"
Kuka ta saka saboda tsabar bata damu da Maamu ba shaf ta manta da batun abincin. Na safe ma da tayi saboda ta burge mijinta ne yaji dadi.
"Wallahi Yaya Harisu ina ta aiki ne na sha'afa."
Ummukulsum tace "wannan ba magana bace Gimbi. Akwai wani aiki da zai sha kanki sama da nata da take asibiti? Yanzu ga jinya ga yunwa daga ita har Rumana"
Ido sharbe da hawaye ta rinka basu hakuri. A ranta kuwa duk tsine musu take yi suna neman jaza mata masifa wurin miji.
Baaba Hure tamkar ta cinyeta da fada. Tana yi Awaisu yana yi don ya kule karshe. Harisu ne ya rinka basu hakuri. Su Tikeke kuwa an sami abin kallo da gulma. Marasa jin hausa sosai babu damar tofawa.
Duk wani haushin Gimbi da yake ji kwanakin baya ya kasa magana tun jiya da ya ga Maamu a wannan yanayin yaji kamar an bude masa ido. A fusace yace mata taje ta dauko abincin. Wani tsoron ya sake kamata domin batayi dasu ba. Hasali ma dai babu sauran abinci a gidan. Awaisu yayi fadan da hausa ya koma saka yarensa kamar ya kai mata duka. Baaba Hure ko a jikinta saboda tun maganar da sukayi akanta take jin Gimbi ba matar kirki bace. Harisu ya ja shi gefe ya soma nasa fadan
"Wani sabon salo ne ka koya zaka zubarwa matarka mutumci a gaban baki. Dubi yadda suke kallonka. Kana tunanin wannan labarin bazai je Fika ba"
Kwalla ce take barazanar fita daga idonsa saboda tunanin yaya Maamu ta wuni. Yaje da azahar daga wurin aiki amma ita dasu Laminde babu wanda ya fada masa
"Yaya ace tun abincin safe saboda Allah"
Harisu ya dafa shi yana murmushi "to kuka zaka yi min? Awaisu 'ya'yanka hudu fa. Muje su koma suyi girkin kafin dare ya karayi a hanamu shiga"
"Bari kawai ma saya a hanya. Karfe tara suke hana shiga sai goma na safe kuma"
Tare suka koma suka shiga motocin. Wasu na motar Sunday tunda babba ce school bus sauran Awaisu ya diba. Gimbi tayi turus a waje ganin Bomoi ya shige gaba abinsa. A dakile Awaisu ya nuna mata bus din
"Idan zaki je ki koma bus din inda mata suke"
Ranta na kuna kamar tace bazata ba ta koma ta shiga tsakiyar Ammu da Hinde. Kallonta suka rinka yi ta kasa motsin kirki saboda sun matseta.
*****
Suna zuwa a kwance suka sami Rumana a gadon da yake gefen na Maamu tana bacci. A kasa kan abin sallah kuma Laminde ce take cin dafaffiyar gyada. Naira hamsin gareta shine ta siyo musu ita da Rumana suka ci suka sha ruwa. Maamu taki ci tana kwance tana hawaye. Yaushe ne danta zai waiwayeta???
Muryar Baaba Hure taji ta soma yunkurin tashi. Maman Rumana ke rike da hannunta ta karasa da ita bakin gadon saboda dishi dishi take gani. A haka ma don anyiwa idon aiki ne.
Hannu ta mika tana laluben Maamu. Ji tayi Maamu cikin muryar dake nuni da tana jin jiki tace "Baaba"
Baaba Hure sai hawaye "Maamu sannu, sannu 'yar uwa. Kai Awaisu ku zuba mata abincin nan"
Gimbi ce tayi saurin mika hannu zata karbi ledojin ya harareta sannan ya bawa Maman Rumana. Ummukulsum tace "Maamu kin rame sosai"
Riko hannun Ummukulsum din tayi "hmmm kayya Ummu jikin tsufa ne kawai, Ina yaran , yaya wajensu Auta Zakiyya"
Rumana cikin bacci taji kamar muryar babanta. Firgigit ta tashi. Abin mamaki harda Mamanta da Baaba. Wani tsalle tayi ta diro ta kankame Harisu. Shi kam kunya ma ta bashi a gaban mutane. Ta tafi zata rungume mamanta ta harareta irin abin 'yar fari. Sai kawai ta koma jikin Baaba ta kankameta.
Sun gama gaisawa Laminde da Rumana suna gefe suna cin abinci sauran suna ta hira. Basu bar asibitin ba sai shadayan dare. Nurses suna ta zuwa ana cewa su bar hayaniya.
Likita ya bukaci ganin Awaisu kafin su tafi. Fada sosai yayi masa duk da karancin shekarunsa akan shi na barin Maamu da yunwa. Duka allurai da maganinta tun azahar ba'a yi mata ba saboda bata ci abinci ba. Sannan jikinta ma yana nuni da alamun rashin kuzari saboda tana bukatar wasu sinadarai a jikinta. Shi dai sai hakuri yake bayarwa yana tunanin wai me Gimbi take yi har Maamu take zama da yunwa. A wani bangaren tuhumar kansa yake da rashin kulawa wadda bai san dalilinta ba
******
Wurin shabiyu da rabi kowa yaje ya kwanata Awaisu da Gimbi suna ta fada. Bashi hakuri take yi amma kamar tana ingiza shi. Bandaki ta shiga tayiwa Anti Bebi text ta sanar da ita. Shawara ta duk da batayi mata dadi ba haka ta karba kafin gobe ta nemi Wangesi.
Wurin Baaba taje tayi sa'a bata kwanta ba. Nan ta kwantar da kai ta bata hakuri ta roketa akan ta bawa Awaisu hakuri. A zatonta tuban gaskene tacewa Awaisu magana ta kare daga lokacin. Ya dai ce to amma juya mata baya ma yayi da suka kwanta. Kafin nan kuma yasa ta bawa Ammu da Maman Rumana dakinta saboda wancan yayi musu kadan. Ita Ummukulsum ta canji Laminde zata kwana a asibitin
Da safe matan suka tayata girki tana ta kokarin jansu a jiki.
*****
Anti Bebi karfe bakwai ta fice daga gida sai kauyen Nasarawa state inda Wangesi yake. Magunguna ya bayar da wasu layu da za'a binne a gidan. Kafin shabiyu ta dawo gida. Wanka tayi ta shirya sannan tace Alhaji yazo ya kaita dubiyar surukar Gimbi. Tun tana chan zazzabi ya kamashi a office ya dawo gida. Wani nau'in asirin akayi masa. Da ya dawo Shuhada ce ta tarbe shi ko kallonta yaki yi. Kudin mota take so ya bata itama ta bar musu gidan.
Suna fitowa daga daki Anti Bebi ta marairace wai yace Shuhada tazo suje tare saboda zaman gidan bazai mata dadi ba. Har ransa yaji dadin ta damu da yarsa amma ita Shuhada bata sonta. Dolenta ta fito suka tafi tare. Anti Bebi ta hakimce a baya Shuhada na gaba. Daga bayan mota take ta bashi umarni yana toh kamar wani bawanta. Kafin su je asibitin Shuhada har kuka tayi ganin yadda Daddynta ya koma a gaban mace.
*****
Alh Mudi da Mama suna bayan mota dreba na jansu zasu je duba Maamu. Fada sosai yayiwa Gimbi a waya bayan ya sami labarin rashin lafiyar a bakin Saminu. Su da suke garin ace basu da labari har su Harisu sun zo shi kuma Saminu yana hanya. Gimbi hakuri ta bayar kawai. Yadda bata damu da Maamu ba bata ga dalilin da sai sunzo dubiya ba.
Dakin yau a cike idan kaga Maamu da Rumana tamkar ranar sallah. Su Mama ne suka fara zuwa ana gaisawa sai ga Anti Bebi ta shigo tana fara'a. Tuni Gimbi ta rikice ganin kallon da Mama da Alhaji suke yi mata. Ita kuwa Anti Bebi don ta bawa Mama haushi ta tafi ta rungumo Gimbi
"Gimbiya yaya mai jikin. Tun shekaranjiya da kika fada min hankalina ya tashi. Jiya da kika min waya kuma baki ne dani ban samu nazo ba"
Mama ji tayi kamar ta rufe Gimbi da duka a wurin.
*KASHE FITILA*💡19
*Batul Mamman*💖
Kallon kallo aka rinka yi tsakanin Gimbi da iyayenta. Gashi maganganun Anti Bebi sun sa ta daskare a wurin kamar wata dutse. Anti Bebi tana lura dasu ta share tana dariya ita