Showing 45001 words to 48000 words out of 112099 words

Chapter 16 - KASHE FITILA Book Complete by Batul Mamman.txt

23 Jun 2024

14008

so ko baya so"


Kowa yayi na'am da wannan shawarar inda aka yanke cewa zasu tafi su uku harda Harisu da Bomai.


Can asibitin kuwa Aunty Baraka ce ta zauna ko da zaa bukaci wani makusancin Maamu.


*****
Da yake jirgin safe Awaisu ya biyu kafin azahar ya iso gida. Yana zuwa ya tarar Gimbi bata nan ga yara sun tafi makaranta. Rita ce ta fito da gudu tana yi masa maraba kamar zata rungume shi. Abin ya bashi tsoro ma yayi saurin matsawa baya sai tayi murmushi ta wayance da karbar jaka.


"Sir how was your trip?"


Fine yace kawai yayi gaba. Saurin shan gabansa tayi ta matso daf dashi tana karairaya "ga abincin na gama hada maka"


A gajiye yake baya son yin magana shiyasa ya wuceta kawai yana mamakin wannan abu da take yi kamar zata shige jikinsa.


Ita kuwa dariya tayi tana tunanin lokacin da nasu aikin zai fara aiki ta shigo gidan ayi waje da Gimbi. Dakinta ta koma ba jimawa taji ana buga kofa da karfi. Ita da Awaisu kusan karo suka yi suna sauri zuwa bakin kofar don jin ko lafiya.


Bashi hanya Rita tayi yana budewa suka hada ido da wata mace da jikinta duk ya motse ga fuskarta kamar ayi amai saboda lalacewar fata. Tana tsaye tana ta susa tana bige bige a jikinta. Maigadi yana bayanta yana son tabata ya fitar da ita amma kyankyami ya hana.


Ganin Awaisu yasa ta dan sakin rai "Awaisu fadawa wannan yaron gidan naka cewa nice Anti Bebi"


Sake kallonta yayi cikin rashin gaskata me take fada. Wannan matar da ko almajira bata kai matsayin a kirata dashi ba itace Anti Bebi. Yana cikin wannan tunanin yaga ta rike wuya tana ta kakari. Da kyar ta saki wuyan tana haki


"Shegu yanzu kuma wuyana akace ku shake. Duk abinku ni Bebi nace dubu sai ceto"


Maigadi ne ya kuma yunkurin miko hannu sai suka ji horn a waje. Da sauri ya tafi ya fita duba waye ya bar Awaisu da Anti Bebi da Rita.


Anti Bebi ta dan nutsu ta soma magana "Awaisu ta inda aka hau ta nan ake sauka. Ka fadawa Gimbiya naji labarin komai daga wurin aljanun da tasa suke bibiyata kuma wallahi dani take zancen domib bata ci riba ba. Yadda tasa nake dandanar balai a rayuwata itama ta shirye gamuwa da nata. Nayi alkawarin ko zanyi yawo tsirara ne sai naga bayan Gimbiya"


Su Harisu ne suka shigo ta karamin gate din mai tafiyar kafa. Karshen maganar Anti Bebi kawai suka ji suka kalli juna.


"Nasan bata nan shiyasa na shigo amma idan na kuma shigowa sai nayi ajalinta" yawu ta tofa a kasa ta juya ta fita suna mata kallon mahaukaciya.


Sai a lokacin hankalin Awaisu ya kai kan bakin nasa. Da faraarsa ya taho yana musu sannu da zuwa. Bomai ya kalli Rita da kayan jikinta


"Yanzu Awaisu meye wannan a gabanka?"


Harisu yace "mai aiki ki"


Yayan Maamu ya daure fuska ya kalleta yace ta basu wuri. Awaisu ya nuna musu kofa su shiga ciki suka ce a'a.


Kawun nasa yace "ba zama muka zo yi ba Awaisu. Ana ta kokarin sanar da kai Maamu bata da lafiya kaki zuwa."


Harisu ya kalla yayi wani murmushin takaici "yanzu abin harda su Kawu kuka hada a ciki? Me na rage ku dashi da har zaka kalawa Maamu cuta kawai don kuna son na zo Fika na baku kudi? Idan kana bukatar wani abu kafi kowa sanin cewa a shirye nake na baka"


Ba su Kawu ba hatta Harisu bai fahimci zancen ba sai da suka nemi yayi musu karin bayani. Nan ya fada musu abin da Gimbi tace Amir ya fada ya kara da cewa yasan bazata taba yi masa karya ba.


"Kazo ka dauke Maamu ka bar min mata cikin damuwa kawai saboda son abin duniya..."


Wani wawan mari irin wanda Awaisu baya jin an taba yi masa tunda yazo duniya Harisu ya kwada masa a kumatun hagu yana huci saboda tsantar bacin rai.


"Ni Awaisu? Ni kake fadawa magana irin wannan?"


Bacin ransa da haushin Harisu wanda ya rasa dalilinsu ne suka kara tsanani a zuciyarsa har hawaye suka fara fita daga idanunsa ba tare da ya sani ba.


"Saboda na fadi gaskiya shine zaka mareni? da me na rageka da zaka sanya mahaifiyata cikin son zuciyarku kai da Baaba Hure"


Ran Harisu ya kara baci yayo kan Awaisu a harzuke. Kwalarsa ya kama da hannu daya da daya hannun kuma ya rinka marinsa shima kuma hawayen yake yi. Muryarsa tana rawa yake magana ga su Bomai na son ya saki Awaisun ya ki.


"Awaisu nine Harisu...ka dawo cikin hayyacinka ka kalleni. Yayanka ne wanda zaiyi komai domin farincikinka da rike amanar da Mahaifinmu ya dauka."


Tamkar karamin yaro Awaisu yake zubar da hawaye ya ma dena kokarin kwacewa daga rikon da Harisu yayi masa. Kirjinsa ya dafe yana kallon dan uwan


"Yaya kirjina ne yake min zafi kamar ana hura wuta. Na rasa abin da yake damuna. Yaya ka taimaka min"


Harisu rungume shi yayi tsam a jikinsa yana shafa masa baya shima kuma yana hawayen.


"Allah baya bacci Awaisu. Ka roke shi zai kawo maka sassauci cikin lamuranka"


Bomai da Kawu suka ja gefe suna kallon wadannan 'yan uwa. A hankali cikin sigar lumana Harisu ya sake labartawa Awaisu ciwon Maamu sannan ya roke shi ya zo su tafi ya dubata. A ransa yana son zuwa amma zuciyarsa tana ta hura masa wutar kada ya yarda da yayansa. Ba karamin yaki yayi ba da tsananta karanta Hasbunallahu wa ni'imal wakeel da Lahaula wala quwwata illa billah sai ya sami kansa da amincewa.


Su Kawu suna murna Harisu yace yaje ya dauko kayansa su tafi yace zuciyarsa bata so ya shiga gidan.


"Yaya kullum da tsoron gidan nake kwana. Amma bari naje na dauko mukullin motar da wayoyina da wallet "


Su ukun suna waje kusan minti shabiyar sai gashi ya fito har da yar jakar kaya. Rita ta biyo bayansa tana tambayar ina zaije ya daka mata tsawa akan ta dena binsa. Wata jeep ya nufa ya kira maigadi ya dan gogeta suka shiga suka fice.


Rita duk ta kidime tayi ta kiran Gimbi shiru bata daukar wayar. Yau tasan gidan babu zaman lafiya.
*****


Daga saloon Gimbi ta fito taje anyi mata kananun kitso da karin gashi da dan mayafinta a rabin kai irin na Anti Bebi babu dankwali ta fito zata shiga mota.


Daga tsallaken titin tun daga nesa Mama ta hangota suna dawowa daga unguwa da Umar. Da sauri ta rinka dukan kafadarsa tana nuna masa Gimbi akan suje wurin da sauri kada ta tafi. Wata irin kwana yayi har suka kusa gwara motocin ta kuwa fito a fusace tana bambami. Mamaki ne ya isheta ganin Mama da kaninta ta dan murmusa. Ba karamin kewar mahaifiyarta tayi ba. Sai dai taji kunya sosai don rabonta da gida tun ranar da ta koma gidan Awaisu da kanta. Sannan ko waya bata taba yi musu ba.


"Idonki kenan Gimbi?"


Ta dan rausayar da kai "Mama nayi zaton kuna fushi dani ne shiyasa na kasa zuwa gidan. Yaya kuke da Alhaji?"


Kaninta ta kallo da ko fitowa daga motar baiyi ba bare tasa ran zai kulata ta murmusa ta leka ta window tayi masa magana kawai sai ya saka waya a kunne shina dole baiji ba. Abin ya bata mata rai sosai kuwa. Kwanakin nan ba karamin kewar 'yan uwanta take yi ba da iyaye.


Mama tace "ban sani ba ko kin hadu da Bebi amma tazo min a kamanni na ban tsoro tana ikirarin ganin bayanki. Gimbi shawara ta karshe zan baki domin indai da rai baa fitar da rabon samun gafarar Allah. Ki tuba ki dawo daga rakiyar wannan mummunar rayuwa da kike yi. Ni da 'yan uwanki babu mai zuwa gidanki wannan umarnin babanki ne. Amma ki sani yadda Bebi tauraronta ya haska har ki mutu bana jin zaki kamota. Yau ga Bebi duniya ta gwada mata ita budurwar wawa ce. Wanda duk ya kamu da sonta a sannu zata yaudare shi ta karar da duk wani abin arziki a tare dashi sannan ta gudu ta barshi."


Shiru Gimbi tayi tana tunanin su Mama basu san wanda ta kama ba. Bokanta na yanzu ba dai ta fadi bukata ba kafin kace kwabo zaka ga yadda kake so indai an kiyaye sharuddansa. Bata samu bakin magana ba Mama ta shige mota suka tafi suka barta a tsaye. Motarta ta shiga ranta a dagule ta kula da wayarta tana haske. Ko da ta duba missed calls din Rita sunfi biyar. Kiranta tayi don tasan babu lafiya. Ai kuwa ta bata mummunan labarin tafiyar Awaisu. Wani zagi ta rinka jerawa Harisu sannan ta tada mota tayi gida.


Kafin ta karasa Ovi tazo don a hanya tayi mata waya. Tambayarta shawara tayi akan me ya kamata tayi Ovi tace da safe ta hada kan yaranta su tafi Fika don kada tayi bakin jini


"Ki sani ko an fadawa boka babu yadda zaayi ace an rufe bakin kowa a cikinsu. Tafiyarki kawai itace mafita. Idan kinje ki san yadda zakiyi ki kwantar da kai a wurinsu sannan ko da Maamu ta fada musu wasu abubuwa ki karyata. Zani wurin boka gobe sai na fada masa a haukata ta idan yaso dole a yarda dake. Mijinki kuma kada ki damu shima zaa sake daure miki shi"


Ovi na fita Rita tabi bayanta "Sis yaya zaki bata shawara haka mu sai yaushe zamu fara namu aikin?"


Ovi ta dafa Rita ta rage murya "kada ki damu wannan shawarar babu inda zata kaita. Kuma bazani wurin Boka ba don gobe ma ni Enugu zamu tafi da wani sabon kamu da nayi "


Tafawa sukayi sannan Ovi ta fice.
*****


Awaisu ke tuki babu mai magana cikinsu har suka isa wani gidan mai suka tsaya yin sallah. Daga nan Harisu ya karbi tukin Awaisu ya zauna a gaba kusa dashi sai bacci. Yana baccin nan banda mugayen mafarkar babu abin da yake yi. A firgice ya farka ya cigaba da kallon titi.


Damaturu suka wuce suka nufi hanyar asibitin. Gaban Awaisu ne ya rinka faduwa akai akai tun kafin su karasa har Harisu yayi parking. Ji yake kamar bashi da laka ga mugun tsoro ya mamaye zuciyarsa. Hannunsa yaji Harisu ya kama suka nufi ICU.
[15/08, 17:45] ‪+234 803 272 5896‬: *KASHE FITILA*💡33


*Batul Mamman*💖






Har suka isa kofar dakin Awaisu a tsorace yake. Dayake kofar ta glass ce ta wajen Harisu ya nuna masa Maamu kwance tamkar bata da rai. Wai a haka ma ta danji sauki kuma ta dan murmure ba kamar lokacin da aka kawota ba. A hankali ya taka ya leka inda Harisu ya nuna masa. Kafafunsa ne suka fara rawa sai gashi yana neman faduwa. Harisu yayi saurin tare shi sai dai yana mikewa ya fice daga cikin asibitin zuciyarsa tana matsanancin harbawa.


Jikin motarsa yaje ya shiga ya rufe kofar sannan ya kifa kansa akan sitiyari. Kuka Awaisu yake yi sosai irin wanda rabonsa dashi tun kuruciya. Kukan da yake yi ba na halin da ya tarar da Maamu bane , kuka ne na tsananin nadama da tausayin kansa. Idan ya mutu a yanzu ya tabbatar bashi da abin da zai kare kansa a gaban Mahallicinsa. Tambaya daya yake ta nanatawa a zuciyarsa. Shin yana ina Maamu ta kamu da ciwokan da Harisu ya fada masa ya daukota dasu? Wata faduwar 6gaba ya sake ji da ya tuna rabonsa da sata a ido tun wata waya da ya hadata da Harisun farkon komawar Rumana Fika.


Mahaifiyarsa abokiyar sirrinsa, abokiyar shawararsa ita ce a wannan yanayin kuma a cikin gidansa bai sani ba. Innalillahi wa inna ilaihi rajiun yayi ta maimaitawa a ransa. Shi dai ba jahili bane. Ya san cewa wurare da dama a Al'Qurani Allah SWT Yayi umarni da bin iyaye da kyautata musu. Hadisai kuwa bazai iya kirga wadanda ya sani masu magana akan bin iyaye ba musamman uwa wadda ta sha wahalar ciki, haihuwa, raino da kula da 'ya'yanta tun zuwansu duniya har sai ta dena numfashi. Uwa ko kana ganin kaiune maiyi mata komai na bukatun rayuwa baka taba girmaa idonta shiyasa ko a gidanka take bata fasa yi maka tambayoyi kamar kaci abinci ko kana jin bacci.


Tunaninsa na karshe shine yanzu idan Maamu ta rasu a wannan yanayin yasan duniyarsa ta gama lalace, lahirarsa kuma dama ba'a magana. Share idanunsa yayi ya koma cikin asibitin.


Dr. Yana tana tsaye da su Harisu ana kokonto ko Awaisu tafiya yayi sai gashi ya dawo. Ganin likita a wurin ya roketa ta taimaka ta barshi ko na minti biyu ne ya shiga wurin Maamu. Harisu ta kalla da guntun murmushi a fuskarta


"Shine Awaisu?"


Shi ya amsa mata da kansa "nine don Allah ki bari na ganta"


Bude masa kofar tayi ta matsa gefe tana murmushi.


Maamu tana kwance tana tunanin yadda rayuwarsu ta sauya cikin dan lokaci. Ga kudi sosai Allah Ya basu amma Ya jarrabesu da mace irin Gimbi wadda ta kasa gane me ta tsare mata. Kamar a mafarki ta jiyo kamshin turaren Awaisu wanda ta dade da saninsa dashi. Tana ayyanawa a ranta wane likitan ne mai wannan turaren taji an kama hannunta an rike gam.


A hankali ta bude idanunta suka sauka cikim na Awaisu. Cikin wata irin murya mai rauni yace


"Maamu" sai ya kawai ya durkushe a gefen gadon yana kuka. Ita ma Maamun hawaye take fitarwa a hankali ta dora hannunta daya a kansa tana shafawa.


Sun dauki kusan minti biyar a haka wadanda suke wajen dakin harda Dr. Yana suna kallonsu wasu suna tayasu kukan.


Sake dago kansa yayi bakinsa har rawa yake yi. Maamu ta rame iyakar rama. Idanuwanta duk sun shige ciki ga uban baki da tayi.


"Ki yafe min Maamu. Don Allah kada fushinki ya zama katanga gareni da samun rahamar Allah."


Murmushi tayi cike da jindadin addu'arta ta karba hankalin danta ya dawo jikinsa tasa hannu ta goge masa wasu sababbin hawayen da yake fitarwa a hankali


"Ban yi fushi da kai ba domin nasan baka san abin da kake yi ba"


Girgiza kai yayi "so nake kice kin yafe min Maamu. Nayi miki alkawari wallahi bazan kara saba miki ba. Daga yanzu har karshen rayuwata akan rokon gafararki da kyautata miki zanyi"


Lumshe idanu tayi a hankali "na yafe maka Awaisu. Allah Ya cigaba da tsareka daga sharrin mutum da aljan. Allah Ya yafe mana baki daya"


Yana kuka yana dariya ya rinka cewa ameen. Ji yayi wani sakayau jikinsa kamar an zare masa wata kaya mai sukarsa a zuciya. Daga shi har ita babu wanda ya sake magana sai lokaci zuwa lokaci su kalli juna suyi murmushi. Shi Awaisu ma har jin ya rinka yi kamar ya zama sabon mutum.


Kusan awarsa daya a dakin kafin Dr. Yana ta sake dawowa tace ya fito a bar Maamu ta huta. Ba don yaso ba ya fita yana jaddada mata cewa a kofar dakin zai zauna tare da su Baaba.


Haka ya fito yana tunanin dole ya koma Abuja ya fara processing kai Maamu asibiti a Egypt ko Saudiyya ko kuma duk inda aka tabbatar masa akwai manyan likitici da kyakkyawar kulawa.


Gaban Baaba Hure ya fara zuwa ya durkusa ya gaisheta. Itama neman ta yafe masa yayi tana kuka tace ta yafe. Daga nan ya gaishe da su Anti Baraka da sauran 'yan uwa da suke zazzaune a wurin. Kallonsa suka rinka yi cike da tausayawa.


'Yan Harisu da na 'yan uwansa mata da suke wurin suma duka suka gaisheshi banda Rumana. Ya kula suna hada ido wata muguwar harara ta jefa masa tare da dauke kai.


Dan murmusawa yayi ya matsa kusa da inda take zaune akan katon kafet din da suka shimfida a wajen.


"Umm Ruman babu magana?"


Ga mamakin kowa tsaki taja mai sauti kuwa ta tashi ta bar wurin. Bata yi nisa ba kukan da take boye ya fashe har suna jiyota. Mamanta ce ta kirata cikin fada tace wace irin dabi'a ce wannan.


Mama uwargidan Harisu ta janyota jikinta tana goge mata ido itama hararar Awaisun take yi ta kada baki tace
"ai dai baza'a daki mutum a hanashi kuka ba ehee. Kiyi hakuri kinji Rumana"


Awaisu ji yayi jikinsa ya kara sanyi ya matsa gefe wurin yayansa yana kara fada masa abin da ake ciki dangane da ciwon Maamu.


Ranar sai wurin shadayan dare suke kama hanyar Fika. Ba don an matsa masa ba nan yaso kwana a kofar dakin Maamu. Ita kuwa wannan ganin kawai da tayi masa ya sanyaya mata rai hankalinta ya kwanta.


*****


Har shabiyun dare babu wayar Awaisu balle text. Gimbi ta kalli wayarta a karo na ba iyaka tayi jifa da ita tana fada ita kadai.


"Wallahi Awaisu baka isa ka wulakanta ni ba. Don ka tafi garinku shine bazaka kirani ba?"


Har wurin biyun dare ta kasa bacci tunani ya isheta. Bata kula da lokaci ba ta kira Ovi a tsohon daren nan. Cikin magagin bacci ta dauka tana tambayar me ya faru.


A hargitse Gimbi take tace "babu lafiya Ovi. Kince kada na kira Awaisu boka yace aiki zai lalace. To amma kinga shiru yaki kirana. Ina tsoron fa kada su juyar masa da kai game da ni komai ya lalace."


Ovi tayi siririn tsaki don ta ma manta da karyar da tayiwa Gimbi dazu sannan ta daure ta bata amsa
"Kamar yadda na fada miki gobe kawai ki bi bayansa . Gara kowa ma yasan cewa basu isa dashi ba naki ne ke kadai. Ki tafi ki taso shi a gaba ku dawo gida"


Cikin zakuwa Gimbi tace to.


A nasa bangaren ji yayi ko kadan baya so yana tunaninta don fargaba hakan yake saka masa. Sannan duk da bai fada mata ba yayi mamaki da har ta kai yanzu babu wayarta domin jin ina ya tafi. Wasu abubuwa game da zamansu da Maamu ya rinka tunawa abin yana daure masa kai. Zarginsa akan Gimbi ya kara karfi amma bazai dauki mataki ba sai ya tabbatar saboda wannan abu ba karami bane da za'a yanke hukunci da gaggawa. Da sassafe ko abinci bai tsaya ci ba yace asibiti zai tafi. Hakan yayiwa su Baaba dadi ya tafi shi kadai. Baaba tasa aka kira Antu Ummukulsum da ta kwana ranar akan cewa yana isowa ta tafi gida domin a bawa da da mahaifiya damar ganawa a nutse. Harisu da ta bawa sakon murmushi yayi yana jindadin hali irin na tasa mahaifiyar. Ba karamin jinjina mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login